Free chapter · Read without an account

Pg33

by Fatima Yushau adam · GIDAN YAN KARYA

Duk da cewa zuciyar Ummul cike tare taf da wani irin tsoro amma hakan bai sa ta hana shi abinda yake yi ba,kalamansa na dazu su suke ta yawo a tsakar kanta,ta rasa dalilin da yasa suka zauna a ranta kuma har take amfani da su wajen hakuri da sake masa ragamar gangar jikinta,sai da ya gamsu da kansa Sannan ya sake bakinta yana binta da wani nutsetstsen kallo,dan mutsu mutsu ta shiga yi saboda yadda take jin wani iri idan gangar jikinsu suka hadu,kasancewar shi jikinsa babu kaya,ga kuma yunwar da take cin hanjin cikinta,dafe cikinta ta yi tana yatsuna fuska,"uhm kina jin yunwa ko?"ya tambayeta yana shafa cikinta,cikin sauri ta ɗora nata hannun a kan nasa da yake shafa shafaffen cikinta, Sannan cikin don fashewa da kuka ta ce "yunwa nake ji cikina kamar zai fashe saboda yunwa"dubanta yayi cike da mamakin kuruciyarta dama ba sai an koshi ne ake cewa ciki zai fashe ba?shi dai bai taba jin wannan kalmar a mazaunin yunwa ba,sai yau a bakinta,dauke idanunsa yayi daga kanta,tare da janyo wayarsa guda,ya saka kira,jim kadan aka aka daga magana yayi cikin yarensu na itopian na kusan minti ɗaya daga nan ya ajiye wayar tare da gyara kwanciyarsa ta hanyar juyowa bangaren da Ummul take,sai da ya dago kanta tare da sumbatar goshinta, Sannan ya ce "yanzu za a kawo abinci ki ci kar cikinki ya fashe dan naga ya dau hanya,a hankali ya sa hannunta a tsakaninsu tana karewa saboda ganin yadda numfashin su yake sarkewa gangar jikinsu na daf da hadewa,hannu yasa yana tattare gashin kanta da duk ya hargitse saboda rashin dankwali,a nan ta samu dama ta lallaba a hankali ta dauki wayarsa tare da juya masa baya,a tunaninta na kuruciya bai ganta ba,da sauri ta shiga loda nomber gentle tana fata a karo na biyu ya dauki wayar,sai dai kuma tana danna kiran taji Dr Bilal yana matsowa bayanta,wanda hakan yasa hannunta ya shiga karkarwa ta kasa katabus bare har ta kai wayar kunnenta,a nutse ya ci gaba da matseta har sai da ya zama ya manne gangar jikinsa da bayanta tare da sanya hannunwansa ya yi mata zobe kansa a kafadarta yana cewa"wa kike son kira?"wayar ce ta subce a hannunta tana kasa cewa komai,saboda yadda jikinta yayi wani irin sanyi tsigar jikinta har wani yar take yi.

"No answer"?ya fada yana goga fuskarsa dake cike da kwantanciyar kasumba a gefen tata fuskar,kokarin juyowa ta fara yi dan aganinta hakan zai rage mata abinda take ji a cikin kashi da bargonta,wani irin numfashi ya kuma sake mata a kunnenta saboda yadda take kokarin sauya masa lissafi da wannan kici kicin juyowar da take yi ajikinsa,tana juyowa suka fuskanci juna tare da hadewar kirjinansu waje daya,wanda hakan yasa Dr Bilal sakin wani irin numfashi me huci saboda yadda yake jin tudun kirjinta a nasa kirjin,to itama sai a nan ta gane wautarta na fuskantar tasa, dan haka sai ta yi saurin sanya hannunta dan raba tsakaninsu,tana mai rufe idanunta jikinta na karbar sakon kallon da yake neman haukata karamin lissafinta,hannu yasa ya janye hannunta da ta raba tsakaninsu yana mai kuma shigar da ita jikinsa, Sannan a miskilance ya bude baki zai yi magana,hasken wayarsa ne ya dakatar da shi daga abinda yake niyar fada mata,hannu yasa ya dauki wayar tare da karata a kunnensa,har mai maganar ya gama magana bai ce komai ba,jim kadan ya kashe wayar, Sannan ya fara kokarin tashi, Sam ya manta da ciwon jikinsa wanda hakan yasa ya fama ciwon sosai,da sauri ya koma yana cewa "ash"tare da dan rufe idanunsa,kama shi ta yi tana masa sannu idanunta har ya cika da kwalla,hannu yasa ya dangwalo hawayen da yatsansa yana cewa"haka hawayenki suke da arha kamar ledar purewater?"bai saurari abinda zata ce ba ya yunkuri cike da jarumta kamar ba wani abu wai shi ciwo a gefen cikinsa,tana kallon shi ya kama hanya ya fice ba tare da ya sa komai a jikinsa ba,tashi ta yi tabi bayansa tana cewa"ka dawo ka sa wani abu ka rufe jikinka, kai baka jin kunyar yawo ba kaya n.....maganar ta ce ta tsaya a makoshinta yayin da ta yi arba da kyakkyawar matar da take zaune a kan kujerar gefen wadda Dr Ya zauna tana ta murmushi ,da gudu Ummul ta koma dakin tana haki,zama ta yi a gefen gadon tana tunanin abinda ya faru tsakaninta da wannan matar da take zaune a falo wadda kana ganinta kaga yar uwa ta jini ga Dr Bilal.

Br Sarah cikin murmushi ta dubi Dr Bilal da idanunsa suke kan hanyar dakin da Ummul ta shiga,ta ce"yaya ina ga fa Ummul ta tsorata da ganina da alama sai na je na cire mata wannan tsoron"dan tsaki yayi Sannan ya dago jikinsa dake kwance cikin kujerar yana bude kulolin da br Sarah tazo dasu,sai da ya bude ya rufe Sannan ba tare da ya kalleta ba,ya ce"shegiyar karyarta ita ta ja mata",jinjina kai Dr sarah ta yi tare da cewa "haka ne yaya kasan wani lokaci zakai ta yiwa Allah laifi hankalinka kwance saboda kana ganin wannan laifin kamar ba komai ba ne saboda kana ganinsa a karamin laifin da bashi da zunibi amma idan Allah ya tashi yi maka hukunci sai yayi maka hukuncin da kai kanka zaka gane cewa duk kankantar sabon Allah to sabo ne kuma Allah yana hukunta bayinsa akan duk wani saba masa da yayi in dai ba ya tuba ya nemi gafarar Ubangiji ba ne,kuma duk kankantar sabon Allah akwai lokacin da zai bibiye ka ko da na wani dan lokaci ne dan ya zama izna gare ka da kuma masu koyi da wannan laifinnaka,duk da cewa lamarin Ummul da akwai kuruciya amma ai tana da ilmin addini,dan haka yanzu zan je na cire mata tsoron haduwa dani"ta fada tana mikewa dan zuwa dakin da Ummul ta shige ta shige,dakatar da ita yayi ta hanyar mikewa yana cewa"zaki kuma tsoratata bari na fito miki da ita nan ɗin "komawa ta yi ta zauna tana kuma sakin murmushi saboda tunawa da haduwar ta su da Ummul shugaban ƙaryata ta africa gaba ɗaya.

*******

Alhaji dan gaske bai dade da shigowa ba,baba me gadi ya zo ya karbi aiki a hannun baffa dan haka suna yin handing over ya tattara yan komatsansa da abinda yake bukata ya tafi gida,ko da ya je gida dakyar ummi ta barshi yasha ruwa saboda zumudin jin halin da Ummul dinta take ciki,cewa"yayi bari dai na kira kiji da kunnenki tunda duk abinda zan fada miki ba zaki yarda ba dan na fahimci cewa gani kike kamar za a cutar da Ummul da hadin bakina"a'a fa baffan Hamza kar ka yi min gurguwar fahimta kai ma kasan babu yadda za a yi na yi maka wannan tunanin ko da ace ba kai ne uban Ummul ba,bare kuma kai ne mahaifinta dan haka babu ta yadda za a yi na ce zaka cutar da yarka ta cikinka"wayar sa ya fara dannawa yana cewa"ato ai wannan tashin hankalin da kike nunawa dole ki sani cikin zargi"to ka yi hakuri ba sai ka kira su ba"wannan kuma daga baya ne"ya fada bayan da wayar ta fara ring sai dai kuma har ya tsinke ba a daga ba,ajiye wayar yayi yana cewa"idan yaga kiran na san zai biyo ba zan takura masa da kira ba saboda yata tana hannunsa"Ita dai Ummu tunda.ta fahimci cewa.baffan kamar a tunzure yake bata kuma magana ba.

Haka su Safwan suka yi shiri suka tafi ba tare da sun yi sallama da Ummul ba kamar yadda suka so,sai dai Ummu ta karfafa musu gwiwa akan cewa da Ummul din ta dawo zata hada su a waya komai dare kuwa,da wannan suka dan samu kwarin gwiwa suka tafi,iyayensu na sanya musu albarka,haka suka bar Ali da mufty cikin kewa.

*****

Tun bayan dawowarsa yake zaune a falon yana tufkawa da warwarewa akan ta inda zai fara,wani abu da ya tuna ne yasa shi dafe kansa tare da fadin "kash anya kuwa ban yi kuskuren barin Dr Bilal da ikram ba?anya yarinyar nan ba zata fada masa abinda nake shirya wa akansa ba?tashi yayi tsaye hankalinsa na son tashi,musamman da ya tuna cewa bai yiwa Ummul barazana ko ya kwabeta akan maganar ba,tabbas dole ya yi magana da Ummul tun kafin lamarin ya kwaɓe masa,wayarsa ya dauka ya shiga kiran baffa, baffa kuwa yana ganin kiran Alhaji dan gaske ya samu faduwar gaba,dan yanzu idan da akwai abinda yake tsoron ji da gani to Alhaji dan gaske ne,da kamar ba zai dauki wayar ba,to amma da yayi wani tunani sai kawai ya dauka tare da dauke numfashi gudun kar Alhaji ya gane halin da yake ciki,"ina ikram take maza hadani da ita a waya akwai maganar da zan yi da ita"take baffa ya shiga wata sabuwar fargaba da tashin hankalin har gumi ya fara wanke masa fuska,sai kawai ya ji Muryar Ummi tana cewa"wai dan Allah muftahu ba zaka zo ka bi min yarinyar nan ba,tun dazu fa ta ce mun zata je gidan su A'isha ta dawo amma har yanzu bata dawo ba"wata yar boyayyiyar ajiyar zuciya baffa ya sauke Sannan ya ce da Alhaji dan gaske "kaji ma ashe bata nan ta je gidansu kawarta A'isha amma yanzu zanje da kaina na kirata sai na bata wayar"take Alhaji dan gaske ya gasgata maganar baffa saboda yaji lokacin da ummi take mitar rashin dawowar Ummul din daga can nesa dan ga dukkan alamu bata kusa da baffan ma, wannan shine ya sashi yarda da abinda baffan ya fada, sai dai kafin ya kashe wayar sai da ya jawa baffa kunne akan cewa shifa baya son ana barin matarsa tana yawo ko da yaushe kamar da ba tare da an nemi izninsa ba,"za a kiyaye in sha Allah" abinda baffa ya fada kenan yana ajiye wayar jin Alhaji shima ya katse.

"Allah yayi miki albarka ummin ikram"da Amin ta amsa, tana mai ci gaba da yan aikace aikacenta na dora sanwar rana kasancewar rana ta fara dagawa.baffa kuma ta barshi da tunanin yadda zai yi ya haɗa Ummul da Alhaji dan gaske a waya.

*****

Tana zaune a bakin gadon hankali ta she,taji an turo kofar dakin an shigo,da sauri ta mike tsaye tana kallonsa idanunta cike da hawaye,karasowa yayi ya kama hannunta tare da zaunar da ita a bakin gadon, Sannan shima ya zauna yana duban fuskarta da take a dame,kafin cikin tsukakkiyar fuskarsa da baya fara a ko murmushi murya a miskile ya ce"me ya haɗaki da br Sarah?"wacece ita a wajenka"ta dawo masa da tambaya a maimakon ta amsa masa tasa tambayar?"zuba mata ido yayi fuskar nan a kimtse,hakan yasa ta fara magana cikin in ina,"Ni ni wal Wallahi ban yi mata komai ba,kawai fa mun hadu a wani store ne shine ta min kyauta na ce bana so nafi karfin a yi min kyauta"girgiza kai yayi yana dan fesar da huci ta bakinsa,tare da hade hannunwansa guri daya yana murzawa kamar wanda yake alwala, Sannan cikin dakakkiyar muryarsa ya ce"bana fahimtar komai dan haka ki min bayani ta yadda zan gane",gyada kanta ta yi tana gyara zamanta ta hanyar matsawa daga kusa dashi, Sannan ta fara da cewa"wata rana ne da na shiga wellcare zan yiwa Aumty zeezee siyayya,shine na hadu da ita a wajen daukar brosh,shine tana ganina ta ce wai na burgeta tana sona za ta yiwa yayanta kamu na tunda ita ba namiji ba ce,kuma in dauki duk abinda nake so zata biya,Ni kuma shine na yi zaton ko irin mu ce yan karya so take kawai ta yi min burga, dan haka sai nace mata ta barshi na wuce ta yi min kyauta ina matsayin yar gidan Alhaji Ahmed dan itopia sai dai na yi mata,shine ta ce to ita tana bukata,"dan shiru ta yi tana murza yatsun hannunta,jin bai ce komai ba yasa ta ci gaba da cewa"a nan dai ta dinga dibar abubuwa kamar wanda zata siye shagon,da naga bata da niyar bari sai kawai na gudu na biya kudin kayan aunty zezee na yi tafiyata, ban san ya ta yi ba, dan ban kuma haduwa da ita ba sai yanzu da na ganta a falonka"ta karasa maganar cikin hawaye tana cewa"dan Allah ya kuke da ita?"kanwata ce ita ce take bina"na shiga uku yanzu zata ce sai na biya kudin da nasa ta kashe kuma wallahi kayan da yawa ba zan iya biyan ko da rabi ba,kuma nasan zata buge Ni saboda na yi karya da babanta"maƙe kafada yayi irin babu ruwansa ɗin nan,tare da tashi tsaye yana cewa"makaryaciya kawai"fita yayi yana cewa "bari na turota dakin tun....ji yayi ta kama shi ta baya da karfi tana boye fuskarta a bayansa,abin sai ya bawa Dr Sarah da ta tashi tsaye tana kallonsu dariya,kai tsaye ta nufesu, aiko Ummul na ganin haka ta kuma kamkame shi tana cewa"dan Allah yaya Dr ka ce ta yi hakuri wallahi yanzu na tuba na daina kuma ba zan sake ba har gaban abada"ina ne gaban abada?"Dr Sarah ta tambaye ta tana ci gaba da dariyarta,gaba daya Ummul ta kasa natsuwa har sai da Dr ya daka mata tsawa Sannan ta yi luf a bayansa tana sakin ajiyar zuciya.

A nutse dr Sarah ta karaso wajensu ta kama hannun Ummul din tana cewa"ki kwantar da hankalinki babu abinda zan yi miki gashi nan yunwa aka ce kina ji shine na kawo miki irin abincin mu na yan gayu"a hankali Ummul ta dago kanta tare da cewa"da gaske kike kin yafe min"?gyada kai Br Sarah ta yi "tana cewa har gaban amada"ajiyar zuciya Ummul ta saki tare da zama a kujerar da br sarah ta zaunar da ita,da kanta ta zuba mata Farfesun naman rago da chips da yaji kwai da sos ,Sai shayin da ta haɗa mata mai rai da motsi ta tura mata gabanta tana cewa,"maza ki ci ki koshi na kaiki gida"ai Ummul ta na jin maganar gida ta fara dibar gara,sai dai duk yadda taso da ta ci da yawa abin ya gagara saboda cikinta ya gushe,kuma dama can cikin Ummul baya daukar abinci me yawa,kyale ta dr Sarah ta yi, sai dai tana zubawa Dr ta bar ragowar a kulolin da niyar idan ta kai Ummul din sai ta bata ta sake ci zuwa anjima,ko rashin cin nata yana da nasaba da jin nauyinta da ta lura Ummul din nayi,ganin yadda Ummul din ta kagu da su tafi.yasa itama br Sarah bata tsaya ja mata rai ba suka fice batare da ko sallama ta yiwa Dr ba.

*****

Alhaji dan gaske sauya tunani yayi akan yake da kansa ido da ido su yi magana da Ummul dan haka wanka kawai yayi ya nufo gidansu Ummul,dan baya jin zai.iya nutsuwa ba tare da yaga Ummul ya ja mata kunne ba,duk da cewa ko a yanzun bashi da tabbacin bata sana'ar da kowa maganar ba.

Daidai lokacin da ya karaso kofar gidan, a daidai wannan lokacin ne br Sarah ta ajiye Ummul a kofar gidan,bata shiga gidan ba duk da yadda Ummul ta so ta shigan, kulalolin kawai ta dauki daga bayan mota ya mikawa Ummul din tana jaddada mata da ta tabbatar zuwa an jima taci abincin,karba Ummul ta yi tare da yin godiya a gefe daya tana mamakin kirki irin na br,Ashe dama akwai masu kudi masu mutunci da sanin darajar dan Adam?ashe halin su zezee da ubanta da kuma wasu tsirarin masu kuɗi da ta sani ne yasa take musu kallo daya,sai da br ta bar layin tana daga mata hannu Sannan ya juya zata shige gida,idanunta akan wajen zaman gentle da ta ke cike da mamakinsa na rashin neman ta da bai yi ba har yanzu, ko da yake ta bar wayarta a dakinta na gidan Alhaji dan gaske dan haka ba zata yi saurin yanke masa hukumci akan cewa bai neme ta ba,tunda a iya saninta babu wanda ya san inda take.

***

A bangaren Alhaji dan gaske kuwa, wani irin mugun shock ya shiga saboda ganin Ummul tare da br Sarah,abinda yaso rikita masa ƙwaƙwalwa kenan, abinda ya kasa fahimta har yanzu shine, a salin alakar Ummul da Dr Bilal,bayan gashi an tabbatar masa alakar Ummul din da gentle,wai me yasa yake son shiga rudu ne, wannan Al amarin fa dole da akwai ayar tambaya akansa,ganin Ummul na shirin shiga gida yasa shi saurin ɓalle murfin motar ya fita, Ummul na shirin saka kafarta a cikin zauren gidansu ta ji an rufe mata baki tare da ciccibarta an sanya ta a mota,da sauri ya rufe motar tare da zagayawa bangaren sa ya shiga yaja motar da gudu ya bar layin,duk kuka da ihun da Ummul take babu me jinta saboda glass din motar ,shi yasa Alhaji dan gaske bai yi amfani da komai ba wajen rufe mata baki,tsawa ya daka mata yana cewa "ki min shiru,ni ba wani abu zan miki ba ka wai dai zan kai ki inda zaki amsa min tarin tambayoyin da suke cin raina,idan kuma kika ci gaba da yi min ihu wallahi ba zan dawo dake ba har abada kin yi bankwana da kowa na ki maciya amana kawai"dif Ummul ta yi sai jan shashshekar kuka da take tana dauke ajiyar tashin hankalin da yake ta ruskarta daya bayan daya daga wannan sai wannan,sai da suka yi tafiya me nisa har sun fara dosar barin gari Daga can bangaren rijiyar zaki wajen dan ta iya, Sannan ya ja yayi burki da karfi har sai da Ummul ta frirgita,

Juyowa yayi yana fuskantarta tare da sanya mata bindiga a saitin kanta,wani irin tsoro ne ya kuma shigar Ummul,dan hatta da dan yatsanta karkarwa suke yi,cikin wata irin gigitacciyar tsawa Alhaji dan gaske ya ce" ke idan har baki fada min gaskiya ba to wallahi sai na fasa kokon kanki da wannan bindigar,dan haka yanzu xan yi miki tambaya ta farko idan kun amsa ta daidai jin haye idan aka samu sabani kin mutu.........

Zahra✍️***

GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol