Free chapter 路 Read without an account

Chapter 6

by Sayyada barrister 路 BIYU A 茒AYA

BIYU A 茒AYA 

***
YOTA 13 
Team of FIVE INK legends 

Dedicated to princess Nimcyluv 馃懜馃徎


GHANA 

Page 6

Shiru su ka yi suna zaune duk sun yi tagumi kamar wa蓷an da ke zaman makoki, babu me magana a cikin su, tun safe suke wajen har zuwa wannan lokacin ba su motsa ba, 拼ar wasan nan da suke yi ma yau babu ita. Aicha ce dake zaune kamar wacce aka yi wa mutuwa ta 蓷ago tayi tozali da matar da ta taimake ta jiya, da sauri ta ce

"Lah ga tanan yau ma"

Suka 蓷ago dukkanin su suna kallonta, ita ma su take kallo, tun jiya da ta koma gida take bin su cikin ranta, tana mamakin me suke yi a gefen hotel? Abin al'ajabin ma yara ne babu me cikakken hankali a cikin su, komai zai iya faruwa da rayuwar su.

Takowa tayi a hankali zuwa inda suke zaune, ga mamakinta ko motsa wa ba su yi ba ballantana ma su ji tsoron ta, a hankali ta zauna ita ma kan dakali dake fuskantar nasu, ta yi magana cikin siririyar muryarta me da蓷in sauraro

"Sannun ku yara"

"Ki bamu abin da kika kawo sai ki tafi"

Cewar 蓷aya daga cikin su, wanda shine ya fi su 蓷an girma, da mamaki take duban su, ta basu abin da ta zo dashi kuma?....

"Ko kema nema ki ka zo yi?"

Yadda suke magana babu ko tsoro yasa tayi mamaki, ta kalli Aicha ta ce

"Me kuke yi anan?"

"Sadaka muke kar蓳a"

Cewar 蓷ayan yarinyar, abin da ya fa蓷a ya gigita ta, what sadaka?" Da 茩yar ta numfasa sabar tashin hankali da ka蓷uwa ta ce

"Wane irin sadaka?"

"Ko mene ne ma muna kar蓳a"

Gasu yara ne 茩anana amma kuma babu ko tsoro a tare dasu, a hankali ta sauke numfashi tare da cewa 

"To gashi ban zo da komai ba, ballantana na baku"

"Ni Alawa nake so"

Cewar Aicha, ta mi茩awa Aicha hannun akan ta iso gare ta amma ta girgiza kanta alamun a'a, ta sauke numfashi tasan tsoron niqabin da ta saka ne take ji shiyasa ta茩i tahowa gare ta. 

Ta mik'e tana dube dube ko zata hango shago amma bata hango nan kusa ba dole sai ta tsallake titi, haka ta mik'e ta iso bakin titi ta sallake ta sayo musu biscuits da Alawa sannan ta dawo ta ce su yi layi, su kayi suna murna ta raba musu sai tsalle su ke yi, ta sauke numfashi tausayi suka bata to ina iyayensu? Musamman ma Aicha wacce ita ka蓷ai tasan sunanta a cikin su, a hankali ta rage tsawonta daidai na Aicha ta ce

"Ina ne gidanku?"

"Mu bamu da gida"

"Bangane ba, ina mamanki?"

"Ta mutu"

Daram 茩irjinta ya bada, tana binsu da kallo 蓷aya bayan 蓷aya tazo kan yaron da ya fara yi mata magana a lokacin da tazo, 

"Ya sunan ka?"

"Muneef"

"Muneef, nice name, ku tafi gida kada ku sake zuwa nan"

Ga mamakin ta suka kece da dariya dukkaninsu har da Aicha wacce bata san ma kanta ba, ta dinga binsu da kallo har suka zauna suna shan Alawa, bata ce komai ba ta juya cikin sauri tana duba agogon wayar ta, tayi sauri ta hau 蓷an mashin ta bar wajen......


************************

Tun da Bilqees ta bar 蓷akin Alaja ta dinga bin kororo虏 lungu虏 sako虏 tana neman ma'aikatan tana sanar dasu Alaja tana neman su a 蓷akin taro, duk da ba wani amsa mata suke ba kawai fa蓷a musu take yi tayi gaba abin ta. Ba a 蓷auki lokaci ba duk suka hallara nan Alaja ta gabatar da jawabi, akan anyi sanyi a restaurant 蓷in, ba a tar蓳an customers yadda ya dace, cikin 蓳acin rai tayi magana 

"Naga kamar kun gaji da aikin ne shine kuke yadda kuke so, to ku sani duk wacce ta kuskura ta zama sanadiyar jawo da茩ushewar wannan restaurant 蓷in to wallahi sai ta fuskanci tashin hankalin da bata ta蓳a sanin akwai shi a duniya ba, ni za ku maida shashasha ban san abin da nake yi ba.

Suka ha蓷a baki wajen bata hakuri 

"Ki yi hakuri Alaja ba za mu gyara kuskuren mu"

Tsaki taja sannan ta ci gaba da cewa

"Na gani a aika ce ba wai a fa蓷an baki ba, na kula har wani ha蓷a kafa蓷a kuke yi dani sabar bushewar ido, to ku sani duk iskancin ku a 茩ar茩ashina kuke...

Ba su ce uffan ba, ta wanke su tas da soso da sabulu, ba tare da ta bari sun sake yin magana ba, sannan ta ce

"Gobe za ayi ba茩i tun safe nake so kowacce ta fito aiki a fara shirye-shiryen tar蓳ansu, kuma manyan mutane ne, don haka ku kashe kanku wajen ganin sun samu farin ciki a cikin wannan restaurant 蓷in"

"Za mu yi 茩o茩arin ganin hakan ya faru"

Suka ha蓷a baki wajen fa蓷an haka, amma Alaja ta daka musu tsawa tare da cewa 

"Ba 茩o茩ari nake so ku yi ba, ku aikata da 茩arfin ku"

Tayi ta musu balbalin bala'o'i sannan ta ce su 蓳acewa ganinta. Kowacce tayi hanyar ta, Bilqees ta mik'e ta koma kitchen duk abin da ta san aikinta ne ta kama yi......


*******************************

Nigeria Maiduguri KIRAWA'S FAMILY 

Zuba mata na mujiya su ka yi suna kallon ta, ganin ta shigo da basket har guda biyu ta ajiye ba tare da ta ce da su komai ba take hawaye. Runtse idanunta tayi tana jin 茩irjinta yana yi mata zafi da ra蓷a蓷i, kamar ta 茩wala ihu ko za ta ji sau茩i amma ina babu hali, Hauwa ce ta yi magana 

"Sis Ashfat me ya faru? Kin fita kina farin ciki yanzu kin dawo kuma kina hawaye"

Ba ta ce komai ba haka kuma bata daina zubda 茩walla ba, Suhaima ta yi magana duk da a lokacin bacci take ji ta ci ta 茩oshi ta kwanta bacci ya fara 蓷aukanta ta ji shigowar Ashfat shine ta bu蓷e idanunta ta 蓷an 蓷ago, a hankali ta yi magana 

"Aunty Ashfat, mene ne?"

"Uhm"

Kawai Ashfat ta iya cewa, Teemah ta ce

"Ko dai ciwon kanta ne ya tashi?"

"Ba shi bane, sis Ashfat wa ya 蓳ata miki rai?"

"Ku kyale ni"

Shine abin da Ashfat ta iya cewa, ta kwanta kan katifa tana sauke numfashi, Hauwa ta janyo basket 蓷in duka biyu ta bu蓷e 蓷aya bayan 蓷aya taga yadda Ashfat ta zuba abinci ta kai haka ta dawo dasu, ta sauke numfashi wato Ya Wahaab ya nuna mata halin nasa kenan, to me yasa take kuka don bai ci ba....

"Sis Hauwa me kike kallo cikin basket 蓷in?"

Cewar Teemah, sauke numfashi Hauwa tayi ta  gyara zamanta tare da cewa 

"Ya Wahaab bai ci abincin ba"

"Shine take kuka?"

Cewar Suhaima, Teemah ta ce

"Shine mana tun da kin ga ta shigo 蓷auke da basket ta dire ta soma hawaye"

"To wa ya sani, in dai Ya Wahaab ne kin kama aiki, ki ma tashi ki wassake ya fi miki, ba kasafai abu yake burge shi ba, maybe baya ra'ayin abin da kika girka ne...

Cewar Hauwa, Ashfat ta katse mata magana ta hanyar cewa 

"Who told you?"

Murmushi Hauwa tayi tare da cewa 

"Ai kin san ala茩ar dake sakaninmu hakan ma ya ishe ki amsa"

"To ba haka bane, cewa yayi, ya ci abinci a side na Ya Sa'eed shine bai samu ya ci wanda na girka ba"

Murmushi Hauwa tayi, ta koma ta kishingi蓷e, Suhaima ta lumshe idanunta da su kayi mata nawi, tayi magana a hankali 

"To sis Hauwa abar magana, da wanne za ta ji"

"To na bari amma da kanta za ta biyo ta hannuna"

"Ke kika sani"

Cewar Ashfat ta ci gaba da hawaye....

*******

Dr Waahab Waseem KIRAWA, Ashfat tana fita ya zauna bakin bed ya sauke numfashi, bai ji komai ba, don shi komansa a faranti yake yinsa, in zayyu to zayyu, in kuma ba zayyu ba haka ma ba zayyu ba, ya mik'e ya fa蓷a toilet ya watsa ruwa ya jima yana wanka sannan ya fito, ya shirya cikin 茩anana kaya ya gabatar da sallah azahar sannan ya 蓷auko system nasa yana dubawa, yana nan zaune har lokacin sallah la'asar, ya idar sannan ya shirya ya fito ya yi wa Mamie sai ya dawo ya wuce parking space ya shiga motar sa ya tada kai tsaye sai Teaching hospital TH.

Yana shigowa cikin hospital 蓷in ya wuce parking space, bayan yayi parking ne ya fito tare da 蓷auko white coat nasa ya rataye a hannunsa bayan ya saka side bag nasa, ya sanyawa motar key kai tsaye ya wuce office nasa, yana isowa ya bu蓷e ya shiga, fes an gyara masa komai tsaf ya zauna tare da sauke numfashi ya ajiye white coat nasa ya kunna system nasa yana dube dube...

Turo 茩ofar da aka yi ne yasa ya dago, aka yi sallama ya amsa, sannan ya 茩araso tare da cewa 

"Our special Medical doctor har ka shigo?"

Ya sauke numfashi tare da cewa 

"Yanzu shigowa na, have a seat"

Ya zauna tare da cewa 

"Tun 蓷azu nake jiran shigowar ka"

"Dr Faisal da fatan dai ba laifi nayi na?"

"A'a akan batun tafiyar ne, ni na ma kammala shiri sai dai Madam ta ce ba zayyu na tafi ba sai da ita"

"Dr Faisal wannan ai abin da ya shafe mu ne ban da ita, how comes ta bimu"

"Kasan Amarya ce, to gashi kuma yarinyar ce, barinta ita ka蓷ai har tsawon 3 months abin bai yi ma'ana ba"

"Na fahimta wannan ra'ayinka ne, bana amarya ba"

Murmushi Doctor Faisal ya yi tare da cewa 

"Let's go straight to the point, naga kuna 蓷asawa da Dr 茒ayyab kuma kaga shine jagoran tafiyar ma baki 蓷aya, kayi masa magana in zayyu na tafi da mata ta"

Murmushi Dr Waahab yayi sosai tare da cewa 

"Ango"

Dr Faisal ya sosa keyarsa tare da cewa 

"Ba zaka gane ba"

"To kada dai kayi min gori, zan yi magana da shi amma ina ga tafiya da ita ba zai zamo matsala ba, duk da haka zan yi magana dashi"

"Yawwa na gode sosai, ya shirye shiryen tafiya?"

"Kasan meye?"

"A'a sai ka fa蓷a"

Cewar Dr Faisal yana gyara zaman sa, Dr Waahab ya ci gaba da cewa

"Ni ko fara shiri ban yi ba gashi tafiya saura 5 days abu kamar wasa"

"To Ya kamata ka fara shiri fah kwanaki ka蓷an suka rage"

"Gobe in sha Allahu zan shirya komai na"

"Ya fi kam, bari na koma office, sai zuwa anjima"

"Ok sai anjima"

Dr Faisal ya wuce, Dr Waahab ya ci gaba da ayyukan sa.....


******************

"Ke Ashfat tashi lokacin sallah la'asar ya yi"

A hankali ta bu蓷e idanunta tare da turo baki ga kanta da yayi mata nawi, ta dago za tayi masifa saboda katse mata bacci da take yi sai taga Ammie ce mahaifiyar ta, ta tashi ta zauna tare da sake ware idanun tana bin 蓷akin da kallo taga ashe ita ka蓷ai aka bari a 蓷akin, zuwan Ammie ne ma yasa ta tashe ta..

"Tashe za ki yi ba wai zama ba, baccin ya isa haka"

"Ammie ban ma san nayi bacci me nawi haka ba"

"Ina za ki sani tun 蓷azu na turo a tashe ki amma sai ace kina bacci"

Ta mik'e tare da yin mi茩a ta ce

"To Ammie zan watsa ruwa sai na gabatar da sallah"

"Da ya fi miki kam, sai ki hanzarta wankan ki samu ki gabatar da sallah don lokaci na ta tafiya"

"To Ammie"

Ammie ta fice, Ashfat ta rage kayan jikinta ta fa蓷a toilet ta watsa ruwa sannan ta 蓷auro alwala ta fito ta shirya cikin doguwar riga ta lace ta feshe jikinta da turare sannan ta gabatar da sallah, bayan ta idar ne ta shirya ta fito kai tsaye kitchen ta nufa tasan a wannan lokacin 拼an'uwanta suna kitchen suna aiki.

Ta shigo ta tadda su sun baza ko ina sai faman girke-girken abincin dare suke yi, ta iso tare da cewa 

"Yanzu a rasa wacce zata tashe ni, kun san lokaci ya tafi sosai shine ba za ku tashe ni ba, har sai da Ammie ta tashe ni"

Suka 蓷ago dukkanin su suna kallonta, ta sauke numfashi ta zauna tana ha蓷e fuska, murmushi Aunty Jamila tayi tare da cewa

"Gaskiya ba ku kyauta mata ba"

"Aunty Jamila ai zan rama"

"Sis Ashfat ni kam gani nayi kin kwanta cikin wani yanayi shiyasa ban tashe ki ba"

Cewar Suhaima, Hauwa ta ce 

"To tun da dai kin tashi ai shikenan, komai ya wuce"

"Bai wuce ba har sai kun kar蓳i laifin ku"

"Tab蓷i ni dai ban yi wani laifi ba, shikenan kina bacci sai mu katse miki bacci"

"Ke Hauwa bana son shashanci kuma wallahi sai na rama ke ma kin sani ba a yi min na kyale"

"Ki yi hakuri Aunty Ashfat in sha Allahu ba za mu sake yi ba"

Cewar Teemah, Ashfat ta sauke numfashi tare da cewa 

"Ke ai ba ki da matsala an yafe miki, da sauran nake"

Ba su ce komai ba, ta mik'e ta zuba abinci a plate wanda ta gani cikin food flask rice and Stew shi already sun kammala sun ajiye a gefe sun maida hankali ga dafa tuken semo da miyar yau茩i...

Ta zauna sai da ta kammala ci sannan ta mik'e tare da cewa 

"Aikin ma ya kammala ba sai na tayaku ba, kun ga tafiyata"

"Ya Ashfat aiki fa har yanzu da saura kinga akwai 茩ulla semo fah"

Cewar Teemah, tayi murmushi tare da cewa 

"I'm patient"

Ta fice tana ji suna ta mita, ta wuce side na Mamie, ta turo 茩ofa tare da sallama, Mamie ta amsa a lokacin tana 茩o茩arin fitowa daga toilet dake 蓷akin. Ashfat ta zauna kan carpet cikin girmamawa ta ce

"Barka da yammaci Mamie?"

"Yawwa barka dai A'isha"

Ta fa蓷a tana me isowa wajen wardrobe, ruwa ta watsa don taji dama dama saboda ji take jikinta wani iri haka, ta 蓷auko doguwar riga mara nauyi ta zura ta iso ta zauna bakin gado tare da cewa 

"A'isha da fatan lafiy"

"Lafiya kalau Mamie, yau tun safe ban ji motsin ki ba"

"Ai yau wuni nayi a kwance, fitar ma wuyanta nake gani"

"Aike Mamie, ba ki son fita kin fi son 蓷aki"

"To muna da ku ina zan fita? Me zan yi? Ai gara dai nayi kwanciya ta"...

Turo 茩ofar da Hauwa tayi ne yasa ta 蓷ago ta katse maganar da take son yi....

"Sis Ashfat ashe dai nan kika zo?"

Murmushi tayi tana sudda kai 茩asa ta ce

"Eh Hauwa, ba dai kun gama aikin ba?"

"Na kawo wa Mamie fruits ne zan koma mu 茩arashe"

"To yayi kyau, ni ma ba shigo na gaida ta ne"

Ta mik'e tana shirin fitowa Hauwa ta ce

"To an gode surka"

Ta juyo ta harareta irin na wasan nan sannan ta fice, dariya Hauwa tayi...

"Surka kuma?"

Cewar Mamie, Hauwa ta ajiye plate dake 蓷auke da yankakkun fruits ta ce

"Eh Mamie surkar ki ce"

"To ki ce ita ce za蓳in Wahaab"

"Yaya da ra'ayi"

"Aiko in dai haka ne nayi farin ciki"

"茒azu ma ta gama hawaye"

"Subhanahu! Hawaye kuma?"

"Eh tayiwa Ya Wahaab breakfast bai ci ba haka ma lunch"

"Gaskiya bai kyauta ba, aiko ka蓷an ne sai ya ta蓳a"

"Mamie zan koma na 茩arashe aikin"

"To in kun gama aikin sai ki 蓷aura min green tea"

"To yanzu kuwa"

Saurin barin bakin 茩ofar tayi saboda jin motsin fitowar Hauwa, ta 蓳uya a bayan Corido ta sauke numfashi, da farko ta karaya akan soyayyar ta, amma tun da Mamie na farin ciki da hakan sai in da 茩arfinta ya 茩are. Ganin Hauwa ta shige kitchen yasa ta fito daga ma蓳uyarta ta wuce 蓷akin Ammie tana shiga ta taddata zaune suna hira Aunty Nazeefa ta gaida ta sannan ta kwantar da kanta a kafadar Ammie...

"Ke ba ki san kin girma bane?"

Cewar Aunty Nazeefa, ta turo baki tare da cewa 

"Kai Aunty Nazeefa kawai don na kwanta a jikin Mamata ya zama laifi"

"Ya ma zama tashi ki barta ta sarara"

"Uhm"

Ta fa蓷a ta mik'e ta fice zuwa 蓷akinsu, tasan gulma ce ta kawo Aunty Nazeefa ko me kuma ya faru a 蓷ayan side 蓷in......





Comments and share fisabilillah

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.