Free chapter · Read without an account

Pg47

by Fatima Yushau adam · GIDAN YAN KARYA

Duk da cewa bai bari sautin kukan ya fito ba amma sai da hawayensa suka zuba, rungume ta yayi yana wani irin bata sumbata ta ko ina ,tsananin farincikin da yake ciki baki ba zai iya bayyana shi ba, wannan dalilin ne yasa shi gwammacewa ya bari hawayensa su zuba,ɗago fuskar ta yayi tare da sanya bakinsa a kan ɗan ƙaramin bakinta yayi masa wata yar karamar sumbata tare da maida bakinsa saitin kunnenta yana saukar mata da numfashinsa sannan a hankali cikin wata irin muryar da Ummul bata taɓa jinta a tare da shi ba,ya ce"Ummul ikram Allah yayi miki albarka ina alfahari da samun ki a cikin rayuwata,ke din ta daban ce haka kuma samun irin ki sai Sa'a alhamdulillah da ka sanya Ummul ta zama ta biyu daga cikin alkhairan da ka bani a duniya,ma ana da ke da iyaye na,domin duk namijin da yayi dacen samun nagartattun iyaye da mace ta gari to hakika ya gama samun alkhairan duniya mafi girma da daraja",shiru yayi yana kallon fuskarta da kuma kyawawan idanunta da suke a rufe, sumbatar idanun yayi wanda hakan yasa ta bude su da sauri,kawar da kanta ta yi daga kallonsa,tana jin wata irin nutsuwar da bata taba sanin akwai irinta a duniya ba,dumin bakinsa ta ji ya sauka a kirjinta,bata san lokacin da ta saki wata karfaffar ajiyar zuciya ba,tare da runtse idanunta da suka yi jawur saboda kukan da suka sha,hawaye ne suka kuma cika idanun saboda yadda kirjinta yake zafin maguzar da suka sha a wajen Dr gen Dan gidan Ahmad Dan itopia,sai dai duk da haka bata hanashi yin abinda yake so ba,sai dai kuma ganin kamar yana son ƙara komawa waccan duniyar yasa ta saki dan Marayan kuka tana jin kamar idan ya kuma yi ba zata kai labari ba,"am sorry oum"ya fada can ƙasan maƙoshinsa,gaba daya hannunta ta sanya ta rungume shi tare da kara shigewa jikinsa naked skin dinsu ya kuma mannewa da juna, sannan cikin wata irin murya wadda ke fita da wata irin sheshshekar da yake kuma dulmiyar da Dr gen zuwa ga wani irin rikitaccen shauki ta ce"Ni ban san ya zan yi ba idan ka ƙara,ina jin ciwo akwai zafi, ka ce zaka nuna min kadan daga cikin kaunar da kake min amma Ni ban gani ba sai tsana da ka nuna min tunda gashi kana son kara yi, gashi duk ka cije Ni ka ji min ciwo a kirji na har yanzu ciwo suke min,ko dan kaga ina jin tausayinka shine kai kuma zaka wahalar da Ni,to idan zaka yi ba zan hanaka ba,amma kana kuma yi zan mutu"ta karasa maganar tana yarfe hannunta guda daya tare da murza fuskarta a cikin kwantaccen gashin kirjinsa,cikin wata irin kasalar da take kuma saukar masa ta dalilin abinda take masa ya sanya hannu ya tattara gashin kanta, sannan ya dora bakinsa a kan goshinta ya sumbata,kafin ya ce"oum ba zaki mutu ba,na hakura ba zan miki komai ba,amma yanzu dole ki fara yin wanka kafin ki ci gaba da baccin kinji"a hankali ta saki masa wani dan shagwababben kuka tana dan dukan kirjinsa sannan ta ce"Ni ba zan yi ba ciwo nake ji ko tashi ba zan iya ba bare tafiya, wallahi Dr gen ka ci amanar baffa da Ummi yanzu idan suka ji abinda ka yi min me Zaka ce da su?"ya subhanallah"ya fada yana tashi zaune tare da ita ajikinsa,idanunsa akanta ya ce"ta ya za su sani idan har ba fada musu kika yi ba?"kwace hannunta ta yi tana share hawayen da suke zurara daga kwarin idanunta,"plz umm babu wanda ake fadawa irin wannan sirrin dan Allah karki fada musu kin ji?"ya fada cikin sanyi kamar ba Dr Bilal ba,bata ce masa komai ba har yanzu sai komawa da ta yi zata kwanta tana ciccije baki kamar me nakuda.

Cikin sauri ya tareta, zata yi magana ya dauke ta cak ya yi bathroom da ita,yana shiga ya ajiye ta akan wata yar kujera sannan ya shiga hada mata ruwan masu zafi,tana zaune tana kallonsa tana kukan sangarta saboda yanzu babu hawaye a idanunta ko digo sai sautin ɗan kukan kamar irin yaro ya gaji da kukan rigiman nan yana so a rarrasheshi,bata yi zato ko tsammani ba ta ji ta tsulum cikin ruwan da ta kira shi da tafasasshe saboda tsananin sharri da raki irin na Ummul,kokarin fitowa ta shiga yi tana cewa "Dr gen ban San cewa kai kasurgumin mayaudari ba ne sai yau,kai ne fa ka ce bakinka ba zai iya misalta son da kake min ba sai dai ka nuna min shi a aikace,amma yanzu shine kake gana min azaba iri iri har da son ƙona min fatar da dama hajiyar Sudan ta gama kwayeta saboda irin tata muguntar,Kai Kuma yanzu kazo zaka karasa, dama wallahi ina jin hada baki kuka yi kai da ita,wa ya sani ma ko fansa zaka dauka a kaina saboda abin da yan matanka suka yi maka"duk abinda take fada yana jinta kuma hakan baisa ya dakata daga rikon tsaurin da yayi mata ba,yana ji tana ci gaba da cewa"idan ka hanani fadar wancan wannan ai ba zaka hanani fada ba,gobe ma ban san me Zaka yi min ba,haka kawai ni ba da laifi ba amma za a rama a kaina Allah ka fidda Ni tun kafin ya nakasani"sai da ya tabbatar ruwan ya salamce sannan ya cireta ya kuma hada wani,nan ma haka ya kuma tsunduma ta a ciki tana faman dukansa da yan koke koken ta tunda taga surutun ba zai fisshe ta ba,abinka da likita kwararre a ko wane irin fanni,tun kafin ta yi wankan ibada ta fara gyangyaɗi saboda yadda ta ji jikinta garau kamar ba ita ce awa daya da suka wuce hannun yan maza suna fafatawa ba,sai da ya tashe ta daga dan baccin da ta fara cikin ruwan ƙarshen da ya zuba mata wasu magunguna da bata san ko wane iri ba ne,ruwa ya canja mata sannan ya tsaya a kanta ya ce ta yi wankan ya gani,a nan dai bata yi masa gardama ba,dan dama ita ba mai yawan turjiya ba ce in dai ba a ɓangaren da za'a taba lafiyar jikinta ba ne.

Tsaf kuwa ta yi wankanta kamar yadda ya tambaye ta ta kuma gaya masa a dazun da su kayi sallar nafila,haka nan ya samu kansa da sakin wani dan Muskilin murmushin da ya tsaya a cikin bakinsa, sannan ya sunkuya yana kallon tsakiyar idanunta da take ta rarrabawa saboda bata son mikewa ya ganta,shi kuma ya ki bata towel bare ta rufe jikinta,hura mata iska yayi a idanun sannan cikin rarrabe kalma kamar baya son fada ya ce"na gama nawa aikin saura ke ki min yadda na yi miki"ware manyan idanunta ta yi a kansa kafin a hankali ta yi kasa da idanunta har zuwa ƙasanshi tana kiyasta tashin hankalin da zata shiga muddin ta yi ido biyu da mugun abun da ya kusan sumar da ita,katse mata tunani yayi ta hanyar ci gaba da cewa"kinga shi ke nan kin rama azabtar da ke da na yi ba sai kin sanar da kowa gen na son Kona ki ba"ya fada yana kokarin zame towel din da yake daure a kugunsa,ai bata san sanda ta sanya kara tare da runtse idanunta ba,a wannan karon duk dauriya da basarwa irinta Dr Gen kasawa yayi har sai da ya murmusa fararen hakoransa da suke jere reras suka bayyana,maida towel dinsa jikinsa yayi , Sannan ya zura dogayen hannayen sa ya daukota gaba ɗayanta yayi dakin da ita,jinta a hannunsa yasa ta yi zaton bai maida towel din sa ba,dan haka ta runga cusa fuskarta a jikinsa wai dan duk kar tsautsayi yasa ta bude idanunta ta yi gamo,kwantar da ita yayi a kan gadon ya yi juyawarsa ya koma bathroom din yana jin wani irin farin ciki da nishadin da tun da ya zo duniya bai taba shiga cikin makamancin sa ba.

Tana jin shigarsa da rufe kofar sa ta bude idanunta tare da dafe kirji tana zazzare ido kamar wadda ta yi gamo da wani mugun abu,sai kuma ta fara lalle kallen inda zata ga kayan ta da yayi mata wurgi da su waje waje,a can kusan kofar dakin ta hango rigar wandon kuma a saman mirror dakin,da sauri ta mike sai kuma ta koma ta zauna tana cewa "ash Ashe har yanzu da sauran azabar"sai kuma ta mike a hankali ta taka ta dauko kayan ta saka ,har zata koma ta kwanta sai kuma ta fasa ta janye bedsheet din da Dr gen yayi yaƙin basasa akai ta watsar a kasa sannan ta bi lafiyar tsurar lafiyayyar katifar ta kwanta abinta tare da shigewa cikin bargon,ko minti ɗaya bata yi ba ta yi baccinta hankali kwance, dan hatta da numfashinta ka saurara sai ka tabbatar da cewa ta na cikin nutsuwa.

Lokacin da ya fito kuwa ai Ummul ta kai kasarsu itopia dan haka shima sai ya kimtsa ya bi bayanta ya kwanta,shigewa yayi jikinta yana kallon fuskarta da take ta wani sheki da annuri, a cikin baccinta ta sakala hannunta ta zagaye shi tare da kwantar da kanta a cikin mayalwacin kirjinsa,lumshe idanunsa ya yayi yana karanto musu addu'a daga nan bai san lokacin da bacci yayi awon gaba da shi ba.

Asuba ta gari Dr Gen oum.

****

Alhaji dan gaske ya zama shi ba me hankali ba kuma ba mara hankali ba,dan wani abun yana ganewa sarai wani abun kuma sai ya ji bai san ma me yake yi ba,da alama dai Allah ya bar shi cikin tunaninsa ne saboda ya nuna masa isarsa da buwayarsa,yadda zaka gane cewa Alhaji dan gaske yana nan da hankalinsa shine,tun ranar da aka kwace masa mota da waya duk inda zai je idan ya tashi sai ya dawo asalin gidansa,daga nan kuma zai zaga duk wajen da ya san yana da kadara, Kai hatta da tsohon gidan su Ummul da har yanzu yake rufe sai ya je,haka zai zauna a wajen da Dr gen yayi gyaran takalmi yayi ta kuka yana kallon wajen, ko kuma ya dinga tsine masa shi da ubansa,baya cin abincin kasa sai dai ya je wajen cin abinci me kyau ya tsaya kamar zai shiga sai yaga wanda zai iya taimaka masa sai ya rokeshi, da yawa mutane kallon mahaukaci suke masa wasu da yawa ma sun sanshi, sai dai kaga ana nuna shi ana maganganu,duk yadda kuke tunanin tsiya da fatara to haka take a wajen dan gaske,tun rigar da take jikinsa a ranar har yau ita ce,a cikin yan kwanakin da basu wuce bakwai ba gaba daya kamannin dan gaske sun sauya har ya zamana sai wanda suka yi masa farin sani ne suke gane shi,to dake bai wani shuka alkhairi ba ga kuma hakkin rayuka sai ya zamana babu me tausaya masa yar sadakar abincin da yake samu ma ya daina samu,sai dai ya dinga bin wanda suka ci suka rage a kasuwa yana dauka wanda imaninsa ya kai imani kuma ya siya masa na yan talla.

****

A bangaren mommy da zezee kam suna cikin kwanciyar hankali ta sanadiyar kulla akalakarsu da Safwan,dan a yau din bayan dawowarsu daga gidan bikin su Ummul raliya ta dawo gidan da zama ,saboda mijinta matafiyi ne idan kuma ya tafi yana dan jimawa,haka idan ya zo yana jimawa kan ya koma,shi yasa mommy ta nemi da ya barta su zauna a tare idan ya so duk lokacin da ya dawo sai ta dinga komawa,shi yasa yanzu suka fi jin dadin zaman fiye da baya,sai dai a bangaren zezee tana jin kewar mahaifinta, akwai dalilin da ya hanata zuwa nemansa shi yasa, sannan ta wani bangaren tana son nunawa mahaifiyarta cewa itama tana tare da ita, saboda duk rayuwar da su kayi ta yi shine tare da nunawa mommy cewa mahaifinta ya fita,shi yasa yanzu take son faranta mata ta hanyar kauracewa duk wani abu da ya shafi abban nata dan ta fahimci cewa haka shine farin cikinta.

****

Tunda bely ta koma garin su ,iyaye ta suka fara yi mata magani sai dai kullum kamar kara ciwon ake,tun mahaifinta na jin haushinta har ya dawo ya fara tausayinta saboda kullum bata da aikin yi sai kukan nadama,ta zama abin nunawa a garin, dan yanzu ko yarinya ce aka ga ta fara dauko lamun bin layin da bely ta hau,yanzu za a fara yi mata misali da abinda ya faru da bely, idan an dace wata bata da rabon shan wahala sai ta gyara wata kuwa bata jin kira,sai dai fatan Allah ya shirya mana zuri a baki daya,a cikin wannan yan kwanakin ne ma har ta ɗan fara samuwa take iya zama,amma kwanakin baya ko tashi zaune bata iya yi, sannan kullum hannunta yana jikinta tana fama da susa,wanda kuma susar idan ta yi sai dai kaga jini yana bin hannunta,kukan nadama kam babu irin wanda bely bata yi shi ba.

****

Saura kiris Dr Gen ya makara sallah koma ace ya makara, dan kafin ya fito daga bathroom sun idar ,Wanda hakan yasa shi tashin Ummul da take tsaka da jin dadin baccinta dan har wasu mafarkai take masu dadi,babu abinda take a gadon sai juyi,ganin ta ki ta shi sai kawai ya tattare hannun jallabiyarsa ya sunkuce ta sai toilet babu shiri ta bude idanunta tana ambatan sunan Allah,sai da ya tabbatar ta ɗan warware sannan ya fice ya barta tana alwala,akan sallayah ta sameshi dan haka sai kawai ta dauki hijabin da ta gani ya ajiye mata ta saka tare da bin bayansa,

Ganin yadda har lokacin Ummul bata daina katin bacci ba, yasa shi takaita karatun da suke yi,ya ce ta je ta kwanta,shi din ma kadan ya kara zama ya kuma komawa ya shige mata kamar wani dan mage suka koma baccinsu.

***

Daga can bangaren su Ummi kuwa ,tunsassafe bak suka shirya zasu suna jiran motar da aka ce zata kaisu gidan Ummul su gani,sai dai kuma motar bata zo ba har sai misalin ƙarfe sha biyu da rabi na rana,wanda daga nan kuma za'a wuce da su tasha , tuni baba Ahmed yasa aka tanadar musu mota guda da zata maida su gida,

Zuwansu gidan yayi daidai da farkawar masu gidan daga baccin gajiyar da suke ta fama da shi,Dr gen shi ya Fara tashi bai tashi Ummul ba har sai da ya je ya sauki bakin da kansa yayi musu karba irin ta mutunci da girma,ya kuma gaida wanda suka dukkansu ba tare da ya tantance wanda ya kamata ace su zasu gaidashi ba,da kansa ya zagaya da su gidan suka gani suna ta sa albarka,duk cikinsu babu wanda ya nemi Ummul dan su mutanene masu wayewa da fahimta har sai da shi da kansa ya ce zai je ya gani ko ta tashi a barcinta, wannan abu da Dr gen yayi a karamin daga darajarsa yayi a gun yan uwan Ummul ba,dan wannan kadai ya nuna musu cewa yar su ta samu wajen da ya dace da ita,adda har da kara masa da cewa idan bata tashi ba ya rabu da ita kawai idan ya so sayi sallamar a waya,dan murmushin sae tsada kawai yayi tare da shigewa upstairs din,Wanda nan ne kawai bai kai su sun gani ba a gidan ,saboda nan din duniyarsa kuma mafarin sarauniyar sa sirrin rayuwarsa,

To kuma cikin Sa'a sai ya je ya tarar da ita ta tashi har tana zaune ma a bakin gadon tana ta mirza ido da gani kuka take son yi saboda jin yunwa ta fara juya mata ya'yan hanji,kai tsaye cloth ya wuce ya dauko mata wata ash din abaya da mahaifinta, sannan ya zo ya kamata ya Kaita har bathroom ya bata brosh tayi daga nan suka kuma fitowa, ya saka mata rigar ya dora Mata mayafin akanta, sannan ya kalleta kafin a hankali ya sunkuya ya sumbaci red lips dinta da suka kuma yin ja,ita dai gungunin yunwa kawai take yi cikin sakalci da tabara,ko da ya kama hannunta dan su fita sai ta ki motsa wa,da ido ya ke tambayarta dalili itama da ido da hannu ta yi masa nuni da kafarta akan ba zata iya tafiya ba, shafa tattausar sumar kansa me Sheki yayi, sannan ba tare da ya tanka mata ba,ya juya bayansa tare da rage tsayinsa,aiko cikin murna ta dane bayansa kamar ba itace me cewa bazata iya tafiya ba,sai da suka sauko dounstais kafin ya bude wannan kofar da zata maida su main falon sannan taga yana kokarin sauketa,makale shi ta yi tana kebe baki kamar zata yi kuka, shima din kwantar da murya yayi sannan cikin lallashi ya ce"bakin agases ne a gidan amma na miki alkawarin bayan tafiyarsu zan kewaya dake gidan a gadon bayana"ware ido ta yi cikin murnar abu guda biyu na farko zuwa da yan agades suka yi da kuma na goyon da zai yi mata ya kewaya da ita wannan katon gidan da take ganinsa kamar aljannar duniya,ta ce da gaske"?jingina mata kai yayi amma bata yadda ba,har sai da ta muka masa yatsanta karami tare cewa"to mu kulla"ba musu ya sakala nasa yatsan a cikin nata ta kuwa hade ta murde sannan ta karasa fita da gudu, duk da cewa har lokacin tana jin ciwo kadan kadan a jikinta.

Binta da ido yayi fuskarsa da shimfide da mayalwacin murmushin da ya zama me arha yanzu a wajen sarauniya ummul.bin bayanta yayi dan ba zai barta daga ita sai su ba kar ta je ta yi masa shirmen da zai daina iya hada ido da kowa a cikinsu.

Yana fita ya sameta a tsakiyarsu, su kuma duk sai kallonta suke cikin sha'awa da burgewa,driver ne ya fara shigo da kulolin break din da Hajiya ta aikowa da su Ummul din,yana gama ajiye wa ya fice, Ummul ta dubi adda hasana ta ce"adda ga abinci ku ci kar ku tafi da yunwa"hararar ta adda Hasana ta yi tana cewa"me kike nufi yan uwansu zasu barmu da yunwa ne,to mu kam mun koshi dan har da babban guzurinmu"duk yadda Ummul ta so su ci ko kadan ne ki su kayi saboda a kashe su kayi,abin mamaki sai kawai ta fashe musu da kuka,wanda hakan yasa suka san cewa Dr gen ba nisa yayi ba, saboda kawai ganin Dr Gen su kayi a gabanta ba tare da ya tuna cewa suna wajen ba,yasa hannu ya rikota yana neman ba asin kukannata......

Hello my fans, na so a ce yau na gama gaba daya dan mu huta gaba daya to amma hakan ba zai samu ba,wata kila sai a pg na gaba za mu karkare labarin namu, duk da haka ina godiya ga Allah da ya kawo mu har zuwa wannan lokaci ina kuma fatan ya kaimu goben da muke fatan karkarewa lafiya na gode.

Daga masoyiyarku me kaunar ku a kullum zahra

Zahra✍️

***

💕GIDAN ƳAN ƘARYA💕

By

FATIMA Y ADAM......

Littattafan marubuciyar.

KUDIRAR ALLAH

KADDARATA SANADIN HASKE

ƁOYAYYIYAR RAIHAN

ƳAR GIDAN YARBAWA

MATAR ƊAN BIRNI

And

GIDAN ƳAN ƘARYA....

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol