Free chapter · Read without an account

Pg24

by Fatima Yushau adam · GIDAN YAN KARYA

Da karfi ta sa hannu ta turesa amma ko gezau bai yi ba, sai ma matsuguni da ya kara yi mata a kan faffadan kirjinsa,tare da kokarin saita kansa ta hanyar shigar da fuskarsa cikin wuyanta yana shaƙar kamshinta,ganin bata da mafita yasa ta ci gaba da kuka tare da kai masa duka a duk inda ta samu,amma maimakon hakan yayi mata amfani sai ma kara shige mata da yayi,yayin da ya dora bakinsa a kunnenta ya fara magana a hankali wadda take fita da wani dan sanyi sanyi da dumin da yake dukan fatar kunnennata yana ratsata da shigewa duk wata gaɓa da ke aiki a sassan jikinta,"babu ruwana yau abinda kika shuka shi zaki girba dan haka ki fada musu ke kanwar me wajenne,zasu rabu rabu dake,ko karyar ce yau ta kare?"ya karasa maganar tana hade fuskarsa da tata,tura bakinta ta yi tana taɓe shi zata ci gaba da kukanta,sai dai kafin hakan ta faru ta ji wani irin sanyi me hade da kamshin mint a bakinta sanadiyar harshensa da ya zura cikin bakin nata,wanda hakan yasa ta hadiye abinda zata fada tare da miyansa,ware manyan idanunta ta yi lokacin da ta ji ya fara juya harshensa me taushi da kamshi a cikin nata bakin,dukan bayansa ta shiga yi tunda ya rufe bakin maganar,amma gentle dai da alama yayi nisa,dan bai rabu da ita ba har sai da ya ji ana dan knocking wani dan karfe dake jikin labulen da aka zagaye wajen da shi,a hankali ya zame bakinsa daga nata yana mata wani irin kallon kasa kasa,idanunsa sun yi wani irin lumshewa kamar wanda yasha kayan maye.

Ummul kuwa samun damar sauka daga jikinsa ta yi tana dan kukanta kasa kasa,cikin kukan take cewa"Allah shi zai saka min abinda ka yi min,kuma wallahi Ummi da vaffa ba zasu kuma yarda da kai ba,dan sai na fada musu abinda ka yi min, ana kallon ka sumi sumi ashe ashe abun ba a fuska yake ba,ba a gane me iskanci a fuska sai.....kan ta kai karshen maganar ya fizgo hannunta gaba daya ta fada kirjinsa,a lokaci daya kuma yana bawa me shigowar damar shigowa,duk mutsu-mutsun da take yi dan kufcewa daga rikon da yayi mata amma hakan ya gagara,hakan yasa ta kwantar da kanta a kirjinsa tana sakin ajiyar zuciyar gajiyar da kanta da tayi,matar taji tana cewa "ko suna bukatar wani abu ne bayan wanda suka yi ci?"ba tare da ya kalli matar ba ya ce"wait bari a tambayi kanwar me wajen?"daga haka ya dawo da dubansa kan Ummul da ta yi kamar ta yi bacci dan har runtse idon ta ke kuma yi da karfi,a hankali ya kai yatsansa guda ya taba fatar idanunta da take ta ɗan farfar, hakan yasa ta bude idon da sauri tana girgiza kanta kamar zata kuma fashewa da wani kukan,"duk da yanayin da ta yi hakan baisa ya fasa tambayar ta ba,"hy kina bukatar wani abu ne Ummul ikram Ahmad Dan itopia"?aiko Ikram ji ta yi kamar ta kwada masa mari,shi kuwa idanunsa yana kanta yake yiwa matar magana da cewa"kije kawai idan da wani abu letter"juyawa ta yi ta fita,tana fita Ummul ta zame daga jikinsa tare da gyara dankwalinta da ya zame mata ta ɗora mayafinta tare da zura takalmanta,hanya ta kama ta fice ba tare da ko waiwayensa tayi ba,a hankali ya kai hannunsa ya shafa bakar gyararriyar kasumbarsa da ta hade da baƙin fatarsa, kafin ya yunkura ya tashi ya bi bayanta.

Cikin sanda take saukowa daga matakalar saman da suke, kai daga karshe ma cire takalman ta yi saboda yana dan bada sauti, tana gama saukowa ta yi wuf zata fice,amma sai taji wata ma aikaciyar wajen tana cewa"hy baby where are you going and are you payment d order?"take Ummul ta yi wani wuri wuri da ita yayin da cikinta ya bada wani kulluu, sai kuma ta shiga yan kalle kalle ganin wajen babu kananun yara yan kuci ku bani hakan yasa ta yi saurin mazewa tare da sanya takalmanta tana wani yatsina fuska, kafin ta ce"me kuke nufi zan gudu ne da kike wani tare ni a gaban mutane wani are you payment"Ummul ta fada tana gwada maganar matar,kafin ta kuma gyara tsayuwarta da jakarta tana duban hanyar da ta sauko ganin gentle tsaye yana rungume da hannunsa yana kallonta kamar ba tare suke ba,harara ta zuba masa tare da yin kwafa a ranta tana cewa Wallahi zaka gane baka da wayo ba dai da Ummul zaka kara ba?maida dubanta kan matar ta yi kafin cikin kara gyara zazzakar Muryar ta ta bude baki cikin dan tirancin da ta iya ta ce?"i know you?"kallon rashin fahimta matar ta yi mata,sai dai kafin ta ce wani abu Ummul ta ɗora da cewa "to idan baki Sanni ba bari na sanar dake ko Ni wacece,Ni kanwar me wajen nan ce kuma ya a wajen Alhaji Ahmed dan itopia dan haka sai a bani waje na wuce ko yanzu na sa a koreku daga aiki a koma can evedu a ci gaba da saran ice da gini"ga tsananin mamakin Ummul sai taga gaba daya sun bata hanya har da haɗawa da sorry ma"ba tsaya nuna musu mamaki ta ba,ta wuce tana harararsu.

Tana tsaye a bakin titi ya karaso ya tsaya a gefenta,dubansa ta yi sannan ta ce"yanzu ke nan duk abinda muka ci munci bulus?kai wallahi da na sani na yi take away na kaiwa yan gida",gani ta yi ya mika mata leda me dauke da tambarin sunan wajen ba tare da ya ce da ita komai ba,karba ta yi tana dan leka cikin ledar,kafin ta dago ta kallesa fuskar nan tasa a dinke kamar koyaushe,tabe baki ta yi tare da cewa dubesa kamar ba shi ne ya gama iskanc.....hannunta da ya kama ya matse cikin nasa yasa ba ta karasa maganar ta ba,sai da gunguni ta karasa, daidai nan me dan sahu yaja burki a gabansu, hannunta yaja suka shige ba tare da ya tsaya yin ciniki ba, Ummul ta ce uhm yau dai zama a kofar gidan yan karya ya sa wani ma ya koya,to muje zuwa idan tusa zata hura wuta"yana jinta amma uffan bai ce ba,ita dama tasan ba tankawar zai yi ba shi yasa ta yi masa hararar da ta saba yi masa ta kasa kasa tana tura bakinta.

*******

Ana cikin maganar zuci da kallon kallo tsakanin sulaiman da Alhaji dan gaske,sai ga mufty da Ali sun dawo,can suka baro baffa a masallaci saboda ya ce ba zai fito su hadu da Alhaji dan gaske ba,domin bai shirya sanar dashi wannan labarin ba a yanzu kamar dai yadda ya shirya saboda gujewa zaluncinsa,duk da yasan cewa Allah yana tare da su kuma shine zai karesu kamar yadda shine ya nufa auren Ummul da jafar (gentle)zama yayi yana ta addu'a akan Allah ya sa su Ummul kar su hadu da Alhaji dan gaske, domin hakan ba karamar fitina zai kawo ba,ko su mufty hanasu fita yayi, sai daga baya da yayi tunanin cewa su da yara ne babu ruwansu, kuma ya gargadesu akan kar su sake su fadawa wani daga waje na maganar bare kuma alhaji dan gaske, wannan tunanin da yayi ne yasa ba ya barsu suka fito daga masallacin,sai a lokacin suka ga ashe har da oga sulaiman a yan jiran Ummul ɗin,mufty dai wajen sulaiman ya nufa yayinda Ali ya doshi gida kai tsaye ba tare da ya nuna alamun yaga alhaji dan gaske ba,ganin da gaske shigewa gidan zai yi yasa Alhaji dan gaske yin azamar yi masa magana ta hanyar kiran sunansa da ɗan daga murya,juyowa Ali yayi yana dan dube dube kamar yana neman inda ake kiran nasa,hakan ya kuma tabbatarwa da Alhaji dan gaske cewar bai Ganshi ba din da gaske,dan haka sai yaji dama dama a zuciyarsa akan fusatar da yayi na zuwan mufty wajen sulaiman,sai da Ali ya tabbatar da cewa Alhaji dan gaske ya yadda da raunin wayon da yayi masa, Sannan ya tsaida hankalinsa waje daya ya dawo da baya, fuskarsa cike da fa a, ya mikawa Alhaji hannu su ka yi musabaha,daga Alhaji dan gaske ya ce"yauwa Ali ka ganni nan tun bayan Sallah magriba nake tsaye ina duba ta inda wani zai zo daga cikinku dan kiran Ummul mu dan gaisa amma kamar hadin baki babu ko daya daga cikinku,gashi ni kuma na yi alkawarin ko zan kwana Anan sai naga ikram zan tafi".

Dariyar yake Ali yayi yana cewa"ayya aiko Ummul din kamar bata nan"take Alhaji dan gaske ya kuma gyara tdayuwarsa bayan ya kalli a gogon hannunsa Sannan ya watsawa Ali tambaya da cewa"ina ta je har kusan tsayin awa biyu da nake tsaye a gurin nan ina jira amma banga dawowarta ba? Sannan ita da waye suka fita?shin idan ita bata san matsayinta a yanzu ba ai shi ubanku ya sani dan me ba zai hanata irin wannan yawace yawacen ba?"Kafin Ali ya kai ga cewa wani abu a daidaita sahu ta faka a daidai inda motar Alhaji dan gaske take, kuma daga da motar sulaiman da suke tsaye da mufty yana gaya masa cewa Ummul din bata nan sun dan fita.

Gaba daya suka zubawa adaidaitan da wanda suke shirin fitowa daga cikinta ido"kan bura ubannan"kalmar da ta fito daga bakin dattijo dan gaske kenan,yayin da sulaiman ya yi sakare yana kallon Al amarin tare da jin sarewar gwiwar da bai taba jin irinsa ba,

Ummul kuwa ko ajikinta dan batasan danbarwar da ake a kanta ba,bare kuma uban gayyar oga gentle,tsaye ta yi ta yi shirin kallon dramar da za a kwasa tsakanin me dan sahu da gentle dan tabbas tasan bashi da kudin da zai biya me dan sahu drop din da ya dauko su,idan ya biya dazu yanzu bata jin zai iya biya shi yasa tuni ta tanadi makaman yaƙi jiran kiris take yi,kamar me dan sahu yasan abinda Ummul take jira kenan jin kudin da zai ce a bashi,ya dubi gentle da ya tambayesa,yana cewa"dubu uku zaku kawo me gida"a gidan uwarwa ya zama me gidan naka saboda ka shirya cuta ko?"Ummul ta fada a fusace dan dama tasan karshen zancan kenan,dan sahu kamar jira yake sai ko ya kashe mashin din ya fito yana cewa "ke ni kike zagi wallahi na fi ki kuruciya yanzu sai na sassamaki"wannan abu da Alhaji dan gaske ya gani ne ya hana shi karasawa wajen sai kawai ya tsaya yana fatan a ce me nafef din nan ya zuciya ya yanki gentle da wuka dan ga dukkan alamu ba za a rasashi da ita ba,a nutse gentle yada hannu ya janye Ummul daga gaban me dan sahun da ya fito kana ya dubesa yana cewa"ka yi hankali Malam karba nan tun kafin na bata maka kamanni"ya fada yana danka masa kudin a hannunsa,dubawa me dan sahun yayi da ya tabbatar kudin da ya furta aka bashi sai kawai ya koma cikin dan sahunsa ya kunna tare da wani irin figarsa take kasa ta tashi tare da kura me shiga cikin kai, cikin wani irin zafin nama gentle yayiwa Ummul rumfa da jikinsa dan kareta daga shaƙar wannan ƙurar.

Ita ma saboda yadda hankalinta ya tashi da ganin ƙurar yasa ta kuma cusa kanta a kirjinsa tana jan numfashi da kamshinsa da ya maye mata gurbin shaƙar kurar,

Gadan gadan Alhaji da gaske ya tunkaresu yana zuwa ya kai hannu zai finciko Ummul daga jikin gentle,Sai dai kuma kafin ya kai ga tabata gentle tuni ya cafke hannun ba tare da ya bari ko kan mayafin Ummul ya je ba,wani irin yarfarwa yayiwa hannun, dayan hannunsa kuma yana zagaye da Ummul da har yanzu take kife akan kirjinsa tana maida numfashinta tare da kamshin da take ta son tantance inda ta taba sanin me shi a cikin kofofin hancinta,wani irin numfashi da hucu Alhaji dan gaske yake futarwa tamkar wanda shima yake dauke da cutar asma,to amma ina shi wannan cutar da yake dauke da ita tafi ƙarfin asma, dan ji yake kamar an saka auduga an toshe duka kofafin hancinsa tare da idanunsa kai jinsa yake kamar gawa saboda tsananin mamaki da tunani kan da suka fara kai kawo a saman kunnensa,ke ya kawo gentle wajen daurin aurensa a matsayin da yake takawa na ba kowa ba a both site?"me ya sa buzu ya ki bari su hadu tun a wajen daurin aure,ya kuma kashe wayarsa har zuwa wannan lokaci ya kasa samunsa?me yasa Alhaji Ahmed dan itopia yaki masa fatan alheri akan daurin auren?kuma har zuwa yanzu bai ji daga gare shi ba? sannan me ye gadinsa da auren da har ya sashi tara wadan nan mutanen,duk da cewa wannan ba zai zama abin kafa hujja ba dan kowa yasan cewa duk inda wani babban mutum yake to al ummah na wajen?dariyar me su mufty da Ali suke masa lokacin da suke masa fatan alheri, Sannan me kalaman su suke nufi da sai yanzu suke dawo musu daki daki?"

Tabbas akwai lauje cikin nadi, to wai me yasa tun farko ya kasa fahimtar komai,hatta da saurin tafiya daurin auren da baffa ya yi ya kamata a ce ya sanya masa ayar tambaya, duba da cewa ba wai yana son auren ba ne kawai tursasawa da barazanar da yayi masa ne yasa shi amincewa,,tabbas bashi da me amsa masa wadannan tambayoyi sai mutum biyun nan,wato baffa da Alhaji Ahmed,to amma gentle ma yana daga cikin wadanda sai yiwa wannan tambayoyin,amma baya jin cewa zai iya tsayawa da gentle dole sai dai ya biyo masa ta wata hanyar,idan yaji abinda bai yi masa ba sai kawai ya kashe shi ya binne gawar ba tare da kowa ya ji ya gani ba.

Da kyar ya iya dago hannunsa da gentle ya yarfar a kasa ya kalla, Sannan ya kalli gentle din da yayi fuska kamar bashi ne yake aikata masa manya manyan laifuka irin wannan ba,wani irin ɗadɗatan miyau ya hadiye wanda har zafi yake masa a makogaro saboda tsananin zafin ganin Ummul a jikin gentle da yake ji,"me ye tsakaninka da Ikram?"Alhaji dan gaske da ya kasa daurewa yayiwa gentle tambaya, idanunsa akan yadda yaga ya dago Ummul din yana kallon idanunta, Sannan cikin taushin murya ya ce da ita" are you okay?"jinjina kanta ta yi kawai saboda zurfaffan tunanin da ta shiga akan gentle din, amma ganin Alhaji dan gaske a wajen tuni ya sa ta manta da wani tunani sai dinbin haushinsa da ya maye gurbin wancan tunanin da take yi, hannunta ta ji gentle ya kama ya saka mata ledar take away dinta,tare da yi mata nuni da ta ta fi gida, Ummul da bakinta baya shiru sai da ta yi masa tambayar da take cinta a rai, sai da ta fara karyar da kanta tare da yin marmar da idanunta masu haske Sannan cikin wani salon murya me dauke da yar sangarta a cikinta ta ce"to yanzu me ye matsayin wannan kayan haram ko halak tunda kaga kary......shiiiii ya fada tare da dora yatsansa saman tausasan lipt dinta da suka kara yin ja saboda aikin da suka sha gun oga gentle,caraf ummul ya rike hannun tare da cusa shi cikin bakinta ta daddage ta gartsa masa cizo, wanda har sai da ya runtse idanunsa tare da cewa ash,sakin hannun ta yi tare da yin baya dan gudu tana masa gwalo fuskarta cikin farin ciki da annuri tana cewa "dama na ce maka sai na rama abinda ka yi min a wajen na lol" ta kuma karasa maganar da gwalo,wani irin tsadadden murmushin da ko ni nan sai da ya tafi dani yayi yana wani lumshe shu'uman idanunsa da suke sakaye cikin bakin glas,yana mai sakin wata yar boyayyar ajiyar zuciya a lokaci daya yana dora hannunsa saman kirjinsa da shafawa.

Wayyo Allah ina wuta Alhaji dan gaske ya jefa gentle,Kai ba ma shiba hatta da sulaiman sai da jirin tashin hankali yasa shi yin zaman dirshan a cikin ƙasar wajen ba tare da ya damu da ɓata kayansa ba,kukan yake sosai wanda ya dauka cewa a zuci yake yinsa, bai ankara da haka ba sai da mufty ya kamo kafadunsa ya mikar da shi tsaye yana cewa"ayya kai wallahi sulaiman kaji matsalar ka kullum ina gaya maka Ummul bata son ragon namiji me kamar mace amma kai kullum burinka ka nuna mata halinka, yanzu me ye na kuka anan?"girgiza kai yayi yana cewa"mftahu baka san me ye so ba dole kaga aibun kukan da nake yi,ba dan ba sai na yi maka fatan ka hadu da haɗarin so kamar yadda na haɗu dashi yayi fata fata da rayuwata, wallahi zuciyata zafi take tunda nake ba a taɓa yin soyayyar da ta firgita ni ta sa ni jin cewa ban iya komai a soyayya ba har yau,gentle yayi mana zarra dole Ummul ta so shi ko bashi da kyau ko ba shi da kudi, yanzu na gane cewa so babu ruwansa da kudi, ko na ce ƙauna, domin abinda nake gani a gabana yafi gaban na kira shi da so sai dai ƙaunar da bata da iyaka ko tasgaro,ƙaunar da ba a gina ta akan son abin duniya ko son zuciya ba, wallahi daga yau na hakura da Ummul zanje na yi jinyar zuciyata na yi addu'a Allah ya sa mun dangana akan rashin Ummul"daga haka ya ture hannun mufty daga ƙafadarsa ya shige motarsa ya tada ita ya bar wajen a hankali.

Wani irin tausayinsa ne ya kama mufty da Ali shima da yake gefe yana kallon Film dinsu na gidan yan karya,ko shi mufty ya bashi tausayi amma fa Maganar gaskiya yana jin kwanciyar hankali a duk lokacin da ya tuna cewa Ummul matar gentle CE,bai kuma samun ntsuwa ba sai yau da idanunsa suka gane masa kalar soyayyar gentle din me taba zuciya,domin cike take da wani irin salon kulawa da sadaukarwa,ko shi mufty da baya jam iyar gentle to yau ya tashi kansa kuma ya sallama ya yar da makamansa.

Da karfi Alhaji dan gaske ya kai hannu ya shako wuyan gentle,gaba dayansa baya hayyacinsa fata kawai yake ya farka daga wannan mummunan mafarkin da yake yi........

Ana yi muna jin dadi Alhaji dan gaske ya ne ko sai mun kai ga Dr Bilal ne surukink😂😂😂

Yadda na zaune ba zai ga gari ba haka mai so bai ga zama ba, Alhaji dan gaske ina bayanka baka ga ta zama ba,tun da ka fada so😂😂😂

To jama a sai mun hadu bayan kwana goma na tafi hutu🫣🫣🫣😂😂

Kar ku manta a duk inda fans din GIDAN YAN KARYA suke ina bibiyar comments Dinku ina jin dadi yana sani nishadi,idan ina bi har kallona ake saboda dariyar da nake sha, dan haka ku sani cewa kuna baza capacity idan mace3zan zauna lissafa ku ko taggin sunayenku sai na kai kwana goma ban gama ba saboda yawanku shi yasa nake amsa a haka,amma dai ina tare da ku love You so much irin much Din nan da😂🥰🥰🥰🥰

Zahra✍️

***

💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol