Free chapter · Read without an account
Pg32
"Kai kuma waye?" mutumin da yake tsaye akan Ummul ya fada yana kallon yanayin da Dr Bilal ya ke tunkaro shi a ciki,bai samu amsar tambayarsa ta baki ba sai ta hanyar wani irin kakkarfan naushin da sai da jini yayi masa tsartuwa ta hancinsa da baki Sannan ya zube a kasa, dan sam bai tsammanin yadda yake din nan wani zai iya yadda shi ta hanyar naushi ba,ganin Dr ya kuma yo kansa yasa shi saurin mikewa tare da ɗaukar jarkar asid dinsa yana cewa"idan ka sake ka tunkaro ni zan watsa mata asid din nan ne, idan kuma ka tsaya a inda kake,kai zan yiwa mummunar illa,dan haka sai ka zaɓa rayuwarka ko ta ta,duk da cewa ita aka bani kwangilar watsawa asid "da karfi Dr ya runtse idanunsa kafin a hankali ya kuma bude su tare da watsa su akan Ummul da take zaune a wajen tana raba idanunta a tsakaninsu,"is ok ka ajiye asid din sannan ka barta tafi,na fansheta da rayuwata"da sauri Ummul ta mike tsaye tana cewa"a'a kar ka yi min haka dan Allah ka tafi ka barni tunda koma meye ni na jawowa kaina,da ban fito daga gidan ba da komai bai faru ba,to amma yaza mu yi da kaddara wadda ta riga fata,tsananin tsoron sabawa Allah da tsoron karka min komai yasa na fito daga gidan,yanzu kuma akan laifina ka salwantar da taka RAYUWAR,akan me Zaka yi min sadaukarwa irin wannan bayan ban cancance ta ba?"kai kuna ɓata min lokaci fa, idan kina ganin baki cancanta da yayi sadaukarwa saboda ke ba to bari kawai na yi aikina kamar yadda aka umarceni"mutumin ya fada yana ƙoƙarin kwance murfin jarkar da asid din yake ciki,da sauri Dr Bilal ya koma bangaren da take tare da kareta yana cewa"noo ka dakata ka bani zabi na kuma zaba dan haka da zabina zaka yi amfani ba da maganar ta ba,ina fatan ka fahimta?"dariya mutumin ya shene da ita har yana nuna Dr da jarkar hannunsa Sannan ya ce"gaskiya wannan mutumin kana da karfin hali ,sai kace wani jinin sarauta, wato ko a cikin wane hali kake sai ka fadawa mutane maganar banza ko?to shike nan zan rabu da ita amma sai na fara hukunta ka akan laifin da ka yi min wanda tunda nake ba wanda ya taba nuna min ko yatsa ba tare da na dau mataki ba"ya karasa maganar yana ciro wata yar karamar wuka a gukunsa,sai sheki take kana ganinta kasan tasha washi,kallon wukar yake yana tunkaro Dr Bilal fuskarsa dauke da murmushin mugunta,sosai hantar cikin Ummul ta ke kadawa saboda tsananin tsoro da rashin hankali,gashi shi Dr din yaki yin wani motsi don kare kansa duk dan kar hakan ya jawowa Ummul matsala,hannu mutumin ya daga ya kaiwa dr suka da kakkaifar wukar,har wukar ta fara yamkar gefen cikin Dr kafin ya kai ga burma masa kamar yadda yayi niya, Ummul ta yi azamar dankar kasa a tafin hannunta ba tare da bata lokaci ba ta watsa masa saitin idanunsa wanda shine ya hanashi kaiwa ga kudurinsa na yiwa Dr mummunar suka da wannan wukar,yana cikin murza idanunsa Ummul ta kuma kama kafafunsa ta janyo su ya fadi kasa wanwar akan wannan jarkar asid din da ya fara budeta,sanadin faduwar da yayi akanta yasa murfin ya fice fit asid din ya zube a gadon bayan mutumin, take a wajen kuwa jikinsa yafara wani irin tururi hatta da kasar wajen zaɓalɓala ta dinga yi, Ummul na ganin haka ta yi saurin kama Dr da jiri ya ke kokarin yar dashi saboda jinin da yake zuba a jikinsa,suna jin ihun mutumin yana neman agaji Amma ina tuni Ummul ta taimaka masa ya shiga Mota, sai dai a inda a ke yinta bata iya mota ba,shi kuma a halin da yake ciki ba zai iya tukui ba,ganin yadda Ummul din ta bi ta rude ba abinda take sai kuka da kiran sunansa saboda yadda idanunsa suke budewa suna rufewa kamar wanda yake shirin shekawa lahira,kama hannunta yayi cikin tsananin dauriya ya ce",zan iya tukin amma sai kin daina kuka"to to ta fada tana saurin goge hawayen da suka yi caɓa caɓa a kyakkyawar fuskarta,dan kwalinta na cire ta daure masa ciwon, Sannan a hankali ta taimaka masa ya koma wajen zaman driver,saboda ita ya daure ya karfafa kansa ya tuka motar suka fara tafiya dan komawa gidan kasancewar yafi kusa akan su tafi asibiti,kuma ya karfafa mata gwiwa akan zai iya treatment din kansa tunda ciwon bai da girma.
***
"Alhaji lafiya dai ko?, naga ka shiga yanayi mara kyau da ganin hoton bayan kuma ni gani nake abin yazo da sauki saboda shi din ba kowa ba ne, me gyaran takalmi ne fa ,kaga kuwa a kwana ɗaya zamu iya yin maganinsa"da karfi Alhaji dan gaske ya shiga girgiza kansa yana cewa"killer kai ne kake ganin kamar abin akwai sauki,baka san jarumtar yaron nan ba, idanunsa ka dai abin tsoro ne bare kuma naushinsa mai dauke da kamshin mutuwa,ban san me yasa nake jin fargaba akan yaron nan ba,Amma ko ma meye ba za mu gagara samun mafita ba,amma yanzu matakin farko da zan dauka shine xan nunawa uban yarinyar kamar ban San komai ba,saboda ina so ya sakankance sosai,idan na yi hakan zan fi samun yadda nake so"daga nan ya tashi ya fice ko gabansa baya gani sosai,yana tafiya killer ya koma ciki a inda ya samu raliya sheme ta suma saboda tsananin wahala,tsallaketa yayi ya debo ruwa masu sanyi ya watsa mata,a firgice ta farka kamar zata shiɗe,dubanta yayi ya ce"ke kika sowa kanki wannan wahalar amma da kin bude baki kin fada mana wanda ya turoki da tuni na sake ki, kin yi tafiyarki"murmushin ƙarfin hali ta yi, Sannan ta ce"ko na fada muku gaskiya ba zaku barni ba dan haka na gwammace ku yi ta min azaba har na mutu idan yaso idan munje gaban wanda baya zalunci kuma ya hanashi a tsakanin bayinsa sai mu hadu mu yi bayani daga nan sai a yi mana hisabi kowa ya wuce inda sakamakon aikinsa ya bayar"wani fusataccen mari killer ya kai mata tare da haurinta da kafa yana cewa"to shike nan tunda haka kika zaba Amma ina mai tabbatar miki da cewa dole ko baki so ba wahala sai ta sa kin fadi wanda ya turo ki"wallahi ba zan fada ba,saboda wanda ya turoni wannan aikin yana da girman da zan iya sadaukar da rayuwata akansa"tsananin takaicin ta ne ya hanashi kara cewa komai,sai ficewa da yayi daga Akurkin dakin tare da rufeta, idanunsa ne suka kai kan wayar lariya da tun da ya kawota ya barta a kan kujerar dan karamin falon gidan,daukar wayar yayi yana jujjuyata ,kafin ya dan saki murmushi yana cewa"idan baki fada ba to wayarki zata fada"daga haka ya cusa wayar a aljihunsa ya fice daga gidan gaba daya bayan ya tabbatar yayi masa rufewar da babu wanda ya isa ya iya budewa idan ba shi da ya rufe ba.
****
Tun Moses na ihu har ya kai ga muryarsa ta dashe,yana kuma cikin wannan mummunan halin wayarsa dake yashe a wajen ta kama ring, da ido daya ya kalli fuskar wayar inda yaga sunan zezee wanda yayi mata saven da masoyiya,yana yawo a saman fuskar wayar,duk yadda moses yake jin tsananin radadi me shiga tsoka hakan bai hanashi jan ciki ya dauki wayar ba,da muryarta ya fara cin karo tana cewa"ya dai moses har yanzu baka cika aiki ba ne na jika shuru"?wata Irin ashariya ya lailayo mata kafin cikin azabar da yake ji ya ci gaba da cewa"Allah ya sine miki albarka zezee sai na ɗau fansa akanki,haka kawai ina zaman zama lafiya kik jawo ni cikin masifa ki jira waiwayowata gareki"daga haka tsananin azaba ta sashi sumewa a wajen.
***
Kaf unguwar nan sai da yaran bely suka karadeta Amma ko sahun Ummul ba su gani ba,ga azalzalar bely da ya hanasu sakat,daga karshe sai karya su kayi Mata akan sun kama Ummul din,saboda ta kyale su su sha iska, Sannan kuma ta tura musu kudi,dake sokuwa ce ba tare da tasa su sun bata wata hujja ta cewa sun kama Ummul din ba,ta tura musu kudi,da kuma address din inda zasu ajiye mata Ummul,su kuwa suna ganin kudi sun shigo suka kama sabgar gabansu.
*****
A hankali yake tuka motar saboda bashi da kuzari ajikinsa, Ummul kuwa ji take kamar ta cire ciwon ta dawo dashi jiki ta,ba dan komai yasa take jin hakan ba sai dan duk a sanadinta ya shiga wannan halin, ga wani irin mamakinsa da yake nukurkusarta saboda sadaukarwar da yayi mata,a ganinta bata da matsayin da zai sadaukar da rayuwarsa akanta,ita wacece dinsa?me ye matsayinta a wajensa?jin motar tana walagigi yasa ta saurin rikesa tare da fashewa da kukan da yake ta cin ranta,jan numfashi yayi kafin ya ce"kina so na kasa karasawa gida damu ne?"da sauri ta girgiza kanta tana toshe bakinta saboda kar kukan ya fito,a haka suka karaso gidan, da sauri me gadi ya bude kofa,tun kafin ya kai motar cikin gareji ya tsayar da ita tsakiyar gidan,da gudu Ummul ta fito tare da zagayowa bangaren da yake,tare da isa me gadi suka kaisa har cikin dakinsa na kasan gidan tunda ba zasu iya kaisa har saman ba,isa me gadi sai sannu yake masa,yana yi yana kallon Ummul da yake ji kamar ya tambayeta abinda ya faru tunda a iya saninsa oga nemanta ya fita sai kuma gashi an dawo dashi ranga ranga da jini ta ko ina a jikinsa,ganin babu dama dai yasa shi cewa"to Hajiya xan iya tafiya?"da hannu kawai ta nuna masa alama akan ya je,fita yayi yana maimaita kalmar sannu da Allah ya kiyaye,yana fita Ummul ta hau saman gadon tare da dago fuskarsa tana cewa"yanzu ya zan yi na taimaka maka?"hannunta ya kama ya dora akan rigarsa yana mata alama da ta cire masa,ba tare da musu ba ta shiga cire masa rigar, idanunsa da suke a lumshe ya bude ya zuba mata a yayin da take kwance kullin da tayi masa da dan kwalinta,dan dagowa ta yi saboda jin kallon da ta yi a jikinta, hada idon da suka yi yasa ta yi saurin maida kanta tana tattare rigar da duk ta ɓaci da jini,naked fatar jikinsa me kyau da sheik da ya baiyana ne yasa ta ɗan kawar da fuskarta a ranta tana cewa,Ni da nake gudun kallonsa ba riga gashi na jawowa kaina ma karshe ni zan cire rigar"tana gama cire masa ta ce"sai kuma me?"ta fada tana kara kawar da fuskarta, dan idan tana kallon jikinsa tsigar jikinta har mikewa take yi,"sai wanka ya fada yana sanya hannunsa a habarta tare da juyo fuskarta saitin tasa,da sauri ta rufe idanunta,tana jin wani irin yanayi me sanyi na shigar ta,cikin dan sanyi sanyi da tsitstsinka kalma ya ce"zaki goge min jinin jikina Sannan na yi dressin ciwon"gyada kanta ta yi kafin a hankali ta zame fuskarta daga rikon da yayi mata ta shi ya nufi toilet din,tana jin yadda idanunsa ke yawo a jikinta hakan yasa taji tafiyarta na hardewa kamar zata fadi,tsayawa ta yi cak, ba tare da ta juyo ba sannan cikin Muryar shugwaba kamar zata yi kuka ta ce"dan Allah ka daina kallona"tana jin lokacin da ya saki wani dan murmuahi ke sauti, wanda yasa ta ji kamar ta juya taga yadda murmushi yayi masa a fuskarsa,dan ita dan tun dake ta haduwa da shi bata taɓa ganin murmushinsa ba,da sauri ta kara gaba ta shige toilet din,ruwan dumi ta haɗa ta saka turaren wanka saboda kore karnin jini, Sannan ta dauki karamin bakin towel ta fice ,a ranta tana cewa"taya zan iya goge masa jiki?a sanyaye ta fito tana takowa gabansa kamar wadda kwai ya fashewa,a ranta kuwa nadama da neman gafarar Allah take,domin tasan wannan jarabawar da yake musu har da hukuncin saɓa masa da suke yi ta hanyar karya da abinda bai basu ba, sun kasa tsayawa a matsayinsu, kullum burinsu su hangi abinda Allah ya bawa wani su yi karya dashi,gashi yanzu abinda suke fata a ce suna dashi ya zama abin tsoro a gare su,dan yanzu tausayin Dr Bilal take ji musamman idan ta tuna hirar Abba dan gaske akansa, wannan ne yasa jikinta ya kuma yin sanyi da Al amarin kudi,a yanzu ta fi so Allah ya barsu cikin rufin asirinsu,tunda wani arzikin masifa ce,jin yana karbar ruwan daga hannunta ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta faɗa,dan ba ta san ta karaso gabansa ba.
A hankali ta haye saman gadon tana kokarin daidaita kanta daga bugun da zuciyarta yake yi,hannunta har rawa yake wajen tsoma shi cikin ruwan, ganin yadda hannunta yake rawa lokacin da zata dan matse towel din ya sashi rike hannun yana kallon cikin idanunta da ta kasa kallon nasa idanun,kafin cikin taushin murya ya ce"kawo na yi da kaina"sanin fada yayi kawai amma tasan ba zai iya ba,yasa ta yi saurin girgiza kanta tare da fara goge masa jikin musamman guraren da jinin yafi tabawa,tun tana yi a darare cikin tsoro tsoro har ta saki jikinta ta goge masa jikin tas, sai wajen yankan ya baiyana,ta yi mamakin ganin wajen ɗan kaɗan amma ya zubda wannan uban jinin,tabe baki ta yi tare da cewa abinka da renon madara kwanan ac dole jini yayi maka yawa"bata san maganar ta fito fili ba sai da ta ji yana cewa"renon madara ke kuma renon nono?"dan tura baki ta yi ba tare da ta ce komai ba,abin dressin ya nuna mata ta je ta dauko,a nutse ya dinga nuna mata yadda za ta wanke ciwon har zuwa kan Yadda zata rufeshi bayan ya sanya magani,ita kanta tsayawa ta yi tana kallon wajen tana mamakin wai ita ce ta yi,dubansa ta yi tare da cewa to kasha maganin sai na yi maka allura"sosai ya ware manyan idanunsa masu kyalli akan fuskarta ba tare da yace komai ba,tura dan karamin bakinta ta yi Sannan ya kuma cewa"to ba gashi na yi maka dressing ba ai shima allurar zan iya yi"ko ya fada yana janyota barin jikinsa inda babu ciwon da hannunsa guda,so ta yi ta janye amma ta kasa saboda ba karamin riko yayi mata ba,hakura ta yi da kokarin kwacewar sai dai jikinta bai daina karkarwa ba.
A hankali ya kai bakinsa saitin kunnenta ya ɗan hura mata iskar bakinsa, wanda hakan yasa jikinta ya kuma ɗaukar rawa,take idanunta suka tara kwalla har ta kai su da zubowa,hannunsa yasa ya tare hawayen tare da yin magana cikin kunnen ba tare da ya janye bakinsa ba,"are you scared me?"shuru ta yi ba tare da ta bashi amsa ba,shima bai jira cewar tata ba ya ci gaba da magana a nutse hucin bakinsa da yake fitarwa yana shiga kunnenta yana kara mata wani irin kasala,"kina jin tsoron wani abu a tare dani,becose kina tunanin zan cutar dake?no ni ba me cutarwa ba jefa waninki ma bare ke da kanki Ummul ikram,duk abinda zaki ga na yi miki akwai dalili,ko kin dauka ban san hukuncin Allah ba?dago fuskarta yayi yana kallon rufaffun idanunta tare da zagaye su da yatsun hannunsa Sannan a hankali ya ci gaba da cewa,"ina sane da duk abinda nake,"Ummul ni me tsantseni ne bana taɓa kayan da ba nawa ba"ya fada yana kara kusanta bakinsa da nata karamin lips din.
******
Sakalo zezee ta yi da waya a hannunta tana maimaita kalaman Moses a cikin kwakwalwarta zuwa kan fatar bakinta,to me yake nufi?fansar me zai dauka a kaina?rashin takamaiman amsa yasa ta dauki wayar ta kara kiransa ,sai dai har wayar ta yi ring dinta ta gama ba a daga ba,wurgi ta yi da wayar tana mai shiga cikin tashin hankali saboda tunanin da yazo ƙwaƙwalwarta akan ko an kamashi ne zai zubawa Ummul asid?sunturi ta shiga yi a dakin hankalinta a tashe,tabbas yan sanda ne suka kama moses shine yake son tona mata siri,komawa ta yi ta zauna tare da cewa"kai mutsiyacin talaka ne,Ni kuma ke arziki dan haka ba zan daga hankali na ba,tunda ina da maganin toshe duk wata matsala ko damuwa da ta tunkaro Ni"(ba dai ko wace damuwa ba Hajiya zezee Salisu dan gaske).
****
Mommy ma dai tata damuwar ta hanata sukuni, so take kawai ta tabbatar da inda raliya take,dan a yanzu ta fara kokonton tana hannun dan gaske,da ace tana hannunsa da tuni ta fadi sunanta, sannan da tuni ba wannan maganar ake ba,to idan bata hannunsa tana wajen waye?kuma me ya hanata kiranta a waya?tabbas ba lafiya ba?raliya bata lafiya"ta fada a fili tana daukar wayarta da tunanin sake gwada kiran raliyar,sai dai kamar ko yaushe wata zuciyar ta kwabeta da yin kiran, wanda hakan yasa ta yi wurgi da wayar tana fashewa da kuka tare da fatan alkhairi ga yar uwarta.
****
Alhaji dan gaske yana zuwa gida,tun kafin baffa ya gama bude masa gate,Kiran killer ya sake shigo masa,daga wayar yayi bayan ya cusa hancin motarsa zuwa cikin farfajiyar gidan,tare da sanyata a amsa kuwa"ina jinka killer"Alhaji ya fada yana kashe motar bayan yayi mata matsuguni a cikin garejin motar,ba tare da ya fito ba ya ci gaba da sauraron killer da yake masa bayanin wayar raliya da ya kai aka fara bincika masa masu kira ko za a samu kiran wanda ya turota leƙen asirin,jinjina Alhaji dan gaske yayiwa killer tare da cewa"aikinka yana kyau killer Ina alfahari da kai ka cigaba da kokari ,da zarar na samu Abinda nake so zan yi maka sallama me kyau ta yadda za kayi bankwana da talauci har jikokinka"Alhaji bai tsaya ya gama sauraren kirarin da killer yake zuba masa ba ya kashe wayar,tare da fitowa daga motar ya nufi cikin gidan.
******
A hankali ya sumbaci bakinnata wanda hakan yasa ta saurin bude idanunta da suka dira akan fuskarsa me cike da kwarjini,dage mata gira yayi kafin ya yi mata tambayar da ta sanya ta zuba masa ido tana kallon tsananin kama da kamanceceniyar da yake mata da wanda ya tambaya din,"waye gentle?"tambayar da yayi mata kenan ta tsaya tana yi masa kallon kwakwaf ,hure mata idon yayi tare da kawar da fuskarsa,"wani mutum ne na musamman a cikin rayuwata"ta fada ba tare da ita kanta tasan lokacin da furucin ya kwace mata ba,cikin wani irin slow motion Dr Bilal ya juyo da kansa saitin fuskar Ummul ikram,kafin cikin wani irin zafin nama me tafe da yanayinsa na natsuwa ya hade bakinsa da nata,wanda hakan yasa ta jan wani irin dogon numfashi kamar wadda take shirin shidewa......
Zahra✍️***
💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕
By
FATIMA Y ADAM......
Littattafan marubuciyar.
KUDIRAR ALLAH
KADDARATA SANADIN HASKE
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
ƳAR GIDAN YARBAWA
MATAR ƊAN BIRNI
And
GIDAN ƳAN ƘARYA....