Free chapter · Read without an account
Pg25
"Muna fiki gaya min abinda kuke shiryawa kai da wancan tsohon munafiki dattijon banzan?"a dan kaikaice gentle ya kai dubansa kan hannun Alhaji dan gaske da yake rike da kwalarsa yana jijjigashi cikin fitar hayyaci,kana ya dawo da dubansa kan fuskarsa da ita ma ta haɗa uban gumi idanunsa sun yi wani irin cikowa kamar me shirin zubda hawaye,kafin ya sanya hannu a nutse ya dauke hannun dan gaske daga kwalarsa ba tare da ya sa karfi ba,kama hanya yayi zai wuce,dan gaske ya kuma tare hanyar har da sanya hannunwansa biyu yana a tare tare hard da tattare hannun rigarsa kamar wani zararre,mufty kuwa ya ce me zai yi ba dariya ba har da durkusawa yana rike ciki,Ali dai murmushi kawai yayi yana gyara tsayuwarsa dan ganin yadda dan gaske zai iya dukan kakkarfar namijin duniya kamar gentle,dan ga dukkan alamunsa so yake ya kaiwa gentle din duka ko zai rage kadan daga cikin bakin cikin da ya ke cusa masa,shi kansa gentle din sai da abin ya bashi mamaki har sai da ya ɗan dafe kansa da ya fara masa ciwo saboda gajiya da takurar da yayi,tare masa hanyar da dan gaske yayi yasa ya koma ya tsaya yana jiran jin dukan da yaga yana shirin kawo masa,ile kuwa haukar dan gaske ta wuce duk yadda suke tunani dan kuwa naushi ya kaiwa gentle Wanda mufty da Ali su ka yi zaton ganin gentle a sheme,saboda yadda dan gaske yakai naushin da wani irin karfi,amma sai reshe ya juye da mujiya dan su dai basu ga lokacin da gentle ya dago daga jiginar da yake da bangon gidansu ba,bare har su ga lokacin da ya kai hannu ya zubar da dan gaske a kasa yana farfarin suma,sun dai ga wucewarsa cikin nutsuwarsa kai baka ce ya aikata wani abun azo a gani ba,da sauri Ali da mufty su ka yi kan dan gaske suna fadin "innalillahi "kai mufty duba ka gani da sauran numfashinsa kuwa?"mufty ya ce "Ni likita ne da zaka ce na duba shi,kai ka duba shi mana,dan wallahi in dai ya mutu a motarsa zamu watsa shi mu kai can kofar gidansa mu ajiye shi,"Ali ya ce dan Allah muftahu,ka daina yi mana fatan masifa"au rage mugun irin shine fatan masifa?"banza ali yayi mana ya fara kokarin ciccibar Alhaji dan gaske da tuni ya daina numfashi babu abinda yake zuba a hancinsa da bakinsa sai jinin da naushin gentle ya jawo masa,a bayan mota ya saka shi ya shiga wajen driving yana cewa muftahu ya shigo su kaisa a asibitin da yake zuwa sai su dawo.
Wani banzan kallo mufty ya yiwa Ali kafin ya juya yana cewa "kai kaga zaka iya amma wallahi ba zan taimaki wanda yake son ganin bayanmu ba"Kafin Ali ya kuma yin wata magana ma tuni ya shige gida abinsa, a ransa yana cewa ina ruwana wanda ya ja ruwa shi ruwa zai doka"haka Ali ya ja motar shi kadai ya wuce da Alhaji dan gaske zuwa asibitin itopias tunda yasan can yake ganin likita ko Ummul sanadinsa ta fara ganin likita a asibitin,yana yi yana juyawa yaga ko ya farka amma har suka iso asibitin bai motsa ba,hakan ya sanya Ali cikin fargaba dan har ga Allah baya son a ce Alhaji ya mutu ta sanadin gentle tunda yasan hukuma ba barinsa za ta yi ba,yana faka motar wasu nouse suka taho da gado suka sanya dan gaske a kai,kasa tafiya Ali yayi ya shiga suntiri so yake kawai a ce masa bai mutu ba.
Suna shiga dashi emagency daya daga cikin nouse din me suna danial yayi saurin danna wani danja wanda take ya aika sakon zuwan emagency zuwa kofisoshin likitocin da suke on duty,cikin kankanin lokaci kuwa sai ga likitoci har guda uku duka suka rufa akan Alhaji dan gaske,a inda suka gano doguwar sumar da yayi tare da raunin da yaji a hancinsa sai kuma haƙoran sa biyu da suka zube,daya daga cikin likitocinne ya gane fuskar Alhaji dan gaske dan duk wanda yake aiki karkashin itopias to ya san Alhaji dan gaske da kuma amincin da yake tsakaninsu na uban gida da yaronsa,Ali ya samu ya tabbatar masa Da cewa suna bukatar yansanda saboda binciken su ya tabbatar musu da cewa hadari ne na duka ko naushi da aka yiwa Alhaji dan gaske"kai tsaye Ali ya ce wa likitan ,kawai ya bar maganar dan bai san inda zai samo wanda ya daki dan gaske ba,shi kuma likitan ya tubure akan cewa dole sai an kawo jami ai,ai ba shi zai yi binciken ba,bare ya ce bai san inda zai ga me dukan ba,shi kuwa a ki ya tubure,sai kawai likitan ya shiga yiwa alin kallon zargi , kafin yayi kwafa ya ne cewa"bari na je na gayawa Dr abinda yake faruwa tunda ni ka nuna kafi karfina,wa ma ya sani ko kai ne ka yi dukan"a maimakon Ali ya ji tsoro ya gudu sai ma ya samu waje ya zauna yana cewa "je ka kira duk wanda zaka kira ina nan ba inda za ni"wani nouse dake bayansa ne ya ce"ai Dr bana jin yana nan"girgiza kai likitan da yakewa Ali masifa yayi yana cewa "naga shigowarsa babu jimawa kai dai ka tsaya a nan kar ka bari wannan yaron yaje ko ina har sai nazo"amsawa nouse din yayi cikin girmamawa,Ali kuwa ko gezau bai yi ba ,sai ma daga wayarsa da ke ringing yayi,Muryar baffa yaji yana cewa"Ali kana ina haka ?amma dai dan gasken yana lafiya ko? "Ey baffa ka kwantar da hankalinka suma kawai yayi ni kuma nan ba da jimawa ba zan dawo"to Allah ya kawoka lafiya wannan lamari bai yi dadi ba ko kadan"ya fada yana kashe wayar,shima alin dauke wayar yayi daga kunnensa yana cije labensa,a daidai nan yaji sautin takun Dr Bilal da yake tunkaro shi cikin nutsuwa fuskarsa me kyau babu fara a ko kadan a cikinta sai tsananin kwarjini da haiba,dayan likitan yana gefensa yana ta zana masa abinda ya faru har da karawa miya gishiri.
Ba dan tsananin kwarjinin Dr Bilal ba da babu abinda zai sa Ali ya gaisheshi,"kaine ka kawo shi"Dr Bilal ya tambayi Ali yana dubansa da idanunsa da suke sakaye cikin fari ƙal din glass,amsa Ali ya bashi da cewa ey taimako na yi shine Abin yake neman juyawa wani iri, dattijo dashi ya dinga neman rigima da mutanen da suka fi karfinsa in ba dan ma ina da imani ba ai da barinsa zanyi ya gama numfarfashinsa har rai yayi halinsa"su ok"Dr Bilal ya fada yana duban dayan likitan kafin ya kuma cewa"Ku bar abin a hannunna zan ci gaba da treatment dinsa so dan haka maganar ya mutu"daga haka ya wuce ya barsu a wajen,hararar likitan Ali yayi yana cewa "da na sani ma tun farko na sanar da kai ko ni waye, to dake bana son fariya da nuna asalina yasa na yi maka shuru,amma nets time ka kiyayi haduwar mu"yana gama magana ya zura hannunsa cikin aljihun rugarsa ya juya yana wani takun suwagares dan ya kuma razana likitan,aiko likitan ya ɗan sha jinin jikinsa dan bai iya cewa komai ba,sai bin alin da kallo da yayi yana tunanin karfa ya je yayi ta aikinsa dan yanzu haka ma dan uwan Dr Bilal ne tunda shi ba gane yan uwansa ake ba saboda tsananin muskilancinsa,take ya ji shakkar alin ya shigesa.
****
Kai tsaye room din da aka kwantar da dan gaske Dr ya nufa, ta kofar da kowa yake shiga ta nan ya shiga,sai da ya tsaya akansa yana kallonsa na wasu yan daƙiƙu kafin ya ɗora da abinda ya kawoshi,cikin ƙanƙanin lokaci kamar wani aljani ko me gani har hanji sai ga Alhaji dan gaske ya farfaɗo,kalmarsa ta farko ita ce"wallahi sai na ga bayanka dan duk duniya ban ga wanda ya isa ya rabani da ikram ba,ko ubanta bai isa ba bare kai wani matsiyaci me facin takalmi"calm down"dakakkiyar muryar Dr Bilal ta daki kunnensa ta yi masa zuwan bazata da wani irin duka da ta yi masa a kirji,da fari sai ya ji kamar Muryar wancan matsiyacin sai kuma da ya ɗan dawo hayyacinsa ya fara tunanin tsananin sanya gentle da yayi a ransa ne yasa yaga Dr Bilal na juye masa shi,natsuwa ya ɗan yi yana fatan ALLAH yasa surukin nasa bai ji kalamanda yake jifan gentle da su ba,me yake faruwa da kai ne haka 2 times kana zuwa nan ta sanadin ita yarinyar da kake magana a kanta gashi har ka rasa hakoranka guda biyu?"Dr Bilal ne yake tambayarsa a nutse sai dai fuskar a kammale take babu wasa bare sassaucin da zai nuna maka cewa a gaban surukinsa na gobe yake,girgiza kai dan gaske yayi tare da shafa hakoransa yana jin wani irin ciwo a ransa, kafin ya ce"Dr duk abinda xan fada maka ba zaka fahimce ni ba,saboda kai baka cikin kalar jarabawar, dan ko ba komai kana da wadda take sonka kake sonta karewa ma iyayenku basu da wata matsala da aurenku lokaci kawai kuke jira, kaga kenan ba zaka taɓa gane fahimtar halin da wanda ya nema bai samu ba yake ciki"a hankali Dr Bilal ya ɗan kauda kansa gefe yana jin takaicin mutumin da babansa yake son ya zama suruki a gareshi,tashi yayi daga dan zaman da yayi bisa kujerar dakin, yana dan shafa kwantacciyar kasumbarsa baka sidik me sheki, sai da ya zo daf da fita Sannan ya ɗan dakata ba tare da ya juyo ba,ya ce"abinda na sani shine jiya baba ya gaya min ya je daurin aurenka kai da yar me gadin ka"yana zuwa nan a zancansa ya kada kansa ya fice ba tare da waiwaye ba.
Shiru dan gaske yayi zuciyarsa na son karbar maganar Dr sai dai wani bangaren na tankwabewa,to amma dai ko ma meye yasan cewa Alhaji Ahmed ba zai yi masa karya ba,dan haka yana samun kwarin jikinsa zuwa gobe zai je har wajensa ya tambayeshi.
********
A can bangaren gidan yan karya kuwa ko bayan da Ali ya koma babu wanda ya tattauna maganar saboda kar Ummul ta ji,dan kaf dinsu babu wanda baya jin dadi da farin cikin farin cikin da take ciki,dan yanzu haka tana can daki tana waya da yan uwanta Safwan da hamza wanda dukkansu babu abinda basu sani ba daga dukkan abinda yake faruwa.
Baffa kuwa har yanzu dakiya kawai yake dan Allah ka dai yasan irin fargaban da yake ciki, duk da cewa idan ya tuna wani abu yakan samun sauki ransa, sai dai sanin halin Alhaji dan gaske yana kashe masa gwiwa Daga kwarin gwiwar da ya samu lokacin daurin auren Ummul, da fuskantar halin da yake ciki ne yasa Ummu jarumai mace ta zauna tana kwantar masa da hankali tare da tabbatar masa da cewa in dai suka bi tsarin da suka tsara daidai in sha Allah zasu kubuta daga ukubar Alh dan gaske,sai da tabbatar taga murmushi akan fuskarsa Sannan ta yi hamdala,shima hamdala yayi ga ubangijin da ya bashi mace ta gari yana kuma yiwa Ummul addu'ar Allah yasa ta kwashe halin mahaifiyarta,murmushi kawai ummi ta yi tana mika masa furar da ta gama dama masa.
Ummul dai bata san sanda Bacci ya kwashe ta ba,yayin da aka bar Ali da mufty suna fama da take away din da Ummul ta kawo, dan basu kwanta ba sai da suka tabbatar cikinsu ya samu gamsuwa.
********
Bangaren gidan Alhaji dan gaske kuwa har zuwa wannan lokacin da agogo yake buga karfe sha biyu da rabi na dare babu wanda ya damu da sanin ina yake bare dalilin da ya hana shi dawowa gidan,Ita dai mommy tana sane kawai dai bata da damuwa da hakan ne shi yasa ta yi kwanciyarta ba tare da ta bibiye shi ko a waya ba,ita kuma gwana ta gwanaye, tana can makale da waya har yanzu tana hira da bely saboda tsananin farin cikin da take ciki,yanzu bely kawai take son yiwa hanyar samun mufty kamar yadda ta ke bukata,duk da cewa zezeen ta so a ce an ci gaba da shiri akan Ummul din tunda ta wani bangaren ai tana taya mommynta kishi, bely ce ta nuna mata cewa su dakata tukunna har ta ana daura aurenta da Dr Bilal idan suka tabbatar yazo hannu sai su farma Ummul da makirci har sai sun ga bayanta, wannan hirar ce ta sanya zezee nishadi har bata san lokaci yaja da yawa ba,karfe daya daidai suka gama wayar,da zaro ido ta yi bayan ganin time din da suka gama wayar,Dr take son gwada kira amma tana tsoro, tunawa da shawarar bely da ta yi yasa ta daure ta fara kiran wayar,ga tsananin mamakinta ji ta yi an daga sai dai ba a ce komai ba,"hello baby sorry Allah yasa ba bacci kake na tashe ka ba?"maimakon ta ji ya bata amsa sai kawai ta ji ya ɗan saki siririn tsaki kafin ya dora da cewa"na yi tunanin jikin abbanki zaki tambaya so idan baki da abin cewa switch the phone"kafin ta kashe shi ya rigata kashewa,mamaki ne ya ishe ta wai dama Abba bai dawo gidan ba,to me ya same shi lafiya kalau fa ya fita?da sauri ta zamo daga kan gadon ta nufi dakin mommy sai dai tuni ta tarar da mommy ta rufe dakinta ta yi bacci,cizon yatsa ta yi tana mamakin yadda mommy take nuna halin ko ina kula ga abban nata,baya ga haka har da wasu dabi u dake nuna tsana ko haushi da ta fuskanta Mommy na yiwa abbannata,ko me yasa?dole dai akwai wani abu a kasa kuma zata bincika a hankali dan gano ko meye,juyawa ta yi ta koma dakinta, ba tare da ta samu me bata amsoshin tambayarta game da rashin lafiyar abban ba.
***********
Washe gari da wuri zezee ta gama shiryawa ta fito, sai a lokacin take sanar da mommy abinda ya faru da abban,kai tsaye Mommy ta ce da ita "ki tafi idan na gama Abinda nake zan sameki"kallon ta zezeen ta tsaya yana yi kafin ta bude baki ta ce"Mommy wai duk haushin auren da Abba yayi ne yasa kike wannan shareshin?amma ai naga yanzu batun lafiya ake bai kamata ki tsaya daka ta kishi ba"wata Uwar tsawa Mommy ta dakawa zezee tana mai nuna mata hanyar fita,cikin tsoron da ya kama zezee ta fice daga dakin tana kuma tsunduma cikin kogin mamaki,to amma wani bangare na zuciyarya fada mata yake ba wani dalili ba ne sai na kishi,idan haka ne kuwa bata ga kaifinta sosai ba,dan da ita ce Ummul ta samu nasarar rabata da Dr ta kuma aure shi to tabbas gawarta za a dauka,da wannan tunanin taja motarta ta bar gidan.
Litan hakori ya sanar da dan gaske cewa ba za barsa ya tafi ba, saboda sai an yi masa hakorin roba an saka masa Sannan akwai ciwo a wajen shima dole sai an yi masa aikin wajen dan haka sai yayi hakuri har zuwa nan da kwana,uku wannan bayanin da ya samu daga bakin likitan da zai yi masa hakorin roba yasa ya saduda,to amma dake wayarsa tuni aka kawo masa ita daga mota sai kawai ya shiga dannawa, Alhaji Ahmed kira, saboda a yanzu shine kawai zai fada masa magana ya yarda da ita dan yasan ba karamin mutum ba ne da zai yi masa karya,lokacin da kiran ya shigo wayar Alhaji Ahmed suna tare da Dr Bilal,dan haka a gabansa ya daga wayar bayan sun gaisa Alhaji Ahmed yayi masa sannu da jiki,ya dora da cewa"yanzu bilalu yake fada min cewa jiya ka hadu da tsautsayi, har ina cewa ke hada ango da tsautsayi ko duk a cikin murnar angowancewar ne?"sai kawai Alh dan gaske ya shiga shafa sanƙon kansa yana washe baki kamar ba shine mutumin da yake sheme ba a jiya,sai kawai ya samu kansa da kasa yiwa Alhaji Ahmed tambayar da ya kira yayi masa,a haka suka rabu da Alhaji Ahmed mutum me barkwanci yana ta kwasarsa.
*****
Tun sassafe baffa yasa Ummul ta shirya ba tare da tasan inda zasu je ba,kumbure kumbure kawai take saboda a tunaninta gidan Alhaji dan gaske zai maida ita daga yajin da ta yi,Ummi ma bata ce mata komai ba,su kuwa Ali da mufty shiryawa su kayi suka fice wajen nemansu dan tuni suka manta da sabgar wani Alhaji dan gaske,mufty ne ma ya ce da Ali "ya zo su je su duba halin da sulaiman yake ciki, duba da yanayin da ya tafi dashi a jiyan,dacewar hakan da Ali ya gani ne yasa bai yi musu ba suka wuce gidansu sulaiman din dan duba lafiyarsa.
Karfe goma daidai ta yiwa Ummul da baffa a cikin asibitin, inda Ummul ta dinga yiwa baffan tambayoyi akan abinda ya kawo su asibiti,ganin ya ki bata amsa yasa ta fashe da kuka tana cewa"baffa ka gaya min ko dai Yaya gentle ne wani abu ya sameshi?"hannunta ya kama kafin cikin rarrashi ya ce da ita"ba jafaru ba ne,Alhaji dan gaske ne jiya ya samu tsautsayi a nan kofar gidan bayan shigarki gida shine muka zo duba shi"tuburewa ta yi ba zata shiga ba har da kukanta,sosai take neman bawa baffa ciwon kai, dan har ta fara shirin zaman dirshen wajen dan ita idan zata yi rigimarta in dai bata zauna ta gurza kafarta a kasa ko ta bubbugata ba to ji take bata nuna karshen rigimarta ba,abin duka baffa ya shiga nema yana cewa"kul kika zauna min anan wajen kaji yarinya yar nema"Amma ina bata saurareshi na tuni ta kai kasa tana tana ci gaba da kukan ba zata duba Alhaji da gaske ba,bata san daga ina ba kuma yaushe ne ya kara so wajen? Ita dai kawai ta ji an yi sama da ita cak,kamar an dauki yar tsana,kafin ta samu damar gane me wannan aika aikar,ta kuma jin Muryar baffa yana cewa"da ka bar min ita na fara zane mata jikinta"kafin baffa ya gama rufe bakinsa Muryar zezee ta karade wajen da wani irin ashar irin na ya'yan maguzawa.......
Wash Allah typing akwai gajiya,
Mu gangara nets PG Dan jin me karfin halin daukar amaryar gentle😂😂😂..
Zahra✍️***
💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕
By
FATIMA Y ADAM......
Littattafan marubuciyar.
KUDIRAR ALLAH
KADDARATA SANADIN HASKE
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
ƳAR GIDAN YARBAWA
MATAR ƊAN BIRNI
And
GIDAN ƳAN ƘARYA....