Free chapter · Read without an account

Pg39

by Fatima Yushau adam · GIDAN YAN KARYA

Da sauri ta sake shi tare da daga rigarsa sama, take idanunta suka kuma firfitowa waje,saboda tsananin razana da mamakin da ya ke nema kashe ta a tsaye,saboda ganin fatar jikin gentle ta yi matukar banbanta da fatar fuskarsa,saboda fatar jikinsa chaculate ce me haske wanda ba za a ace masa baƙi ba,shi kuma fuskarsa kai tsaye za a kirata da baƙa,janye jiki ta yi daga gareshi tana kallon fuskarsa sai kuma ta dawo ta kalli jikinsa,kafin ta nuna shi da yatsa bakinta na rawa ta ce"yaya Dr daga jiki, daga fuska kuma yaya gentle me hakan yake nufi?".

Bai amsa ta ba sai juyawa da yayi ya karasa bakin mirror ya sanya hannu ya shiga daye fuskar da take kan ainahin fuskarsa,sakin baki da hanci da ido Ummul ta yi tana kallon abin al'ajabin da tunda uwarta ta kawo ta duniya bata taɓa gani ba,tana kallonsa sake da baki ya dauki wani abu ya goge fuskarsa sai gashi ta kuma dawowa fes ta cikakken Dr kuma pilot BILAL AHMED ƊAN ITOPIA,tsananin shock da kidima yasa Ummul ta tafi luuu zata fadi sai dai kafin ta kai ga zubewa ya tare ta a jikinsa,dan marin fuskarta ya shiga yi amma da ta bude idon ta ganshi sai ta kuma sumewa,kwantar da ita yayi a kan gadon ya dauko gorar ruwa a firinji ya shafa mata amma ko da ta farka tana kuma ganinsa zata koma,numfashi ya sauke yana tunanin ta inda zai fara gyara wannan gagarumar barnar da ya tafka,dama kullum rana ta Allah da tunanin ta yadda zai fidda kansa a wajen Ummul ya ke,yasan cewa akwai ciwo abinda yayi din to amma ya ya iya, idan ba hakan yayi ba ba zai taba samun soyayyar gaskiya ba ,tunda shima yana son yaga yayi aure ya tara zuri'a masu albarka kamar mahafinsa,ya san dama zai sha wuya da karamar ƙwaƙwalwar Ummul ba kamar iyayenta da suka fahimce shi kuma suka ci gaba da ta ya shi yakin nema ba tare da sun bayyanawa Ummul din komai ba.

Kwantar da ita yayi a jikinsa saboda bai san ta yadda zai sanar da su ummi halin da ake ciki ba, tunda dare ya fara yi,haka ya ci gaba da rukonta a jikinsa yana rasa abin yi, dan shaf ya manta waye shi a daidai wannan lokacin da yake tsaka me wuya dan bai san wane irin hukunci Ummul zata yi masa ba,amma dai yana fata ta yi masa sassauci ta hanyar barinsa da ita muddin rayuwa ko da zasu rayu ba tare da digon soyayyarsa a ranta ba,ko da zata ce tana so ta rayu da shi a matsayinsa na gentle ba Dr Bilal ba,shi dai burinsa numfashin ta ya kasance a kusa dashi wannan ka dai ya ishe shi farin ciki da rayuwa me dad'i.

******

Tun mommy na ci gaba da kokarin dauriyar rike nata kukan har tazo ta kasa rike shi ta shiga taya zezee nata kukan ba tare da ta samu damar rarrashinta ba,sai da suka yi me isarsu kana suka hakura, sai a lokacin zezee ta dago kanta tana cewa "mommy karashen labarinki shine halin da nake ciki a yanzu ni da Abba wanda har yanzu ya ki gane cewa akwai Allah,mommy duk da cewa Abba shine ya haifeni amma wallahi ba zan taba yafe masa ba,saboda shine silar shigata duk wani hali da nake ciki a yanzu, dan da ace Abba bai kawo Dr Bilal cikin rayuwata ba da yanzu ina nan ina farin cikina kamar ko da yaushe,mommy Abba ya cutar da ke amma ina so kamar yadda kika dau shekaru kina hakuri dashi to ina so yanzu ma ki ci gaba da hakuri dashi na wasu yan kwanaki, na tabbata miki da cewa da idanunki sai kin zubar masa da hawaye saboda tausayin halin da zai shiga"girgiza Kai mommy ta yi tana dan sakin murmushin yake , sannan ta ce"zezee baki san zafin mutuwar iyeye ba ne,zezee ko da gaisuwar mutuwar iyayenka wani ya ki zuwa maka fa zafinsa kake ji,.sannan ba ka taba daina jin haushin wannan mutumin har sai ranar da ya wanke kansa ta hanyar yi maka gaisuwa ko da a hanya ne,bare kuma wanda yasa hannu da kansa ya kashe maka su akan idanunka kana ji kana gani aka raba ka da salihan iyayenka, wallahi zezee ki bar ganin cewa ubanki bai da hali kuma kina jin haushin sa to ko yau ya fadi ya mutu sai kin ji ciwon mutuwarsa bare kuma nawa iyayen da suka zama abin alfahari na".

Rungume juna suka yi suna ci gaba da kukan da babu me rarrashinsu,turo kofar da aka yi aka shigo shine abinda ya dakatar da kukansu tare da sakin juna suna kallon mai shigowar,"raliya"mommy ta ambata tana leken bayanta dan ganin ko ita da waye,ganin babu wanda ya shigo bayan ita yasa mommy saurin karasawa ta rufe kofar da key sannan ta dawo ta rungume raliya tana sambarka da farincikin ganin raliyar,"zezee da ke yiwa raliya kallon rashin sani ta ce"mommy wacece wannan?"hannun raliya mommy ta kama suka zauna Sannan ta dubi raliyar ta kuma dubi zezee ta ce"zezee wannan ita ce macen da na sani a cikin dangina gaba daya, Allah ne ya kawo min ita lokacin da nake tsaka da bukatar wani makusanci,ita ma kuma ta neme ni ne saboda rashin sanin dangin kusa da na nesa,a takaice dai wannan da kike gani da kakarta da abbana uwa daya Uba daya suke"rungume raliya zezee ta yi tana cewa"to amma mommy me yasa ban taba ganinta a gidan mu ba?"murmushi mommy ta yi sannan ta bawa zezee amsa da cewa akwai dalili amma ko ma meye zaki sani saboda a yanzu ba mu da lokaci dare yayi sosai".

Raliya ta ce"haka ne nima bana so dan gaske ya dawo ya sameni dan ban shigo nan din ba har sai da na tabbatar yayi nisa"mommy ta ce"ashe dai dazun ke ya gani ba gizo kika yi masa ba"?jinjina kai raliya ta yi tana duban zezee da ta ke dan gyangyadi saboda alluran da aka zuba mata na bacci a cikin ruwan da ake kara mata, sannan ta ce"aunty bilki muje mu bar zeezee ta yi bacci ko ta ɗan samu relief"Mikewa su kayi gaba daya suka fice daga dakin.

Suna fita mommy da take a zaƙe da su fito taiwa raliya tambayar da take cin ranta ta ce"raliya me yake faruwa ina kika shiga?"wani dan kujerar dutse suka zauna raliya tana cewa"ke dai kawai a yi sha ani"daga nan ta kwashe yadda su kayi da dan gaske ta gaya mata,kuka mommy ta sa tana cewa"Ni na jawo miki raliya da ban Sa ki wannan aikin ba da ba zaki sha wahalar da kika sha ba"dariya raliya ta yi sannan ta kalli mommy tare da cewa"wa ya ce miki aikinki kadai na yi?"kamar ya mommy ta fada cike da alamun mamaki da son karin bayani,dariya raliya ta kuma yi tana cewa"kar ki damu lokacin da zaki san komai ya kusa amma dai ina so na tabbatar miki da cewa daga yau ki fara bacci har da munshari domin burinki yana daf da cika na son ganin yadda rayuwar dan gaske zata sauya, sannan ki shirya karbar kadarorinki ki fara amfani da computer dan neman karin haske a cikin harkokin kasuwanci"mommy zata yi magana raliya ta dakatar da ita ta hanyar cewa"bana bukatar wasu ƙarin tambayoyi daga gareki,kawai ki yi amfani da maganata amsoshinki kuma zasu zo har inda suke su sameki,ni na wuce zan kuma bullowa idan na tabbatar dan gaske baya kusa"daga haka ta gyara zaman jakarta ta mike ta bar mommy da baki sake cike da mamakinta.

******

Lokacin da Alhaji dan gaske ya fice daga dakin moses kai tsaye gida ya wuce ba tare da ya kuma waiwayen dakin zezee ba,tunda ya koma yake kaiwa da kawowa ya rasa wane irin tunani zai yi,da farko dai zuciyarsa ta ayyana masa da ya je ya bawa Alhaji Ahmed hakuri akan abinda yayi masa, wannan shawarar takarbu a ransa, sai kuma ya fara kokarin tattara takardun kamfanoni da gidajen da ya mallaka ya kuma sake musu guri dan ji yake ajikinsa kamar zai rasa su,daga nan kuma sai ya fara lissafin ta inda zai fara neman su Ummul, shima take zuciyarsa ta aiyana masa cewa zai iya samun su ta hanyar Dr Bilal,sai abu na gaba,yadda zai kashe killer a cikin wannan asibitin, to amma a wannan bangaren ya duba ya murza ya ga cewa sai ta hanyar daya daga cikin likitocin da suke kula da moses ne kawai zai samu biyan bukatarsa,idan yaso yana gamawa da wannan sai ya koma kan Alhaji Ahmed wanda ya yanke shawara cewa da zarar ya yi masa afuwa bisa laifin da yayi masa zai sa a shiga har gidan a kashe su daga shi har uwar Dr , daga nan sai ya fara yiwa ya'yan dauki dai-dai,tunda a yanzu yana ganin babu wani sirri na dukiyar Alhaji Ahmed da bai sani ba,kai shi gani yake har ya fi Alhaji Ahmed sanin sirrin dukiyarsa karshenta ne kawai bai sani ba,amma tabbas yasan zai mallaki duniya da zarar ya gama da Alhaji da iyalansa,wadan can kananun kwari ne a wajensa dan yasan ko bai kashe baffa ba to tabbas zai iya rayuwa da Ummul ba tare ya samu wata matsala ba, wannan tunanin nasa shine dalilin kawo yar nutsuwa a zuciyarsa.

*****

Ko da yan unguwa suka kai bely station hajaran najaran suka bayar da bayanan abinda suka sani,daga nan suka yi tafiyarsu suka barta anan,cikin halin mutuwa ko rai,yan sandan ne suka sa aka dan to mata treatment ta ɗan dawo hayyacinta,to ashe su da manufarsu ta yin hakan dan cikin dare suka bude wajen suka dauke ta suka fita da ita can bayan gari wani kango suka yi abinda suka ga dama da ita wajen su hudu ko wanne sai da yayi yadda ya so da ita sannan suka barta a nan a yashe Babu alamun nunfashi.

*****

Cikin dare Ummul ta farka ta ganta a jikin Dr Bilal,ai ko wata irin kara ta kwalla tana kokarin barin jikinsa,cikin zafin nama ya kamata tare da rufe mana baki yana cewa"Ummul Are You ok"?Amma ina bata ma sauraron abinda yake fada kokowar kwace kanta kawai take daga gareshi saboda yadda take jin tsananin zafinsa ko fuskarsa bata son bude ido ta gani,rikon tsaurin da yayi mata ne yasa ta kasa kwatar kanta daga gareshi,hakan yasa ta fashe da wani irin kuka me sosa ran me saurare,rungumeta yayi sosai yana jin kukan har cikin ransa yana cizonsa,"am sorry"abinda ya shiga fada a cikin kunnuwanta ke nan,girgiza kanta ta shiga yi tana bugun kirjinsa da duk karfin ta amma hakan bai sa ta ji zafin da ke ranta ya ragu ba,cikin kuka ta shiga cewa"me yasa me na yi maka zaka shiga rayuwata ka dinga wasan ƙwallo da ita?me na yi maka?wace irin tsana ka yi min?me yasa zaka raba Ni da abinda na fi so fiye da kaina?me yasa ka zama silar bakin ciki na?Ni fa ina son Yaya gentle a duk yadda yake, kuma zan rayu dashi a ko wane yanayi dadi ko tsanani,dan Allah ka dawo min da yaya gentle shi nake son gani shi nake son ji,da shi na saba",wani irin zafi kansa ya dauka, hatta da zuciyarsa ta dauki zafin kalaman Ummul duk da cewa gentle din da take ambata ba kowa ba ne face shi da kansa,to amma shi ba haka yake so ba,so yake Ummul ta karbe shi ta bar maganar gentle ta manta dashi a rayuwarta,sosai ya samu kansa da jin kishin gentle din fiye da yadda bata zato,baki tasa a kirjinsa ta gartsa masa cizo tun karfinta har sai da ta fara jin gishiri_gishirin jini a bakinta, sai dai ga mamakinta har lokacin yana rike da ita babu wata alama da ta nuna mata cewa ya ji zafin cizon da ta yi masa,shatin jini ne ya fito a jikin farar rigar baccinsa kadan wan da shi ya kuma.tabbatar mata da cewa ta bula masa fata da hakorinta,wai kuka sai ta ji kamar zata ji tausayinsa har ta kai hannu zata taba wajen sai kuma ta fasa ta janye hannun da sauri tare da maida kanta kan kirjinsa ta kwantar tunda ta gwada duk wata hanya ta kwatar kanta amma ta kasa hakan yasa ta mika wuya amma ba dan ta karaya ba.

Dr Bilal yana jin duk irin kiriniyar da Ummul take masa har zuwa kan cizon da ta yi masa,amma bai nuna wata alama ta cewa ya ji ajikinsa ba bare ta sa ran abinda ta yin zai kwaceta,yana jinta ta gaji har bacci ya debeta, sai a sannan ya ɗan motsa ka ɗan dan ya fahimci inda baccinnata ya dosa,ganin bata motsa ba yasa shi gyara kwanciyar tasu sosai akan gadon yana shafa gashin ta da duk ta hargitsa shi,idanunsa akan kyakkyawar fuskarta da dan karamin bakinta da ta cunoshi kana gani kasan cewa wannan baccin na rigima ne,ka sa daurewa yayi har sai da ya kai bakinsa kan nata ya ɗan tsotsi lebanta na kasa da tafi cuno shi gaba,kusan minti ɗaya sannan ya saki ya tashi ya dauko wasu kayan bacci masu kyau riga mata hannu me santsi sai gajeren wandon da bai rufe mata cinyoyinta ba, da kyar ya iya daurewa ya sanya mata kayan ba tare da ya biyewa zuciyarsa da take masa tsunkuli ba,maida ta cikin jikinsa sosai yayi kamar wanda aka ce za a kwace masa ita yana neman baccin da yake don kauracewa idaniyarsa.

****

A can bangaren su Ummi da baffa kuwa hankalinsu yq kwanta, saboda duk abinda ya kamata su sani akan gentle ko na ce DR Bilal sun sani, Sannan sun amince da dalilansa na yin hakan,shi yasa suka kwantar da hankalinsu suka bude sabuwar rayuwa a ɓangaren da ya basu su zauna kafin abubuwa su lafa,ba a kusa suke da juna ba shi yasa duk iface ifacen da Ummul ta ke yi basu san tana yi ba, wannan ke nan.

****

Da asuba har ya fita Sallah Ummul bata farka ba,shi kuma tsoron tashinta yake saboda rikicin ta ɗan haka ya fice ya barta a cewarsa idan ya dawo bata ta shi ba ya tasheta,bai ta fi ba sai da ya tabbatar ya rufe ta ta waje sannan ya fita suka hade da baffa,

Bai jima da fita ba kuwa Ummul ta farka daga yin addu'a kuma ta fara murza ido zata saki dan ƙa,idar, hasken agogon dakin ne ya haske mata ido ta ga lokaci wanda hakan ne ya sa ta yi saurin mikewa ta nufi hanyar ficewa, to amma tana murda handile din kofar ta ji kofar a rufe gam,idanunta ne suka cika da ruwan hawaye ba dan taso ba ta shiga bayinsa ta dauro alwala,tambayoyi na cin ranta sai dai bata jin zata iya tsayawa a gabansa bare har ta yi masa wadannan tambayoyin,duk Acikin abin nan babu abinda yafi daure mata kai sai irin yadda take ganinsa a wajeje daban daban kuma duk kusan a lokaci daya, duk sanda zata rabu da Dr a asibiti to yawanci idan ta dawo zata samu gentle a kofar gidan, Sannan ya aka yi bayan yaran dan gaske sun kama shi ya kubuta,kai gaskiya Dr Bilal ya raina mata hankali ,abubuwan da ta dinga tunawa ne suka sa ta kuma jin wani irin haushi da tunzurin zuciya akansa.

Hijabi ta gani kato me kauri har kasa a saman gadon, dan haka ta dauka ta warware tana shirin sawa ta lura da kayan dake jikinta,sosai hankalinta ya tashi ta shiga tambayar kanta wanda ya cire mata kaya har ya sauya mata da wannan fandarinka ɗin?yanzu fa duk wanda ya canja mata kayan yaga jikinta kenan?ji ta yi hankalinta ya kuma ta shi,ganin lokaci zai wuce yasa ta hakura da tunanin yadda aka yi kaya suka zo jiki ta ta tada sallar .

****

Lokacin da baffa da Dr bilal suka fito daga Masallaci,baffa yake tambayar jikin Ummul yar daru,To anan ne Dr Bilal yayi masa bayanin abinda yake faruwa cikin nutsuwa,dan jim baffa yayi daga bisani kuma ya ja dogon numfashi yana cewa"bilalu ina ganin ya kamata a ce mun bar gidan nan ma ana mun koma inda muka fi wayo,saboda idan har muka ci gaba da zama da Ummul a cikin wannan yanayin to tabararta karuwa zata yi ba zata taba tsayawa ta fahimceka ba,musamman idan tana ganin umminta,dan haka kawai mu tafi yau din nan kuma yanzu ba sai an jima ba, Sannan ko sallama ba za mu yi mata ba,idan kun koma gida ma yi waya"Dr Bilal yace"a'a baffa ba za ku koma wancan gidan ba, kasan har yanzu dan gaske yana neman ku ruwa a jallo, kuma ba yanzu ne lokacin da ya kamata ya san komai ba,na fi son komai abishi daki_daki kuma Asannu ta yadda abin zar girgizashi matuƙa"baffa ya ce haka ne kafi ni gaskiya a wannan gabar"jinjina kai DR Bilal yayi Sannan ya ce na gode baffa, yanzu ku shirya zuwa an jima akwai gidan da na jima da tanadar muku dan haka can za a kaiku, da akwai security da na sa za su yi gadinku kafin komai ya zo karshe in Sha Allah"to madalla babu abinda zamu ce da kai wanda ya wuce mu yi ta muku addu'a Allah ya ci gaba da kare ku daga sharrin makiya ya inganta rayuwarku ya baku zuri a ta gari,su kuma su Alhaji dan gaske Allah ya shirya su idan bama su shiryuwa ba ne Allah ya shiga tsakaninmu da su,yayi mana katangar karfe da su"da Amin Dr Bilal yake ta amsawa har suka rabu da baffa.

Baffa yana shiga bangaren da suke, ya yiwa Ummi bayanin abinda suka tattauna da surukinnasu,to itama dai ta gamsu da shawarar baffan amma dai ta so a ce ta ga Ummul din kafin su tafi,fahimtar hakan da baffa yayi ne ya sa shi zama ya kuma yi mata bayani ta yadda zata fahimta ta bar Ummul din ita kaɗai,sosai ta gamsu , dan haka karyawa su kayi kawai ta shiga haɗa musu kayansu da basu wuce a zuba a jaka daya ba.

*****

Ko da ya koma a kan sallaya ya sameta hannunta rike da Alkur'ani tana karatu amma fuskarta shaɓe shaɓe da hawaye har da shan majina,mai da kofar yayi ya rufe tare da cire key din, sannan ya karaso ya zauna a bakin gadon yana kallonta har ta kai aya ta yi addu'a suka shafa a tare,ƙin kallonsa ta yi amma haka nan take jin kallon da yake yi mata yana kassara duk wata gaba da laka tare da jinin da ke guda a cikin jikinta,tsananin kwarjininsa ya hanata yi masa fitsarar da ta so yi masa dan ya rabu da ita ta tafi wajen ummin ta su bar masa gidansa,sai ma samun kanta da gaida shi da ta yi,sai dai ji take kamar ta zane kanta saboda takaicin abinda take yi ɗin,a nutse ya amsa mata a can kasan makoshinsa yana mai ci gaba da karade ko ina nata da kallon kurilla, wanda ita kuma yake matukar cutar da ita wajen kasa sarrafa kanta da take yi, ta shi ta yi ta linke abin Sallah sai dai ta kasa cire hijabin saboda, kayan da suke jikinta,kanta yana kasa ta ce masa"dan Allah na dan tambaye ka?"uhm ya ce yana kuma zuba mata narkakkun idanunsa da suke sanyata sanyin jiki,"um um hmmm dama cewa zan yi ko kasan wanda ya sauya min kaya?"shi abin nata ma dariya yaso bashi,sai dai a maimakon hakan sai cewa yayi da ita"na sani matso na nuna miki shi"da wauwa irin ta Ummul ko kuma nace shirme irin ta auntanci da kuruciya sai ko ta taka zuwa har gabansa tana dan kalle kalle ko zata ga wani bayan su a cikin dakin,ganin bata ga kowa ba yasa ta ɗan kalli gefensa saboda fa kasa kallon idanunsa da bata fiya ganinsu ziryan din su ba acikin glass ba,ta ce" waye dan Allah ka fada min ina son na tafi inda gun um....kafin ta karasa yasanya dogayen hannayensa ya janyo ta jikinsa tare da zame hijabin da take ta faman nuku nuku a cikinsa.......

Zahra✍️

***

GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol