Free chapter · Read without an account
Pg36
"What"abinda ya faɗa kenan idanunsa akan video da yake kallo,kafin cikin rudewa ya kuma dawo da video yana kallo , gaba daya ma ya manta a ina yake,shirin ficewa yake daga Masallacin kunnuwansa suka kuma ji masa wani tashin hankalin da ya zo masa a matukar bazata, bazatar da ba zai taba mantawa da ita a rayuwarsa ba,wani maroki ne yazo tsakiyar saitin kunnuwansa,yana kara tabbatar masa da sunan wanda aka bawa auren zezee,ta hanyar cewa"yau Allah yayi lokaci yayi an daura auren ZINATU Salisu dan GASKE da dan shawalwalin mijinta MUSA gobir, akan sadaki naira me dukan Naira dubu ɗari biyu lakadan ba ajalan ba, Allah ya bada zaman lafiya ya kawo kazantar.....ai kafin marokin nan ya karasa fadar abinda yake son fada, Alhaji dan gaske yayi wani irin juyowa tare da kai masa naushi a bakinsa, yana cewa"Allah ya tsine maka albarka da wannan mugun fatan naka"hankade marokin ya kuma yi sannan ya koma cikin Masallacin yana zare ido kamar sabon mahaukaci, idanunsa ne suka tsaya akan Alhaji Ahmed da yake gaisawa da wasu mutane dake gefensa,kamar wani kububuwa haka ya yi kan Alhaji Ahmed yana ji kamar ya kasheshi a karo na biyu da ya ci amanarsa,babu zato babu tsammani Alhaji Ahmed dattijon kirki ya ji an cakumi wuyansa,kafin ya kwaci kansa mutane sun rufe Alhaji dan gaske suna kokarin janye shi daga cukumar da yayiwa Alhaji Ahmed mutumin da kowa yake ganinsa da kima da martaba.
Tsananin yadda dan gaske ya haukace yasa suka kasa raba shi da Alhaji Ahmed,fadi yake"a wannan karon ba zan kyale ka ba,maci amana,idan ka san baka son auren tun farko ai sai ka fada min ba sai ka yi kutunkutun akan lamarin 'yata ba,to wallahi yadda kasa a ka yi auren nan yanzu zaka sa a raba shi dan 'yata ba za ta taɓa auren wani banza da bamu san daga wace duniyar ya fado ba,"ganin Alhaji dan gaske bakinsa ya ki shiru kuma ya ki sakin Alhaji Ahmed yasa securitys dinsa suka shigo Masallacin suka yi masa daukar amarya, suka fice dashi yana harbin iska da kafafunsa kamar wani karamin yaro.
Shima Alhaji Ahmed fitowa suka yi da shi suka bude masa mota ya shige, suna ta ture yan jarida yan tsegumi da ko ba a kira su ba sai ka gansu a waje da zarar an fara wani abu me daukar hankali,
Hakan yasa suka koma kan Alhaji dan gaske da yake ta zuba ruwan bala I,yana fadar maganganun da shi kansa bai san yana fadar su ba,yan jarida kuwa abin nema ya samu take suka fara baza hotunan Alhaji dan gaske a duk wata gidan jarida da tv,take suka bawa labarin sa take da suna ,WANI MAGIDANCI YA HAUKACE A YAYIN DA AKE DAURA AUREN YARSA,wasu kuma su sanya,A WAJEN WANI DAURIN AURE AN SAMU SABANIN DA YA TADA TARZOMA A TSAKANIN IYAYEN ANGO DA AMARYA.da dai sauran iriren labaran da yan social media suke yadawa ba tare da sanin tartibin abinda ya faru ba.
Da kyar wani yaronsa ya dannashi a mota ya shiga ya ja motar suka bar filin Masallacin, su kuwa yan tsirarin dangin ango tafiya su kayi ba tare da sun damu da abinda uban amarya yayi ba,tunda dama dakyar aka lallabasu suka ziyarci daurin auren kuma dama yan uwa ne na can nesa wanda suka jima da musulunta.
****
Kai tsaye gidan ya maida Alhaji dan gaske,ko da suka zo gidan tuni zezee ta cika gida da gayyarta, mommy ma ta gayyaci wasu daga cikin kawayenta,sai wasu yan uwan Alhaji dan gasken da ya manta da su sai yanzu saboda yana cikin fariniki yasa a ka dauko su daga can kauyensu,su zezee an sha wanka fuskar nan tasha makeup sai taunar cingum take tana kallon kawayenta daidai saboda ta yi musu zarra ta auri mijin kerewa Sa'a, ta auri Yong billionaire,suna tsaka da sabga suka ga Alhaji dan gaske ya shigo Kamar mahaukaci babbar rigar tasa ma ta hannu ya zura wuyan hakan yasa ta yi leɓatu tana jan kasa,take falon yayi tsit sai idanu da suka bi Alhaji dan gaske dashi,zezee kuwa tuni jikinta yayi sanyi hankalinta ya tashi, dan tasan babu abinda zai birkita abbanta kamar ace an fasa daurin aurenta da dr Bilal,ta shi ta yi tabi bayansa sai dai tana zuwa ta samu ya kulle kansa a dakin, hakan ya sa ta koma nata dakin tana tunanin yadda za ta yi ta san abinda yake faruwa, ita gashi ba wani sanin danginsa na kauye ta yi ba,hasalima ta rainasu ba wanda take gani da girma bare ta je ta tambayesu abinda ya faru a wajen daurin auren,to ko ta tambaye su ma su basu san komai ba,tunda suna daga can waje kuma ba sanin angon su kayi ba dan haka kai tsaye ba za su iya tabbatar da abinda ya faru ba.
***"
Alhaji dan gaske kuwa yana shiga ɗakinsa ya rufe kansa tare da zama dirsham yana sakin wani irin kukan gardawa, sai da yayi me isarsa Sannan ya goge fuskarsa yana cewa"wallahi duk wanda ya sani fitar da hawaye na to sai na sashi ya fitar da na jini,tabbas ba zan kyale ku ba gaba dayan ku,tun daga kan Alhaji Ahmed har zuwa kan ahlinsa,kai ma gentle dole zaka biya bashin wahalar da rayuwata da ka yi,wayarsa ya daga ya kira killer,ba tare da jinkiri ba killer ya daga yana zuba masa kirari,cikin tsawa dan gaske ya tare shi da cewa"Kai killer Ni zaka yaudara? wannan wane dan iskan kuka dauka kuka turo min?"cikin mamaki killer ya ce"ya haj shine wanda ka sa mu kwamushe maka mana"a gidan Uwar ka wannan ya zama shine gentle, wait
na tambaye ka,wai me kasha ne kafin ka fara wannan aikin?"na rantse da me sama ya haj ban sha komai ba, ai kasan bana wasa da lamarinka dole na kiyaye kuma na kasance cikin hankalina tunda ina so na yi maka daidai"dafe kai Alhaji dan gaske yayi cike da takaici Sannan ya ce"ka sake duba video da ka turo min kafin ka ci gaba da wannan shashancin naka"daga haka ya kashe wayar"tare da zare babbar rigarsa yana cewa,"bari na je da kaina na sace ikram ɗin dan ba zan bari na yi asara goma da a shirin ba",yana cire babbar rigar ya fice ta can baya ba tare da ya bari kowa ya ganshi ba.
*****
A hankali take bude idanunta da suka yi mata nauyi matukar nauyi,da farko dishi dishi ta fara gani,a hankali kuma ta fara ganin komai daidai, sai dai ta ɗan shiga mamakin ganin a inda ta budi ido,to amma sai ta yi tunanin ko canja mata daki aka yi a cikin asibitin, wannan tunanin da ta yi yasa ta maida idanunta ta rufe su, bayan ta ɗan dafe kanta da yake ɗan Sara mata kadan kadan,a dan firgice ta kuma bude idanunta saboda tunawa da iyayenta da kuma gentle da yake hannun dan gaske, take ta tuna da sharadan da ya gindaya mata wanda hakan yasa ta fara kokarin sauka daga gadon, a inda kuma ta fahimci cewa wannan gadon fa ba irin gadajen asibiti ba ne, sai kawai ta shiga bin dakin da kallo, kafin ta maida idanunta wajen kofar da ta fara jin motsin shigowa.
Shi dinne Dr Bilal sanye cikin sky blue din riga wadda aka yi zanen heart a jikinta da kalar baki, sai bakin wando, kayan sun yi masa kyau sun haska cachulate din fatarsa me sheki, fuskarsa babu yabo babu fallasa yana takowa a hankali cikin yanayinsa na nutsuwar da yake karawa kyakkyawar fuskarsa kwarjini,dauke kanta ta yi daga kallonsa tana jin wani irin raunin zuciya wanda hakan yasa idanunta suka cika da kwalla suna gab da zubowa ta ji saukar hannunsa yana dauke kwallar da suka fara zubowa, Sannan ya zauna a gefenta yana kallon fuskarta da take a dame,"cikin kukan da yake shirin kwace mata ta ce"ina ummi da baffa da su ya Ali?a ina nake nan ɗin?"wannan tambayoyin sun min yawa ban san wanne xan fara amsa miki ba"ya fada yana duba allurar da ya shigo da ita a hannunsa,magana zata yi ya dakatar da ita ta hanyar dora yatsansa a kan labbansa, duk da haka ba ta yi shurun ba sai ma wata tambayar da ta kuma watso masa idanunta akan allurar da yake haɗawa,"ba yau ne Za a daura auren ka da zezee ba?"matso ta yayi ba tare daya bata amsar tambayar ta ba,ganin abinda yake shirin yi mata yasa ta ɗan fara ja da baya tana marairaice fuska da kokarin yi masa magiya akan allurar da yake shirin yi mata.
"Karki fara rokona saboda ba zan yi hakuri ba,kuma mene damuwarki da aurena da zezee?"cikin gunguni ta ce"Ni ce ko me damuwa tunda an yi min alkawarin idan aka daura auren za a saki min mijina"waye mijin naki?"
Ya fada yana janyo ta jikinsa, a dan rude ta ce "dan Allah karka min allura bana so, kuma ka daina taba ni saboda ni matar aure ce"bai ce mata komai ba ya janye rigar ta ,take fararen cinyoyinta suka bayyana,bai tsaya a nan ba har sai da ya kai ga bayanta a in da zai soka mata allurar,ganin fa da gaske yake allurar zai yi mata kuma allurar ma a jikinta inda bai kamata a ce wani kato ya gani ba,yasa ta sakin kukan takaici tana mutsu mutsu dan saboda ta hanashi damar yi mata allurar,shi kuwa Dr bilal bai yi wata wata ba ya hade bakinsa da nata tare da rike ta da hannunsa guda, hannun daya kuma ya shammaceta ya tsira mata allurar da ta sanya ta kuma fashewa da kukan damuwar abubuwa da dama,bai rabu da ita ba sai da ya lailaya mata sannan ya maida ita ya kwantar ya mike zai fice daga dakin,da sauri ta tashi ta bi bayansa cikin kuka take cewa"dan Allah ka kira min baffa da Ummi"bai ce komai ba ya fice daga dakin, zama ta yi a gurin tana ci gaba da kuka da tunanin ta yadda zata yi ta samu ganin Alhaji dan gaske.
Ko da ta ji an kuma bude kofar dakin an shigo bata dago ba,dan a tsammanin ta shi ne ya kuma dawowa,amma ga tsananin mamakin da ya hade mata da farin cikin da ta kasa sarrafashi,sai taga umminta da baffa da Ali ga mufty gaba dayansu a gabanta suna mata dariya,rungume ummi ta yi tana dariya me hade da kuka, mufty ne yace"lallai wannan yarinyar shagwaɓa tana damunki fa ke da zaki yi murna kin farka baki Margaya ba"Ali ya ce da yanzu muna nan muna cin hinkafa da wake"dakuwa baffa yayi musu yana cewa"da ba aganku a yadda kuke ba yanzu"Ummul kuwa wajen baffa ta rarrafa ta kwantar da kanta a kafadarsa tana cewa"baffa yaya gentle ha.....mufty ne ya katseta da cewa "wai yarinyar nan yaushe kika zama mara ta ido ne?"Ali ya ce "kai me yasa baka da girma sai na jiki? memakon ka yi mata albishir din da zai faranta mata rai sai kawai ka kama tsokanarta"da sauri Ummul ta janyo jiki ta koma wajen Ali tana cewa"don Allah ya Ali fada min yaya gentle ya dawo ko?"hannu ya mika mata yana cewa me ye tukuicina?".
"Duk abinda kake so zan baka"shi kenan rufe idanun ki"da sauri ta rufe idanun, ji ta yi ya kama hannunta sun fara tafiya,taji alamun ya bude kofa sun fita inda bata san ko ina ba ne.
******
Kai tsaye Alhaji dan gaske asibiti ya nufa, sai dai yana zuwa ya samu labarin cewa ai an sallami su Ummul tun safiyar yau ɗin,bai tsaya neman karin bayani ba ya koma motarsa ya figeta kamar zai tashi sama,bai tsaya a ko ina ba sai a kofar gidan baffa, cikin tashin hankali yake murza idanunsa dan ya tabbatar da abinda yake gani,saboda ganin kofar gidan har yanzu a garkame kamar yadda take tun jiya,Safa da marwa ya fara yi a kofar gidan, kafin ya shiga tambayar mutanen da suke dan wucewa, sai dai duk maganarsu ɗaya ce basu san inda mutanen gidan suke ba,karshe har gentle ya koma tambayar inda yake,amma kowa sai ya ce masa bai san inda gidansu yake ba,Alhaji dan gaske kamar zai yi hauka,wayarsa ya dauko ya shiga kiran layin baffa sai dai kash,.layin a kashe wannan matar take ce masa,komawa yayi tambayar makota su dinma Abu daya suke fada masa na cewa tun jiya da suka tafi asibiti ba su dawo gidan ba,mota ya koma ya shiga ya fara zagaye layin yana tambaya ko zai samu inda suka tafi ko su ko gentle, dan yasha alwashin duk wanda ya samu a cikinsu ba zai daga masa kafa ba.
*****
Zezee dai ta kasa samun sukunin zuciyarta,su kansu jama ar da ta tara a hankali suka dinga sulalewa suna guduwa Saboda duk sun fahimci cewa mutanen gidan basa cikin nutsuwa,bely ce kawai ta yi ragowa acikin kawayenta,itama daga karshe tashi ta yi ta kama gabanta saboda itama tana da Tata damuwar da take son maganceta.
Tana fita gidan su Ummul ta wuce dan ayi ta ta kare, domin ita bely sakamakonta yana ga jarrabar da Ubangiji yayi mata ta fadawa soyayyar kamilin mutum da ba zai taba yadda yayi rayuwa da ita ba,wanda ita har yanzu bata fahimci irin son da take yi wa mufty din ba.
Zezee kuwa tana cikin dakin waya a hannu tana ta gwada kiran Moses wanda har yanzu hankalinta ya kasa kwanciya a kan furucinsa.cikin sa a kuwa sai gashi kiran ya shiga,ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta ji an daga wayar sai dai shiru ne ya biyo bayan daga wayar, sai ita ce da kanta ta gaji ta fara magana da cewa"moses dan Allah idan da kai nake magana ka ce min wani abu dan na fahimta"da Ni kike magana amma a yanzu ba zan sanar da ke komai ba ,har sai kinzo asibitin Aminu Kano kin sameni"na shiga uku Moses me zanzo na yi a asibiti kuma?"idan ba zaki zo ba ki barshi ban yi miki dole ba, amma ki sani nine nake da duk wata amsar tambaya da kike nema akan aurenki da Dr,dan haka idan kin ga dama ki zo, zan turo miki da lambar dakin da nake",kit ya kashe wayar,ya bar zezee da bin wayar hannunta da kallo zuciyarta na wani irin tsallen fargaba da tashin hankali,shin me yake nufi da cewa shi yake da amsar tambayar ta akan aurenta da Dr ,tunaninta ne ya yanke lokacin da ta ji shigowar sako wayar ta,dubawa ta yi taga lambar dakin ne har da kwatancen dakin gaba ɗaya,jiki a sanyaye cike da fargaba ta tashi ta xari key din motar ta ta fice,sai da ta fito taga gidan ya koma shiru kamar yadda yake a baya, wannan ne ya kuma daga mata hankali ta tabbatar da cewa akwai matsala game da aurenta da Dr bilal.
*****
Kusan awa biyu Alhaji dan gaske yana bulayi a anguwar su Ummul amma ko me kama da 'yan gidansu bai gani ba,bare gentle da dama ba wanda yasan daga duniyar da ya faɗo,jan motar yayi ya bar layin tare da nufar asalin gidan da ya ajiye raliya wadda sai yanzu ta fado masa, ya kuma ji a ransa zai samu wata mafitar ta bangaren ta muddin ta sanar dashi wanda ya turota wajensa leken asiri,to amma bai bar wajen ba sai da ya tabbatar ya bar yaran da zasu dinga gane masa duk wani motsin wanda zai gifta ko ya shiga gidan.
Yana barin wajen bely ta tsaida Tata motar, itama dai hankalin nata tashi yayi saboda rashin samun mufahun a gida, gashi wayar da ta ki shiga sabanin da da sai dai ya ƙi dagawa,juyawa ta yi ta bar layin da tunanin zuwa dare zata dawo, tunda ita bata san halin da ake ciki ba,ta yi tunanin dai kawai sun tafi anguwa ne.
******
Zezee tana karasawa asibitin ta yi fakin tare da nufar bangaren da Moses yake kamar yadda ya kwatanta mata,tana tafe tana duba lambobin dakin, duk wani taku da zata yi sai ta ji wani Irin mummunan bugun zuciya,tabbas da za a bata daki a wannan lokacin to itama tsaf zata kwanta saboda yadda take jinta ba daidai ba musamman bangaren zuciyarta.
Lokacin da ta karaso kofar dakin sai da ta ɗan tsaya tana maida nunfashinta kamar wadda ta yi tseren gudu, Sannan a hankali ta tura kofar dakin ta shiga ba tare da sallama ba,tunda dama ba ɗabi'ar ta ba ce,sai dai tana shiga numfashin nata da yake kai kawo ya karasa tsayawa cak saboda razana da abinda idanunta suka gane mata.
Na komai ne ya razanata ba sai ganin halin da moses yake ciki,a kife yake bayansa a bude babu kyawun gani,wai a hakan ma Dan ana kulawa da shi ne sosai,sai rabin fuskarsa da tururin asid din da ya taba ta wani yi damege kamar tabon kuna,"a hankali ya tashi zaune ya ɗan jirkice yana cewa"ya kika tsaya ki karaso mana, wannan abin da kuke gani shine sakamakon aikin da kika sani na zubawa yarinya asid,sai kin karaso za ki ji naki sakamakon da ya bayar"girgiza kai ta shiga yi tana kokarin juyawa dan duk tunanin ta ya bata itama zai watsa mata asid din ne, kamar yadda ya fada mata zai dau fansa.
Sai dai tana juyawa ta ci karo da wani mutum da bata taba ganin fuskarsa ba,sai dai taga kamar moses a fuskarsa, yanayin fuskar babu digon rahma,kai wannan daga ganinsa ma shi lokacin da su musan suka karbi Musulunci shi jin karba yayi, sosai taji tsaronsa ya kamata ,hakan yasa ta dinga ka da baya har ta kai ga shiga dakin sosai,take mutumin ya saki murmushin da ya kara masa muni yana cewa"idan kin ga kin fita daga dakin nan to ki tabbatar da cewa tare da mijinki ne Musa gashi nan a zaune"......
****
Ali bai saki hannun Ummul ba har sai da ya kawota tsakiyar falon, Sannan ya cire hannunsa daga kan fuskarta tare da juyawa ya bar falon,Ita kuwa Ummul idanunta basu dira akan kowa ba sai gentle da yake zaune cikin kayan da ta sanshi da su, idanunsa a kanta yana mata kallon har hanji......
Dan Allah ku dinga taya Ni share saboda yanzu bana iya share ko ina kuma ana ta kura min da tambaya,
Zahra✍️
***
GIDAN ƳAN ƘARYA💕
By
FATIMA Y ADAM......
Littattafan marubuciyar.
KUDIRAR ALLAH
KADDARATA SANADIN HASKE
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
ƳAR GIDAN YARBAWA
MATAR ƊAN BIRNI
And
GIDAN ƳAN ƘARYA....