Free chapter · Read without an account
Pg35
Yana zuwa bakin gate din ya kira Alhaji dan gaske a waya,yana fitowa ya miƙa masa wannan abun,yana bashi ya juya yayi tafiyarsa,shima Alhaji dan gasken komawa yayi cikin gida,tare da rufe kansa a daki, Sannan ya dauki wannan abun recording din ya jona a jikin computer tare da saita komai, komawa yayi ya jingina yana sauraron tattaunawar Ummul da gentle,zuciyarsa banda ƙuna babu abinda take yi ,domin duk wata kalma da take fitowa daga bakin gentle jin ta yake kamar zubar ruwan dalma a kahon zuciyarsa,maganar tana karewa recording din ya tsayar da kansa.
Mikewa yayi yana zagaye dakin, kafin cikin daga murya ya ce "wato ko wace irin kalar azaba za a ayi maka ba zaka rabu da ita ba?to lallai zaka san da wa kake yi"daga haka ya dauki wayarsa ya kira killer,killer yana daga wayar Alhaji dan gaske ya fara magana da cewa"killer a yau nake so ka dauko min wannan karamin matsiyacin ka tabbatar da cewa ya kwana cikin ukubar da zai gwammace bai taba sanin ikram ba,in so kafin wayewar gari ya fara danasanin sanin Ikram a rayuwarsa",an gama yallaɓai baka da matsala in dai nine zan cika umarnin ka ba tare da an samu matsala ba."
Kashe wayar yayi ya koma ya zauna yana ƙulla yadda zai yi a gobe a Daura auren zezee da Dr Bilal.
****
Ko da Ummul ta koma gida samun kanta ta yi da kasa ci gaba da tunanin da yake neman zautata, saboda kalaman gentle,to amma fa duk da haka ta wani ɓangaren tunanin gentle din da kuma Dr Bilal ya kasa barinta ƙwaƙwalwarta.
Killer suna gama waya da Alhaji dan gaske, ya bar raliya tare da yaransa guda biyu,shi kuma ya debi yara biyu suka fita neman gentle.
Unguwarsu Ummul suka fara zuwa daidai wajen da gentle yake zama, kasancewar dare ya ɗan fara yi shi yasa anguwar ta yi shiru kamar babu wani dan Adam dake rayuwa a cikinta,guri suka samu suka yi fakin motarsu tare da kashe ta gaba ɗaya,daga nan suka fara irga sakanni zuwa mintina zuwa awannin da gari zai waye suka ga ta inda gentle zai ɓullo.
*****
Tunda suka kwantar da mota bacci ya sace su ba su bude idanunsu ba sai karfe takwas na safiya,take killer ya fara baza ido a wajen zaman gentle sai dai babu shi babu dalilinsa,da sauri ya juya inda yaransa suke yana cewa dasu "maza ku fita ku dinga zagaya layin nan kamar sauran mutanen anguwa,kowa na tura masa hoton yaron, dan haka da kun ganshi ku yi kirana ni kuma zan zo da mota wajen tare da wannan kyallen da za a sa masa a fuska,amma ku tabbatar da cewa shine kafin ku kira ni"yes oga" suka fada tare da ficewa daga motar suna mai gyara shigarsu duk dan su saje da Al ummar gari masu mutunci.
Har misalin ƙarfe goma gentle bai zo wajen aikinsa ba,bare su killer su kama shi,gashi kuma Alhaji dan gaske ya matukar daga musu hankali akan lallai dole su nemo shi a duk inda yake a fadin duniyar nan, wannan ne yasa suka kuma dagewa wajen binciken anguwar da wajen anguwar dan neman killer.
A bangaren Alhaji dan gaske kuma, tun da sanyin safiyar ya shirya yayiwa gidan Alhaji dan gaske dirar mikiya,a inda yayi gurfane a gabansa yana ladabin da ya saba, kai ka ce ba shi ne wannan makirin mutumin ba,a inda ya dinga kawo masa kauli da baadin hujojinsa da yasa yake so a Daura auren zezee da Dr Bilal a gobe,kai tsaye Alhaji Ahmed ya amince da bukatar dan gaske, wanda hakan ya sanya Alhaji dan gaske farinciki mara adadi, Sannan ya rage masa kuncin rashin auren Ummul,yana barin wajen Alhaji Ahmed kai tsaye office ya wuce dan fara shirye shiryen daurin auren da sauran mutanensa.
****
Alhaji Ahmed da kansa ya kira Dr Bilal a waya ya sanar dashi yadda su kayi da Alhaji dan gaske,Dr Bilal bai yiwa mahaifinsa musu ba ya amsa da cewa "Allah ya nuna mana goben dama nima na gama nawa shirin",suna gama wayar da baban ya fice daga ofishin yana sanya abin magana a kunnensa da alama wata magana ce me muhimmanci ta fitar da shi daga asibitin, dan yana fitowa mota ya shiga ya fice daga asibitin gaba daya.
Karfe uku na rana, killer suka kuma zagayowa kofar gidansu Ummul,a inda suka taki Sa'a, suka ga gentle zaune a kan ɗan dutsen da ya ke zama yana wankin takalmi kansa a kasa kamar kullum rabin fuskarsa a rufe da p.cap,duban juna killer da yaransa su kayi tare da sakin murmushin samun nasara,dan sun san yau ko banza zasu sha kaya masu tsada su shiga manyan hotels masu tsada.
ba tare da gentle ya Ankara ba su killer suka mamaye shi tare da sanya masa farin kyalle a fuskarsa, wanda hakan ya taimaka musu wajen sanya shi a motar da suka kawota gab da shi ba tare da kowa ya kula ba,wucewar motar kawai Ummul da ta kawo kai wajen ta gani.
bin ƙurar motar da ido ta yi hankalinta na son ta shi, Amma dan tabbatar da abinda take zargi sai ta juya ta kalli wajen zaman gentle, sai taga komai a hargitse dan hatta da takalman da yake wankewa a yashe suke a wajen,kai kana gani kasan cewa tashin da yayi ba na shiri ba ne,hannu ta ɗora a kanta kamar zata kurma ihu, sai kuma ta koma cikin gidan da gudu tana ƙwallawa Ummi kira,cikin sauri Ummi ta fito daga daki zanin ta har neman kuncewa yake saboda yadda kiran da Ummul take kwala mata ya kidimata,da gudu Ummul ta rike Ummi tana nuna mata hanyar waje, hakan sai ya kuma gigita ummin ta shiga tambayarta,"lafiya me kika gani?me ye ya tsorata ki? Wa ya biyo ki?Ummul ki nutsu ki fada min abinda yake faruwa kar ki je ki kashe kanki kin dai san matsalarki"cikin haki da numfashin da ta kasa sarrafasu ta ke nunawa Ummi hanyar waje tare da cewa "ya yay yaya gentle sun dauke shi sace shi sukayi sun tafi dashi a mota, wallahi Ummi da gas......sai.kawai numfashin ya karasa daukewa ta tafi kasa yuuuu zata fadi Ummi ta yi saurin tarota tana salati tare da kiran taimakon jama a saboda daga ita sai Ummul a gidan.
Da gudu baffa da ya kawo kai cikin gidan ya shigo yana tambayar Ummi ko lafiya?kasa yi masa bayani ta yi sai jijjiga Ummul da take faman yi, dan ta manta da wani batun asibiti,shima durkusawa yayi yana taba hancin Ummul din kafin ya mike da sauri ya fice daga gidan.
yana fita kuwa yayi ya samu me dan sahu ya ajiye wani zai juya, cikin hanzari ya tsaida shi, sannan ya koma cikin gidan yana cewa Ummi ta dauko mayafinta su tafi asibiti,komai ma kasa yi Ummi ta yi dole sai shi ya shiga ya dauko mata hijabi ya bata, sannan suka dauki Ummul din suka fice da ita,sai da suka shiga dan sahun baffa ya lura da kayan gentle da suke watse a gurin ga kuma gidan da basu rufe shi ba, da sauri ya kuma fita ya kwashe kayan gentle ya tura a zauren sannan ya rufo gidan ya koma ya shiga nafef din yaja da gudu suka bar layin.
****
Su killer suna barin cikin gari ya kira Alhaji dan gaske ya sanar masa aiki fa ya kammala,kai tsaye Alhaji dan gaske ya basu umarni da su kai shi gidan da suka ajiye raliya.
Sosai Alhaji dan gaske yayi murna da wannan albishir, dan haka ya mike daga kan kujerarsa ta office yana mai yiwa kansa kirari, saboda yadda ya tashi da sa a a wannan rana gashi yana ta cimma burikansa,ficewa yayi daga office din ya nufi gidan su Ummul dan zuwa yanzu yasan ta fahimci ko shi waye, dan haka ba zai sha wuya wajen sarrafa rayuwarta ba,musamman da ya samu damar kwamushe gentle dan haka yanzu yana da babbar damar da zai juyata yadda yake so.
*****
Cikin hanzari nouses suka taho da gadon marasa lafiya suka dora Ummul hankalinsu a tashe dan da yawansu sun gane fuskarta,musamman nouse din da aka yiwa kyauta,kasancewar Dr Bilal baya nan dole sai wasu likitocinne suka rufa a kanta dan ganin sun daidaita numfashinta ya dawo daidai,sai dai da alama abin ya fi karfinsu, hakan yasa dole suka shiga neman layin Dr Bilal,sai dai nan ma sun kasa samunsa, hakan yasa suka hakura suka fara bata iya taimakon da zasu iya bata.
*****
Tun daga nesa Alhaji dan gaske ya hangi gidan garƙame da kwado, amma bai gasgata ba har sai da ya zo kofar gidan, sai kuma ya cika da mamakin inda suka tafi gaba dayansu,a iya saninsa in dai ba asibiti ba to ba sa rufe gida gaba daya dan Ummi ba macece me yawan fice fice ba sai abinda yayi matukar kamawa ko ya zama dole,fitowa yayi daga motar yana kalle lalle ko zai ga wanda zai iya tambayar sa inda suka je,sai dai bai ga kowa ba har tsawon mintuna biyar, har ya hakura zai shiga Mota sai ya hangi tahowar mufty, hakan yasa ya dakata har mufty ya karaso,shima mufty din kallon kofar gidan nasu yayi cike da mamaki kafin ya juyo yana gasawa Alhaji dan gaske wani irin kallon rashin yarda,hannu Alhaji dan gaske ya daga yana cewa"nima zuwana kenan na tsaya ina neman wanda zan tambaya inda mutanen gidan suke"cikin yanayin fusata mufty ya ce"akwai wani wanda za a yiwa tambayar ina suke da ya wuce kai"girgiza kai Alhaji dan gaske yayi Sannan ya ce"kaga muftahu mu bar wannan maganar yanzu kamata yayi da mu fara neman inda suka tafi gaba dayansu"ba tare da mufty ya tanka masa ba ya ciro wayarsa ya shiga neman lambar baffa,sai da ya kira kusan sau uku Sannan baffa ya daga wayar,kai tsaye mufty ya tambaye shi ko lafiya suka dawo suka tarar da gidan ba kowa,cikin damuwa baffa ya ce"muna asibiti Ummul ikram ce babu lafiya"take mufty ya rude ya shiga tambayarsa abinda ya sameta, bai ma bari ya bashi amsa ba ya juya zai koma titi yana neman layin Ali dan ya sanar dashi abinda ke faruwa.
Shima Alhaji dan gasken bai tsaya wata wata ba ya shiga Mota ya tayar, sai da ya zo saitin mufty din sannan ya leko yana cewa"ka zo mu tafi tare na san ba zasu wuce dan itopias hospital ba"ko kallo bai ishi muftty ba bare ya sa rai zai shiga motarsa,kafin ma ya kuma cewa wani abu mufty ya tare dan sahu ya shige abinsa,girgiza kai Alhaji dan gaske yayi yana cewa"yaro bai san wuta ba sai ya taka muje zuwa ɗan halal ka fasa",daga haka ya bawa motarsa wuta ya falfaleta sai dan itopias hospital.
****
Sosai zezee ta shiga tashin hankali, ta kasa samun natsuwa duk da albishir din da abbanta ya kira yayi mata,kalaman Moses sun hanata sakat, ta kasa fahimtar abinda yake nufi da daukar fansa,wanda tsoron kalaman nasa su ne suka taka rawar gani wajen hanata fita ko nan da can,duk da cewa wani bangaren na zuciyarta yana karfafata akan cewa koma me ye zata iya fansarsa da kudade, idan ta tuna wannan ne kawai take dan samun nutsuwa a ranta, ko kuma idan ta tuna cewa gobe iwar haka ta zama matar Dr Bilal,
****
Dakyar likitocin da suke kan Ummul suka samu numfashinta ya dawo sai dai har yanzu bata farka ba, Sannan bugun zuciyarta shima bai gama dawowa daidai ba,a cikin haka mufty da Ali suka karaso asibitin a tare, daga nan kuma sai motar Alhaji dan gaske wanda ganinsa a wajensu ba alheri ba ne,yana zuwa kuma ya bukaci ganin Ummul shi kadai a cewarsa shi mijinta ne kuma ganinsa zai iya daidaita bugun zuciyarta,dake likita jams ne da alhakin kula da Ummul din, kuma yana da alaka me karfi da Alhaji dan gasken yasa ya bar shi ya shiga ba tare da kowa ya bi bayansa ba,wanda hakan ko kadan bai yiwa su baffa dadi ba,sai ma fargaba da suka shiga, fatan su ya fito lafiya ba tare da wani abu ya samu Ummul ba.
Daidai lokacin da ya shiga a daidai lokacin Ummul take farkawa bayan taja wani irin dogon nunfashi, sai dai bude idanunta da zata yi sai akan Alhaji dan gaske wanda ta ke ganinsa dishi dishi,kafin kuma a hankali idanunta su fara ganinsa tar,zuba masa ido ta yi har ya karaso bakin gadon ya tsaya yana cewa"dama na ce ganina zai sa ki samu daidaituwar bugun zuciya tunda nine bugun zuciyar taki,to ya kika ga wasan?ko har yanzu kina ganin cewa barazanar banza nake miki yanzu na kuma baki samfur, ga baffanki da duk yayunki da ummin ki a waje, Sannan ga wancan Dr da ban san me ye shi kuma matsayinsa a wajenki da har kike son kare rayuwarsa ba,ko da yake ban sani ba ko maza biyu aka aura miki tunda ubanki ya iya yaudara ba"rigarsa ta rike katamau kafin ta bude bakinta da yayi mata nauyi ta ce"dan Allah karka kasheshi na yi maka alkawarin zan sa ya sakeni kuma zan aureka dan Allah na rokeka"ta karasa maganar Muryar ta na rawa alamun kuka ne yake daf da kwace mata,"kin makaro yarinya amma abu daya zan yi miki shine idan har zuwa gobe bai bani takardar sakinki ba,to zan sake shi ya dawo ke da kanki ki sa ya sakeki,amma fa sai a lokacin da za a daura auren zezee da dr Bilal a goben,ana daura auren zan sake shi,amma fa idan daga baya auren zezee ya samu matsala to komai zai dawo baya dan kuwa zan kama gentle na daure har sai kin fanso auren zezee da na ki auren,ma ana ki tabbatarwa da Dr cewa idan har bai auri zezee ba,to kuma ba zaki aure shi ba,na san wannan hanyar ita kadai ce zata sa Dr ya auri zezee ko da baya so, tun da naga alamun cewa shima ya na daf da tabbatar da kansa a gareki a matsayin masoyi,ba zan yarda wancan tsohon nasa ya ci gaba da raina min wayo ba,dan naga alamun bakinsu ɗaya,idan har kin yadda ni kuma zan saki gentle dinki, kehar ma na barku ku yi rayuwar aure ko ta sati daya ce,".
Cikin kukan da yake danne mata numfashi ta ce"na yadda na amince da duk sharadinka amma dan Allah karka taba min ahlina"make kafada yayi yana cewa "baki da matsala in dai har nima zaki cika min alkawarina,daga haka ya shafa gashinta da yake a hargitse yana sakin wani murmushin mugunta, sannan ya fice daga dakin yana wani takun fadi dan ji yake komai ya tafi masa daidai ya gama.
Bayan fitarsa sai da likitoci suka kuma taruwa akan Ummul Sannan ta ɗan fara samuwa, har lokacin kuma suna ci gaba da neman layukan wayar Dr Bilal.
*****
A ranar Alhaji dan gaske ya gama gayyatar daukacin Al ummar da yake so su halarci gagarumin daurin auren tilon yarsa. ba shine ya samu nutsuwa ba sai wajen sha biyu na dare, daga nan ne ya samu lokacin zama da mommy da kuma zezee dan tattaunawa akan yadda za a ci gaba da gudanar da taron shagalin bikin,ita kanta zezee sai a lokacin ta samu nutsuwar zuciya daga halin fargaba da wasi wasin da take akan moses.
****
Bely kuwa lokacin da ta tabbatar da cewa yaranta yaudararta su kayi ba karamin hauka ta yi ba,gashi gaba dayan su ta rasa su a waya da duk wani mazauninsu, wannan yasa ta kasa yarda da wasu yaran, sai ta fara kokarin canja salo, ta hanyar sawa ranta sace shi uban gayyar da kansa,idan yaso ta daddaureshi ko ta sanya masa abun maye yasha tayi yadda ta so da abinta taga nan ta kasheshi ta binne gawarsa dan tasan muddin ya rayu ba zai barta ba.
****
Farar safiya in ji Alhaji dan gaske, dan saboda tsananin zumudi karfe tara ya sanya lokacin daurin auren,zezee ma a wajen ta wannan rana ta zama a bar sanyawa a cikin tarihi, sosai ta gayyaci manyan kawayenta irinta yan birni ya'yan masu dashi ,hatta bely sai da ta daure ta ajiye damuwar zuciyarta akan mufty ta halarci dauren auren zezee.
****
A safiyar ne kuma a ka wayi gari an rasa mara lafiya guda tare da ahlinta gaba daya a cikin asibitin,saboda a jiya kin tafiya su Ummi su kayi wanda daga ƙarshe sai daki guda aka basu gaba dayansu dan su kwana,saboda a cewarsu ba za su tafi ba tare da sun ga farfadowar yarsu ba,sai dai gudun sunan Asibitinsu ya ɓaci sun ki fallasa abin, sai a junansu suke ta jajanta Al'amarin, hankalinsu ya tashi sosai musamman da suka ji wasu daga cikin nouses suna tsegumi akan cewa Ummul kanwar Dr Bilal ce,gashi har safiyar ba su ga Dr Bilal ba bare wayarsa,sai suka fara tunanin ko yayi tafiya ne ba tare da ya sanar da su ba,dan haka sai kawai su ka rufe bakin sauran ma aikatan kafin su ga abinda zai biyo baya na game da batan mutanen a cikin asibitin.
****
A can kuma ɓangaren su killer sun kwana suna azabtar da bawan Allah gentle, azabar da ya ji ne ya sa shi bude baki yayi magana akan cewa su fada masa duk abinda suke so zai yi musu in dai zasu sake shi, wannan bayanin da yayi suka turawa Alhaji dan gaske da yake wajen daurin aure suna jiran wakilan ango da shi kansa angon,duk da yana cikin jama a,amma hakan bai hana shi tura musu text akan cewa su sa shi ya rubutawa Ummul saki uku Sannan ya fada da baki suna yi masa video dan ya zamar masa shaida a wajen Ummul din da iyayenta.ya na tura musu sakon ya tashi yana tarbar iyayen ango da angon da aka ce masa yana cikin mota ba zai samu fitowa ba saboda jama,a,bai damu ba saboda ganin uban angon a wajen nan aka zauna aka fara gabatar da shaidu da duk wani matakai na daurin aure...
***
A can bangaren su killer suna ganin sakon Alhaji dan gaske take suka fara aikata duk abinda ya sanya su,suna gamawa suka dauki gentle suka saka a mota tare da barin gidan dashi,sai da suka tabbatar ba wanda yake ganinsu Sannan suka hankadoshi daga cikin motar suka ƙara gaba.
****
"Mun yi abinda ka samu a halin yanzu mun mai dashi inda muka dauko shi"sakon da kuller ya turawa Alhaji dan gaske ke nan lokacin da ake kokarin daura auren hakan yasa har aka daura auren bai san an daura ba, saboda video da killer ya turo masa ya dauke masa hankali...
Idan Allah ya tashi yin hukuncin sa kai bawa ba ka isa ka tare ko mai ba,bi duniya a sannu domin abinda ya baka tsoro wata rana shi zai baka dariya,
Idan Allah ya kaimu da rai da lafiya za mu ji kuma muga abinda sakamakon zai bayar.....
Zahra✍️
GIDAN ƳAN ƘARYA💕
By
FATIMA Y ADAM......
Littattafan marubuciyar.
KUDIRAR ALLAH
KADDARATA SANADIN HASKE
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
ƳAR GIDAN YARBAWA
MATAR ƊAN BIRNI
And
GIDAN ƳAN ƘARYA....