Free chapter · Read without an account

Pg41

by Fatima Yushau adam · GIDAN YAN KARYA

Cikin tashin hankali mommy ta rike zezee tana tambayarta abinda ta gani ta rude haka,amma ta kasa magana sai haki da nuna hanyar falon,ganin haka yasa mommy ta kama hannunta suka shiga falon,sai ya kasance ma mommy tafi zezee tsorata saboda ita bata san Moses ba,baya ta yi tana rike zezee a dan tsora ce tana tambayar moses da yake kwance akan kujera irin kwanciyar da ake yi masa asibiti,"kai waye?gurin wa ka zo?"dariya Moses ya yi tare da cewa Ni mijin yarki ne kuma gurinta na zo"ya dubi zezee yana ci gaba da cewa"kin dauka zaki iya guje min ne?to kyale ki na yi kawai saboda na tabbatar miki da cewa duk inda zaki shiga ina tare da ke dan ko ubanki Salisu dan gaske bai isa raba ni da ke ba, duk shu'umancinsa kuwa,saboda yanzu ba da bane,idan a baya ya ci galaba a kaina to ina mai tabbatar muku da cewa banda yanzu,dan haka sai ki zo ki daura damarar yin jinyar mijinki"ya fada yana wani murmushin mugunta.

A fusace zezee ta nuna shi da yatsa tana cewa"wallahi baka isa ba ka yi kaɗan na zauna na yi jinyarka,kuma dole ka bar gidan nan tunda ba na ubanka ba ne"ware ido yayi tare da cewa waww yarinya amma kin burgeni da wannan karfin halin naki,to na ji ba gidan ubana bana ne,amma ke ma ba dan darajar gidan na uwarki ba ne da sai na ce baki da iko dashi,yanzu duk ba wannan ba dan Allah kizo ki kaini daki na huta kin san dai halin da nake ciki dole ki lallabani dan kar ki jangwale min masifaffan ciwon da kika jawo min"daki kuma?" ta maimaita yana zaro idanunta waje,numfashi mommy ta ja sannan ta dafa kafadar zeezee cikin kwantar da murya ta ce"zezee barshi kawai kar ki daga hankalinki muje ciki yanzu zan sa a kaishi inda zai zauna,ko mai yayi farko yana da karshe Allah yasa wannan ya zama darasi da sanadin dawowarki cikin hayyacinki"babu yadda zezee ta iya sai bin bayan mommy da ta yi tana yi tana waiwayen moses,sai dai kuma kalaman mommy sun dawo da iya hayyacinta,in sha Allah zata koma ga Allah ko ta samu sassaucin ƙaddarar ta.

*****

Dr gentle yana fita Ummul ta saki ajiyar zuciya, kafin ta mike tsaye ta karasa gaban mirror tana kallon kanta,ganin yadda ta yi kyau yasa ta saki murmushi tana cewa"wallahi na yi kyau dama haka turawan nan suke ji idan suka saka irin wannan kayan?"ta yi tambayar da babu me bata amsa,can kuma ta tsaya da abin da take yi lokacin da ta tuna halin da take ciki,cikin sanyin jiki ta koma bakin gadon ta zauna, zuciyarta na hasaso mata lokuta da dama da gentle ya dinga raina mata hankali,akwai lokacin da suka je gidan cin abincin nan ya raina mata wayo da cewa ta fada musu wai ita kanwar me wajen ce,sai kuma kyautar da aka yiwa nouse da sunanta,jikinta me ya kuma yin sanyi haka nan take ji a ranta da zuciyarta Dr gentle bai cancanta da tafiyar ta ba,sosai take jin kewar gentle dinta wanda take ji da ace Dr zai koma mata gentle dinta na baya me nema kullum da sai ta fi farin ciki da oda zuciyarta da kaunar gentle ta ginu wanda mafarin kaunar shine tausayi,idanunta ne suka sauka akan wayar sa da take kawo haske, da sauri ta dauko tana kallon screen din wayar da sunan wanda ya kira yake ta harbawa,bata fahimci sunan da aka yi save da shi ba dan wani yare ne da tasan ba turanci ba ne,tana gab da katsewa ta daga ba tare da ta tsaya sauraron me kiran ba,ta fara magana cikin kuka da sanyin murya dan sosai take jinta kamar wata marainiya"dan Allah idan har me saurarona yana jin Hausa kuma idan har ba bakinsa daya da me wayar ba,to dan Allah ya taimaka ya kawowa rayuwar Ummul ikram dauki,bani da kowa yanzu ya rabani da yan uwana da iyayena saboda a gaban idona suka tafi suka barni suna kallo ina daga musu hannu amma ba wanda ya damu da ya tsaya yaji damuwata,dan Allah a zo a dauke ni da ga gidan nan tun kafin na hadiyi zuciya na mutu"ta karasa maganar cikin rera kukan da duk wanda ya ya saurara zai tausaya mata yasan cewa kuma tana bukatar taimako.

Cak kukanta ya tsaya lokacin da ta ji wata kamilalliyar muryar dattijuwa tana cewa"yi shiru ikram da kaina zan zo na dauke ki daga gidan tun da baki son zaman gidan babu me takura miki,idan su sun gudu sun barki Ni ina bukatarki dan haka ki kwantar da hankalinki kinji"sosai Ummul ta ji wata irin natsuwa da kaunar matar da bata taba gani ba kuma bata san wacece a wajen Dr gentle ba,dan haka sai ta yi shiru kamar yadda matar ta umarce ta,tare da cewa"to mama na yi shiru amma dan Allah ki zo yanzu saboda bana so ya dawo ya kuma cewa zai yi min wanka ya shafa min mai,wai dan wayo ha....ƙit ta ji matar ta kashe wayar ,bin wayar ta yi da kallo kafin ta ajiye tana cewa"ai dai ta ce zata zo ta tafi da ni,ni wallahi koma wacece zan bita tun da su Ummi sun daina sona"wannan ne abinda ya kara karyar mata da zuciya ya sanya ta kwanta a kasan wajen tana ci gaba da kuka ga kuma wata irin kewar yaya gentle dinta da take ji yana bin ko wace gaba da jinin dake gudana a jikinta.

******

Babu laifi bely ta ɗan fara dawowa haicinta sai dai kuma wata sabuwa in ji yan caca,tun bayan rashin da ar da yan sandan nan su kayi mata, bata sake jin lafiyar mutuntakarta ba,domin kuwa wani irin azabar kaikayin da bata taba sanin da shi a duniya ba ne ya sameta,bata isa yin zaman minti ɗaya ba ba tare da takai hannu wajen nan ba,da dai taga abin yana neman haukatata sai ta kuma kiran likita ya dubata a inda ya tabbatar mata da cewa ,mugun infection ne ya kamata me tsananin wuyar magani saboda ba na iya mutum daya ba ne,a yanda ya fasa mata ya ce,wanda take ji shine ma me sauƙin saboda shine ya bayyana ragowar dole sai ta je asibiti sun yi mata test sannan zai san irin maganin da zai dorata a kai,hankalin bely ya tashi ganin kwana ɗaya ta yi tana amfani da magungunan da ya bata amma kamar kara mata wutar azaba ake,har ta kai ga bata iya sanya komai a jikinta,ko bacci zata kwanta sai ta bude jikinta ta sakarwa kanta fanka take dan samun yin baccin shima tana yi tana farkawa saboda azabar kaikayi,har ta kai ga wajen sun fara yin jini da zarar ta sosa,a yau dai tuni ta yanke shawarar tafiya asibiti a yi test dinta sannan taga babban likitan da zai iya magance mata damuwarta.

****

Alhaji dan gaske yana fita daga Company kai tsaye killer ya kira ya gaya masa inda yake so yazo su hadu,babu jimawa killer ya zo ya shiga motar Alhaji ya rufe yana cewa"ya haj ka kwantar da hankalinka a wannan karon ba zan yadda na yi maka ba dai dai ba dan haka ka fadi abinda kake so yanzu bayan issues din waɗancan mutanen"juyawa dan gaske yayi yana fuskantar killer da idanunsa da suka yi wani irin ja kamar an kunna wutar aci balbal a cikinsu,sai da ya ja wasu yan sakanni kafin ya furzar da wani irin zazzafan tururin hucin wutar da ke ci a cikin ransa sannan ya ce"killer da wa kake ganin zamu fara,dan ko uban dan a yanzu ba iya dukiyar su ce burina ba,har rayukansu sun shiga cikin lissafin burikan da nake son cimmawa"killer ya ce"ya haj Ni ina ganin ka fara ta kan uban tunda shi ɗan har yanzu bai san komai akan dukiyar ubansa ba,kuma naga shi yafi ganewa saka wannan fararen kayan dan haka nake ganin cewa ba zaka sha wahala wajen karbe komai daga gare su ba,a ganina idan ka fara kashe dan shike nan ka toshewa kanka hanyar samu, sannan a yanzu Dr bai san komai da yake tsakanin ka da ubansa ba,dan haka kawai mu bi ta kan uban shi kuma ɗan sai ka lallabashi ta ƙasa ka kwashe komai sai kawai a sasu bacci daga shi har yan uwan nasa,amma dai yanzu ka bani nan da kwana biyu zan kamo maka shi wancan karamin kwaron da hannunka zaka fasa masa kokon kai da bindiga"jinjina kai Alhaji dan gaske yayi cike da gamsuwa akan shawarar da killer ya bashi.

Wayarsa ce tayi kara kamar shigowar sako, yana duba fuskar wayar yayi wata uwar zabura hade da kunduma wata uwar ashar yana cewa kai"killer Zo ka ja motar nan ka kaini First bank dan naga abun nasu ya koma rainin hankali,dazu da na duba balance naga sun kwashe min almust 20mill,yanzu kuma an kuma kwashe 30mll, amma dai bari na fara ji daga gare su tunda Ni ba sanin harkar da ta shafi bank na yi ba"ya fada yana tsane gumin da yake tsatstsafo masa,canjin guri su kayi da killer Wanda ya figi motar sai first bank.

Kafin su kai ga karasawa bankin,daya daga cikin ma aikatan da suke masa managing Company ya kira shi a gigice yana sanar dashi cewa an kawo musu takarda daga kofishin nnpc ,kuma'a take ba tare da karbar wani uzuri ba an rufe musu Company har sai an gama bincike a kan Company ɗin,wata irin guguwar tashin hankali ce ta kuma mamaye shi,cikin tashin hankali ya ce"da killer su juya zuwa kofishin, wannan wane irin bala i me,ake son talautashi cikin yini guda,bai gama da tashin hankalin kwashe masa miliyan hamsin ba,sai ga shi ana shirin gurguntashi ta hanyar son kwace masa Company da yafi ko wane Company a cikin kamfanunuwansa,a wannan lokaci tarwatsewa ne kawai zuciyar dan gaske ba ta yi ba,amma duk wani bugu ta riga ta gama yinsa.

******

Ko da Dr gentle ya dawo dakin tsit ta yi ta daina kukan sai sheshsheka da ta ci gaba da yi, tana manne da gado ta hade kanta da gwiwa kamar wata marainiyar da ta rasa uwa,a gabanta ya ajiye dan bowl din ds ya ciko shi da chips da kwai ga kuma sos a gefe abin gwanin sha a wa kamar ba girkin namiji ba, hannunsa kuma yana rike da kakkauran shayin da ya hado mata yana dan juya spoon din da yake ciki saboda zafin shayin ya ragu,wani irin miyau Ummul ta hadiya saboda yunwar da take ji,amma sai ta wani kau da kai tana yatsina fuska kamar ta ga abun kyama,fuskar nan babu alamun wasa sai tsananin fuskewa da kwarjinin sa me tasiri musamman a wajen masu kiriniya da fitina irin su Ummul,ya ce"oya ki cinye yanzu ko kuma "....sai yayi shiru bai karasa ba,ganin ba wasa ga kuma yinwar da take neman karta yasa ta sa hannu a bowl din ta fara ci,mika mata shayin yayi ba tare da ya ce mata komai ba,shima karba ta yi ba tare da musu ba,yana kallonta har ta cu iya cinta ta fara cakula saboda jinta ce masa ta koshi ta san ba yarda zai yi ba,ita kuma haka Allah yayi cikinta baya iya daukar abinci me yawa,dan kansa ya ga dama ya janye daga gabanta ga mamakin ta hannu yasa ya cinye ragowarta ya kuma shanye raguwar shayin,da taga ya kalleta sai ta wayance da sakin hawaye tana kawar da kanta daga kallon da take masa tare da sanya hannu tana kare kirjinta da taga ya zubawa ido,wani kallo ya watsa mata kafin cikin muryarsa ya ce"wane dare ne jemage bai gani ba (a'a fa Dr gen daga yin wanka sai kace ka ga dare ko dan baka san Ni imar daren ba ne) Ummul kuwa ganin yaki daina kalli ta yasa ta mike zunbur kafin yayi wani yunkuri ta bude kofar ta fice da gudu,dafe kansa yayi cike da mamakin kuruciya da sakalcin Ummul.

Ummul kuwa tana fita falon ta ci karo da wata dattijuwar mata na shigowa bakinta dauke da sallama, da gudu kuwa ta yi wajenta ta rungume ta tana sakin kukan tabara kai ka ce ta san matar,to amma ko bata santa ba zuciyarta ta bata ita ce su kayi waya da ita yanzu , sannan duk da bata tsaya ta kalli fuskarta sosai ba jikinta ya bata cewa mahaifiyar Dr Gen CE,"to ba gani na zo ba meye na kukan"hajiyar Dr ta fada tana dago fuskar Ummul, daidai lokacin Dr Gen ya fito wanda yake yiwa hajiyar tasa kallon mamakin ganinta,kallonsa ta yi tare da cewa "maza je ka dauko min a baya ta saka mu tafi"wai kuma sai da hajiyar ta yi maganar abaya Ummul ta tuna a halin da ta fito to amma ta gode Allah da yasa kayan basu da sharara kuma bata tsaya a gaban hajiyar ba,Dr Gen bai ce komai ba ya juya, jim kadan ya dawo hannunsa dauke da ash din abaya me shegen kyau, da sauri Ummul ta zame ta yi ƙasa tare da durkushewa tana mai nuna tsananin kunyarta ga hajiyar,ganin haka yasa hajiyar ta juya tana cewa "idan ta saka kayan ka kawo min ita mota mu tafi"tana juya baya ya karaso ya duka gaban Ummul din tare da dagota suka mike tsaye,kasa ta yi da kanta saboda ganin yana kallon ta cikin wani irin yanayi kamar wanda zai yi kuka sai dai dake shi din jarumi ne sosai ya yi kokarin boye rauninsa akan Ummul din a gabanta.

Saka mata rigar ya shiga yi dake me botirance,a kasalance yake saka mata rigar kamar ba za'a gama sawa ba,botiran ya shiga balle mata wanda suke tun daga saman wuyanta har kasa,yadda yake ɓalle bitiran ma kansa wani irin yanayi yake saukar musu su gaba ɗaya,dan ita kanta Ummul din ji take kamar kafafunta ba zasu dauke ta ba,yana zuwa kan botiran tsakankanin kirjinta ta yi saurin rike hannunsa saboda jin yadda yake gogar jikinta yana tada mata da duk wata tsiga ta jiki,cikin rawar murya ta ce"Dr Gen mam mamma na jirana fa"wani irin rikitaccen kallo ya watsa mata da idanunsa da ta kasa tantance launinsu a daidai wannan lokacin,da sauri ta yi kokarin ja da baya amma sai dai ina ta makaro dan tuni ya hade tazarar dake tsakaninsu tare da shigar da hannuwansa ta cikin rigar abayar inda bai gama balle botiran ba,yana wani irin kai kawo da hannunsa a duk sassan jikinta kasancewar rigar tana da sulbi shi yasa hannunsa wucewa kawai yake yi,cikin wata irin sheshshekar da bata san tana yi ba ta bude baki zata yi magana amma sai caraf ya samu damar sanya harshen sa cikin bakin take maganar ta koma tare da miyansa da ya tara mata,a hankali kuma cikin wani irin salon da sai waɗanda suke cikin yanayi na kewa da muradin abinda zuciyarsu ta jima tana kauna, take kuma fatan samun yar karamar damar da zasu amayar da salon kaunar su da suka jima suna adawa abincin ruhinsu.

Tun Hajiya na kallon hanya har ta gaji ta koma cikin mota ta zauna tana irga yawan lokutan da Ummul ta shafe basu fito ba daga ita har wanda take kira bata son zama dashi din a taimake ta a ɗauke ta daga gidansa,jinjina kai kawai ta yi tana gyara zamanta ɗan tasha alwashin sai ta tafi da Ummul kuma ba zata dawo da ita gidan ba har sai ta furta da bakinta ta hakura ta yafe masa zata zauna da shi, dan haka ta yi damarar zaman jiran fitowar su ko nan da awa biyu ne.

A can kuma falo tuni dan gidan dan itopia ya manta waye yake jiran su a waje saboda ya shiga wata yar karamar duniyar da yake fata da burin shiga shida Ummul ikram yar fininanniyar matar shi me sanya bashi ciwon kai,daga can bakin kofar falon aka yi knocking wanda shine ya tunatar da Dr gen waye yake jiransu, a nutse ya shiga mayar mata da botitan a bayar da duk ya kwance su, duk da cewa sauri yake wajen maida mata bitiran amma ba ka fahimtar haka saboda komai nasa a nutse yake yinsa,sai dai ya gama sa mata sannan ya kalleta da idanunsa da har yanzu basu dawo daidai ba,kana muryarsa a can kasa ya ce"Ummul baki tausayi na, ba zaki yafe min ba ko da kin ji dalilina na yin abinda na yi?"shiru ta yi bata bashi amsa ba,sai ma zame jikinta da ta yi ta fara tafiya kamar wadda kwai ya fashewa a ciki, zuba masa ido yayi har ta fice dan shi kan baya jin zai iya fita ya haɗa ido da hanyarsa a wannan yanayin da yake ciki,tana fita ta samu Hajiya a kofar falon, kama hannunta ta yi tana cewa"Ummul ko kin fasa tafiya ne na barki a nan din naga kamar baki son tafiya?"da sauri Ummul ta girgiza kanta,sai dai kuma har suka fice daga gidan idanun ta yana kan kofar hanyar shiga falon da ta bar Dr Gen.

*****

Wanda bai san waye Alhaji dan gaske ba idan ya ganshi zai iya tausaya masa halin da ya shiga,saboda lokacin da ya je ofishin nnpc na nan Kanon kin sauraransa suka yi a cewarsu Babu ruwansu tunda kamfanin ba anan suke ba,dan haka yayi hakuri dole ne a fara binciken yadda a kayi ya samu Company saboda asali sun san me Company, kai magana dai da Alhaji dan gaske yake ganin ta karama sai gashi ta zama babba,yana barin wajen Alhaji Ahmed ne ya fado masa sai dai ba zai iya zuwa su hadu ido da ido ba,dan haka ya fara kokarin ganin Dr Bilal dan yasan shi kadai ne me fada aji a fadar mahaifinnasa,

Tun kafin ya gama neman hanyar ganin Dr Bilal din sai ga wani kiran daga dayan companin takalmansa da ke Abujan shima dai kamar wancan sun rufe shi sai bayan an yi bincike,Yanzu karamin kamfanin dake nan Kanon ne kawai yayi ragowa,duk inda kuke zaton hankalin dan gaske zai je ya je,sai gashi yana bulayi a titi har wajen karfe goma na dare, daga karshe dai ya koma gida inda ya na shiga falonsa ya tarar da wani tashin hankalin, to tashin hankali mana dan moses babban bala i ne rasuwarsa da ta yarsa,gashi yayi masa ganin bazata a cikin falonsa yayi kane kane yana baza iko kamar wani sarki, wannan da cikakkiyar lafiya ce dashi da ba su san me zai aikata musu ba,haka ya tsallake shi ya shige dakinsa yana Safa da marwa, wayarsa ya daga ya kira Dr Bilal take ya saukar da kai yayi masa bayanin abinda yake faruwa da taimakon da yake so a yi masa na karbar masa hakkinsa,ga mamakinsa babu wani musu Dr Bilal ya ce ba damuwa ya bashi lokaci zasu yi magana da babansa.

Wannan maganar da su kayi da Dr ita ce tasa ya san samu sassauci saboda yasan ko waye dan itopia a cikin kasar nan da wajenta ko da iya mutuncinsa da kowa ya sani zai iya karbe masa dukiyarsa musamman ya samu su dan jona shi a fam dinsu ko da ace dangantaka ce me tazarar sama da kasa ne......

Zahra✍️

***

GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol