Free chapter · Read without an account
Pg26
bude baki zezee ta yi zata kuma lailayo wani ashar din da ba zai yi mata maganin komai ba,cikin sauri bely da suke tare tasa hannu ta rufe mata baki tana cewa"zezee wai me yake damunki ne ?kina Hauka ne?to yanzu wa kikewa wannan zagin shi da bai san kina yi ba ko ita da bata san da zuwanmu ba?"kuka zeze ta sanya tana cewa"bely ba zaki gane ba,ni kadai nasan yadda nake ji idan naga Dr Bilal da wannan mayyar yarinyar,kina ga fa duk da ta auri abbana amma ba su rabu da juna ba wannan wace irin masifa ce?dan Allah ki sake ni na je naga inda zai kaita"girgiza kai bely ta yi tana cewa"maza ki share hawayenki kar ki sake ki kuma yin wani abu makamancin wanda kika yi yanzu.
kullum ina gaya miki idan har kina son samun kan Dr ya amince da aurenki to dole ne sai kin kwantar da kai kin aro wasu dabi un da kika san yana so,kamar dai yadda Abba yake fada miki amma har yanzu kin kasa yin control din wannan banzar kishin naki da kuma bakin ciki da hassadar Ummul da shine yake kara hargitsa lissafinki"bely Ummul bata da abinda zan yiwa bakin ciki da hassada dan haka kima daina wannan batun"taɓe baki bely ta yi tana cewa "ai dama ba zaki yadda ba,muje kawai tun kafin kisa kallo ya dawo kanmu".
Daga Dr Bilal da ya saɓi Ummul a kafada har baffa da yake binsu a baya basu kula zezee ba duk da cewa sun ji zagin da ta kunduma,bare kuma Ummul da ta ke ta kanta,dan bata gane wanda ya dauke ta ba har sai da kamshinsa da ya zama hadda a kofofin hancinta,ya sanar da ita cewa shi din ne,wurga kafafunta ta ci gaba da yi tana kukan ya sauketa babu inda zata,sai dai duk abinda take yi a banza wai an tsikari kakkausa,duk inda suka zo giftawa sai dai taga mutane suna dauke ido,hatta da baffa dakatawa yayi da bin bayansu,wanda hakan ya daurewa Ummul kai,to me yasa baffa yana kallo Dr ya dauke ta amma bai ce komai ba?to wai shi wannan Dr ko dai yana tsafi ne?dan tsoronsa da mutane suke ji ya fara bata tsoron itama ,acikin masu tsoron kuma wai har da baffanta,kai lallai wannan abin dubawa ne da mamaki lallai baffa baya cikin hankalinsa tunda har wani namiji zai daukar masa ita ya rungume ajikinsa amma bai ce komai ba,bata san inda suka shiga ba saboda nisan da ta yi cikin tunaninta,ji ta yi kawai ya ajiye ta akan kujerar dakin,wanda hakan ne ya bata damar fahimtar a inda suke,zunbur ta mike tana kallon Alhaji dan gaske da yayi suman zaune saboda mamaki da al'ajabin tantirin surukinsa, dan kaf cikin sunaye ya duba babu sunan da ya dace dashi kamar tantiri shi yasa kai tsaye ya bashi sunan,dakakkiyar Muryar Dr ce ta katse masa tunanin da yake akan yadda gentle da Dr suka mayar da matarsa yar tsana abar wasansu,"naga ana fama da ita akan ta shigo dan ta dubaka amma ta ki, shi yasa na rage mata aiki na kawo maka ita har nan saboda sanin matsayinta a gunka?"wani kallon ka maidani sakarai dan gaske yayiwa Dr Bilal,sai dai ya kasa maida martani da wata mummunar kalma, karshe ma sai yaken da yafi kuka ciwo yayi yana cewa"tabbas ka kyauta"ya fada a ransa tana cewa"kaji da iskan yaro wato har jaddada min kake kasan matsayinta a wajena amma kake dauko ta ajikinka har zuwa gabana saboda ta tantiranci da tsarin ido.
Cikin kuka Ummul ta ce"to ina ruwana da abinda ya sameshi bayan shi ya jawa kansa, da za ace dole sai na zo duba shi?"daidai lokacin zezee da bely suka shigo dakin, daƙyar zezee ta iya daurewa bata maida martanin maganar da ta shigo taji Ummul na yi ba,bely kuwa sai yau ta taɓa ganin Ummul,wanda kuma take anan ta daina ganin laifin zezee akan haukar kishin da take yi,abinka da karuwa kuma me naman wajen zama take ta wani sake fuska tana gaida Abba da Dr da yayi wani fuska kamar bai san da shigowar su ba,dan kaf hankalinsa yana kan Ummul sai dai a zahiri zaka yi tunanin hankalin yana kan wayarsa dake hannunsa,duban Ummul ta yi cikin salon kissa irin nasu na tsoffin ƙaruwai ta ce"ayya baby me ye kike kuka ai naga jikin abban yayi sauki ko yanzu zai iya tafiya gida,ki yi shiru ki daina kuka zai warke"ta fada tare da kai hannunta kafadar Ummul sai dai tuni Ummul ta doke hannunta tana watsa mata harara saboda yadda ta ji zafin hada kukanta da tayi da dalilin rashin lafiyar abban,bayan hasali kukan da take na bakin cikin ganinsa ne,ita fa yadda ta ke jin tsanar mutumin nan bata ƙi a ce ya mutu ba.
Murmushin yan duniya bely ta yi kana ta ce"sorry"daga haka bata kuma magana ba sai dai fuskar ta har yanzu akwai murmushi"zezee kuwa duk hankalinta yana kan Dr ji take kamar ta hadiyeshi, "Dr Barka da safiya?"shiru dakin yayi kowa yana sauraron jin irin amsar da Dr zai bawa zezeen,sai dai har sun fidda rai zai ce wani abu, sai kuma kamar daga sama suka ji muryarsa me taushi da take fidda kalamai ɗaiɗai kamar dan koyo ya na cewa"ya kika kwana? I'm sorry jiya na ɗaga miki hankali,ban san baki san da rashin lafiyar ba"wayyo dadi kashe zezee,.ai hatta da Abban nata sai da ya saki ajiyar zuciya tare da jin wani dan karen sanyin dad'i, wannan wane irin bazatan ci gaba ne?gaba daya zezee ta kasa boye farin cikinta,dan tunda take ko gaisuwarta Dr zai amsa a ginshire yake amsata wani lokaci ma sai dai taga motsawar bakinsa ko da kuwa wajenta ya je,to amma yau gashi har da sorry,a yangance ta bude baki ta ce"no karka damu ai nasan tunda yana tare da kai babu wata matsala shi yasa na yi bacci har da minshari"dago kansa yayi daga kallon waya ko na ce kallon Ummul ta kasan idonsa dan babu wanda zai kawo yana duban inda take ma bare a akai ga tunanin kallo,ya yiwa zezee kallo daya kallon da tun haduwar su bai taba yi mata ba,kai sai yau ne ma zai iya tantance kamanninta,"thanks"ya kuma fada har fuskarsa na ɗan saki kamar zai yi murmushi sai dai baiyi murmushin ba,zeze kuwa ai yau ji take ba ya ita don fuskanta kawai zaka kalla ka tabbatar da tsananin farin cikin da take ciki,
Ummul kuwa tuni kukanta ya dauke, ji tayi dakin ya kuma yi mata zafi ga wani irin nauyi da take ji a kirjinta jamaran aza mata dala da sauran dutse,so take ta tashi ta fita sai dai wata zuciyar na rike ta akan ta tsaya taga karshen hirar Dr Bilal da zezee,dan tsaki ta saki lokacin da ta ga Dr ya kalli zezeen kallon da yayi mata guda daya dan tantance kakanninta,amma sai Ummul taga kallon har ya wuce n Shari a, har kamar ma yana mata dariyar da ta wuce murmushi,muskutawa ta ɗan yi a ranta tana cewa"to ma Ni ina ruwana ne,can da matsalar su,sai dai abin mamaki ta kasa kauda damuwar abinda ya faru a ranta,har ji take kamar gentle dinta ne a tsaye yake yiwa zezee hira har da dariya,maganar da Abba yayi ce ta sanyaya dawowa hankalinta, "yauwa Dr nace ko zaku dan tafi office dinka da zezee ka ɗan nuna mata wasu abubuwa da suka shafi harkar lafiya tunda ita ma nouse ta karanta dan ma tsaya shiririta ne amma da yanzu ta zama cikakkiyar likita"al adar Dr ce bai cika bata amsa instantly ba ,hakan yasa sai da yayi dan jim kafin ya dage kafadunsa yana gyara zaman farin galashinsa a idanunsa,wani irin farin ciki ne yake neman kashe zezee daga tsaye, yayin da bely take ta zungurinta akan ta rage wannan rawar kan ita ma ta ɗan ja masa aji,amma ina ta yi nisa bata gane yaren bely dan har wani yi take kamar zata kamo shi jikinta,dariyar farin ciki Abba yayi yana jin cewa ya jefi tsuntsaye biyu ne da dutse daya saboda shima hakan zai bashi damar kallon sahibarshi a kusa dashi yadda yake so,ba tare da Dr Bilal ya kuma cewa komai ba ya nufi hanyar fita, cikin rawar jiki zezee tabi bayansa tana wani kwarkwasa kamar zata karye,ta gefen ido Ummul ta bisu da kallo tana kokarin daidaita numfashinta da yake kokarin toshewa,karfafa kanta take yi tare da tuna tar da ita matsayinta d matsayin zezee a wajen Dr, sannan Dr b gentle ba ne, wannan karfin gwiwa da ta bawa kanta ya sa ta dinga kokarin maida nutsuwarta jikinta,Abba kuwa kallonta yayi yana washe baki kafin ya ce"ikram yaushe zaki koma aikin ki ne?"banza ta yi da shi saboda wutar da take balbala a cikin ranta ta kasa mutuwa duk kuwa da yadda take ta kokarin kashe ta,sai dai hakan ya gagara sakamakon saka mata Dr da gentle da take a matsayin abu guda duk da tasan cewa karya zuciyarta take mata.
Zezee kuwa suna fita daga dakin a maimakon taga sun kutsa cikin asibitin sai kawai taga Dr ya nufi hanyar fita ba tare da waiwayen bayansa ba,bely da ta taho tsegumi ta ɗan yafito zezee tare da yin kasa kasa da murya tana cewa"ke ina ga fa fita zaku yi?idan haka ne kuwa tabbas aikin boka ya ci kin ga sai mu koma ki kara masa kudi a fara wani aikin"ƙifta mata ido zezee ta yi suna ci gaba da bin bayan Dr da zaka iya rantsewa bai san zezee tana bayansa ba,sai da suka zo wajen motarsa yasa hannu ya bude ya shiga ya zauna, da sauri zezee ta zagaya dayan barin tare da sanya hannu ta bude zata shiga,take Dr y katse hanzarinta da cewa"where are you going with me"wani irin shock ne ya kamata,sai kawai ta saki murfin motar tana binsa da kallon mamaki,baki bude bata iya rufewa ba har sai da ya ja motarsa ya bar harabar asibitin gaba ɗaya,"anya ko wannan mutumin bashi da aljanu"?tayiwa bely tambaya idanunta na cika da hawaye,dan bubbuga bayanta bely ta yi cikin rarrashi ta ce"karki tada hankalinki zezee tun da aka fara da haka alamu ne na mun fara cin nasara dan haka karki karaya"tafiya zezee ta fara yi kamar zata kifa tana cewa "muje kawai bely ba zan koma dakin nan wannan tsinanniyar yarinyar tayi farin ciki ba"da sauri bely ta kama hannunta suka.karasa wajen mota ta saka ta sannan ta koma ta shiga ɓangaren driver taja motar suka fice daga asibitin gaba ɗaya,har suka fice zezee na waige waige ko zata hango motar Dr tunda ita dai bata ga fitarsa daga cikin asibitin ba.
*****
Kamar walkiya haka Alhaji dan gaske yaga dacewar Ummul daga dakin karar rufo kofar kawai ya tsinkaya saboda yadda ta rufota da karfi"tabbas sai na nemowa ikram temako dinga dukkan alamu yaron nan so yake yi haukatata"Alhaji dan gaske y fada yana maida kansa ya kwantar akan fulo,yana jin zuciyarsa sawai tunda ko ba komai ya samu tabbacin Ummul matarsa ce.
****
Ummul kuwa tana fita bata tsaya a ko ina ba sai can nesa da dakunan asibitin inda ta yi burki a tsakiyar bishiyoyin da suke ta rangaji sun yiwa ɗan dajin kawanya wanda hakan ya sa aka samu inuwa da iska me dadin shaka a wajen,rungume bishiyar ta yi tana sakin wani irin nunfashin da ya tokare mata makoshi,tun tana fidda shi a nutse har ya fara yi mata wahalar fita take ta fara jansa da karfi kamar zata fice a hankalinta,kokarin lalubo inhela take amma ina babu ita a cikin aljihunta babu dalilinta, shaf ta manta bata dauko ta ba amma hakan baisa ta daina neman ta cikin aljuhun rigarta ba,abin kamar Al mara haka taji an sanya mata inhelar a abakinta da kofofin hancinta,shakarta tayi ba tare da shiri ba,a lokaci daya tana dawowa hayyacinta tare da kallon wanda yayi hanzarin kawowa rayuwarta ɗauki.
***
Basu jima da fara tafiya ba, bely ta ci wani uban burki ,har sai da ta samu la adar zagi da ga motoci da mashinan dake bayanta,amma hakan ko ajikinta,kokarin gangarawa bakin hanya take,zezee ta jijjigata dan duk maganar da take mata belyn bata san tana yi ba,har sai da ta kai ga girgizata,bata kula da maganar da zezee ke mata ba har sai da ta tsaida motar a bakin hanya, sannan ta dubi zezee a yayin da take kokarin fita daga motar ta ce"zezee wuce gida kawai za mu yi waya dan wallahi ba zan bar wannan damar ta wuce ni ba"sai a lokacin zezee ta kalli inda taga hankalin belyn yayi,wani uban tsaki ta yi tare da zabgawa belyn harara wadda tuni har ta yi gaba dan haka bata san me zezee ke yi ba,a fusace zezee ta koma wajen driving tana cewa "aikin banza, a kan wani banzan talaka take kokarin kashe mu",da gudu ta figi motar ta bar wajen.
Bely kuwa inda mufty yake tsaye yana kokarin tare dan sahu ta nufa, ba ta yi masa magana ba sai dai ta tsaya a kusa dashi kamar itama jiran me nafef din take,cikin sa a kuwa tana tsayawa a daidaita sahun da babu kowa ta tsaya a gabansu,sai da ta bari mufty ya fadi inda zashi sannan itama ta fadi wajen, dan haka me nafef ya dauke su gaba ɗaya.
A hankali mufty ya karkace ya dauko iPhone din abokinsa da ya aro ya fara dannawa,yana wani basarwa,kafin can bayan wasu yan dakiku ya kara wayar a kunnensa,ya fara magana kamar gaske,"ya akayi habibu bakin namu sun karaso?ok to ka ɗan ce musu su jira xan dauko motata a kofar ruwa kasan waccan da na fito da ita, na bawa wani bawan Allah da na ga yana tafiya cikin rana abin tausayi ga yara ya dauko daga makaranta,um kai dai habibu to me ye amfanin arzikin idan ba mu taimakawa masu bukata ba,ok ok to ba damuwa ina nan karasowa"yi yayi kamar ya kashe, sai can alam din da ya saita ya dauki kara,cikin sauri ya daga yana cewa"wai ke meye ne tun dazu kike damuna da kira bayan na sallame ki"dan zare ido yayi kafin ya cigaba da cewa"oho two million dinne yayi miki kadan a sarin kaya,to ba zan kara miki ba,tunda ba aurar ki nayi ba"daga haka itama ya kashe yana zabga tsaki,da yan motoci irin na an damesa din nan,bely dai na cikin adaidata amma ta yi kamar bata ciki sai dai dukkan hankalinta da kumnuwanta suna kan mufty.....
Gumi ne ya fara karyowa mufty ganin har sun kusa zuwa inda zai sauka amma ita wannan taki sauka,dan kallonta yayi tare da cewa"ina zaki ne Hajiya?"take bely ta saki murmushin nasara dama abinda take jira kenan,dan haka ta ɗan gyatta zamanta fuskar ta da murmushi ta ce"wace Ni da amsa sunan Hajiya a gabanka"wayyo dadi su mufty an samu abinda ake so ƙarya ta shiga har ta samu wajen zama,dan haka take ya kuma gyara zama yana sakin wani dan munafikin murmushin da ya kuma tafiya da bely yana cewa "kar ki damu ai ko wane mutum da irin matsayinsa dan haka idan kin amsa ma baki laifi ba"a hankali a hankali bely ta dinga jan mufty da hira har suka karaso bai sani ba,sai da me nafef ya yi masa magana, Sannan ya ankara,bai bari an shiga dashi layi ba,ya sauka a bakin titi,anan bely ta bashi wayarta ta ce ya sa mata nomber sa,jikin mufty har rawa ya fara yi yayin karbar wayar saboda ganin karshen iphone ce,dakyar ya saita kansa ya sa mata nomber,laluben aljuhunsa yafara yi yana cewa,"to kai ya za mu yi da kai ina tunanin fa bani da cash sai dai na yi maka transfer, dan duk na rabarwa almajiran kan hanya kudin da na fito da su, saboda ban san zan hau dan sahu ba"bely ta yi saurin cewa "A'a je ka kawai zan bayar idan yaso nan gaba ko na ce haduwa ta biyu sai ka biya ni"murmushi yayi tare da cewa"baki da matsala sai na ji ki"juyawa yayi yana cewa ba sai na biya kin ba in kin ganni,kaji uwar son banza wai zan biya ta,ita fa anufinta tunda ta hadu da dan gidan dantata ko dan itopia kakarta ta yanke saka"ya karasa fada yana shekewa da dariya dan a tunaninsa ya gama tashin kan bely da ƙaryarsa.....
******
Baki Ummul ta bude zata yi ihu, ruf ta ji ya rufe bakin da wani abu me sanyi da zaki ga wani irin kamshin mint me dan karan dad'i,babu shiri ta hadiye kukan tare da miyansa da ya zazzage mata a bakin ta,sai kuma da ta hadiye ta dago tana furje furje har da kakaran amai,shi dai yana tsaye a daf da ita yayi mata rumfa ta yadda bata isa yin wani motsi ba tare da ta taɓa shi ba,"meye a kayi miki har yake neman tada miki ciwo?"mul mul ta yi da baki kafin idanunta su cika da kwalla zuciyarta na bugawa da tuna dalilin zuwan ta nan din,"stop crying"ya fada yana kai bakinsa daf da fuskarta yana hurawa a hankali,rufe idanunta ta yi tana shaƙar kamshin bakinsa da jin dadin iskar da yake hura mata,"ko dai nine?"ya fada kasa kasa a cikin kunnuwanta cikin wata irin murya,da hakan yayi sanadiyar tada duk wani tsiga na jikinta,karasa shigewa jikinsa ta yi tana zagaye shi da dukkan hannuwanta duk da cewa basu rutsa shi ba,bakinsa ya kuma shi,garwa cikin kunuwanta yana cewa"yaya gentle ne kaɗai yake sanya Ummul ikram cikin yanayin irin damuwar,bayan shi kuma sai waye?"rasa abin yi da Ummul ta yi akan halin da ya tsinci kanta yasa ta fashe da wani dan Marayan kuka me ratsa zuciyar me saurare..........
Zahra ✍️***
💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕
By
FATIMA Y ADAM......
Littattafan marubuciyar.
KUDIRAR ALLAH
KADDARATA SANADIN HASKE
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
ƳAR GIDAN YARBAWA
MATAR ƊAN BIRNI
And
GIDAN ƳAN ƘARYA....