Free chapter · Read without an account
Pg49
A bangaren zezee da angonta ma rayuwa ta mika, haka A'isha da nata angon, gaba daya sun hade kansu duk da cewa zezee ta girme musu amma haka suke rayuwa kamar wasu aminai,zezee da A'isha sosai suke kokarin koyi da Ummul dan duk wani abu da zaka gani a tare da ita game da rayuwar ta da dr gen Sai ta baka sha'wa.
Mommy tana gama idda suka daidaita da wani babban mutum me suna Alhaji idiris, duk da tana babba amma sai da da ta yi bincike akansa sosai kafin ta amince da aurensa,daga karshe ma ta gano yana da alaka da baban Dr gen kuma shima ya tabbatar da kyawawan halayensa, a gidanta ta ci gaba da zama,sai dai duk sanda zai yi tafiya idan har a girkinta ne to zasu tafi tare, Mommy Tana son Alhaji idris, shi yasa take kara in soyayya.lokaci dayaa ta canja kamar ba ita ba,rayuwa kenan.
***
Kwanci ta shi asarar me rai, Ummul ta budi ido lafiya da samun yaranta mace da namiji,kai zo kuga murna wajen wannan family, duk wanda yake son ganin dariyar Dr gen kuwa to ranar ya ganta,haka wanda bai taba gani ba to a wannan rana ya fara ganinta,yara sun ci sunan baba Ahmad da ummi, wannan kara ce ta Dr Gen ya kuma ce nan da shekara biyu in sha Allah zai kawo baffa da Hajiya.
To kun dai san mutuniyar taku an ci kwakwa wajen rainon yan biyu kafin daga karshe ta yaye su ta tattarawa Hajiya su itama Dr gen ya maida ita makaranta,amma da sharadin zata bashi wasu yan biyun nan ba da jimawa ba,aiko kamar ya fada a harshen mala,'iku shekarar da su baba karami suka cika shekara biyu a ranar Ummul ta samu wani cikin.
Zezee ma ta haihu da ita da A'isha,
Su mufty an gama karatu an dawo, sun kuma taho da matansu daga cikin dangin Ahmed dan itopia sai dai mu ce Allah bada zaman lafiya,
Dan gaske dai har yanzu yana nan yadda yake shirme ma sai abinda ya karu, sai dai dake yana samun kulawa daga ɓangaren zezee da su Dr gen bashi da wata matsalar rayuwa,amma fa ba a Isa a bashi kudi a hannunsa ba dan yaga su yake komai yawansu, shi yasa sai dai ayi masa duk wata bukata ba tare da an bashi kudi ba.
Ta wajen Musa tsohon mijin zezee ma, duk wanda ya sanshi a baya idan yagan shi yanzu ba zai gane shi ba,ya samu lafiya sai dai tabo kuma shima sai idan ya bude jikinsa,Dr Bilal ya bashi aiki a cikin gidan man su na nan Kano, Sannan ya bashi Shawara yayi aure,haka kuwa aka yi da kansa ya nemo wata yarinya da take kawo musu tallan abinci station din su,dake yarinyar tana da hankali shi yasa bai wani ja abun ba ya bayyana ta a wajen yan uwansa,nan da nan aka yi maganar aure a ka gama,dake suma yan uwansa yanzu sun san sunan morarsa shi yasa wannan karon suka tsaya aka yi komai da su,karamin gida Dr Gen ya nema masa ya bashi rabin kudin rabin ya ce ya biya da kansa,Dr gen Tasha addu'a daga nan aka yi biki, to kuma.zezee da ta ji labari sai kawai ta bashi kudin rabin gidan har da wasu kudade da su kayi alkawarin ba shi.
***
Zezee da kanta ta nemo inda kawar ta bely ta ke a lokacin har ta haihu ta samu diyarta mace da take ta kafkaffa da ita saboda gujewar rudin zamani,jari ta bata Sannan ta siya mata karamin gidan da zata zauna saboda bala'in bishiyoyin ta,bely har kuka tayi saboda farin ciki ,mijinta kuma bai hana ba,dan haka sukan koma can gidan da rayuwa ita da yarta da ko yayeta ba ta yi ba,amma a ranta har ta shirya hanyoyin da zata bi wajen tarbiyyar yarta, dan a yanzu rayuwar tsoro take bawa bely.
****
Bayan tsawon wani lokaci.
Can na hango muku sarauniya Ummul sanye cikin wasu irin kananun kaya masu matukar daukar hankali,sai dai kuma kasancewar cikin ƴaƴanta zata fito sai ta dora bakar riga me budedden gaba akan kananun kayan,saukowa take daga upstairs din dake ta can karshen falon,sai kuma ta yi turus ganin yadda yaran suka canjawa falon kamanni da littafai da duk kayan karatunsu ga kuma Abby dinsu a tsakiyarsu suna ta faman hayaniya a kansa, shi kuma yasa hannu ya toshe kunnuwansa yana faman girgiza kansa,cikin yar sarsarfa ta karasa wajen tana tana kara bin ko ina na fakon da kallo da kuma Dr dinta da yayi wani shiru duk yayi kalar tausayi, dan karamin ma yana kan ruwan cikinsa ne ana assignment dinsa hankali kwance kamar ya dora akan teburin karatunsa,dan tafa hannu ta yi tana karasowa tsakiyar falon kafin ta bude baki ta ce"ai ga shi nan da ba ka hanasu abinda suke yi ba , zasu sanya ka ciwon kai da hayaniyarsu,shi wannan ma saboda iko akan ruwan cikin ka yake assignment din"suna jin muryarta duk suka juyo tare da barin barnar da suke yi,tsayawa ta yi tare da rike kugu tana binsu da kallo daya bayan daya su ukun,kafin ta tsada idanunta kan baba karami tare da nuna shi da yatsa tana cewa"kai sumimii kasau ta shi ka fara gyara falon nan tun kafin ranka ya ɓaci yanzu,ke kuma uwar karadi maza ki kwashe kayan nan, kafin na yi blinking eyes dina yanzu na ga komai ya dawo neat"ai ko da gudu suka tashi suna rige rigen kwashe kayan,shi kuma baffa karami tsuru yayi yana jiran nasa hukuncin sai kifkifta ido yake kana ganinsa kasan cewa a tsorace yake, kunnensa ta kama ta murde har sai da ya saki kuka Sannan ta ce" assignment din kenan kuma akan Abby,Abby teburi ne?"girgiza kai ya shiga yi ba tare da yayi magana ba,sakinsa ta yi tana harararsa kana ta ce"maza tashi anan ka wuce kuje wajen baba asabe ta gyaraaku kuzo ku tafi weekend gidan Hajiya dama yanzu ta kira Ni ta ce ta turo driver zai zo ya kwasheku,daga nan zai wuce ya kwaso ragowar dan haka ku shirya kafin ya karaso"ƙin tafiya yayi sai ma saukowa daga jikin Abby din da yayi ya matsa jikinta da yana sakin wasu sabbin hawayen, tsugunawa ta sannan ta kamo shi ta rungumeshi tana cewa"to my baffa ku dinne ba ku jin magana wallahi ga Abby dinku Kun san cewa kuna damunsa amma sai ku yi ta masa ihu a ka,ko da yake ma ai shi yake son hakan tunda shi ya zo ya zauna a cikinku"ta fada tana dora hannunta saman tattausar sumar Dr Gen da yake kwance har yanzu shiru kamar me bacci,Ummi karama da baba karami suma suna gama kimtsa falon suka matson kusa da ita ta haɗasu ta rungume tana sumbatarsu,daga nan suka mike zasu tafi, sai jin Muryar Abby dinsu su kayi yana cewa abin har da son kai Ni ba zaku min Sallama ba,dan nasan daga wajen baba asabe wucewa za ku yi"ya fada yana tashi zaune, aiko da gudu suka dawo suka rungume shi har hada baki suke wajen fadin i love You my Abby"take Ummul ta turbune fuska kamar zata saki kuka , sai suka yi kanta gaba daya dan sun san halin uwarsu shagwababbiya ce har yanzu abin kuka baya yi mata wuya,baba karami ne ya ce"mami me ye za ki yi kuka?turbune fuskar ta kuma yi Sannan ta ce"shi ne ni ba ku ce min i love You ba sai Abby dinku bayan kuma yana kallona ina shan wuyan kawo ku duniya bai karba ya rage min b...kafin ta karasa fadar abinda zata fada sun hada baki wajen fadin i love You mami kowanensu na kai mata sumbata a bangaren da yake so,da gudu suka fice ba tare da waiwaye ba dan basa so Abby ya ce ba su yi masa kiss ba,suna tafiya ta yi masa gwalo tare da ta shi ta haura sama da gudu,binta yayi a nutse kuma a hakan ya taddata a dadai kofar shiga bedroom dinsu,kamata yayi tare da yin sama da ita, bai a jiyeta a ko ina ba sai a saman tattausan katifar gadon su, bayan ya zame mata rigar da ke saman kayan yana binta da wani rikitaccen kallo kamar idan ya kamata ba zai barta ba sai ya cinye ta tasss ba tare da ya bar ragowa ba.
A hankali ya bi jikinta ya kwanta kamar wani marayan da bai da uwa bai da uba,yayin da yake jan numfashinsa da wata irin zazzafar kaunar da ba zai iya fadarta da baki ba,a aikacen ma sai dai yayi iya wadda zai iya amma bai isa ya bayyana ta yadda ya kamata ba,hancinsa ya dinga bi yana cusawa a jikinta yana shako kamshinta da kullum sai ya ji wani sabon sauyi a cikinsa,duk yadda yasan Ummul dinsa ciki da bai amma har yanzu ya kasa rarrabe ainihin kayan kamshin da take amfani da su,dan yanzu idan yaji wannan to in Sha Allah anjima wani kamshin zai ji daban,ko da zai kuma jin irin sa kuwa to za a kwana biyu.
A bangaren Ummul din ma se take ji kamar tana jin fiye da yadda yake ji, wani irin riko ta yi masa a cikin jikinta kafin ta ɗora kanta a ruwan cikinsa tana shaƙar nasa kamshin da ya hade da nata yake sanyata cikin wani irin yanayin shaukin kaunarsa da bata jin cewa akwai matar da take yiwa mijinta kwatankwacin sa,"Dr gen, my hero, my hub,my nur ,my everything, my life"Ummul da ke cikin wani irin yanayin shauki take fada tana sumbatar duk inda bakinta yayi karo dashi a jikinsa,daga nan dai labari ya canja salo, da gudu na bar dakin Dan wallahi sanin sirrin dr gen sai Ummul ikram, sai dai muce Allah ya kawo cikin na hudu mu samu Hajiya.
Alhamdulikkahi aka kulli halin
Ina godiya ga ubangi da ya bani ikon kammala wannan labarin me suna GIDAN YAN KARYA...ina rokon kuskuren da na yi ya gafarta min,ina kuma rokonsa da yasa Al umma su yi amfani da darasin da ke cikinsa.
Karin bayani
Darasin dake bangaren rayuwar su Ummul ,wato GIDAN YAN KARYA. ya zo da nishadi wanda shine dalilin da yasa ya ci sunan GIDAN YAN KARYA, na farko dai shine rayuwar su Ummul ta zo da wani salo da zai bawa me karatu nishadi da rage damuwa idan har yana cikinta duk da cewa babu wani abu da ya cancanta da mutum sama da komawa ga Allah da yawaita salati da tashin tsakar dare,zan iya cewa wannan ma yana daga cikin abinda yahaskaka rayuwar GIDAN YAN KARYA , ku sani shi Allah baya hukunci da abinda ba daga zuciya yake ba,domin lada da zunubi yana daga abinda bawa ya niyata,
Shi yasa Allah yayiwa Ummul babban tukuici saboda duk da yadda ta kasance me son ta ganta cikin rayuwar masu kuɗi ,sai kuma ta kasance me tsare martaba da mutuncinta bata taɓa daukar abun wani ba, sannan ba su taba shiga wata rayuwa dan samun abun duniya ba,ga shi dai Allah yayi musu baiwar da zasu iya yin komai su samu abinda suke so, wannan kadai zai iya kawo musu daukaka domin Allah yana son bayinsa masu biyayya a gare shi,amma duk da haka kafin su kai ga wannan matsayin sai da Ubangiji ya jarrabasu ta hanyar shiga halin tashin hankali da fargaba,
Na farko dai akwai ribar yadda da ƙaddara wadda take cikin rukunin imani
A kwai amana da gaskiya domin duk yadda suka kai ga son nuna cewa su yan karya ne, basa iya daukar kayan wani.
Uwa uba samun tsayayyu kuma nagartattun iyayenda suka yadda su bar komai su tsaya gaban Ubangiji domin nemawa ƴaƴansu shiriya.
Sannan suka yadda su koyawa ƴaƴansu rokon Ubangiji tun kafin su san kansu bare su san sai suna da damuwa ko bukata zasu tsaya wajen Ubangiji.
Wannan shine kadan daga cikin kyawawan dabi un GIDAN YAN KARYA,
Amma na san kun san rayuwar duka wadan nan mutanen akwai bayyanannen darasi a cikinta,kuma ko wanne bangare da irin darasin rayuwarsa.
Dan gaske
Dr Bilal
Zeezee
Bely
Muna fatan Allah Ya tsare mu da shiga mummunan rayuwa makamanciyar ta wadan nan mutanen ya tsare mu da yin mummunan karshe,ya kare mu da yin aikin nadama,
Allah ya shirya mu da mu da zuri ar mu ya kare su daga sharrin zamani,
Allah ya sa mukansance daga masu koyi da kyawawan dabi u irin na GIDAN YAN KARYA mu kuma kasance masu yarda abinda ya kasance na kuskure a cikin rayuwarsu,amin
Masu aure Allah ya zaunar da su lafiya da mazajensu marasa aure ya basu mazajen aure na gari,
Allah ya shirya yan mata kannenmu da yayunmu da kuma ƴaƴanmu,
Idan akwai wanda na yiwa ba daidai ba ko da acikin rashin sani ne ina fata ya yafe min ,saboda Ni ajizace🙏🙏🙏🙏
Idan akwai abinda na manta ko na yi kuskure Ku bar shi a matsayin ajizanci domin nasan ba zan ce kaf labarin nan na yi shi ba tare da na manta wani abu daga cikin kabarin ba,to idan haka ta kasance a yi min afuwa tun da an yi ginshikan.
.......
ga wanda basu karanta sauran littafai na ba su neme ni kai tsaye ta wannan number ***
akwai free akwai paid na gode
Sai mun hadu a wani sabon book din in Allah ya bamu yawan rai..
Daga ni taku Zahra(Fatima y Adam)✍️