Free chapter · Read without an account

Pg30

by Fatima Yushau adam · GIDAN YAN KARYA

Duk da yadda zuciyar gentle take azalzalarsa da ya shaƙe wuyan ɗan gaseke har sai ya mutu,amma hakan baisa ya kasa dakewa ba,ko a fuska ba zaka taɓa gane cewa yana cikin fushi ba,domin shi a ko da yaushe fuskarsa ta kan ɓoye asirin zuciyarsa,baffa ya kalla da idanunsa da suka dan canja launi duk da cewa ba kowa ne zai fahimci hakan ba, kafin cikin taushin murya ya ce"ina Ummul zamu tafi?"take dan gaske da tun fahimtar wanda ya shigo masa gida ya kai makura wajen harzuka,dan haka gentle yana rufe bakinsa ya bude baki yana cewa"kai dan gidan uban waye da zaka tafi da Ummul?na ce ubanka waye?"kallon da gentle yayi masa ne ya sashi hadiyar miyan da ya kusa yi masa karo saboda ya haɗiyesa ba bisa ƙa'ida da shiri ba,babu abinda yake tunawa sai zafin naushin gentle din da har yanzu idan ya tuna sai ya firgita, wannan dalilin yasa shi maida dubansa kan baffa yana cewa"ka sanar dashi ya rabu da Ikram saboda yanzu matar aure ce kuma nine mijinta,kai ne kawai zaka bashi wannan tabbacin ya hakura daga keta hakkin aure da yake yi"hannu baffa yasa ya share gumin fuskarsa, Alhaji dan gaske yana kallonsa yana kuma hankalce da tashin hankalin da ya shiga,dan kuma son samun hujja yasa ya dawo da maganarsa ta baya,"buzu ka sanar da wannan yaron ya bar wajen nan dan ba zan taba bashi matata ya tafi da ita ba,hasalima ina mai baka tabbacin cewa daga yau ikram ta zo gidan aurenta kuma daga yau zan fara karbar hakkina na aur.......tamkar wani mayunwancin zaki haka gentle yayi kan Alhaji dan gaske,wanda tuni ya sakawa bujensa iska ya juya da gudu saboda kaucewa mahangurbar da gentle yake shirin kai masa.

Yana shigewa ya rufe kofar glass din ta ciki yana cewa"Ni zaka kawowa sabon iskanci wallahi da ga kai har tsohon munafikin dattijon nan ba zan barku ba"mommy da hayaniyarsa ta fito da ita daga daki,ta karaso inda yake fuskarta cike da mamaki ta ce"Abban zezee lafiya kai dai waye haka?"Ni da wancan tsohon banzan da yake son raina min hankali mana, ina ji ina gani wani kato ya dinga rike min mata,to idan ma munafuntata kuka yi yau zan nuna muku ni ba a cin tuwo dani asha miya lafiya, yau zan tabbatar muku ikram tawa ce mallakina ce ni kaɗai",

A can gate kuwa tun gudun dan gaske gentle ya kalli baffa,duk ya yi wani iri dashi abin tausayi,ya ce"baffa karka damu babu abinda zai faru da Ummul,domin har abada ta haramta ga ko wane namiji ma bare kuma ɗan gaske"baffa ya ce"a'a fa jafaru barin Ummul a cikin gidan nan tare da dan gaske akwai hadari kana jin fa abinda yake fada"cikin natsuwa gentle ya ce"calm down baffa everything is fine babu wani abu da zai yi mata"daga haka ya juya ya fice daga gidan,ya bar baffa cikin tarardadi da jimamin halin da Ummul take ciki.

***

A can bangaren yaran da bely ta sanya aikin sato Ummul kuwa,tun suna zuba ido har suka gaji suka kira belyn,"Hajiya har yanzu fa yarinyar nan bata fito ba"a fusace bely ta ce "ku yi ta zaman jira har nan da karfe sha biyu idan bata fito ba sai ku tafi ku koma da sassafe,na baku dai daga nan zuwa jibi ku kawo min ita ko ta halin yaya"baki da case Hajjaju"yaron ya fada yana kashe wayar tare da ci gaba da zaman jiran bullowar Ummul.

***

Tun Ummul na ganin kamar abin na wasa ne har dai ta tabbatar da gaske kulleta a kayi ba tare da tasan lefin da ta yi ba,kuka ta fara yi kamar wadda take cikin kurkuku,har aka kira Isha ta tashi tayi,amma shiru kake ji babu alamar wani zai zo ya budeta,dan gaske kuwa ya kasa ya tsare yana zaune a falon yana jiran lokacin da yake ganin ya masa daidai dan tunkarar dakin Ummul,mommy bata san me yake faruwa ba,hasalima ba ta san cewa Ummul na cikin gidan ba,bare ta yi tunanin dan gaske ya kulleta,karfe sha daya dai-dai na bugawa ya shige daki ya watsa ruwa Sannan ya sake fitowa,lokacin da ya fito babu kowa a falon dan tuni mommy ta shige bedroom dinta dan yanzu gaba daya ta fita daga hanyar dan gaske tsakaninta da shi sai kallo,a baya ma bata taɓa kai kanta gareshi ba,bare yanzu da bai da lokacinta sai na abinda yasa a gaba,kai tsaye ya tunkari dakin Ummul din yana kokarin bude kofar, wayarsa dake gaban aljihunsa ta yi haske alamun kira ya shigo,hakan yasa ya fasa shiga dakin bayan ya bude kofar, ya daga wayar tare da karawa a kunnesa,"Hallo oga matar nan fa ta ki yin magana duk wani launin azaba an yi mata amma taki fadar komai"cikin yin kasa da murya sosai dan gaske ya ce"ka ci gaba da bincikarta da launin azabtarwa kala kala,dole zata yi magana,duk da cewa ina zargin wannan tsinannan yaron Dr Bilal ne yasa ta,kawai ina son samun tabbaci ne daga gare ta,Abinda nake so da kai idan har zato na ya zama gaskiya ina ganin kawai zan fara kashe tsohon nasa kafin ya bi bayansa,amma dai zan bari ya fara auren zezee ta yadda zan samu komai cikin sauki"daga haka ya kashe wayar yana cewa,duk wanda ya ci tuwo dani miya yasha a hankali zan gama da duk wanda yake son raba ni da farin cikina".

Komawa yayi da baya tare da bude kofar dakin Ummul a hankali,a jikin kofar ya ganta a manne kamar tana a tsorace,kallon nazari yayi mata kafin ya saki dan guntun murmushi yana mai shafa sankonsa da yake ta sheki ya kuma kara masa muni, Sannan ya bude baki ya ce"a karo na biyu kin kuma jin sirri na wanda hakan yake nufin dole ne kikasance a karkashin ikona da son ranki ko da ƙin ranki,dan haka wanne kika zaɓa?"ya fada yana kanne ido daya irin na tsaffin yan iskannan, Ummul da gaba dayanta a tsorace take da jin hirar Alhaji dan gasken ta kuma hade bayanta da jikin bangon da take kamar zata shige ta cikinsa,ganin yadda duk tsiwa da bakin Ummul ta kasa cewa komai yasa shi kuma sakin wani makirin murmushi,yana cewa "yarinya ki hakura ki sallama min kanki domin a yanzu banga wani mahaluki da ya isa hanani tabbatar da ke a matsayin matata ba"wani irin yunkuri Ummul ta yi ta raba bayanta daga jikin bangon da ta mannewa kamar salatif, tana yi masa kallon neman karin bayani da rashin fahimtar abinda yake nufi,a maimakon ya ce wani abu sai kawai ya shiga matsowa gareta yana taku yana sakin makirin murmushi tare da shafa sankonsa zuwa habarsa da babu gashi ko sili ɗaya,girgiza masa kai ta shiga yi tana ja da baya ba tare da kanta ya kawo haske akan maganganun Alhaji dan gaske ba,dan har yanzu tana cikin shock da tsoron kisan da ya ambata kuma ga makusancinsa da ga ubangidansa kuma surukinsa na gobe,hannunsa da ya kai zai taɓata ne ya dawo da ita hayyacinta, cikin sauri ta goce tare da shammatarsa ta dau hanya zata fice daga dakin amma sai ya sanya ƙafarsa ya tadeta,kif ta kifa a kasa amma duk da haka bata yi sanya ba kokarin tashi take dan ta samarwa kanta maboya,ganin haka yasa dan gaske nufar kofar da shirinsa na rufe ta,sai dai abinda ya gani yayi matukar razanashi da bashi mamaki,hakan yasa ya tsaya cak hannunsa rike da kofar yana kallon wanda ke tsaye a bakin kofar ya zuba masa idanunsa masu haske wanda a yanzu suka sauya launi,

Da gudu Ummul ta nufesa ba tare da wata wata ba ta fada jikinsa har sai da ya ɗan yi kamar zasu fadi saboda yadda ta rungumesa da dukkan karfinta,cikin in Ina dan gaske ya fara magana da cewa"Bilal kai ne a wannan dare haka?ko zezeen ta san da zuwan ka ne?to amma ba nan ne hanyar ɗakinta ba"a hankali Dr Bilal ya dauke idanunsa daga kallon da yake yiwa ɗan gasken,kafin a hankali cikin maganarsa me aji da ke fita dai-dai ya ce"na kira wayarku duka baku daga ba,so gashi ina son yin maganar auren cikin gaggawa dan ina tunanin ina da tafiya da asubar yau zuwa Chaina,shi yasa na zo,so bayan na shigo na ji gidan shuru amma naji kamar daga ta nan akwai mutane shi yasa na karaso nan din"ey ey ey haka ne kasan wani lokaci auren yara kananu yana da wuyar sha ani,shi yasa kaji muna ɗan hayaniya,muje muyi magana ko?"Dr Bilal bai ce komai ba ya fara kokarin janye Ummul da ta cukuikuiye shi daga jikinsa,amma sai ya ji ina hakan ya gagara, ɗan duban Alhaji dan gaske yayi tare da cewa"ba a yiwa yara haka yanzu duk ka firgitata bata cikin mutsuwarta ka manta da ciwonta ne?"girgiza kai dan gaske yayi yana washe baki kamar tsohon sakarai,kana ya ce"haka ne "ke sake shi kije ki kwanta babu abinda za ayi miki"da sauri Ummul ta maida kanta ta makale a kafaɗa tare da ƙara ƙarfin riƙon da ta yiwa Dr tana cewa"dan Allah Dr Bill ka kaini gida tsoro nake ji"dan gaske ya bude baki zai yi magana Dr Bilal ya dakatar dashi ta hanyar wucewa zuwa can kujera da Ummul ajikinsa,ya zauna tare da ita, Sannan ya ce"pls zan kaita gida idan ta nutsu sai ka daukota"wani irin kakkauran miyau dan gaske ya hadiya,a ransa yana cewa "wannan shine ga koshi ga kwanan yunwa,tabbas ba dan yaron nan yazo min da albishir me dadi ba da wallahi a daren nan sai na yiwa ikram kaca kaca dan ba zan taba bari ta bar gidan nan ba tare da na jaddada igiyar aurena a kanta ba,idan babu shi ma sai a daura dan dole,"ko hakan bai yi ba?"Dr ya tambaye shi cikin kara tsare gira kai ka ce shine babba saboda tsananin kwarjini da iya ladabtar da me laifi,"to to hakan ba laifi amma da ka bari ni na kaita kar na saka aiki,tunda nine wanda hakkinta ke kaina"kar ka damu hanyar zan yi"ya fada yana duban tsadadden agogon hannunsa inda ya nuna sha biyu da kwata cif_cif.

Kamar wadda aka tasa daga barci haka zezee ta farka a firgice babu salati babu hailala,haka ta sauko daga saman gadon ta tunkari hanyar fita daga bedroom dinta,tana kusantar falon tana da ɗa jin kusancin hancinta da kamshin Dr Bilal.

***

A hankali Mommy ta farka tare da sanyawa kofarta key ,baya da haka ta kuma shigewa toile ta rufe, Sannan ta ciro karamar wayar da take amfani da ita wajen kiran raliya,ta sanya sabon layi kamar yadda ya saba,har ta kai hannu zata danna kiran bayan ta gama loda lambar sai kuma ta tsaya cak ,tana dan wani nazari,"anya kuwa ya dace ta kira raliya ba tare da ta san a inda take ba?tabbas tunda har raliya bata kuma kiranta ba hakan yana nufin tana cikin Matsala,innalillahi kar dai Alhaji ya gano leken asirin da raliya take?idan ko haka ne gaba daya suna cikin hadari musamman raliyar da take hannunsu a yanzu,da sauri ta cire layin tare da yin floshin dinsa, Sannan ta fice daga toilet din tana Jin fargabar tabbatar da abinda take zargi ya samu raliya.

Maganar da ta ji daga falon ne ya dakatar da ita daga shirin fitar da take yi,a hankali ta bude kofar tare da lekawa ba tare da ta bari ta yi wani motsin da zai janyo hankalinsu ba,sosai ta yi mamakin ganin Ummul da Dr Bilal, ganin Abba bai bata mamaki ba,to amma me ya kawo su a wannan lokacin? Sannan meye hadin Ummul da Dr da zata yi masa irin wannan irin wannan rungumar?to ko dai bata da lafiya ne?to amma kuma taga yanayin Ummul din kamar a tsorace take ko dai wani abu ya sameta?bata da halin fita bare ta samu amsar tambayoyinta hakan yasa ta ci gaba da tsayuwar dan son jin abinda ke faruwa.

****

Alhaji dan gaske ne yayi gyaran murya tare da cewa"to mu fara yin maganar da ta kawoka idan ya so sai ku wuce taren"a mutse Dr bilal ya kalli Ummul da har yanzu kanta yake kife akan kirjinsa numfashi ma a tsorace take fitar dashi, Sannan ya dawo da dubansa kan dan gaske tare da cewa"da yiwuwar a kawo kudin aure nan da kwana biyu da ga nan sai ku tsaida lokacin da yayi muku"yana gama maganarsa ya mike tare da Ummul din,wanda hakan yayi daidai da fitowar zezee da ga inda ta boye saboda tsananin farin cikin da maganar Dr ta sanyata,ba tare da ganin gabanta ba ta yi kansa tare da rungume shi ta barin hagunsa, Ummul kuma tana damansa,a maimakon ubanta yayi mata maganar sakarcin da ta fito tana yi sai shi ma ya shiga yage baki kamar ana tala cingum,dan a hakikanin gaskiya maganar Dr Bilal ta Kore Masa duk wani bacin rai da ya shiga a yau,Abu daya ne ya ki wuce masa,shine bakin cikin kallon Ummul rungume a jikin surukinsa ya kuma kasa yin wani katabus dan hana hakan,a hankali Ummul da ta ji ana jijjigata ta dago kanta daga maboyar da ta yi masa a kirjin Dr,ji ta yi kanta yayi wani irin sarawa saboda ganin zezee jikin Dr ,sannu a hankali ta fara janye wa daga jikinsa saboda a lokaci daya taji tsoronta na ficewa bacin rai na maye gurbinsa,hanata hakan yayi ta hanyar janyewa daga ɓangaren da zezee take, tare da cire hannunta daga wuyansa, Sannan ya mayar da Ummul gurbin yana takawa a hankali cikin kasaita da nutsuwa dan fita daga falon,sai a lokacin kuma zezee ta lura da Ummul din, take duk wani farin ciki da take ciki ya gushe,fuskarta ta kwabe da wani irin bacin rai da tsana me tsanani ga Ummul ɗin,ja ta dinga yi da baya domin a yanzu kalaman cin mutuncinta sun kare akan Ummul din ,bata jin wata kalma zata goge bakin ciki da tsanar da take ji akan Ummul,tana kallosu kamar yadda ubanta yake kallonsu suka fice daga falon.

Da gudu ta koma dakinta tare da waɗawa saman gadonta tana ɓarkewa da kukan bakin ciki da takaici wanda ba zai taba kare mata ba in dai ba ganin bayan Ummul ta yi ba,ta kuwa sa dambar ganin bayan wannan fuskar da take ganin duk saboda ita ne Dr yake yi mata haka,ta daura aniyar sabauta rayuwar Ummul ta ko wace hanya koda kuwa za su yi mutuwar kasko.

Yaraf dan gaske ya koma ya zauna saman kujerar da tafi kusanci da shi,yana yi yana share gumi,kafin kuma kamar wanda aka tsikara yayi saurin mikewa tare da karasawa jikin window, budewa yayi yana kallon harabar gidan tare da motar Dr da ya ke ficewa daga gidan bayan baffa ya bude masa kofa,"shet ya fada yana cizon yatsa,ji yake kamar yabi bayansu dan shi Sam bai yarda da Dr Bilal akan Ummul ba,duk da cewa kuwa ya zo masa da magana me dadi akan zezee.

*****

A kunnen Mommy komai ya faru, itama dai a wannan lokacin ta ɗan fara zargin wani abu tsakanin Ummul da Dr Bilal,musamman ta yadda yake rungume da ita a jikinsa ba tare da ko dar ba, bare ya kawowa ransa cewa matar surukinsa ce,anya kuwa babu wani boyayyan Abu da su dukansu basu sani ba?babu tantama akwai ,sai dai ita bata da goyon bayan mijinta bare a ce zata taya shi yaki,haka bata fatan zezee ta auri Dr saboda tana da tabbacin baban zezee yana da manufa akan auren, kuma ba manufa ce ta alkhairi ba kamar yadda ta yi zato a baya,wanda shine dalilin da yasa take taya yar tata zumudin kasancewa matar Dr.

***

Sai da baffa ya ga fucewar Ummul da Dr daga gidan Sannan hankalinsa ya ɗan kwanta,duk da cewa har yanzu yana cike da tsoron Alhaji dan gaske da abinda zai yi musu ,muddin ya san cewa ba dashi aka daurawa Ummul aure ba,to amma dai ya fauwalawa Allah komai yasan yana tare dasu kuma zai kawo musu mafita cikin sauki kamar yadda suke rokonsa.

A bangaren yaran bely kuwa basu fuskanci komai ba,daga karshe ma tafiyarsu su kayi a cewarsu gobe da safen sa koma su jira fitowar Ummul din Dan su samu damar cika aikinsu.

*****

Gudu sosai yake falfalawa a saman kwaltar sai dai kuma tukuin cike yake da nutsuwa,baka jin sautin komai cikin motar sai saukar ajiyar zuciyar Ummul,wadda ke kwance luf cikin lumtsumemiyar kujerar bangaren me zaman banza,hannu yasa ya dan rage mata sanyin a c da kuma karfin airfreshner saboda matsalar asmarta,a hankali Bacci ya ɗan fara daukarta sama sama,tana yi tana buɗe ido kamar wadda take tsoron a saceta,ji ta yi ana bude gate,bayan hon din da ta saki,kafin kuma ya sulala motar zuwa cikin gidan, bai tsaya a ko ina ba sai cikin garejin motocin da suke jere reras kamar wanda suka zo Company itopias din gaba ɗaya,a dan zabure ta farka tana zare idanunta a cikin tafkekiyar harabar gidan da take haske yarwa inda fitilu kamar rana,fitowa yayi daga motar tare da zagayawa bangaren da take ya bude mata, ba tare da ya ce komai ba,a dan taorace ta kallesa Sannan ya kalli gidan tana cewa"gidanmu na ce ka kaini"juyawa yayi ya san kalli gidan kamar irin bai san gidan ba shima, Sannan ya dubeta da kallon da take jinsa har cikin kashin ta,like kallon gentle dinta,"kin gwada min gidan ne?"kasa kasa ta yi magana irin ta gunguni" hakan yasa ya ce"ko me zaki ce yanzu ba zan fita dan kaiki gida ba,ki fito muje,idan Allah ya kaimu safiya sai ki tafi"fitowa ta yi kamar gaske amma a maimakon ta bi bayansa sai kawai ta dau hanyar da taga sun shigo a nufinta zata tafi gida,bata ankara ba sai jinta ta yi asama kamar wata yar baby ya daga cak yana taku da ita a hannunsa kamar wanda ya dauki yar tsana......

Zahra ✍️

Ku yi hakuri idankunji rashin dadin pg din nan dan Alkur'an a kasuwa na yishi

N💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol