Free chapter · Read without an account

Pg37

by Fatima Yushau adam · GIDAN YAN KARYA

Da gudu ta karasa gabansa ta durkushe tare da dora kanta akan ƙafarsa bakinta fal magana amma ta kasa cewa komai,hannu yasa ya dago fuskar yana dan ɗage mata gira tare da yi mata alamun tambaya,kuka ta sanya tare da dan kai masa karamin duka daga nan kuma ta shige tsakanin kafafunsa ta ɗora kanta a cikinsa,tana cewa"me su kayi maka sun dakeka da yawa ko?ina da ina suka ji maka ciwo?"sun baka abinci kaci?" hannunsa ya dora a kanta fuskarsa tana dan washewa daga kirnewar da ta yi, Sannan cikin ƙasa ƙasa da murya ya ce"kin manta da dalilin da yasa ya sace ni amma kin zo kina ta wani shige min"ya faɗa ba tare da nuna alamun wasa ba,da sauri ta tashi da ga zaman yan borin da ta yi a gabansa idanunta har sun cika da kwalla,alamun tashin hankali duk sun gaba bayyana a tare da ita,a hankali ta juya zata bar wajen, yayi saurin riko hannunta da dan karfi wanda yayi sanadin fadawarta jikinsa,kokarin tashi take yi,ya kuma sa hannu ya shigar da ita jikinsa tare da cusa fuskarsa a tsakanin wuyanta yana dan shaƙar numfashi da kamshinta da ya manne da jikinta,kafin cikin nutsatstsiyar muryarsa me cike da kamewa ya ce"sorry hakan ba zata taɓa faruwa ba,ko kin manta kalaman zuciyata a ranar da abin zai faru?to idan kuma tunanin da wani abu a duniya da zai sa na rabu da ke un wuri ki daina,ashe ma ke nan wahalar banza na yi na dagewa da na yi babu dare babu rana na ajiye kowa na ajiye komai na taho neman soyayyar gaskiya wadda ta yi tsananin wahala a cikin Al ummar mu".

Dago fuskarta ta yi tana masa kallon neman karin bayani,saboda acikin kalamansa akwai wanda suka zo da sarkakiya ko kuma tace wanda yayi su a bai bai, "me kake nufi da kasha wahala wajen naman soyayyata Ni da ko fada min ba kayi kana sona ba, Sannan ba a fada min ba ko neman yardata ba a yi ba,aka daura min aure da kai to duk me ya kawo wata wahala?"lumshe idanunsa yayi yana bude su a lokaci daya sannan yasa hannu ya ɗan ja karan hancinta yana cewa"dadina dake idan kika ta shi yi min tambayoyi har sai kin min kure tambaya, gaskiya ba zan iya amsa wannan tarin tambayoyin ba sun yi min yawa"cikin mamakinsa da ya cikata ta ce"amma wane tambaya ne me yawa a nan?wai me yasa duk sanda zan yi maka tambaya sai ka ce ba zaka iya amsawa ba?"ta karasa maganar cikin taɓe baki kamar zata yi kuka,"dan dafe kansa yayi yana yatsuna fuska kamar irin yana masa ciwon nan,tuni Ummul ta manta da tambayoyinta ta shiga yi masa sannu, dama yayi hakanne dan kaucewa tarin tambayoyin nata da ba shi da amsar bata a yanzu, tashi ta yi tare da kamashi tana cewa "ka kwanta kafin Dr Bilal ya zo ya dubaka"mikewa yayi yana ce mata"zan shiga dakin da aka sauke Ni Na Dan yi wanka na huta ina ga stress ne kawai,idan na yi bacci zai sake ni"ba ta ce komai ba sai rakashi da ta yi har cikin dakin sai da taga ya shiga bathroom Sannan ta fita ta koma wajen su Ummi da su ma take da tarin tambayoyin da zata yi musu.

****

Koda Alhaji dan gaske ya Isa gidan sai ya samu killer da yaransa suna ta dube dube a cikin gidan,suna ganinsa suka kuma rudewa fuskarsu duk ta nuna alamun rashin gaskiya,dubansu yayi a cikin harzukar da yake,ya ce"kun kyauta kuma ku tabbatar da cewa idan har baku kawo min wannan matsiyacin yaron dashi da ikram din gaba daya ba,to wallahi ba zaku tsira da ga sharrina ba,yanzu ina ita waccan karamar yar iskar take?"duk cikin su rasa wanda zai bashi amsa yayi har sai da ya kuma maimaita tambayarsa cikin tsawa da hargowa, Sannan killer ya sadda kai kai kasa cikin irin ladabin da suke yiwa uban gidansu,ya ce"ya haj sai dai a yi hakuri fa dan harka ta baje,saboda yanzu dawowarmu ke nan daga maida wancan dan lawahal din muka samu gidan a bude matar ta tsere,shine muka tsaya muke dubawa dan muna tsoron mu bi sahunta saboda ba mu sani ba ko kwalawa ne suka farke gida.....kan ya karasa Alhaji dan gaske ya kife shi da wani zazzafan mari yana wani irin fidda huci kai ka ce kububuwa ce taga Nama,fuskarsa tuni ta jike sharkaf da gumi kamar wanda yayi waka a shaya,kafin cikin sarkewar harshe ya nuna killer da yatsa yana cewa"amma dai an yi tsinannu asararru wanda iyayensu suka tsine musu bayan sun haifesu a kwararo,Ni zaku ciwa mutunci ku kwarewa rigar arziki"shiru yayi yana Safa da marwa hannunsa a goye a bayansa ya rasa ma wani irin tunani zai yi,su kuwa suna tsaye kamar gumaka babu wanda yayi motsi a cikinsu sai ka kasa da suka yi da kawunansu,duk cikinsu babu wanda ya nuna yaji zafin zagin da alhaji dan gaske yayi musu,sai da ya gama kaiwa da dawowarsa bai samu wani mafita ba hakan yasa ya kalli killer yana cewa"to yanzu me ye mafita ta ina zamu fara?".

Killer ya ce"ya haj,barin gidan nan ya kamata mu yi tun kafin kwalawa su cimmana dan ina kyautata zaton da sa hannun dan lawahal din da muka kwamuso mun yi zaton gentle ne "kash kash wallahi killer kun kashe kanku dan ni duk ta inda aka bi a ka zagayo zan iya fidda kaina,to amma ba zan barku ba domin har yanzu banji na karaya ba,dole mu sake sabon shiri,yanzu dai kamar yadda ka fada din ku yi saurin barin gid, saboda baku san abinda zai biyo baya ba"killer ne ya basu umarnin su dauko duk wani abu da suka san zai musu amfani,a cikin tattara kayan da suke yi ne suka samu wata farar takarda an yi rubutu a jikinta,sunan raliya da suka gani a jiki ne yasa killer saurin bin bayan Alhaji dan gaske wanda saura kiris ya bar wajen,hannu yasa ya dakatar da shi,ba tare da ya fito ba ya tsaya tare da sauke glass kasa yana tambayar killer din lafiya?mika masa takardar killer yayi ba tare da ya ce masa komai ba, bude takardar Alhaji yayi yana cewa"wannan kuma ta mece ce?"a fili Alhaji dan gaske ya fara karanta takardar kamar haka("nasan a lokacin da zaka ci karo da takardar nan na jima da yin nisa, shi yasa nake son na sanar da kai cewa har yanzu kana da damar tuba ma ana kana da sauran lokaci,wanda basu gaza awanni biyar ba,idan kuma har baka tuba daga lokacin da ka karanta takardar nan zuwa faduwar ranar yau ba,to ka fara gudun ceton rai, ka fara tunanin hanyar da zaka kubuta daga hanyar shiga bakin fusataccen zakin da ya kwana goma bai ga nama ba, Sannan daga yau na baka assignment kai da kanka zaka gano wanda suka sani aikin kula da kai,saboda ba mutum daya ba ne ba kuma biyu ba ne,dan haka ka je ka yi nazari daga nan zuwa dan ragowar lokacin da kake dasu,daga karshe ina tunatar da kai cewa ka yi hattara maza na nan bisa kanka"daga karshe ta rubuta daga raliya.

Duk da yadda Alhaji dan gaske yake son boye razanarsa amma hakan ya gagara,yaga takardar yayi ya cusata a bakinsa ya taune ya hadiye idanunsa sun yi jajur,Sannan ya ja motar da gudu ya bar kofar gidan, ƙwaƙwalwarsa kuwa tuni ta shiga aikin nazarin maganganun raliya,shin su waye suka san sirrinsa da har zasu turo masa raliya?to akan me suke son sanin sirrinsa?me ye alakarsa da su?me suka sani akansa?a yanzu me ye shirinsu akansa da har take cewa ya fara gudu ko ya mika wuya yayi nadama?waɗannan tambayoyin sune suke neman sashi hauka fiye da abinda ya faru tsawon awanni uku baya.

******

Tabbas ba dan mutuwa lokaci ba ce da a wannan lokacin zezee zata iya hadiyar zuciya ta mutu,juyawa mutumin yayi zai fita,zezee ta yi karfin halin tare shi da cewa,"dan Allah bawan Allah ka fada min abinda yake faruwa saboda ka sani a cikin duhu ka fiddani haske"juyawa yayi ya zai fita yana cewa"ki kwantar da hankalinki keda kike da me wuka da nama a hannu ai ba sai kin nemi karin bayani daga bakina ba"yana gama fadin haka ya fice tare da kulle kofar ta baya.

Cikin tashin hankali zezee ta koma gaban gadon moses bakinta har rawa yake,wajen furta sunansa,"moses dan Allah ka sanar da ni abinda yake faruwa kar zuciyata ta buga ba tare da na fahimci inda maganar mutumin can ta dosa ba"murmushin da ya karawa fuskarsa muni yayi Sannan ya ɗan gyara kwanciyarsa ta yadda zai ji dadin yi mata bayani dalla dalla ta yarda zata fahimta.

Sannan ya ce "ya kamata ki zauna saboda idan kin zo faduwa bani da lafiyar da zan tare ki Sannan rashin tare kin zai iya jawo miki ciwon shanyewar barin jiki, kin ga kuwa idan kina zaune komai zai fi zuwa da sauki".

Samun kanta ta yi da zaman yan bori a kasan wajen, ba tare da kyankyamin kasancewar wajen dakin asibiti ba,har zuwa lokacin jikinta karkarwa yake ,Sannan zuciyarta bugawa take da sauri saboda tsananin fargabar abinda zai fito daga bakinsa.

Sai da ya ɗan ja numfashi kafin ya fara da cewa"zezee ban taba shiga tashin hankali da tsoro da razani ba sai ranar da abinnan ya faru dani, Sannan tun da na musulunta ban taba jin tsoron Allah kamar na wannan lokacin ba, Sannan ban taba yin nadamar aikata wani laifi ba sai a wannan rana, wato bayan mun gama waya da ke, ban tsaya komai ba na kira wani abokina na sanar dashi Abinda nake so,to dake shima irina ne dan harkalla ne take ya sanar dani in zo na karba kawai babu wata matsala,hakan yasa na je har wajen aikinsa na karbo asid din, a ranar na fara zuwa kofar gidanku tunda kin sanar dani zata iya fitowa a kowa ne irin lokaci,sai dai ko da na je, har wajen karfe goma babu ita babu labarinta,har zan tafi sai wata zuciyar sharrin ta ce na cigaba da zama har zuwa safiya ko Allah zaisa na dace, dan na sawa raina cewa ta wannan sanadin zan sameki ko da baki aure ni ba nasan zaki bani damar da zan famshe ladan aikina a kanki, wannan burin nawa shi yasa na tsaya har zuwa karfe sha biyu da mintuna.

ina zaune a inda na boye na ga mota ta fito, ban san su waye a ciki ba,amma rigar mace da naga ta fito daga kasan murfin motar yasa na raya a raina cewa xan gwada sa,ata ko zan dace,hakan yasa na dinga binsu a dan sahu har sai da naga gidan da suka je,a lokacin na karaya shi yasa na yi tafiyata, sai kuma da asuba dake ƙaddarata ce take kirana,na kuma jin kwarin gwiwar komawa,

To a hanyata ta komawa ne na ci karo da yarinyar da kika bani hotonta na zuba mata asid"a nan ya ci gaba da bata labarin yadda su kayi da Ummul da kuma mutumin da ya zo ya kwace ta da yadda aka yi kaikayi ya koma kan mashekiya.

Yana zuwa nan a labarin ya ɗan yi shiru , Sannan ya dora da cewa"ina cikin wannan halin babu mutum gabas da kudu da Arewa wanda zai iya taimako na, har ta kai ga na sume ban san inda hankalina yake ba,ni dai kawai na farka na ganni a cikin dakin nan,ban tashi sanin wanda yasa aka kawo Ni nan ba sai bayan kwana ɗaya da farkawarta,ba kuma kowa ba ne wannan mutumin sai wannan da ya kwaci yarinyar a wajena, kuma sai a lokacin na san suna da alaka da ita ,duk da cewa ba fitowa yayi fili ya sanar dani ba,Sannan ya nemi da na bashi tarihin rayuwata, Ni kuma na gaya masa ba tare da na boye masa komai ba, anan ne ya ji burina na son aurenki kuma duk saboda son da nake miki ne yasa na aikata abinda naso aikatawa har ya dawo kaina,a take a nan ya yi min alkawarin zai mallaka min ke a matsayin mata,ban tabbatar da abinda ya ke fada min ba har sai ranar daurin auren da ya zo ya kunna min videon daurin auren".

Wata irin shakuwa zezee ta dinga yi kamar wadda ake zarewa rai kafin ta tafi luuu ta fadi a wajen babu alamun numfashi , wannan mutumin ne ya shigo da sauri tare da likitan da ta duba ta ta tabbatar da cewa bata mutu ba, amma zuciyarta bugunta ya haura yadda ake bukata dan haka komai zai iya faruwa da ita idan ba ayi hanzarin Kawo Mata dauki ba.

Cikin gaggawa kuwa aka bata gado likitoci suka rufu a kanta dan ceto rauwarta.

*****

Koda Ummul ta koma dakin bata samu kowa ba, fitowa tayi tana kwalawa Ummi kira, hankalinta a tashe tana fata ALLAH yasa ba taleko ta koma a kayi mata ba,karo ta ci da ya Ali hannunsa dauke da robar rufaida yougout yana kaiwa bakinsa cikin nishadi, kallon mamaki ummul ta yi masa kafin ta ce"lallai ma ya Ali wato kai duniya sabuwa ta dawo maka,bayan kasan akwai aiki gabanmu ko?"shima kallon mamakin yayi mata sannan ya lashe lebensa da yougout din ya zuba yana cewa"ke ce dai aiki yake gabanki tunda baki san mun riga mun tsira daga sharrin tsinannen can ba"kamar ya ?"bai kai ga bata amsa ba,Ummi dake kitchen ta kwala mata kira,kalle kalle Ummul ta shiga yi saboda bata san a ina ne Ummi take kiranta ba,ya Ali ne ya kama hannunta ya Kaita har zuwa kitchen din,gaba daya Ummul mamakin abinda suke faruwa ne ya ke kuma kamata,hakan yasa tana gama karewa kitchen din kallo ta karaso gefen Ummi da take wanke kifi tana cewa.

"Ummi wai me yake faruwa ne ya naga kuna yin abubuwa kamar irin kun samu gidan nan naku, Sannan kuma hankalinku kwance bakwa tunanin abinda Alhaji dan gaske zai iya aikata mana, ya kamata fa kusan cewa muna cikin hatsari daga mu har shi me taimakon namu dan dai bai sani ba ne"dan murmushi Ummi ta yi Sannan ta dafa kafadar Ummul tana cewa"ikram ki kwantar da hankalinki kisa a ranki cewa kina cikin tsaro a inda kike cikin kariyar Ubangiji ta hanyar bawansa da ya aiko cikin rayuwarmu domin ya taimake mu daga halin da muka riski kanmu"shiru Ummul ta yi wanda hakan ya nunawa ummi cewa Ummul din har yanzu ba ta fahimci abinda take nufi ba,ko da yake ta mata uzuri tunda har yanzu a cikin duhu take dan haka zata rabu da ita, har lokacin da ya dace ta sanin yayi,dan haka sai ta kuma yin murmushi tare da cewa"Ummul ba dai mune damuarki ba tare da jafarunki da kuma likitan ki?to ki kwantar da hankalinki babu abinda zai same mu"tura karamin bakinta ta yi tana cewa"haba Ummi da kanki kike kiran wani likita nawa bayan kinsan yaya gentle ne nawa"to shike nan na daina fada,amma kema ina so ki ajiye duk wata damuwa ki kwantar da hankalinki kinji"gyada kai Ummul ta yi amma ba wai dan ta gama gamsuwa ba, sai dan kawai ta samu nutsuwa da inda suke ne,har zata fice sai kuma ta dawo da baya tana cewa da Ummi"to amma Ummi shima yaya gentle yana tare damu ko?"yana tare damu babu inda zashi"wani dan tsallen murna Ummul ta yi tare da rungume Ummi ta baya sannan ta sake ta ta fice.

Kai tsaye dakin da gentle yake ta nufa dan ta ga ko ya farka ta kai masa abinci.

****

Alhaji dan gaske kai tsaye dakin mommy ya nufa ba tare da sallama ba ya murda kofar ya fada,tana ganinsa ta yi wata irin zabura tare da yin wuki wuki alamar rashin gaskiya na bayyana akan fuskarta da jikinta,tsayawa yayi yana kallonta na dan wasu dakiku, kafin ya ce"ina zezee?"jin abinda ya fada yasa ta samu abin fidda kanta daga zargi, ta ce dashi"kaga nima tun dazu nake neman wayar ta amma ba a dagawa yanzu ma kuma gwadawa nake yi ko zan dace, wallahi abban zeze gaba daya bana cikin nutsuwata saboda tunanin halin da take ciki, dan an ce min dasu a firgice ta fice daga gidan, ga danuwar da muke ciki ta rashin sanin abinda ya faru a wajen daurin aure"zama yayi bakin gadonta yana cewa"abinda ya faru dazu da safe ba abu ne me dadin ji ba,amma dai ina so ki sani ,an rusa farin cikin yarki saboda an daura mata aure da wani can bare wanda bata sanshi ba bamu sanshi ba, Sannan ba mu san daga duniyar da ya fado ba,Ni kuma an ruguza min duk wani shirina,komai nawa yana neman lalacewa amma ni Alhaji dan gaske nasha alwashin ba zan fadi ni kadai ba,dole mu yi mutuwar kasko ga koma waye yake son ganin bayana"ya kare maganar da cewa"sake kiran zezee din ko zata daga, saboda a halin yanzu na san a kwai boyayyun bakiyana da suke gaf da ganin bayan duk wani nawa da ya shafeni, dan haka ba zan yi saken da zasu shammaceni su raba Ni da komai nawa ba".

Cikin saurin da ya haifarwa da mommy rawar hannu ta shiga kiran, zezee, cikin sa a kuma sai a ka daga,"cikin saurin murya Mommy ta ce"dan Allah ina me wayar take?"moses da shine ya daga wayar bayan yasa wata likita ta miko masa ita daga cikin jakar zezee din ya ce"lafiya ba lafiya ba, amma dai yanzu Ku zo nan asibitin Aminu Kano emagency saboda ta ɗan samu attack"what"Alhaji dan gaske da yake sauraronsa ta hanyar sanya amsa kuwa da mommy ta yi ya fada yana tashi tsaye,"idan kun zo gwaji daga bakinta"abinda moses ya fada kenan ya kashe wayar,cikin hanzari Alhaji dan gaske ya fita, Mommy da tuni ta dauki mayafinta tabi bayansa kirjinta na dukan uku uku saboda fargaban abinda zasu je su tarar.

*****

A hankali ta bude kofar tare da yin yar karamar sallama,da sauri ta juya zata koma ganin yadda yake bacci hankali kwance, daga shi sai dan boxes wanda ko cinyoyinsa bai gama rafewa ba,har ta sanya kafarta daya a waje hannunta akan handle din kofar, sai kuma ta tsaya can kamar wadda aka tsayar,kafin a hankali ta fara juyowa a cikin wani irin slow, kirjinta na dakan tara tara,bude idanunta tayi akan gefen cikinsa inda shatin yankan da aka yi masa ya bayyana, gashi nan ya ɗan fara warkewa, sai kuma idanunta suka koma kan......

Zahra✍

️***

GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol