Free chapter · Read without an account
Pg20
Shi kansa gentle kasa rike kansa yayi har sai da yayiwa Ummul kyakkyawar tarba,ta hanyar zagaye ta da hannunsa biyu,tare da dan bubbuga bayanta na alamun rarrashi saboda kukan da take ta yi, dansanda kuwa da aka ture har ya fadi tashi yayi yana muzurai a ransa yana cewa"wallahi ba ki ture banza ba dan sai na rama akan kwarton naki,Abba kuwa mikewa yayi ba tare da wani jinkiri ba ya fizgo Ummul daga jikin gentle, ji yake kamar zai dauke ta da mari,ita ma din da sauri ta fizge hannunta daga nasa,tana jin kamar garwashin wuta ya dora Mata,dpo kuwa jinjina kai yayi tare da dan bugun teburin gabansa yana cewa "baku san a inda kuke ba ne?wato a nan din ma hali zaku nuna mana?to lallai wannan yaron ba ka daku ba dole sai ka samu daidaituwar hankali sannan zaka bar wajen nan"alhaji dan gaske ya karbe da cewa "abinda ya kamata ke nan dpo"Ummul kuwa wani irin kallo ta watsa masa kafin ta bude bakinta"ta ce"wallahi sai dai ku mai damu tare Amma muddin ina wajen nan babu wanda ya isa maida gentle cikin cell tunda bai yi muku komai ba,kuma wallahi zaku ga abinda zai faru da ku,sai na fadawa manyan ku abinda kuke aikatawa tsinannu marasa imani masu karbar cin hanci"wata zabura dpo yayi yana cewa"kaji min yarinya ni zaki zaga har da yi min barazana?to wallahi kema sai na jefa ki a cell ko na kwana ɗaya ne"yatsina fuska ta yi tare da cewa"Allah ko to da kake wannan maganar kasan Ni din ko wacece?"ban sani ba amma ko ke wacece yau sai kin shiga cell"dakewa ta yi a ranta tana cewa"ko da Alhaji a wajen nan sai na yi halin dan na fahimci ta hanyar yinta Allah zai taimake mu a wajen wadan nan mugayen,
Alhaji dan gaske kuwa dariya yayi yana mamakin kuruciya irinta Ummul,to banda abin kuruciya a gabansa shi da yasan ko ita wacece zata nemi rainawa mutane hankali amma dai ba ri ya zuba ido yaga iya gudun ruwanta.
Gentle kuwa tun bayan janye Ummul da Alhaji dan gaske yayi daga gareshi,ya sunkuyar da kansa kasa ba um ba Umm to a wajen da Yakamata ma yayi magana bai yi ba bare anan da sai an bashi umarni,harara Ummul ta watsawa dpo din tana cewa "yanzu ba jimawa za ka yi bayani da yaren da kowa zai fahimta"dariya yayi yana jin maganar Ummul kamar wata tatsuniya, sai dai kuma kafin ya rufe haloramsa daga dariyar rainin hankalin da yake yi,wani kurtun dan sanda ya shigo office din cikin sauri da rawar jiki ya mikawa Ummul wayar da ke hannunsa,kamar ta yi tana boye mamakinta dan kar dpo ya ganota,shi kuwa dpo masifa ya bude baki zai yiwa wannan dan sandan saboda shigowar da yayi kai tsaye ba tare da an bashi umarni ba,tsayawa yayi yana kallon Ummul da ta sanya wayar a amsa kuwa saboda hakan dan sandan ya fada bayan ya bata wayar,Muryar babban mutum suka ji yana magana kamar haka"ranki ya dade mun ji duk abinda yake faruwa daga nan, dan haka a halin yanzu umarnin ki kawai muke jira, shin kina bukatar a maida wannan mutumin zuwa cikin cell a maimakon yaron da yasa aka kama ne?"shiru Ummul ta yi zuciyarsa cike da tunanin akan wannan al'amari da bata san daga ina yake ba,to amma sai ta yi tunanin ko dai yaya mufty da ya Ali ne suka hada wasan tunda dama sun saba yi hakan, wannan tunanin da ta yi ne yasa ta sakin Dan karamin murmushi kafin ta ce"kawai so nake a lissafa duk yan sandan da suke da hannu cikin kama gentle duk a koresu a kawo wadanda za su iya kamanta gaskiya akan aikinsu,shi kuma wannan tsohon zai ci darajar baffa na shi yasa zan rabu da shi,dan nasan idan aka kulle shi baffana ba zai ji dadi ba dan haka a rabu dashi"shike nan ranki ya dade yanzu zaki iya tafiya da shi,a waje akwai motar da zata maida ku gida"daga haka ba a jira cewarta ba aka kashe wayar,bin wayar da ido ta yi kafin ta saki murmushin farin ciki a ranta tana cewa"ko ba komai yan uwana sun fitar da ni, wata karyar ma ashe tana da rana".
Dariyar dpo da Alhaji dan gaske ne ya dawo da ita daga tunanin da ta tafi,dop har da kwanciya saman teburinsa yana buga hannunsa ajikin teburin, Alhaji dan gaske kuwa kallon zaki zo hannu yake yiwa Ummul,tare da mamakin karfin halinta,kallon dpo Abba yayi yana cewa"ka bar dariyar nan ka sa a maida min wannan yaron cell,ita kuma wannan kayi mata uzuri saboda akwai yarinya a tare da ita, sannan kuma tana da matsayin da ba zan iya daukar hukunci a kanta ba,kar ka damu da wannan shirin nata, kawai ka ɗauke shi tamkar Film ka kalla ko kuma littafin Hausa ko tatsuniyar gizo da koki".
Dagowa dpo yayi har yanzu bai bar dariya ba,yana cewa"wallahi Alhaji tun da nake ban taba ganin yarinya me abin dariya ba irin wannan,ga rashin tsoro duk da nasan cewa biye shi take a cikin ranta,tsananin karfin hali ne kawai,gashi ta iya tsara drammer duba dai yadda ta yi actin kamar wata actress"duban Ummul yayi da murnushi akan fuskar sa yana cewa ,kin ci darajar Alhaji amma yau da kin san da wa ye kike, amma zan nuna miki asalina a kan shi wancan maras kunyar da kike yin komai akansa,wai ma meye tsakaninku da shi ne bayan wancan dangantakar dake tsakaninku?"cikin muryarsa da ke fita a nutse a can kuma kasan makoshi da wani irin sauti na daban ya ce"alaƙa ta musamman irin ta in babu ke babu Ni,ma ana rayuwata"gaba daya binsa suka yi da ido har da Ummul din da take masa kallon tsakar ido,shi kuwa idanunsa a rufe suke kansa a jingine jikin bango hannunsa rungume a kirjinsa, ba cin suna kallonsa babu ta yadda za ayi su ce shi yayi wannan dogon maganar,dpo na shirin yin magana wayarsa ta yi kara hakan ya sa shi fasa fadar abinda yake shirin fada,gani kawai su ka yi ya mike tsaye jikinsa na rawa goshinsa na hada wani irin gumi a lokaci daya duk karfin fanka da a c dake office din,fifita ya shiga yi da hularsa yana haɗawa da share gumi,tambayarsa Alhaji dan gaske ya shiga yi, amma kafin ya ce wani abu an turo kofar office din an shigo,wani kamilallan mutum ne sanye da kayan yan sanda wanda yake dauke da tambarin sunansa da matsayinsa na dpo,sai kuma wasu dake bayansa suma sanye cikin kayan aiki,suna shigowa ba tare da bata lokaci ba suka kama karbe duk wani abu na aiki da yake tare da wancan dpo,sai da suka su take shi tas sannan sabon dpo ya ce da su"kuke ku hada su da taguwar yaran nasa kusa su a cell"daga haka yaran suka tasa keyarsa,suna ga da fita ya juyo ya kalli Ummul yana cewa"dan Allah ke wacece da har matsayinki zai iya sawa a Korea Ni daga aiki har da tagomashin lalata min takardu an ya ke din kuwa mutum ce"? Ita kanta Ummul da yake yiwa wannan tambayar bata san me zata ce masa ba domin abin ya fi karfin kanta,dan wannan lamarin yafi ƙarfin shirin su yaya mufty, tabbas wannan shirin gaske ne,to ta yaya hakan ta kasance?"bata da me bata amsa dan haka sai kawai ta yi karfin shararawa dpo harara tana cewa "kar ka damu dpo wannan al marin daga Allah yake,sai dai fatan hakan ya zame muku darasi da ku da masu irin halinku"tana rufe baki suka tasa keyarsa sai cell da shi da gaba dayan yaransa da bakinsu ya ke a haɗe.
Alhaji dan gaske kuwa tsananin mamaki ya sa ya kasa koda motsi, bin bakunansu da kallo kawai yake yi,ga kuma radadin maganar gentle da ta zamar masa kamar garwashi a tafin hannu,dubansa sabon dpo yayi tare da cewa malam zaka iya tafiya idan kuma kaima kana bukatar shiga cell din ne to sai ka fada,dan dai har yanzu muna kan umarnin Madam ne"Madam kuma Ummul ta maimaita a fili tare da saurin kallon gentle da har yanzu yake a yadda yake,harara ta banka masa, a ranta tana cewa dube shi dan Allah ko gajiya ba yayi kullum baki a ɓame ko tsoron bakinsa yayi wari baya yi,dpo ne ya katseta da cewa "ranki shi dade zaku iya tafiya"gentle ne ya fara fita ita kuma tabi bayansa zuciyarta damfare da tambayoyin da ta rasa wanda zata yiwa su,suna shiga motar ta kalle sa tana so ko da shi su dan tattauna maganar amma ina bata ga fuska ba,hakan yasa take ta mutus-mutsu ta neman hanyar da zata yi masa magana,dan matsowa ta yi kusa dashi tare da leka fuskarsa da yayi kamar yana bacci dan tunda suka shiga motar idanunsa a rufe suke bakinsa labbansa ne kawai suke motsawa suna dan fidda sauti kadan,da alama dai ambatan Allah yake yi ko kuma salatin annabin Rahma,(wanda ake so ko da yaushe mutum ya lazimci yinsu wato tasbiyi da hailala da salatin Annabi suna kara nutsuwa ga mutum tare da tsananin kwarjini, ga saurin cika mizani, Allah kasa mu dace duniya da lahira Amin,)"na ce ba" ta fada cikin 'yan kame kame,bude idanunsa yayi akanta wanda hakan sai da ya sanya kirjinta ya bada wani sautin faduwa tare da saurin kawar da kanta daga gare sa"uhmm ta ji ya fada tana jin idanunsa akanta, cikin in ina ta ci gaba da cewa"um dama dama cewa nayi ko kasan wani abu game da wannan al'amarin da ya faru?"shiru bai yanka mata ba,hakan yasa ta juyo a dan cike tana cewa "ko kadan fa dan Allah dan Allah, wallahi neman zarar dani al'amarin yake,ko kai baka mamaki baka son sanin wani abu ne?"ware idanunsa yayi akanta tare da cewa"karya mana shi na sani kin yi daga haka ban san kome ba?"dum ta yi cike da nazarin maganarsa,sai kawai ta samu kanta da zuba masa ido zuciyarta na son saka mata kokwanto akansa,"wai kai waye ne"?bata san sanda bakinta ya furta hakan ba,"tun kafin ki fara sona ya kamata ki min wannan tambayar,me yasa sai yanzu?"ya fada yana tashi sosai da tsareta da idon da ta fara tunanin inda ta san me irinsu,kawar da kanta ta yi tana tura karamin bakinta, kafin ta ce"waye ya fada sonka nake ni ba sonka nake ba tausayinka nake"really "ta ji ya ambata daf da kunnenta wanda take dumin numfashinsa ya bugi fatar kunnenta,dan zabura ta yi saboda abinda hakan ya haifar mata,wani dan makalallen murnushin da ya tsaya iya labba yayi kafin ya kuma cewa".
"Ni ba kowa ba ne face almajirin da yake neman na cin abinci kullum"daga haka ya maida kansa ya kwantar tare da rufe idanunsa,samun kanta ta yi da zuba masa ido, duk da cewa bata ganin komai sai bakar fuskarsa da har yanzu bata isa tantance ainahin kanninsa a haka ba,idan kika cika kallo na zaki iya jin kin daina sona saboda muni da talauci"samun kanta ta yi da kai masa bugu a kan kirjinsa sai da ta yi mai isarta sannan ta hakura ta ci gaba da gunguni a saman fatar bakinta,shi kuwa gentle ko gezau bai yi ba shi yasa ta gaji dan kanta ta rabu dashi,a haka suka karaso gida,dubansa ta yi kafin ta fita ana cewa"ka je gida ka yi wanka sai ka dawo nan kaci abinci nasan basu baka abinci ba tun jiya ko?"a maimakon ya bata amsa sai bude idonsa yayi akanta tare da jefa mata tambayar da ta zo mata a bazata,"maki so na ko?"tura karamin bakinta ta yi kawai ta fice daga motar, kanta ta leka wajen driver ta ce dashi "to kai bawan Allah mun gode duk da cewa bamu san daga duniyar da Allah ya turoki ba amma dai mun godewa Allah mun kuma gode muku, ka karasa ladanka ka kaisa gidansu dan Allah kaji"driver ya amsa da in Sha Allahu ranki shi dade"Allah ya biya bakinka"ta fada tana shigewa gidansu,shi kuma driver yaja mota su kayi gaba.
Dpo kuwa ganin Abba bashi da niyar tashi yasa shi dukan teburin gabansa yana cewa "Alhaji ka tashi ka tafi tun ina ganin girmanka"ajiyar zuciya alaihi dan gaske yayi tare da maida dubansa kan dpo yana cewa"dan Allah yallabai tambaya daya zan yi maka ka temaka ka bani amsa tun kafin jinina ya hau"ina jinka dpo ya fada tana yin wasu rubuce rubuce akan takardun gabansa,numfashi Abba yaja , sannan ya ce"dan Allah dpo daga ina aka turoka waye yayi duk wannan abubuwan al ajabin da suka faru?"wannan ba huruminka ba ne dan haka ka tashi ka tafi abu daya zan gaya maka shine ka sani cewa Allah baya bacci a kuma duk lokacin da ya so shi me taimakon bawansa ne"daga haka dpo bai karawa bawa Abba damar yin wata magana ba ya tashi ya fice daga office din ya bar Abba da ya shiga tunani akan haɗa al'amarin nan da Dr Bilal,lallai Dr Bilal ya san wani abu akan wannan al'amarin dan Ummul bata da wani me tsaya mata idan aka dauke shi, shi kuma bashi ba ne,dama tuni ya gane take taken Dr Bilal din gashi kuwa ta tabbata,tashi yayi saurin fita a ransa yana cewa "ai ban ga ta zama ba tashin hankali ya sameni surukina da son abinda nake son mallaka ".
*******
Duk a gida ta samu yayunnata,rungume Ummu ta yi tana cewa"ummi na yi kewarki jiya ban kwanta a kusa da ke ba"yaya mufty ya ce "mu da ba a yi kewarmu ba sai mu mutu"sakin ummi ta yi ta zo gabansu ta rike hannayensu shida ya Ali tana cewa, "yaya na yi kewarku musamman wajen zuba karya duk da cewa yau kun fanshe ta kwana biyu da ba a taba ba"kallon rashin fahimta duk suka yi mata,yayin da Ummu ta sako mata maganar gentle da take cin ranta, Ummul ta ce"to ai yanzu tare muke dashi ya fito kuma ai su yaya ne su kayi kome amma naga suna kallona irin haka kamar basu san komai ba"ke banga ne ba ke kike nufi?"yaya ki yayi mata tambayar yana kallon mufty da yake tunanin ko shine tayi wani abu ba tare da sun sani ba,amma sai shima mufty din ya shiga yiwa alin kallon ko shi din ne,ganin haka yasa Ummul ta warware musu abinda ya faru tun daga farko har karshe,Ali da yake tsaye take ya jishi a zaune, Ummi kuwa hannunta shiga tafawa, kafin ta ɗora da cewa, Ni yar nan yau kuma karyar ta ku rana ta yi muku kenan?"amma dai wannan abu da ban mamaki yake"Ummul da ta kuma shiga cikin tunani ta yi shiru tana dogon nazari wai ko zata iya tuna wani abu da yasa hakan ta faru,amma ta kasa tuna komai,yaya mufty ne da yaga nazarinsa ya ce"kai ina tunanin sulaiman ne"Ali ya girgiza kai tare da cewa "Wallahi ba sulaiman ba ne,kai har ka manta cewa shima sulaiman din ya tsani gentle kamar yadda Alhaji ya tsaneshi,dan haka Ni nasan ba ta yadda za ayi ya fitar da shi"Ummi ta ce"haka ne Ali ba sulaiman ba ne,kar ku sawa kanku tunani har ya haifar muku da wata matsalar kawai ku bar abin a yadda Ubangiji ya shiryoshi dan kawai ya kubutar da bawansa"wannan kalaman na mahaifiya sune suka sanyawa Ummul nutsuwa har ta tashi ta shiga sabgiginta, tana yi tana lewa kofar guda dan ganin ko gentle ya dawo,har sai da Ummi ta yi mata magana, akan ta barsa yanzu haka yana dan hutawa ne dama ai ba zai yiwu a ce daga fitowar sa ya dawo aiki ba, Ummul dai hakura ta yi ba wai dan ranta ya so hakan ba.
*****
A can bangaren zezee kuwa yau gaba daya yini ta yi a daki, ko kofar dakin ta kasa fitowa ta yi, babu abinda take sai sake saken yadda za tayi ta rama cin mutuncin da aka yi mata akan Ummul da ta zama ita ce Ummul a ba isin komai,wayarta ta janyo ta dokawa bely kira,belyn na dagawa ta fashe mata da kuka,ba ta dakatar da ita ba,har sai da ta yi me isar ta Sannan ya yi shiru tare da fara korawa Belyn bayanin abinda ya faru,wata uwar ashar belyn ta yi kafin ta ce"kar ki damu kawata ina da yadda za mu yi da ita,zamu san yadda za mu yi mu janyota cikinmu mu lalata rayuwarta ta yadda ko wanda bai da tarbiyya ba zai so zama da ita matsayin mata ba,a wannan karon kukanki ya kare zamu ci nasara,dan zamu ɓullo mata ta inda bata taɓa zato ba,ba ita ta yarda da karya ba, to da halinta na karyar zamu lalata rayuwarsu daga ita har yan gidansu ba zasu kara alfahari da kasancewarsu a GIDAN YAN KARYA ba"sai a lokacin zezee ta samu natsuwa saboda tasan muddin rayuwar Ummul ta lalace babu ita babu shiga rayuwar Dr Bilal,ta shi ta yi ta yi wa ka ta kimtsa dan zuwa gidan bely din.
*****
Alhaji dan gaske yana fita daga polistation kai tsaye, wajen uban gidansa Alhaji Ahmed dan itopia ya nufa, dan su karkare maganar auren ƴaƴansu,tarba ta arziki ya samu kamar yadda aka saba yi masa,daga bisani Alhaji Ahmed ya zo ya zauna suka fara magana,inda suka karkare magana akan tsayar da ranar daurin aure,sai dai baban Dr Bilal ya sanar dashi ya jira karasowar Dr Bilal din dan jin ta bakinsa akan tsayar da lokacin ,dan basu sani ba ko yana da nasa lokaci na musamman da yake son a yi auren,tunda dama su bikinsu babu bidia saboda albarkar auren suke bukata kawai,gumi Alhaji dan gaske ya dan share tare da kakaro murmushin karfin hali, ya ce"to badamuwa bari mu jira shin Allah ya kawo shi lafiya"ya fada a ransa yana jin fargaban zuwan Dr Bilal din saboda yana tsoron sabon al'amarin da zai zo musu dashi.....
Na gode sosai da addu'o in ku gareni,kuma alhamdulillah jiki yayi sauki sai dai fatan Ubangiji ya kare mu da lafiya me amfani, Allah ya bar zumunci da kauna ,gidan yan karya fans ko na ce gidan yarbawa fans dan ban san wanne kuka fi so ba😂😂😂hausawa dai sun ce da tsohuwar zuma ake magani, nasan ba zaku manta da zahla uwar gidan Ab ba?"
Once again appreciate
🙏🙏🙏🙏🙏🙏🙏
Zahra💕
By
FATIMA Y ADAM......
Littattafan marubuciyar.
KUDIRAR ALLAH
KADDARATA SANADIN HASKE
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
ƳAR GIDAN YARBAWA
MATAR ƊAN BIRNI
And
GIDAN ƳAN ƘARYA....