Free chapter · Read without an account

Pg18

by Fatima Yushau adam · GIDAN YAN KARYA

Alhaji dan gaske,rike makogaransa yayi kamar wanda aka shake,idanunsa a warwaje kamar wanda aka saka masa igiyar rataya,dakyar ya samu ya daidaita numfashinsa har da sakin ajiyar zuciya,kana cikin hargagi kamar wani karamin yaro ya ce"kai wannan yaro kacika cikakken dan iska, idan ba tsananin iskanci ba ya za a yi ka na cin albarkacin ubanta sannan kana bi kana lalata masa 'ya? to ka tabbata yau sai ka yi kwanan cell dan ba zan taba bari a ci dunduniyar buzu ba ina ji ina gani, bayan Allah ya bani halin bi masa kadinsa"ya kare maganar da soma daddanna wayarsa,sai a lokacin Ummul ta dawo hayyacinta tare da saurin zamewa daga rumfar da gentle yayi mata,ba tare da ta kalli kwa daga cikinsu ba ta dauki hanya zata tafi,Alhaji dan gaske ne ya yi saurin tsayar da ita yana cewa"ina zaki je ikram ko har kinji sauki zaki koma aiki?"daga kasa kai kawai ta yi tana ci gaba da tafiya,shi kuma kamar wani zararre ya bita dan sauri babbar rigarsa sai hardeshi take yi,yana cewa"to ai shike nan zo ki shiga Mota mu tafi tunda nima gidan zan nufa"dan tsayawa ta yi sai kuma ta waiwaya ta kalli gentle da tun barinta wajen ya ke tsaye harɗe da hannayensa yana binta da wani irin shu'umin kallo, kafin zuwan maganar Alhaji dan gaske kallon nasa ya juya zuwa kallon gargadi, cikin sanyin jiki ta girgizawa Alhaji kai tana kokarin ci gaba da takunta,shan gabanta alhajin yayi yana cewa"saboda wancan dan iskan ya kalleki shine kika fasa yin abinda zuciyar ki take so na bina?anya kuwa ikram kema baki fara shiga farkon wannan tsinannan saurayin ba?"runtse ido Ummul ta yi tana jin tsanar mahadin sunanta da ya kasance sunan da Alhaji dan gaske ya fi yawan kiranta dashi,barantana kuma shi kansa me kiran sunan,ji ta yi kamar ta dalla masa mari amma sai ta dubi girmansa wanda yake daf da kasa,ta dauke kanta tana cije bakinta da tunanin hanyar da zata bi ta gyarawa mutumin nan zama,bude mata kofar motar da yayi ne ya dawo da ita hankalinta, kafin ta yi wani yunkuri wata adedeta da bata san daga ina ta bullo ba ta faka a gabanta, sai kuma gentle da ya kara so gaban me daidaitan yana yiwa Ummul din wani irin duban da ya ke kusan sumar da numfashinta,take wani sanyi ya ya fara ratsa kasusuwanta saboda yadda kallon yake ratsa dukkan gabbanta yana shigewa duk wata kofa da ke kai sako zuwa cikin jininta,da ido yayi mata alamun da ta shiga nefef din,aiko kamar wadda ake sarrafawa haka ta shige nafef din tana hadi hade jikinta waje daya irin na masu jin matukar sanyi,me adedeta din ya, kalla ya ce"ka kula,daga haka ya juya ya bar wajen, yana jin idanun Alhaji dan gaske akansa wanda ya ke tamkar gumki a wajen.

Sai da Alhaji dan gaske ya ji karar tafiyar dan sahun sannan ya motsa daga ƙamewar da yayi,sai dai bai daina bin gentle da kallon mamaki ba,tabbas Yaron nan idan ba Aljani ba ne to tabbas yana aiki da manyan matsafan duniya domin abin da ya gani da idonsa yafi karfin soyayyar Allah da Annabi sai dai idan kurwarta ya sude,ai ko shi da yake babba baya jin ikram tana bashi rabin girman da ya ga ta bawa wannan me facin takalmin,karar jiniyar motar yan sanda ce tasa shi sakin wani mugun murmushi yana shafa sankonsa bayan ya zame hular kansa,suna tsaida motar ya nuna musu gentle akan su tafi da shi sai ya neme su,daya daga cikinsu ne ya ce"ai alhaji dole sai munje office ka shigar da statement"a harzuke ya ce"ba zan je ba ina da abin yi, wannan da kuke gani ba shi da wani galihu ko matsayin samun me belinsa dan haka bani da lokacin da zanje ina shigar da bayanan laifinsa, ku shigar da laifin shirin yin fyade ga yarinyar da yake cin arzikin ubanta saboda a kofar gidansu ya ke gyaran takalmi,kuma a nan na kamashi yana shirin keta mata haddi sabida yaga safiya ce kuma babu yawan al umma a kewayen nasu,dan haka ku tafi zanzo ko daga baya ne "cikin girmamawa suka amsa tare da tasa keyar gentle da ko gezau bai yi ba,haka kan fuskarsa babu wani yanayi da zai nuna maka halin da yake ciki,suna barin wajen ummi ta leko kofar gidan, saboda lokacin da ta ji karar motar yan sanda ta shiga wanka ne,kafin ta fito kuma sun tafi,mamakin ganin Alhaji dam gaske ta yi a kofar gidan,bayan sun gaida ne ya shiga gaya mata karya zalla kamar dai yadda ya fadawa yan sanda,ga mamakinsa bai ga wata firgita ko tashin hankali a tare da Ummi ba sai tambayar da ta yi masa akan ina Ummul din take?"cikin mamakinta da bai sake shi ba ya ce"ai ta tafi tun dazu can gidan,dan kar a tayar muku da hankali me yasa na ce kawai ta tafi ba sai ta koma cikin gidan ba tunda Allah ya kiyaye",to Allah ya kara kiyaye gaba"abinda Ummi ta fada kenan ta kada kai ta koma cikin gidan.

Cikin sanyin jiki Alhaji dan gaske ya ja motarsa ya bar kofar gidan, zuciyarsa cike da sake sake akan yanayin da Ummi ta nuna masa,bangare daya kuma yana murmushin mugunta dan ya san wa ya sanya aikin ladaftar masa da gentle ,cikin sauki ya gefi tusntsu biyu da dutse ɗaya.

A vangaren Ummi kuwa ,babu abinda yafi damunta irin a wane halin gentle yake ciki,dan tsananin takaici ne ya hana ta tambayi alhajin wane devision din yasa a aka kai gentle,sam a zuciyarta bata yarda da maganarsa ba,hasalima da ita da tatsuniya bata banbanta su ba,tana zaune tsuru ta rasa abin yi banda kama wancan ta saki ta dauko wancan,har lokaci ya ja,daga karshe kiran Ali ta yi a waya ta sanar da shi abinda ke faruwa,tare da ce masa ya je ya duba ko wacce devision ya ga ni ko gentle din na can,da ya kawo mata shawarar cewa da wannan laluben a tambayi Alhajin mana,tsaki ta yi ta kashe wayar saboda Ummi tana da matukar zuciya akan laifin da aka yi shi cikin sani a ka kuma mai maita shi saboda mugunta,ta rasa me yaron nan yayiwa Alhaji dan gaske ya tsaneshi,dan ita fa bata ji haushin Ummul akan abin da ta yi masa ba tunda shima ba imani gareshi ba.

*****

To haka Ali ya bar aikinsa ya shiga neman gentle devision devision, amma har kusan karfe hudu bai samu wani labari ba,sai dai abinda bai sani ba, tun a devision din farko ya dace, sai dai su sun boye ne saboda umarnin hakan aka basu daga sama, wannan dalilin ne yasa Ali har ya gama bulayinsa bai samu inda aka kulle gentle ba,karshe dai da kansa yayiwa Alhaji dan gaske waya yana rokonsa da ya gaya masa ko abinci ne ya je ya kai masa,amma sai alhaji ya nuna masa cewa idan su basu san girman laifin da gentle yayi ba to shi ya sani dan haka dole ya karbi hukunci daidia da laifin da ua aikata saboda ya zama darasi ga masu son aikatawa,bai kara sauraren Ali ba ya kashe wayarsa,take Ali ma ya ji ya tsani Alhaji dan gaske, dan shima har ga Allah bai yadda da abinda alhajin ya ce gentle ya aikata ba, daɗin daɗawa da ya nuna musu cewa su basu san muhimmancin yar uwansu ba kenan har shi bare karan kaɗa miya ya fi su sanin darajar Ummul kenan,kwafa yayi kawai tare da shan alwashin ko dan wannan isa da ikon da Alhaji dan gaske ya nuna musu sai ya fito da gentle daga kurkukun masifar da aka saka shi.

******

Ummul da bata san abinda yake faruwa ba,tana can tana aikinta cikin kwanciyar hankali,duk motsi sai dai kaga fuskarta na murmushi,ko da zezee babu wanda ya ji kansu yau,dan ita ma zezeen da tata damuwar,tasan dai yau Abba ya ce mata dr zai zo amma tun safiyar take dako da saran ganinsa, amma babu shi babu alamunsa,ta kasa zama ta kasa tsayuwa, so take kawai yazo ta dan ya ci maganin da boka ya bata,duban agogon da yake buga karfe hudu na yamma ta yi, xama ta yi tana cewa na shiga uku ni zezee Allah dai yasa mutumin nan ba halin zai yi min ba"ta fada kamar ta rusa kuka, yayin da ta shiga neman wayar abbanta dan ta san a matsayin da take,ya na dagawa ta fashe masa da kuka,ya Salam "Alhaji dan gaske ya fada tare da cewa"ki shiru yanzu zan kira babansa nasan ko da bai yi niyar zuwa ba dole zaizo idan ubansa ya sa baki"kashe wayar yayi ya tafi lalubo ta Alhaji Ahmed dan itopia,ringin daya kuwa ya daga, bayan gaisuwa,Alhaji dan gaske ya ce"yallabai dama so nake na ji dan nawa zai zo dan mu shirya tarbarsa"dariyar dattijontaka Alhaji Ahmed yayi sannan ya ce"haba dai sai kace wani bako har sai an yi masa wata tarba"ai girmansa ne yallabai"Abba ya fada cikin kara ƙanƙan da murya,"to shike nan yana nan tafe kan hanya ya sanar da ni akwai wani dan uzuri da ya sameshi amma yanzu zai karaso"to to madalla yallaɓai a huta Lafiya", yana ajiye wayar ya maida kiransa kan zezee inda yayi mata albishir din cewa dr yana kan hanyar zuwa wajen ta,wani uban tsalle ta yi tare da fadawa toile aka shiga dirzar fata kamar zata sauya fatar.

Karfe biyar daidai ta ji shigowar mota, da gudu ta leka ta window inda ta gansa shi kadai ba tare da kowa ba,yana zaune ta cikin motar ya zuro kafarsa duka biyun yana waya,zuba masa ido ta yi tana kallon tsantsan baiwar kyau da kwarjini, Masha Allah kamar shi yayi kansa kuma sam hakan baya shi jin kamar yafi kowa,sai dai kuma ai yana dizga yammata kamar ba zai taba aure ba,sauri ta yi ta ar wajen takara fesa turare kana ta fice daga dakin,kai tsaye kitchen ta nufa , anan ta samu Ummul ta gama hada komai da aka sa ta yi, kaiwa kawai za tayi,dubanta zezee ta yi fuska babu yabo ba fallasa ta ce "je ki kara kimtsa wajen sannan kizo ki dauki kayan abincin ki kai"kallonta Ummul ta yi tare da cewa "ai tun dazu na gyara falon kamar yadda momy ta sani"hade fuska zeze ta yi tana watsa mata kallo kafin cikin tsawa ta ce"ba zaki yi abinda na sa ki ba ke nan ko?"cikin sauri Ummul ta fice ba tare da ta bata amsa ba,jikinta ne ya bata cewa akwai abinda zezee take shiryawa dan banza bata kawo ta kitchen,Dan haka sai ta fasa tafiya ta koma daga jikin window kitchen din ta na leka zezee, Ita kuwa zezee tana tabbatar da tafiyar Ummul ta yi saurin ciro kullin abu daga kugunta,ta bude lafiyayyar soyayyar shinkafar da ta ji kayan dadi tana ta zabga kanshin meenat cuisin spicess and corry,sai da ta barbade abincin nan tas sannan ta juya tare da maida maganin inda ta dauko shi,ta fice daga kitchen din ba tare da ta ankara da Ummul dake labe jikin window ba.

Ummul kuwa cikin sanda ta koma kitchen din ta bude abincin ta dauko bakar leda ta juye , sannan ta wanke fulas din da toka, daga nan ta sake zuba wani abincin ta zuba su duka a cikin basket tabar kitchen din, tana ta mamakin rashin imanin zezee dan ita a zatonta ma guba ta zuba masa dan ya ci ya mutu saboda haushin abinda yake mata,da wannan mamakin ta karasa falon tare da yin sallama cikin siririyar muryarta,a nutse ya amsa ba tare da ya dago idonsa daga kan laptop dinsa da yake ta aikin shafata ba,cikin maganar zucin da bata san ta fito fili ba,ta ce "um Ni da na sani ma ban canja abincin ba na kawo masa a haka, tunda gani yake har hanji wata kila zai gane an saka magani aciki"wani irin magani aka saka?"ta tsinkayi dakakkiyar Muryar sa a tsakiyar kunnenta,tuni ta ware idonta akansa, sai dai tunani ta shiga yi anya kuwa shi yayi maganar? ko dai jin kunne ta yi ko kuma aljanunsa ne sukayi maganar,tunda ta ga alamu yana dasu bishiyar kuka guda,saboda bata ga wata alama da yake nuna cewa shi ne yayi maganar ba,hakan yasa ta share tana jan ayatul kursiyu da suratul jin,tana cewa ko da aljanun ne ma ni Ummul na fi karfinsu tunda ina da ayar Allah ina da Annabi Muhammad s.a.w"hakan ya sa ta ci gaba da aikin jera abincin,daidai nan zezee ta shigo tana wani takun kasaita kamar wata dawisu ansha kyau kamar za a canja halitta,zama ta yi tare da ce masa "baby sannu da zuwa da har na yi zaton ba za ka zo ba?"idan kujerar da ke wajen ta tanka to Dr ma ya tanka,shuru ta yi tana jin takaicin dizgata da yake gaban yar aikinta,sai da ya fidda rai da samun amsarsa,kana ta ji ya ce"Barka fatan kina lafiya"?dariya ce ta kusa kufcewa Ummul da take daf da fita daga falon,ita kuwa zezee dadi ne ya rufe ta musamman da taga ya ajiye laptop din ya sauko kasa tare da janyo plet din da Ummul ta shake masa da abinci wanda kana gani kasan har da zubin mugunta,kallon abincin yayi sannan ya saki murmushi A can kasan zuciyarsa wanda babu wanda yasan yayi shi daga shi sai zuciyarsa,sai da ya wanke hannunsa sannan ya saka hannu a abincin tare da yin Bismillah ya fara ci cikin nutsuwa.

Murna da farin ciki wajen zezee kuwa kamar an ce mata bukatarta ta biya,to ko ba a fada ba dama ta yi a manna da bokan nata akan duk abinda ya ce,sosai ya ci abincin wanda hakan ya bawa zezee mamaki,wato shi dai sam baya yi wa cikinsa mugunta, gashi gana daya Al'adar sa ta cin abinci irin ta gargajiya ce kamar ba dan da ya tashi cikin arziki ba,kamar ba dan da yayi rayuwa a kasashen waje ba,komai na sa sai ya kamanta shi da addini da kuma sunna ta ma aiki Sallallahu alaihi Wasallama,muryarsa ce ta katse mata tunani, sai a lokacin ta lura ashe har ya mike ,kai ka ce dama abincin kawai ya zo ci,dan marairaice fuska ta yi tana cewa"haba baby wai tafiya zaka yi?"gyada mata kai kawai yayi ba tare da ya dakata da tafiyar da yake yi ba, sannan ya ce "ina da babban uzurin da zan yi wanda a cikinsa kika samu lokacin ganina"shiru ta yi ba dan ra ayun kanta ko dan amincewa da abinda ya ce ba,sai dan bin umarnin boka da ya ce daga nan har zuwa maganin ya fara ci kar ta sake ta yi masa musu da gaddama idan ba haka ba abin zai lalace, hakan yasa ta bishi dan yi masa rakiya.

A bakin gate suka hango Ummul tana kuka kamar ranta zai fita kai kace mutuwa aka yi mata,dauke kai zeezee ta yi, amma ga mamakinta sai taga Dr Bilal ya sauya hanyarsa ta isa ga motar sa ya juya zuwa gate inda baffa yake ta yiwa Ummul fada akan ta yi shiru kar ta tara masa jama'a"Baba me yake faruwa ne?"Dr ya tambayi baffa da muryarsa me kwarjini kuma cike da ban girma ga baffan,baffa ya ce"wallahi yanzu muna tare da Ummul mahaifiyarta ta kira Ni take sanar dani cewa yaron da yake zama a kofar gidana yana gyaran takalmi shine me nan gidan yasa aka kulle shi akan lefin ya kama shi yana kokarin ketawa Ummul din mutunci,kuma an rasa inda aka kaisa shine take kuka"cikin kuka Ummul ta ce"wallahi baffa karya ne ba haka abin ya faru ba sharri kawai aka yi masa"cikin fusata zezee ta ce"uban nawa ne zai wa talaka matsiyaci kamar me gyaran takalmi sharri?"Ummul bata kulata ba saboda yanzu Bata da lokacin tanka mata,dan tsaf zata huce haushin ubanta akanta.

Idanunsa da suke sanye cikin farin glashi ya zuba mata na dan wasu sakanni,kafin ya maida sunansa kan baffa ya ce"amma kaima kana ganin abinda aka fada din ba haka ba ne?"shuru baffa yayi saboda yadda zezee ta zuba masa ido tana jiran jin shima zai ƙaryata me bashi abinci kamar mara kunyar yarsa,ganin baffan yayi shiru ne yasa Dr cewa"ina ganin tunda har babban mutum kamar Alhaji dan gaske ya zo da magana irin wannan dole a tsaya a duba a yi kuma bincike dan tabbatar da laifinsa,idan har ya aikata hakan sai a tura shi zuwa kotu"wani uban tsalle Ummul ta daka tare da zubewa tana burgima a wajen, cikin kuka take cewa "Wallahi babu wanda zai kai gentle kotu kuma ai ni aka ce ya yiwa laifin dan haka dole nice shaidarsa, kuma wallahi idan ba a fito da shi ba duk abinda ya faru da mutum shi ya janyowa kansa, kawai dan kunga kuna da kudi shi ke nan sai ku sanya talaka bawan Allah a gaba kuna gallaza masa, wallahi Allah ya isansa ba zai ya ce ba har kabarinku yana balbala da wut......bugun da baffa ya kai mata da kafa ne uasa ta yin shuru da maganar sai dai ba ta yi shiru da kukan ba,ta wani gefen kuwa harara kwando kwando babu irin wadda bata aunawa Dr ba, dan kawai ya ce a tsaya a yi bincike idan ya aikata sai a kaishi kotu.

Sandar gadinsa baffa ya dauko yayo kan Ummul da ita, tana ganinsa kuwa ta mike da gudu ta yi bayan Dr tare da rirrike rigarsa,da sauri zezee ta matsa kusa da su tare da fincike hannun Ummul din daga jikin rigar Dr Bilal tana cewa"dalla matsa daga jikin mijina wa ya sani ma ko da yardarki yake taba mutuncin naki shi yasa kika yi ruwa da tsaki akan sai an sake shi,tunda dama ai nasha kama ki da wasu mazan suna lalubeki har da me wan.......tassssss,saukar kakkarfan marin da taji akan fuskarta yasa ta hadiye ragowar zancenta, tana bin hasken wutar da suke yi mata shawagi a cikin idanunta da kallo.......

Tofa yanzu ainihin wasan zai fara"

A cikin mutum ukunnan waye ya zabgawa zezee mari ne?"

Dr Bilal ko Ummul ko baffa,kai ko ma wani ne daga can gefe, muje dai zuwa muji yadda wannan rikici zai kaya

Shin wane hali gentle yake ciki ne

Waye genlt ne?kuma waye Dr Bilal?😂😂😂😂😂😂😂amsar ku na wajen

Hajja zahra me capacity.

Ku biyo ni dan ganin yadda zata kaya

Team gentle a yafe Ni, nasan yau na taro Mach har da August 😂😂😂😂😂😂

Team zezeee ina neman yafiya kar na ga motar police a kofar gidana😂😂😂😂

ZAHRA......✍️

***

💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol