Free chapter · Read without an account

Pg44

by Fatima Yushau adam · GIDAN YAN KARYA

"Ana dawowa gida bangare na ya zo,bai ce min komai ba ya shige dakina ya kwanta,ina ganin yanayin da yake ciki na fahimci cewa akwai matsala,daga Ni sai mahaifinsa ne muke gane damuwarsa saboda Bilalu jarumi ne da wuya kaga abinda zai yi masa jijjigar da zai bayyana damuwarsa a fuska,amma idan yana cikin farin ciki wani yana iya fahimta shima daga cikin makusantansa,ya jima a dakin ban tunkare shi ba har sai da na tabbatar da cewa ya samu natsuwa daga koma meye ya dame shi,cikin natsuwa na tambayeshi me yake faruwa?"budar bakinsa sai cewa yayi "Hajiya na fasa auren nan ku nemi wata har yanzu damar na hannunku?"daga haka ya mike zai fice, ganin da gaske fitar zai yi ba tare da ya cire ni daga duhun da ya sani ba yasa na kamo hannunsa na dawo dashi na zaunar, sannan na ce"pilot ya kamata ka sanar dani dalilin fasa wannan auren saboda na san dole akwai dalilin kuma sanin zai bani kwarin gwiwar fuskantar mahaifinka da maganar"sai da ya ɗan yi jim kafin ya sanar dani iya abinda ya gani daga haka bai sake cewa komai ba ya fice ya barni zaune cike da mamakin wannan rashin tarbiyya da rashin tsoron Allah irin na Nafisa.

Ni kaina ban yi kasa a gwiwa ba na nufi bangaren babansu na sanar masa da abinda ke faruwa da kuma hukuncin da Dr pilot ya yanke,ya jinjina lamarin sosai kuma bai ga laifin Dr akan hukuncin da ya yanke ba,dan haka kai tsaye muka aika musu da sako, yan uwa kowa aka sanar masa an daga auren, dan haka bakin da suka riga suka zo da wanda suke shirin zuwa duk suka koma gidajensu.

Daga nan ko wata daya ba a yi ba,sara ta samo masa wata yar uwar mijinta da suke zaune a nan Abujan,a nan ma dai ba mu sha wata wahala ba ya amince dan dama ya ce damar tana wajen mu,amma wannan karon cewa yayi ba zai je ya ganta ba kawai idan mun yadda da nagartar halayen ta bashi da damuwa,dan haka mun yi bincike sosai saboda gujewa samun wata matsala,daga nan aka fara shirin biki gadan gadan,bikin ba a fi sauran kwana biyar ba,sarah ta zo min da maganar da ya tashi hankalinmu gaba daya,wai ta je gidan su yarinyar da pilot zai aura, tun daga bakin kofar falon take sallama amma ba su ji ba,saboda idan Allah ya tashi kama mutum zai kama shi ne ta inda bai taba zato ba,jin basu amsa mata sallamar ba yasa ta shiga falon tana yan dube dube sai ta ji alamun magana daga can kuryar dakin mahaifiyar yarinyar,zama ta yi a falon ba tare da ta kuma yin magana ba,sai kawai ta jiyo Muryar 'ya da uwar suna tattaunawa akan yadda zasu kwashi dukiya da zarar an yi auren, abinda ya bawa sara tsoro shine jin har da batun kisa a cikin lamarin, ba ta bar falon ba har sai da suka gama tataunwarsu suka fito, sai dai kawai ganin ta suka yi a zaune ganin da yayi matukar razana su da sanya su cikin borin kunya, tambayar ta suka shiga yi wai yaushe ta shigo basu ji ta ba,budar bakin sara sai cewa ta yi "lokacin da kuka yi nisa wajen shirya mugun nufinku akan dan uwana"daga haka bata kuma cewa da su komai ba ta tashi ta tafi,maman na ta kiranta amma bata ko waiwaye su ba bare ta dakata, wannan shine sanadin fasa auren Dr na biyu.

Daga nan bamu karaya ba, muka kuma nema masa,sai dai ita wannan abin ya zo da sauyi dan har an daura auren sai dai a ranar da aka kaita, pilot ya jita tana waya da saurayinta akan cewa a Cikin daren zai yi hayar mutane su shiga su kwashe komai su kashe shi, daga nan sai ta fito su yi auren su tunda dama kudin da zai aureta ya rasa, yanzu kuma gashi sun samu hanyar arziki, wannan shine sanadin rabuwarsa da ma ce ta uku.

Tun daga nan sai muka kara daukar lokaci kafin muka nema masa auren, wannan karan ma yar wani yaron Alhaji ce,wanda shima daga karshe a ka samu labarin ha'incin da yake yiwa alhajin sannan da auren manufar da zai yiwa 'yarsa Dr,shima tun kafin a je ko ina aka fasa,to tun daga lokacin ne muka ji tsoron matan, shi kansa Dr ya ce baya son a kuma nema masa wata mace ya hakura da auren,daga nan ya koma aikinsa na yawo a sama sannan aka fara shirin gina wannan asibitin tasa ta Kano saboda shiryen shiryen dawowa da muke gaba daya,an dauki tsawon shekara daya kafin a kuma yin maganar aure,, sai kuma rana daya katsam Dr ya zo da maganar auren kanwar abokinsa Dr tukur,

Tukur wanda a lokacin bashi da wani amini kuma abokin shawarar sa sama da Dr Tukur dan aminta ce tun daga kuruciya,a lokacin bilalu bai yadda da wani abu wai shi so ba,abinda ya sa yayi saurin amsar rabi a ransa gani yake babu sauran mata masu so dan Allah babu kuma sauran amana,shi yasa da ya ga hankalin rabi a da kuma kusancinsa da dan uwanta ya sa yayi saurin nuna bukatar aurenta dan a ganinsa muddin ya yi sake rabi ta kufce masa to ba zai kara samun mace me nagarta irin ta ba,duba da yadda suke matukar wahala.wannan yasa ba a dauki lokaci ba a ka fara shirin bikin da ba a taba yi ba,kankace komai yan itopia sun fara sauka da sauran dangi na kasashen waje,hatta da shi kansa pilot din munga sauyi a wajensa dan yana dan sanya baki cikin shirin bikin ba kamar na baya ba da saidai muyi komai yana kallon mu.

Anyi biki lafiya an gama wannan yasa muka dauka cewa munyi dace wahalar mu ta zo karshe, to ashe Abin ba haka ba ne,dan tun da aka kai amarya pilot ya kasa gane kanta ta ki bari yayi wata mu amalar aure da ita,to dake shima Muskilin kansa ne sai kawai ya rabu da ita, sai ya zamana babu ruwan kowa da kowa,idan ta tashi za ta yi masa girki da duk wani aikace aikacen gida amma babu batun yin wata rayuwar aure,sai da suka dauki tsawon wata biyu a haka,amma Dr bai taba yi min wata magana makamanciyar matsala a gidan sa ba,duk lokacin da na tambaye shi cewa yake ba wata damuwa,to dake shi dama sai ta kai ta kawo ake fahimtar wani abu a fuskarsa dan haka yasa muke cikin kwanciyar hankali, saboda ko daga ɓangaren rabi a bama ganin wani sauyi ko wata alama da zai nuna mana cewa ba sa irin zaman da miji da mata suke yi.

Bayan wata uku da yin auren,bilalu ya gama hutunsa na tukin jirgi,washe Garin wata Alhamis ya shirya ya yi sallama da matarsa ya tafi yawansa na Yulin jirgin sama,dan wani lokacin idan ya tafi yana yin wata yana yawo a sama,wani lokaci kuma ko kwana biyu baya yi ke har kwana ɗaya ma yana yi,kafin ya kuma tafiya ma yana yin kwana biyu sai kuma ya zauna ya kula da majinyata a babban asibitin Abuja da yake aiki,dan a lokacin ba a gama ginin asibtinsa na Kano ba,

kwanan sa biyu ya juyo Abuja ba tare da ko mu mun yi zato ba,dan a yadda muka rabu dashi zai kwana biyu kafin ya dawo,kuma haka na sanar da matarsa, dan na san shi ba zai gaya mata ba,babu wanda ya sanarwa dawowarsa hakan yasa matarsa ta sakankance.

yana saka motarsa a wajen ajiye motoci ya fito,me gadi sai sannu da zuwa yake masa bayan ya bude masa motar ya fito,duban motar Dr Tukur ya yi yana cewa me gadi"bako mu kayi?"ey wallahi yallabai tun dazu yana ciki kusan awa uku ke nan"Dr bai saurari zubar da me gadin yake masa ba ya wuce zuwa cikin gidan,kasancewar daga nan gate akwai yar tazara kafin ka shiga ainihin gidan,a hankali yake tafiya duk da cewa akwai kuzari a tare da shi amma haka kawai ya tsinci kansa cikin wani irin bugun zuciya tare da sanyin jikin da suka saukar masa a lokaci ɗaya,har zai danna alarm din da yake kai sakon sallama cikin babban falon da acikinsa aka rarraba corridor da dakunan gidan suke ciki,sai kawai ya fasa ya juya ya zagaya ta can wata kofar da ko matar gidan bata san da ita ba, shi kadai yasan da abarsa kuma shi ne ka dai ya isa ya bude ta,yana zuwa ya bude da key din motarsa dake hannunsa sannan ya saka kai,duk takun da zai yi sai ya ji yanayin bugun zuciyarsa ya karu,a haka har ya isa cikin babban falon,cak ya tsaya yana bin falon da kallo,a tunaninsa zai shigo ya samu Dr Tukur a falon tunda ga zahiri nan dai tabbas ya zo gidan to amma yana ina?"yayiwa kansa tambayar da babu me bashi amsa,zama yayi cikin daya daga cikin kujerun da suka yiwa falon kawanya yana kallon corridor da dakunan rabi a suke, kafin yayi tsam ya kuma mikewa ya nufi dakinnata abin da ya jima bai yi ba tun farkon zuwanta gidan rabansa da bangarenta,tun daga farkon doguwar barandar yake jin magana kasa kasa tare da dariya alamun dai ko su waye suna cikin nishadi,turus yayi daga bakin kofar zuciyarsa na wani irin bugu,kafin a hankali ya jingina bayansa da jikin kofar yana mai runtse idanunsa da yake jin har wani yaji yaji suke yi masa,kansa kuwa tamkar zai tsaye saboda sarawar da yake yi.

Acan cikin dakin rabi a kuma ita ce tare da Dr Tukur mutumin da yake ganinsa tamkar wani dan uwansa na jini,suna maganganun da basu san cewa kamar mashi haka suke shigewa kunne da zuciyar Dr Bilal ba,

Runtse idanunsa ya kuma yi yana mai tuna asalin alakarsu da Dr Tukur.

Tun suna secondry school da su kayi a can itopia suke tare, hatta da iyayen Dr Tukur sai da suka hakura dashi saboda ya ki komawa hutu dan duk sanda suka samu hutu a gidansu Dr Bilal yake kare shi har a koma, iyayen Dr Bilal su suke masa komai,a haka har suka fara jami'a itama dai haka suka yi rayuwa kamar a baya har Allah yasa suka kammala,Dr Tukur ya dawo gida Nigeria shi kuma Dr Bilal ya juya karatunsa zuwa na pilot, wannan shine ya raba haduwarsu ya kuma rage karfin dangantakarsu,amma duk da haka suna tare da juna,sai bayan tsawon wani lokaci Bilal ya gama karatunsa har ya biyo iyayensa suka dawo Nigeria anan ne kuma abotarsu ta dawo sabuwa da Dr Tukur,sai dai duk wanda yasan Dr Bilal ya san shi ba mai yawan kwarafniya ba ne ba shi da son shiga abinda babu ruwansa,wani lokacin ma ko sanya shi ka yi ciki baya shiga,shi yasa bai damu da zuwa gidan su Dr Tukur akai a kai ba,kuma shi kansa Dr Tukur din bai damu da hakan ba,sau daya Bilal ya taba zuwa gidansu ya ya gaishe da mahaifansa daga nan bai kara zuwa ba, sannan ba kowa ya sani a gidan ba,hatta da kannen Dr Tukur ba zai iya tantance su ba, bai ma san ko su nawa ne a gidansu ba bare har ya tantance fuskokinsu.

Duk abinda ya faru akan neman auren da muke yiwa bilalu Dr tukur ya san komai,kuma tare da shi ake shiga cikin jimamin abubuwan da suka faru,

Dafe kansa yayi yana jujjuya shi yana tuna lokacin da Dr Tukur ya takura masa da sai ya je gidansu, shi kuma Bilalu baya son Dr Tukur yaga kamar baya son zuwa gidansu shi yasa ya hakura ya je,amma ko da suka je sai suka samu basa nan duka sai a cewar Dr Tukur shima bai san zasu fita ba,dan haka sai ya sa kanwarsa rabi a ta kawo musu ruwa da abinci wanda a lokaci daya yanayin nutsuwarta ya dauki hankalin Dr Bilal duk da cewa shi bai kasance me kallon mata ba, amma a lokaci daya rabi a ta yi masa a yanayin tarbiya ya kuma yadda zai aureta ba dan so ba sai dan ya samu yaya na gari,ashe bai sani ba macizai ne masu mugun dafi a tare dashi.

Yana zuwa nan a tunaninsa ,yaji wani abu kamar ruwa ya cika idanunsa,yana kai hannunsa ya ji ashe hawaye ne suke kokarin zubo masa,da sauri ya shanye su yana girgiza kansa tare da dawowa asalin Dr Bilal dakakken namiji jarumi me juriya".

Shiru Hajiya ta yi tare da sanya hannu ta dauki tissue tana tsane kwallar da ta cika idanunta, Ummul kuwa ji take tamkar ta fada cikin bakin Hajiya saboda tsananin zakuwa da ta yi taji abinda Dr Gen ya ji a cikin dakin rabi a wanda har ya sanya shi a cikin yanayin da bata taɓa ji ko ganinsa a ciki ba,ganin Hajiya ta ki cewa komai yasa ta ɗan jijjiga hannunta tana cewa"dan Allah Hajiya ki fada min me ya faru? Me ya ji suna fada ?kuma me yasa Dr Tukur bai tsaya a falo ba ya bita har dakin sirrinta duk da cewa yana matsayin ƴaƴanta amma idan har babu wani dalili babba bai kamata su bar ko ina dake cikin gidan su zauna a kuryar ɗakinta ba?"sosai Hajiya ta ji dadin tambayoyin da Ummul ta yi mata wannan shine ya bata damar,murmusawa tana ci gaba da cewa"Ummu duk me tausayi da imani idan yaji irin ha'inci da cin amanar da Dr Tukur yayiwa abokinsa kuma amininsa sai ya zubda masa hawaye,bari dai na bude miki labarin Ummul Rabi'ah ba kanwar Dr Tukur ba ce,ya bashi aurenta ne kawai dan ta kwashe masa takardun wasu kadarori da ko mu ba mu san yana da su ba , Sannan shi din ma Dr Tukur ba gaya masa yayi ba,tsananin binciken da yake akansa tun suna matasa shine yasa ya sani,ashe Dr Tukur ba dan Allah yake tare da bilalu ba,tun asali akwai shirin da yake akansa dan ya mallaki dukiyarsa da ya tara da guminsa ba da gumin wani ba ,ba kuma kudin babansa ba,ba na Hajiyarsa ba, wallahi Ummul ko ni ban san bilalu yana da gidan marayu ba,ban san yana da asibiti a itopia ba, ban kuma san yana da kamfanin da ake kera masa manyan motoci ba, Sannan ban san yana da gidan cin abinci a kano ba,duk sai da wannan abin ya faru, wai ashe Dr Tukur ya jima yana neman ta yadda zai yi ya kwace wadannan kadarorin saboda yana takamar cewa bamu san da su ba,dan haka ko ya kwashe su ya kashe Dr ba wanda zai sani,idanunsa ya rufe ya manta cewa akwai lauyansa wadda ba kowa ba ce sai yar uwarsa be sarah , Sannan ya manta da wanda yafi mu sanin komai wato Allah masanin gaibu,bayan haka kuma Dr Tukur yayi aure kafin dawowar Dr Bilal amma ko da ya dawo bai gaya masa ba,kuma rashin shigar da Dr Bilal cikin family dinsa duk yana cikin tsarinsa na son cimma mummunan kudurinsa"hasali ma iyayen bogi ya nunawa Dr Bilal a matsayin iyayensa saboda ganin bai sansu ba,Muryar su kawai yake ji ta waya kuma yasan halin Dr bai da tsayawa yin kurilla balle ya fahimta"kukan da Ummul take yi ne ya dakatar da hajiya ta tsaya tana kallon Ummul din na dan wani lokaci kafin ta ce"ummul ki yi shiru yanzu ai lokacin kuka ya wuce sai dai mu godema Allah"sannan ta ci gaba da bata kabarin da cewa"babu abin da yafi gigita mu da shi kansa Dr gen kamar yadda de tukur ya rufe mu ya mu kayi sabon Allah cikin rashin sani,wato ashe Dr Tukur bashi da wata kanwa gaba daya gidansu su uku ne duka maza,tsananin son zuciya yasa yasa matarsa ta amince da auren Dr Bilal saboda kawai ya samu abinda yake so,shi yasa ashe ta ki yadda da bilalu ya san sirrinta"

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"Ummul ta fada tana dora hannunta akan bakinta idanunta a waje gasu cike da hawayen da suka kasa daina tsiyaya, ba karamin shock ta shiga da jin wannan mummunan al'amarin ba,"Hajiya aure kan aure ke nan ta yi?"gijjiga kai Hajiya tayi tana cewa "tabbas Abinda su ka yi kenan kuma cikin saninsu ba wai jahilai ba,sun sani sun take akan abin duniyar da zasu mutu su barshi"Hajiya iyayensu fa sun sani suka barsu"?hannun Ummul din ta kama tana cewa"Ummul ke da na gaya miki cewa da iyayen bogi yayi amfani a matsayin iyayensu shida rabi a kuma sune suka bada auren rabi ar ga Dr ,Dr Tukur fa ya jima yana shirinsa akan Dr Bilal dan haka wannan duk ba abin mamaki ba ne, Ummul ki daina kuka kinji"ta fada tana janyo ta jikinta dan ganin ta kasa sarrafa kukannata shi yasa hajiyar har ta fara tsoron kar ciwonta ya tashi,duk rarashin da Hajiya take yi mata bata ji bare ta fahimta Dr gen dinta kawai take buƙatar gani a gabanta ta rungume shi ta rarrasheshi ta fada masa tana sonsa a ko wane irin yanayi da ko wane irin suna, tana sonsa a matsayin gentle tana son sa a matsayin Dr Bilal,tana son sa a matsayin pilot,Shi yasa take ji kamar ta rufe ido ta bude ta ganta a gaban jarumin mijinta da ya cancanci biyayyarta da soyayarta da kulawarta, Allah Sarki Dr gen Ashe kalubale ne a cikin rayuwarsa haka duk dan saboda abin duniya ake son ganin bayansa, tun da ba dan Allah ya kiyaye ba Alhaji dan gaske shima auren manufar yaso yayi masa da yarsa zezee,gashi kuma har yanzu bai fita daga cikin kalubalen rayuwarsa ba,to wannan wace irin rayuwa ce,kana talaka ba ka zauna lafiya ba saboda tunanin cin na gobe ashe wanda ya tara yafi wanda bai ajiye ba cikin masifa da tarardadi.

Hajiya tana rarrashinta ta ci gaba da cewa"yana gama saurarensu sai kuma ya ji shiru alamun sun Wada wata Duniyar dan haka sai ya ja jikinsa ya bar wajen ya koma falo ya zauna tare da kwantar da kansa jikin kujerar idanunsa a rufe,shi kansa ba zai ce ga tsawon lokacin daya dauka a wajen ba,ya dai ji sun fito suna shewa kai kace mata da mijin da suke zaune a cikin gidansu cikin farin ciki da annashuwa ne.

Ba karamin shock suka shiga ba ganin wanda ba su taba zato ba a zaune a falon,kallon juna suka shiga yi dukkansu a mutukar razane musamman Dr Tukur da ya gama tsara yadda zai gabatar da rayuwarsa,amma dan karfin hali sai ya wani mazaje ya taka zuwa gaban Dr Bilal yana cewa"ba dai yanzu ka shigo ba?kamar tare muke dan nim......yadda Dr Bilal ya dago kansa da kallon idanunsa kawai da yayi ya hanashi karasa abinda yake son fada,take jikinsa ya dauki rawa dan wannan yanayin da yaga Dr ka dai ya tabbatar masa da cewa kashinsa ya bushe,a haankali Dr Bilal ya mike tare da cewa"kuje na barku da Allah"daga haka ya nuna musu hanyar fita, hatta da mayafi bai bawa rabi a damar dauka ba haka suka fice daga gidan sun kasa cewa komai bare su samu damar kare kansu.

Tun daga wannan lokacin Dr Bilal ya fidda rai da samun matar aure irin wadda yake fata,ya kuma hakura da abota,dama ba gwanin yin abotar ba ne,yana da abokan karatu da na kasuwanci amma kowa da huruminsa babu wani aboki da ya kuma jawowa jikinsa,sai da ya samu nutsuwa sannan Ni da kaina na bashi shawarar ya yi badda kama ya koma Kano tunda muma mun kusa komawa amma dai ya fara zuwa,hatta da sana'ar da zai yi ni na bashi shawara akai"kuka sosai Ummul ta ke yi na tsananin tausayin Dr gen Wanda har sai da Hajiya ta kasa rarrashinta .

Daga karshe sai da Hajiya ta kira Alhaji ya zo har dakin ya samu Ummul ya rarrasheta Sannan ta yi shuru da yin kukan sarari ta koma na zuci,sai kuma da baban ya tuna mata da maida lamarin ga Allah Sannan ta mike ta shige bathroom ta dauro alwala ya fara jero Sallah dan yiwa mijinta addu'a Allah ya sa ya fi karfin azzalumai.

*******

Sai da Alhaji dan gaske ya ci dariyarsa ya koshi Sannan ya mikawa killer hannu yana cewa"bani wukar nan na yi masa yankan rago a nan yanzu yanzu ba sai an jima ba"zare wukar killer yayi daga cikin kufenta sai wani irin sheki take yi ya mikawa dan gaske yana cewa"ya haj saboda irin wannan lokacin na tanadi Wannan, dan Wannan ko shekinta sai ya yanka makogaron dan akuya"karba dan gaske yayi yana cewa"ina maka albishir da manyan kudade har da kadara da zarar wancan miskilin yaron ya karbo min kamfanoni na, ina gamawa zan baka ka maida ita gidanta saboda wancan dayan tsinannan yaron Dr da ita zan aika shi inda ka tafi"ya fada yana lasar wukar da harshen sa,danko wuyan gentle ya yi ya matso da fuskarsa gab da tasa kamar zasu hade kana ya ce"me ye fatan ka na karshe?"wani kayataccen murmushi Dr Gen yayi Sannan ya ce"fatana na karshe shine naga bayanka na ga kana yawo kamar mahaukaci naga kana kuka ka mozanta a idanun duniya, wannan shine kawai Fatana"yana kaiwa karshen maganarsa dan gaske ya sheke da dariya har yi yake kamar zai fadi daga kan kujerar,sai da yayi me isarsa Sannan ya dago kansa yana bude idanunsa akan gentle,take annurin fuskarsa ya dauke sai muzurai yake da yiwa gentle kallon mamaki,tunda a iya saninsa gentle ne yanzu a gabansa,amma dan rufe idon da zai yi ya bude wai sai yaga Dr Bilal a gabansa,shakuwa ce ta kamashi kamar wanda za a zarewa rai.........

Ina baku hakuri da jina shuru jiya na dan shiga uzurine, amma gashi nan na hade muku pg biyu a maimakon daya😂😂😂saura na ji kun ce bai kai ba😂

Zahra✍️

***

💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol