Free chapter · Read without an account

Pg31

by Fatima Yushau adam · GIDAN YAN KARYA

Duk yadda take jejjefa kafarta tare da kaimasa duka da kananun kuka ,amma hakan baisa ya sauketa ba har sai da ya Kaita can kuryar dakin da tunda take bata taɓa shiga me kyansa da tsaruwarsa ba,a saman gadon da yaji lafiyayyar shimfida ya direta yana mai jefa mata wani irin rikitaccen kallon da yasa ta yi gum da bakinta ba tare da shiryawa hakan ba, ƙasa ƙasa ta ci gaba da kukanta ,bai hanata ba sai ma shigewa da yayi wani dan daki wanda kofarsa ta yi kama da kofar drower kayan sawa,da sauri ta tashi zaune tana karewa dakin kallo'kafin ta ɗan tabe baki tana cewa"dan Allah duba daki kamar ba za a mutu ba,talakawa na can na shan wahala su kuma suna nan suna jin dadi idan sun fita suna yi mana kallon dai dai"idanunta ne suka kai kan wayoyinsa,take ta saki ajiyar zuciya tana mai jan jikinta zuwa inda wayoyin suke,duka wayoyin babu security ko daya, sosai hakan ya bata mamaki,wadda take ganin zata fi mata sauƙin sarrafawa ta ɗauka, ba tare da tunanin komai ba ta shiga loda nomber gentle ta fara kiransa,sai dai kash wayar a kashe take,bata yadda da hakan ba ta kuma kira ,har yanzu a kashe ake ce mata,zata kuma kira kenan ya fito daga wajen da ya shige tun dazun,kugunsa daure da karamin towel da alama shirin wanka yayi, Ummul ta na ganinsa ta mike tsaye akan gadon tana ihu hannunta saman fuskarta tana karewa,hakan da ta yi yasa shi fasa shiga toilet ya nufota kai tsaye ba tare da ta sani ba,saboda har yanzu tsalle take akan gadon tana kukan tashin hankalin ganinsa a haka,hannunta kare a saman fuskarta,yana zuwa ya haura saman gadon bai tsaya ɓata lokaci ba ya fincikota gaba ɗayanta,saboda yadda abin yazo mata a bazata yasa ta kuma rikicewa da ihun kuka,kuma rikitata yayi ta hanyar toshe mata baki da nasa bakin,ware idanunta ta yi sosai tana jin abin kamar a mafarki,fizge fizge ta shiga yi domin kwatar kanta sai dai a banza tun tana yi da kuzarinta har ya kai da ta yi lakwas bata iya motsi sai hawaye da yake zurarowa ta gefen idanunta,babu abinda take a cikin zuciyarta sai neman gafarar Ubangiji domin tasan ita me yawan saɓa masa ce a cikin wannan yan kwanakin,wanda ita kanta ta kasa gane abinda yasa hakan take yawan faruwa da ita,tunda yanzu ma ba dan ya kwatota a hannun wancan azzalumin ba da shima tuni yayi mata fiye da wannan abin da Dr yake mata,sai dai ta wani bangaren na zuciyarta ji take yana karfafata,ta wani sashe take ji ana fada mata kamar ba laifi take aikatawa ba,to amma ta yaya zai zama ba laifi ba?bayan daga ita har Dr da gentle din Musulmai ne kuma duka sun san cewa babu halacci a taɓa matar da ba muharramarka ba,amma me yasa suke mata haka?"bata da me bata amsar tambayoyinta banda ta ci gaba da zub da hawaye da neman gafarar Ubangiji a ranta.

Sai da yaji ta yi ladab Sannan ya zare harshensa daga bakinta,yana daga fuskarta tare da kallon idanunta da suke a rufe gam sai hawayenta da suke bin gefen idanunta,a hankali ya kai hannunsa ya shafo hawayen kafin ya kai bakinsa kan idanun yayi masa kyakkyawan sumbatar da ta jita har tsakiyar kanta,zamewa ta yi daga jikinsa tana cewa"duk abinda mutum yake yi dai Allah yana ganinsa,kuma duk abinda ka min ba zan taba yafewa ba har kab......wani irin fincika yayi mata tare da hade fuskarsu waje daya bakinsa daf da nata, yayin da tuni Ummul ta hadiye maganganunta sai idanunta da ta shiga rabawa tsakanin sama da kasa,dan ita kam ta dage ba zata kalli haram ba,namiji a tube gabanta dan rashin ta ido, wannan ai ɗebewar albarka ne,dumin bakinsa ta ji saman idanun yana sumbatar sa, kafin ya janye,yana cewa"karasa mana,ko na karasa miki?"ya fada yana shigar da hannayensa cikin jikinta,da sauri ta rike hannun idanunta na taruwa da kwalla har zata yi magana sai kuma ta fasa, a hankali ta zame daga rikon da yayi mata ta koma ta kwanta,irin kwanciyar nan ta babu yadda zanyi,dan ta haɗe jikinta guri daya ta wani dunkule,shi ma bai ce komai ba ya sauka daga gadon sai da ya gyara zaman towel dinsa Sannan ya shige toilet din,da harara ta karasa kana ta maida idonta ta kuma runtsewa a ranta tana cewa, "Allah ya kawo min bacci kafin ya fito dan nasan tsaf zai iya fitowa ba towel din, tunda na lura babu digon kunya a cikin idanunsa,yana Abu kamar ba zai aikata ba"ta karasa mitar tata a fili hadi da dan sakin karamin tsaki.

****

Alhaji dan gaske dai ya kasa samun sukuni a zuciyarsa akan tafiyar Dr da Ummul, ɓangare ɗaya kuma zuciyarsa na azalzalashi yana ci gaba da nazari akan maganar da yaronsa killer ya kawo masa,"kai ba zai yiwu ba dole na san matsayina a yau ba sai gobe ba"fita ya yi daga ɓangarensa, bai zame ko ina ba sai bakin gate dan karamin dakin da baffa yake kwana,kwankwasa kofar yayi tare da cewa"buzu fito ina son magana da kai"take cikin baffa ya murda,amma sai ya dake ya aro jarumta da karfin hali ya ɗorawa kansa, Sannan ya taho a nutse ya buɗe ƙofar,kallon tsaf ɗan gaske yayi masa, kafin ya nunasa da yatsa yana cewa"ka tabbata cewa kashinka ya bushe duk ranar da na gama bincike na kuma tabbatar da zargin da nake muku kai da wancan tsohon banzan,dan na fahimci cewa kun maidani wani sakarai kai kana tunanin kamar bazan aikata abin da nake fada ba,uhm ka saurari ranar da zan gane abinda kuke boye min".

daga haka ya tafi ya bar baffa tsaye ba tare da ya bashi damar kare kai ko wani hanzarin ba,ajiyar zuciya baffa ya sauke Sannan ya juya ya koma cikin dakin, dama yayi alwala dan haka sai kawai ya tayar da Sallah domin mikawa assamadu lam yalid walam yulad kukansa.

***

Zeezee na komawa daki,ta dauki wayar ta,tare da danna wasu nombobi,jim kadan aka daga,tsaki ta yi saboda jin Muryar wanda ta kira cikin maye,amma duk da haka sai ta daure ta fara magana cikin bacin ran da take ciki,"moses dan Allah ka wartsake daga wannan mayen,saboda ina bukatar magana da kai"Moses ya ce"haba zezee kin san dai ni duk irin hadin da zan yi wa kaina hakan baya sawa na kasa gane fari da baki dan haka fadi damuwarki kawai masoyiya yanzu zan cika ba tare da jinkiri ba"inda ace bata da bukata a wajensa da tuni ta kashe wayarta saboda kiranta da masoyiyarsa da yayi,,amma yanzu sai ta daure ta kai zuciyarta nesa saboda abinda yake gabanta yafi gaban duk wata damuwa da take da ita ko zata zo a nan gaba,"cikin kakkausan lafazi ta fara fada masa abinda take so ayi mata,tana kai aya ,ya ce"wannan karamin aiki ne a wajena in dai akanki ne dan haka ki sa ranki a inuwa ki zuba ido,ke dai kawai ki turo da hotonta yanzu "kashe wayar ta yi Sannan ya tura masa hoton Ummul,sai da ta tabbatar komai yayi dai-dai Sannan ta samu dan sauƙi sauƙi a ranta,har ta samu kwanta daniyar lalubo baccinta da ya gudu.

****

Ko da ya fito daga bath,kallo daya yayi mata ya dauke kansa, wannan dakin ya koma ya sanya kayan bacci danniya fito kamahinsa na kuma kama dakin kamar wani Company turare,a hankali ya karasa gaban gadon tare da sunkuyawa daidai kanta ya ɗan zuba mata ido na wasu mintina,kafin daga bisani ya gyara mata kwanciyarta saboda yadda ta takure, Sannan yaja tattausan blanket ya rufe ta, addu'a yayi mata ya tofa mata har jikinta, Sannan ya fice daga dakin, yana duba wayarsa inda yaga nomber gentle da Ummul ta kira a dazun,share nomber kawai yayi abinsa ba tare da ya tsananta bincike akanta ba.

*****

Duk lokacin da Dr ya fita sallar asuba baya dawowa Sai gari yayi haske,dan haka yau ma yau ma kamar koda yaushe zama yayi a masallacin,sai dai rabin hankalinsa yana kan Ummul da ya bari tana Sallah,dan tun wajen karfe hudu saura da ya dubata ya sameta akan sallaya tana sallah bai kara dubata ba,sai da zai fita Sallah ya ɗan leƙa ya ganta dai akan sallayar Sannan ya tafi.

Ummul kuwa tana sallame Sallah ta yi hanzarin mikewa ta fice daga dakin,dakyar ta iya gane hanyar da suka shigo,tana zuwa tayi Sa'a kofar falon a buɗe,dan haka ficewa kawai ta yi tana dan waige,bata ci karo da kowa ba har ta ƙarasa bakin gate,dakin me gadin ta duba taga yana Sallah dan haka ta yi wuf ta fice bayan ta cire ƙaton kwaɗon da ya garƙame karamar kofar dashi,tana jinsa yana ta uhm uhm uhm"amma bata kula shi ba ta fice da gudu,tana cewa"idan ka bata Sallahrka a kan abinda ba zai yiwu ba kai ka sani"hanya ta dauka duk da cewa bata gane kan anguwar ba,dan duk shiru irin na anguwar su zezee wannan tafi shi,dogon layi ne sosai shi yasa har ta fara gajiya da tafiya, gashi babu alamun ko babur din gida bare kuma na haya,sai ta ji ta fara dana sanin fitowa,tunani ta fara yi ko ta koma tunda duk irin doguwar tafiyar da ta yi har yanzu ta kasa cimma Babban titin da zata iya gane hanyar gida,dan tsayawa ta yi tana kallon babban layin da ya ke shimfide da kwalta da manyan gidajen da basu fi a kirga su ba,take wani irin tsoron da bata ji shi tun farkon fitiwarta ba ya mamayeta,juyawa ta yi tana kallo nisan tafiyar da ta yi wadda ta tabbata idan komawa zata yi sai ta gane kurenta.

Juyawar da zata yi taji ta yi karo da mutum,da sauri ta daga kanta dan ganin ko waye,sai dai ba ta gane kowa ba dan fuskarsa a rufe take , Sannan kato ne daga jikinsa hannunsa rike da wata yar jarka da wani abu kamar ruwa a cikinsa.

*****

Zuciyarsa ta kasa jurar zaman ba tare da ya san halin da Ummul take ciki ba,duk da cewa ko kadan bai taba kawowa ransa zata iya ficewa ta far gidan a irin wannan lokaci ba,duba da cewa bata san hanya ba, tashi yayi ba tare da ya karasa karatunsa na ranar ba,ya fito ya zura takalmansa ya nufi gidan, fuskarsa na boye damuwa da fargabar da yake ciki,a kofar gidan ya samu isa me gadi yana ta hangen hanya,yana ganin Dr ya ce"yauwa yallaɓai kai nake ta jira,saboda yarinyar nan fa ina Sallah kamar ita nake tunanin ta fita,tun da na idar kuma na fita na bi hanya amma ban sameta ba,shi yasa na dawo ina jiran zuwanka dan kayi saurin binta ko a mota ne dan nasan yanzu bata isa ta kai babban titin ba",ba tare da Dr Bilal ya ce masa komai ba ya shige gidan,sai da ya koma ciki ya dauko key din mota Sannan ya fito ya shiga motar tare da yi mata key,tuni isa ya bude masa gate Dan haka da gudu ya fice daga gidan yana kokarin daidaita nutsuwarsa kamar yadda ya saba.

******

Duk son Bacci irin bely amma yau da wuri ta farka ta kira yaranta,akan lallai su fara neman Ummul tana so su sake ta daga nan zuwa dare,hakan yasa suka bazama suka koma gidan Alh dan gaske suna jiran fitowar Ummul ɗin.

******

Alhaji dan gaske ma da asusubar fari ya samu sakon killer akan yana so ya sameshi a tsohon gida inda yake tsare da raliya,saboda akwai bayanan da zai bashi akan maganar aurensa da ikram da kuma raliya da har yanzu ta ki bude baki ta yi magana,dan haka jallabiya kawai ya sa ya fice,gari ko haske bai yi ba, Sallah ma ba dan killer ya tasheshi ba da ba zai yi ba sai rana ta fito.

*****

Bangaren Ummi kuwa tun asuba take kiran baffa akan ita fa ta kasa nutsuwa da inda yace mata Ummul take,duk da cewa tasan bata da matsala da hannun da take,to amma abinka da uwa zuciyarta ba abinda take sai saƙe saƙe,gashi yau su Safwan zasu koma makaranta tun jiya da dare suke mitar rashin dawowar Ummul din,har fitar su masallaci sai da suka leko suka yi mata magana,akan basa son tafiya basu ga Ummul din ba,kwantar musu da hankali ta yi akan in sha Allah idan bata dawo ba,ko sun tafi zasu yi waya dan su yi sallama,basu san ita kanta dauriya take yi ba.

******

Alhaji dan gaske yana zuwa kofar gidan ya tsaya bai fito daga cikin motarsa ba sai da ya fara kiran killer ya sanar masa cewa yazo,yana zaune killer ya fito ya bude masa kofar gidan,sai a sannan ya fito daga motar ya shiga gidan,killer ya maida kofar ya rufe,tun daga farfajiyar gidan yake jiyo sautin kukan raliya saboda yankan bayan da killer ya gama yi mata yanzu wai duk dan ta yi magana amma raliya ta ki yi,yana shiga ya kalli yadda take jin jiki ko ina a jikinta jini ne,hakan yasa ya dubi killer yana cewa"duk da wannan halin da take ciki bata fadi komai ba?"killer ya gyada kai yana janyowa Alhaji dan gasken, abin zama,sai da ya ga ya zauna Sannan ya bashi amsa da cewa"Alhaji wannan matar da kake gani na jima banga mace me shegen taurin kai da jarumta ba kamarta,duk wani kalar rashin imani na gwada mata amma taki bude baki ta yi magana,shi yasa kawai na ce kazo kaima ka gwada mata irin taka salon muguntar ko zata ji Uwar bari ta fadi gaskiya"kar ka damu killer yanzu muje ka fada min sakon da yasa ka kira Ni nan din,domin yafi damuna akan wannan, ita kuma wannan ka ci gaba da gana mata a zaba safe da dare ,sau daya zaka dinga bata abinci shima dan kar ta mutu ba tare da ta sanar dani Abinda nake so sani ba ne"daga haka suka fice daga ɗan dakin suka bar raliya na fidda numfashin wahala.

Suna fita suka samu waje daga can bakin hanyar fita daga gidan, Sannan killer ya dubi Alhaji dan gaske yana cewa"Alhaji na kammala ragowar aikina saboda na binciko maka yaron da aka daura auren dashi"wata irin mikewa dan gaske yayi yana zazzaro ido"kafin dakyar ya iya bude bakinsa ya ce"a ina yake? dan gidan uban waye? waye ubansa a garin nan?me yake takama dashi?hannu yasa a a lajihunsa ya dauko wayarsa tare da dannata ta Kawo haske, Sannan ya ce"na san zaka yi min wadannan tambayoyin shi yasa na samo maka hotonsa tare da dan karamin tarihinsa"killer ya fada yana mikawa Alhaji dan gaske wayar bayan ya fito da hoton saman screen din wayarsa,tun kafin Alhaji yasa hannu ya karba wayar jikinsa ya fara karkarwa idanunsa suka fara wani irin zugi kamar an zuba masa barkono,zuciyarsa kuwa sai wani irin tsalle take,haka nan ya tsinci kansa da fargabar ace gentle ne mijin Ummu wanda ya rasa dalilin hakan,yana karbar wayar ya kafawa hoton ido zuciyarsa na wani irin tsalle da daka kamar zata fado daga mazauninta ta fito...

******

"Yar kyakkyawa kin san me ye a cikin jarkar nan?"mutumin da Ummul ta ci karo dashi ya fara yana dago mata jarkar dake hannunsa,cike da tsananin tsoro Ummul take kallonsa tana girgiza kanta,murmushi me sauti yayi kafin ya kuma cewa"kin san asid?"daga masa kai ta yi alamun ta sani jikinta na daukar wani irin rawa idanunta kamar zasu fado saboda yadda ta firgito dasu jin sunan abinda ya ambata,"good girla amma dai na san baki taba ganinsa a zahiri ba ko?"da sauri ta gyada kanta tana dan fara ja da baya,shima takawa ya fara yi yana Binta a hankali Sannan ya ce"to wannan shine asid kuma an bani shine musamman saboda ke,dan an ce na watsa miki a fuska"hahh ta fada kamar irin zata shide din nan tare da sa hannu ta kare fuskarta,kirjinta na dukan tara tara saboda tsananin tsoro numfashinta har ya fara sarkewa,murmushi ya kuma saki yana cewa"ki kwantar da hankalinki ba yanzu zan watsa miki ba har sai na maida mugun yawu akanki,saboda ina ganinki naji kin tafi daniii"ya karasa maganar cikin irin Muryarsu ta mashaya yana wani langabar da kai,ai ko Ummul da gudu ta Shammace shi ta yi wani layi da yake cike da ci yayi kamar daji,bai yi wata wata ba yabi bayanta da nasa gudun da bai wani yi da yawa ba ya cimmata.

Dai-dai lokacin motar Dr ta kara so wajen har yayi gaba sai kuma ya dawo ya tsayar da motar tare da fitowa,hanyar ya shiga dubawa wanda yana cikin dube,dube ne yaci tuntube da takalmin Ummul din yashe a wajen, cikin faduwar gaba ya shiga bin layi kan da ido kafin a nutse ya fara bin hanyar da yaga alamun sahun kafafu,a daidai bakin layin ya kuma cin karo da warin dan kunnen Ummul din wanda hakan ya tabbatar masa da ba lafiya ba kuma tana a ta wajen nan,kutsa kai ya shiga yi da sauri yana ture dogayen reshunan da suka yiwa layin kawanya,yana tafiya yana duba hagunsa da damarsa,kamar daga sama yaji kukan Ummul tare da sheshshekar numfashin da kana ji kasan cewa ciwonta yana gab da tashi,da sauri ya shiga bin sahun inda ya ke jiyo sautin,

Abinda ya gani ne yayi matukar razana shi, wanda hakan sai da ya bayyana har akan miskilar fuskarsa da lokaci daya ta kuma hadewa tamkar hadarin gabas,cikin wani irin takun mazantaka kai kace zakin da ya kwana goma bai ci nama ba ne....

Na yi nan dan ba zan tsaya Dr Bilal ya hadiye Ni ba

Afuwan wallahi kwana biyu na yi busy da yawa shi yasa kuke cikin tsilla tsilla,amma ina sha Allah yanzu zamu ci gaba har Allah ya sa mu kammala lafiya

Sannan karku manta ban ce muku Dr fari ba ne,kawai dai kalarsa chaculate ne wato asalin kalar utopians People's Kala me kyau da tsada, duk wanda yasan kalar yan itopia to shine kalar Dr Bilal,

Zahra✍️ayi busy ne afuwan ba kullum ake kwana a Gado ba,😂😂

***

💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol