Free chapter · Read without an account

Pg27

by Fatima Yushau adam · GIDAN YAN KARYA

A Ahankali gentle ya ya dago fuskarta yana kallon idanunta da gashin idanun jike da hawaye,janye ta ya shiga kokarin yi amma ta ki sakinsa sai ajiyar zuciya take saki,da kansa ya kama hannunta ya cire daga zoben da ta yi masa,ya maida ita jikin bishiyar yana kallon fuskarta da take dan danshi danshin gumi,labbanta duk sun jike sun kara yin wani ja gwanin sha'awa,a hankali ya ɗan sunkuya yadda zasu yi daidai da ita,ya sumbaci labban ta kana ya dago ya sumbaci saman idanunta zuwa tsinin hancinta,kafin ya gangaro wuyanta ya sanya fuskarsa yana shaƙar dauwamammen kamshinta da yake sanya shi cikin wani irin zazzafan yanayi, Sannan ya koma kamar ruwa ya kwantar da kansa a kirjinta yana sauraron bugun zuciyarta da yadda kirjinta yake sama da kasa,a hankali ya sanya hannuwansa ya zagaye ta daga ita har bishiyar,kafin cikin wata yar kankuwar murya me dan zurfi da amo ya ce"amsa my question"maimakon ta bashi amsar da yayi mata tun farko akan dalilin damuwarta,sai kawai itama ta jefa masa wata tambaya da sanya shi dagowa daga jikinta yana kallon tsakiyar idanunta,ganin bai bata amsa ba kuma ya tsaya yana kallonta yasa ta kuma cewa"kana da dangantaka da Dr Bilal ne?"dogon hancinta ya ɗan ja kafin ya rukota suka zauna a kan kujerar dutsen da ke girke a wajen,sai da suka zauna Sannan ya ce"me kika gani da ya saki wannan tunanin?"kwantar da kanta ta yi a kafardarsa tare da lumshe idanunta,kafin ta ce"kawai dai kuna yi min kamanceceniya ne ta aiyukanku, maganarku, kamshinku,tafiyarku,miskilancinku,shariyarku,komai da komai har yanayin tsayinku,fatarku ce kawai ta banbanta,shi yasa nake tunanin ko kuna da dangantaka?"kai tsaye ya amsa mata da cewa"babu wani abu"daga haka yayi kokarin sauya zancan ta hanyar mikewa bai ce komai ba ya kama hannunta ya miƙar da ita suka fara tafiya,har suka fito harabar asibitin bata kuma ce masa ba,dama shi ba cewar zai yi ba,kamar an wurgota haka suka ganta a gabansu,take Ummul ta shiga diri dirin yadda zata yi ta kaucewa nouse din tunda tasan bata cika mata alkawarinta na takalmin da ta ce zata aika Mata ba, har ma da kuɗin da ta ce zata dora Mata a kai,fahimtar hakan da gentle yayi ne yasa shi rike hannunta sosai wanda hakan yasa ta tsaya ba dan taso ba,amma fa kugunsa ya sha mintsinin Ummul wai dan duk ta samu ya saketa.

Yake kawai ta shiga yi tana amsa gaisuwar nouse din,ita kuwa nouce ta ci gaba da cewa"wallahi Hajiya kullum sai na zuba idon ganinki a asibitin nan,dan nasan ko naje gidanku ba za a barni na shiga ba,in dai har ba kin san da zuwa na ba,shi yasa na cigaba da addu'a Allah ya nuna min ke ko dan na yi miki godiya addu'a kuwa nasan ko ban ganki ba zata biki"sokoko Ummul ta yi tana raba ido ta kasa cewa komai"nouse kuwa ci gaba ta yi da cewa"tun a ranar da kika yi min alkawarin takalmi ina zaune a gida na ga sakon sabon takalmi da kudi har one mill kamar yadda kika fada,yanzu gashi na bude camist dina na kaina na saka duk wani abu da mara lafiya ke bukata, yanzu haka kanwata ce take zama daga safiya zuwa yamma idan na tashi daga aiki Ni kuma sai na zauna,cikin kankanin lokaci Allah ya saukar da albarka a cikin lamarin, wallahi tunda nake a rayuwa ba a taba faranta min irin yadda kika faranta min ba,tabbas da za a dinga samun masu hali irinku masu fada da cikawa da talauci yayi nesa da Al ummah, Ummul Allah yayi miki albarka Allah yasa kika gama da iyayenki lafiya Allah yakareki daga dukkan sharri ya tsare ki daga sharrin zamani, Allah ya baki miji na gari wanda zai so ki ya riritaki wanda zai iya sadaukar da farin cikinsa saboda ke,ya baki yaya na gari masu albarka"nouse ta karasa maganar tana fashewa da kuka,wanda yasa jikin Ummul kara yin sanyi kamar kankara,cikin sanyin jiki Ummul ta daga kafadarta tana cewa"babu kome Allah ne ya baki ba ni dan haka ki gode masa, Allah ya baki Sa'a a cikin nemanki,ki daina kuka kar mutane su dauka wani abu ne ya faru"gingina kai kawai nouse ta iya yi Sannan ya wuce ta bar Ummul cikin tsananin mamaki,ci gaba suka yi da tafiya ba tare da daya ya tankawa daya ba.

Har suka je gida basu yiwa juna magana ba,sai dai lokaci_lokaci Ummul ta kan juyawa tana kallon gentle da yaki bari su hada ido,suna sallamar me dan sahu ta juya zata shige gida,sai dai kafin ta karasa shiga zauren ya riga ta shiga,canja hanya ta yi zata wuce ta gefensa yayi saurin tare hanyar,wanda hakan yasa ta fada jikinsa,kwacewa ta yi tana cewa"pls Yaya gentle tsoro nake ji wallahi ina jin tsoro"dago fuskarta yayi ya tallafe da tafukan hannunsa kafin cikin natsuwa ya ce"me kike tsoro?ke fa yar baiwa ce, gashi nan ta dalilinki mutane suna samun tallafi"cikin shashekar kuka ta ce"wallahi yaya jentle ni ba yar baiwa ba ce,aljanune suke son amfani da shegiyar ƙaryata su cutar da bayin Allah ko ni da kaina,to idan ba Aljani ba ta ya mutum zai san abin da daga Allah sai Ni da kai da wadda aka yiwa alkawarin muka sani? Idan ba aljani ba ne to dole daya daga cikinmu ne yayi wannan aikin wato ko Ni Ko kai,Ni kuma nasan ba Ni ba ne ,tunda bani da kudin da zan iya kyautar dubu hamsin ma bare one million"nima bani da ko ten thousand Naira bare nayi abinda kike tunani,ai kin san ko waye gentle dinki KO?"ya faɗa yana hade fuskarsa da tata,gigiza Kai ta yi tare da cewa "Ni ban san komai a kanka ba,Abu daya na sani ,shine kai me gyaran takalmi ne"to me yasa kike so na bayan baki san ko Ni waye ba?shuru ta yi domin ita kanta bata san me zata ce ba,dan hatta da son da ake magana bata san ya yake ba,kallonsa ta danyi Sannan ta ce"so kuma me ye so din kuma ya ake ganesa?"sakin ta yayi yana nuna mata hanyar shiga gidan,ba tare da ya bata amsar tambayar ta ba,ita ma din bata takura ba dan tasan idan bai ga damar yin maganar ba ta dage sai yayi to sai dai ya maida ita zararriya,sai da ya ga shigar ta gidan Sannan ya juya ya fice ba tare da ya tsaya bude kayan sana ar sa ba.

A yinin ranar nan kaf Ummul ta yi shi ne cikin tunani da son gano wanda yake yin kyauta a matsayin ita ce ta yi,daga karshe da taga zata bawa kanta aiki da damuwa sai kawai ta watsar da tunanin bayan ta sanyawa ranta cewa temako Allah yayiwa bayinsa ta inda ya so,taimakon ya je gare su.

A bangaren baffa kuwa sai da Ummul ta bar asibiti Sannan ya shiga ya duba Alhaji dan gaske,wanda suka sha hira har yana ce masa,in sha Allah da an sallame shi Ummul zata koma aikinta,duk da cewa shi Alhaji dan gasken yasa a ransa ba dan Ummul ta ci gaba da aiki ne yake son ta koma ba,sai dan ya kara kusanta kansa da ita.

Lokacin da zezee ta koma gida, a falo ta samu Mommy Tasha wankanta ta sanya tv a gaba tana kallo,duk da cewa tana cikin damuwar abinda Dr yayi mata ,amma hakan bai hanata tsayawa kallon mommy ba,kafin ta bude baki ta ce"Mommy kin fasa zuwa asibitin ne?"kai tsaye Mommy ta amsa mata da cewa"na fasa zuwa saboda mun yi waya dashi ya ce gobe da wuri za a sallame shi"jinjina kai kawai zezee ta yi ta wuce dakinta,da ido mommy ta bita tana jin tausayin halin da mijinta ya sanya tilon yarta da take da ita kwalli daya a duniya,hannu ta sa ta share hawayen da suka zubo mata,tana jin tausayin kanta akan rashin yan uwa da iyaye,tabbas duk wanda yayi rashin iyaye yayi rashi babba a duniya, saboda ko damuwa ce ta yi masa yawa bashi da inda zai jingina a share masa hawaye,mutum daya ne zai iya maye gurbin iyaye ta wata fuskar shine miji, shima idan ka yi sa a,to ita a rashin sa ar ma karshe ce.

****

alhaji dan gaske ya warke tas, dan idan ba gaya maka a kayi ba baza ka taba cewa yayi rashin haƙora har biyu ba,kwanansa biyu a ka sallameshi,kuma har aka sallame shi Mommy bata je ta duba shi ba,sai dai idan ta ga dama ta Yi kiransa a waya ta masa sannu ta kashe abinta,shi kuwa ko aijinsa dan a tunaninsa duk kishin ya auri Ummul ne yasa take masa waɗannan abubuwan,domin shi tunaninsa bai taba kawo masa cewar mommy tasan babbar illar da yayiwa rayuwarta ba,saboda bata taɓa nuna masa wata alama ta ta sani din ba,shi yasa ya bawa banza a jiyarta,ko da ya dawo gidan bai bi ta kanta ba ya ci gaba da sabgarsa,musamman ta bangaren ganin cewa auren zezee da Dr Bilal ya tabbata,dan tun ranar da ya ambaci wata guda ya fara kirge, wanda a cikin kirgen watan ne har ya auri Ummul da sauran abubuwan da suka faru.

****

Ummul na shirin komawa aiki gidan Alhaji dan gaske,kamar daga sama sai ga yaya Safwan da yaya Hamza sun dura,ba tare da sun sanar da zuwansu ba,ai gaba daya Ummul karamin haka ta nemi, daga da kalli Wannan sai ta juya ta kalli Wannan ta rasa inda zata sanya ranta dan farin ciki,kai gaba daya guda ma ya kasance cikin annashuwa,saboda family ya hadu, wannan dalilin ne ya hanata komawa aikin, ko baffa bai takura mata ba, saboda yasan yadda yan uwan junan su ka yi tsananin kewar juna.

Ko da Abban zezee ya koma gida ya ga Ummul bata je ba,sai da ya dauki waya ya kira baffa ya ji dalili rashin zuwannata,jin dalilin yasa hankalinsa ya dan kwanta.

*******

A can bangaren sulaiman kuwa tun da ya koma gida yake rashin lafiyar da aka kasa gane mafarinta,likitoci ne Mahaifinsa yake kawowa tun daga na gida har na waje suna duba shi,sai dai dake cutar bata asibiti ba ce ,kamar ba yi ake ba,shi ka dai yasan me ke damansa,yar uwarsa da ake son hadasu aure Ita ce kullum a tare dashi,wanda hakan ya fara sanya masa tausayinta musamman idan ya tuna yadda zafin so yake,hakan yasa ya fara dan kulata kadan kadan har Allah ya sa ya ɗan fara samun sauki daga azabar da zuciyarsa take masa.

*****

Gaba daya suna zaune a tsakar gida, Ummul na tsakiyar yar uwanta ana labari kowa da irin tashi salon karyar,Hamza ne kawai bawan Allah da bai damu da rayuwa ba a cikinsu,amma Safwan ma yana buga capacity na karya a cikin makarantar su, sau daya an sha kuresa daga karshe dole Hamzan ne yake shiga ya fidda shi,amma duk da haka bai sauya ba,yan mata kuwa suna shan karya da gayu,kasancewarsa yana da yawan abokai ya'yan masu kuɗi shi yasa yake yadda yake so,kun san dai dan talaka idan ya kasance me hazaka a cikin aji to kowa ji yake dashi musamman masu kuɗi,dan shi har sai da amsa yake a biya shi babu ruwansa ya shiga cikin gari ya baza karya ya dawo,gashi da farin jini ba ga maxan ba baga yan matan ba,suna cikin wannan hirarrakin ne,wayar mufty ta hau burburbur alamun kira yana shigowa,daga wayar yayi a karo na uku zai kashe, Ummul ta yi saurin kwace wayar tana cewa "Wallahi sai mun ji wadda take kiranka kana kashewa" daidai lokacin da ta danna ok, Shi kuma mufty ba tare da yasan ta daga ba,ya ci gaba da yi mata magiya kar ta daga wayar,sallama bely ta fara yi tana sakin murmushin jin abinda mufty yake faɗa,ware ido Ummul ta yi har da bude baki zata yi dariya sai kuma ta yi saurin rufe bakin da tafin hannunta tana amsa Sallamar,"ina wuni "?Ummul ta fada tana yiwa mufty da yayi sakare yana kallonta gwalo,daga can bangaren bely ta amsa cikin kwantar da murya tunda ta gane wadda ta daga wayar,Safwan kuwa alamu yake mata da ta sanya wayar a amsa kuwa,ita kuma ta makale masa kafada,"me wayar yaki karba amma yanzu zan sa shi ya karba"Ummul ta fada tana murmushi,bely ta ce"pls idan ya karba yanzu dan Allah ki sashi ya ci gaba da daga kirana kin ji kanwarmu"karki damu my aunty"daga haka ta mika masa wayar,kin karba yayi ta kuma mika masa tana yi masa alamu da ya karɓa,kamar wani karamin yaro haka ya shiga kunkuni kafin ya ce"pls Ummul xan karba yanzu amma netx ba zan kuma....zaro masa ido ta yi tana nuna masa cewa har yanzu fa tana kan layi kuma tana jinsu,shiru yayi tare da karbar wayar Sannan ya tashi dan ba zai iya amsa wayar a gabansu,saboda kaf din su basu iya komai ba banda zallar iya zaro karyar,kunyar kula mace suke ji shi yasa yanzu mufty duk ya diririce,ya kasa yin wayar a gabansu.yana fita suka kwashe da dariya,a in da wayar Ummul ta fara nata burbur din,zubawa fuskar yar karamar itel dintata ido ta yi,tana ta kallon lambar gentle da take ta kai kawo,Hamza ne ya ce"ke kina sa wani yana daga wayar gashi kema ana kiran ki kinki ki daga"yaya Ali ya ce"ita ai me dalili take yi, gentle ne yake kira kuma taki dagawa ne saboda tana fushi akan balaguron da yayi kwana biyu bai gaya mata ba"ta shi ta yi ta bar wajen,tana mamakin ƴaƴanta Ali shi kadai ne yake gane duk wani motsinta da abinda yake nufi.

Mufty na shiga daki ya kara wayar a kunnensa,sama sama yake amsawa bely hirarta,ita kuma bata damu ba haka ta ci gaba da kokarin sanya shi dole ya saki jiki da ita,ta yi nasara dan kuwa tun mufty yana sakin tsaki har ya hakura ya fara sakin jikinsa, daga karshe dai tuni ta ja ra ayinsa akan zai kawo mata ziyara gidansu,suna kashe wayar ta tura masa da address din gidanta, sai da mufty ya ɗan yi nazari kafin ya tashi ya fara shirin zuwan.

***

Ummul tana shiga daki wayar na kuma yin zum zum zum, bata tsaya bata lokaci ba wannan karon ta daga,dan tasan muddin ta kuma ƙin dagawa zai iya hakura da kiranta gaba ɗaya, tana sa wayar a kunnenta ta sanya masa kukan rashinsa da yake ta nukurkusarta tun bayan rabuwar tasu ta shekaran jiya"ya Allah" ya fada can kasan maƙoshinsa tare da lumshe idonsa yana furzar da wani xazzafan huci ta bakinsa,kana ya kuma yin wani furucin cikin murya me taushi,"kin san Allah ki ka ci gaba da kukan nan yanzu zaki iya ganina a nan kusa dake kuma ba zan fito ba har sai garin Allah waye, bayan na tabbatar da cewa na kore duk wata ƙishin ruwa da ke tare dake"dif kake ji Ummul ta dauke wuta, ko alamun kukan babu, kafin cikin sanyi da kewar da ke kulluɓe da ita ta ce"yaya gentle duk abinda ka faɗa nasan zaka iya aikatawa sai dai ina da tabbaci akanka nasan ba ka ci Haram ba, dan haka ba za ka iya zuwa ka kwana dani a daki daya ba,muddin ban zama mallakinka ba"shine kwarin gwiwarki?"ya fada kamar yana mata rada a cikin kunne wanda har sai da ta ji yo hucin numfashinsa ya ratsa cikin kunnen ya wuce zuwa cikin kwakwalwar ta da zuciya da duk wani jini da ke zagayawa a cikin jiki da bargonta,"idan kin musa ki rufe idanunki yanzu zaki ganni a kusa dake ina lashe wannan hawayen da suke ta bulbula daga cikin kyakkyawar kwayar idaniyarki"wani irin sanyi ta ji ya rufe ta har hakoranta suna hadewa,dunkulewa ta kuma yi, yayin da ta ji yana kuma cewa"na taho?"a'a ta fada tana kashe wayar gaba daya,a lokaci daya tana maida numfashi kamar wadda ta yi gudun ceton rai.

Daga nasa bangaren ma,kallon wayar ya tsaya yana yi kafin ya dorata akan kirjinsa yana sakin wani dan lafiyayyan murmushi.

****

Tsaf mufty ya gama shiryawa,su Safwan sai dariya suke masa da tsokana,duban agogo yayi yaga har karfe tara ta yi,sai yaji jikinsa yayi sanyi, kamar ya fasa,amma kasancewarsa mutum ne don cika alqawari,sai kawai yayi harama ya fice yana cewa,ai ganin gidan nasu kawai zan yi na dawo gobe na koma in Allah ya kaimu,zuwa yayi ya fara sanarwa da Ummi, ta daga kansa ta yi masa addu'a tare da jaddada masa kar ya wuce goma a wajen budurwa,da in Sha Allah ya amsa mata danniya fice daga gidan,

Kai tsaye ya tare da ke dan sahu ya bashi kwantancen gidan da yake can wajen nothwets, Kasancewar ba wani nisa ne tsakaninsu ba yasa nan da nan suka karaso ya biya me nafef din shi kuma ya tsaya yana kallon gidan da anguwar da suke a tsare,ba wani hatsaniya dan gidajen da suke wajen basu fi uku zuwa biyar ba,da alama yanzu ake gida areal,wayarsa ya daga ya kirata,kira daya ta daga,ce masa ta yi ya shigo kawai,karasawa yayi ya kwankwasa gate din, wani iyamurin me gadi ne ya zo ya bude masa,yana ta washe baki, me gadinne ya raka shi har falon bely sai da ya ga zamansa Sannan ya juya ya koma bakin aikinsa,tunda ya zauna yake kai kawo da idanunsa a falon,tunani yake ko mutanen gidan sun yi barci tunda dare ya dan fara yi,zamansa bai fi da mintina goma ba,ya fara jiyo kamshin turare tare da takun takalmi,

daga kansa da zai yi idanunsa su kayi mummunan ganin da ya kusa shidar dashi a zaune........

Zahra✍️💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol