Free chapter · Read without an account
Point of No Return
by NorthernAngel · His Rose
Cikin wata quiet, calm voice Zafar yace, "Zara, please drop it." Sai dai bai gama rufe baki ba muryar Shalele ta ratsa office ɗin, "Excuse you—" Cikin hanzari babanta ya dakatar da ita da cewa, "A kul Zara'u, kar inji bakinki." Haɗe rai yarinyar tayi sannan ta gyada kai. Zafar kam tuni ya haɗe girar sama da ƙasa nan da nan, the atmosphere turning incredibly tense. Zara dake aikawa yarinyar wani ƙasƙantaccen kallo dripping with pure disdain tace, "Ashe kina jin maganar babanki. Did he just skip the lesson on basic dress codes? Because it’s quite apparent that if he had told you how ridiculous you look in a professional space, you would have changed—" Da wata deep, calm voice Zafar ya sake cewa, "Enough, Zara. Ba nace kiyi shuru ba? From this point on, Zara'u is going to dress appropriately. Shikenan." Cikin zafi Zara ta daki table ɗin shattering the corporate silence tana cewa, "No, it's not enough! Why does the truth bother you guys so much? Why would a father let his daughter come to a corporate headquarters dressed like this? Like, didn't you feel any shame walking into the building with her? Or, Baba, don't you even feel protective when everyone is ogling your dau—" Cikin wani irin tsawa Zafar yace, "Zara, stop it! Who gave you the right to judge people? Are you their creator? If you have an issue with her outfit, take it up with her. Why are you humiliating an old man in my office? Me yasa baki da kunya ne? Where on earth are your manners?" Zara data saki baki tana kallonsa, stunned for a split second, ta rufe bakin kafin ta fara magana calmly but defensively, maintaining her fierce posture: "I’m not trying to play God or judge anyone. I am simply questioning the underlying motive behind a father letting his daughter dress so provocatively just to come visit my husband's private office." Cikin wani irin ɓacin rai Shalele ta miƙe tana dukan table da ƙarfi, "Enough! How dare you speak about us like that? What motive—" Bata ƙarasa ba Ghost yayo kanta yana barking ferociously, yana neman birkicewa lokaci guda. Cikin sauri Zafar ya taro karen yana kiran sunansa trying to hold back the massive beast. Zara dake zaune tana aikawa Shalele wani kallo tace, “Sit down, Zarina." Ta faɗa, muryanta na dropping into a chillingly calm, low register. "You are screaming in my husband's office, slamming tables, and triggering my dog. I suggest you control yourself, unless you want me to have security throw you out of this building.” Da mamaki Alhaji Waziri ke kallon Zafar da ke tsaye bai ce komai ba sai ma kare da yake ta bawa magana, completely aloof, kamar bai jiyar abun da yarinya ƙarama ke musu ba. Hankali kwance Zara ta ci gaba da magana, her voice sharp and calculated: "And besides, I wasn't talking to you. I was having a conversation with your father. My actual concern is protecting my husband's reputation, not how your father lets you dress in public." Daga haka ta juya kan tsohon, "Baba, to be completely frank, ban ji daɗi ba. Out of respect for your ties to our family, I am choosing not to have security escort your daughter from the premises right now. But this outfit of hers is a direct threat to my husband’s image. I mean, look at her. If people see her walking around the executive floor like this, they will honestly think you brought an unprofessional distraction into my husband's—" Bata ƙarasa maganar ba sakamakon jan hannunta da Zafar yayi da wani irin ƙarfi, instantly cutting her off. Ya ɗagata daga kan seat ɗin da take zaune kafin ta ƙarasa insult ɗin da ke bakinta. Ya juya tare da kallon Alhaji Waziri, ya fara magana his voice tight but maintaining respect: "I am so sorry for this embarrassing display, Alhaji. Please overlook my wife's childish behavior. I will personally arrange a position for your daughter, probably in the Abuja sector where it will be much easier to integrate her. You understand the corporate protocols under this roof, and she doesn't fit the current requirements of this headquarters. Please, accept my apologies for my wife’s behavior." Tunda ya fara maganar har ya gama, kan Alhaji Waziri na ƙasa, ya kasa ɗagowa ya kalli Zafar saboda maganganun da Zara ta faɗa, musamman na ƙarshen which completely stripped them of their dignity. Zafar kuwa na gama faɗin haka, ya juya ya fice daga office ɗin yana jan hannun Zara da ƙarfi, his grip firm and unyielding, yayin da Ghost ya rufa musu baya cikin sauri. Suna fitowa, Zafar ya kalli inda PA ɗinsa yake, inda sukayi exchanging a brief, knowing nod shortly shi da Alkasim ɗin. Alkasim ya gane aikin da aka ba shi na sallamar Alhaji Waziri daga office ɗin formally, sannan ya rufo ƙofar. Yana riƙe da hannun Zara dake gefensa calmly, though her heart was racing, Zafar yayi pressing elevator ɗin ya buɗe suka shiga, Ghost na biye da su. Wani irin shuru ne ya ratsa ciki, babu wanda ya cewa wani uffan, the silence inside the elevator was suffocating. Zara dai sai satar kallonsa take; yayi folding arms ɗinsa ya kurawa guri guda ido cike da wani irin ɓacin rai, his jaw clenched tight, ko kallonta baya son yi. Zara dai sai taɓe baki take, hannunta ɗaya na jikin Ghost tana shafa shi a hankali seeking some comfort. Haka suka fito daga elevator ɗin, Zara ta fara tafiya tare da Ghost yayin da Zafar ke biye da su closely, acting like a protective shield despite his anger. Kowa matsawa yake yana basu hanya yayin da ake binsu da kallo; wasu cike da burgewa, wasu kuma pure envy. Kowa yana kallon su a matsayin wasu perfect powerful couple that found everything they need in each other. Suna zuwa waje, Zara ta fara nufar hanyar motarta, inda cikin sauri Zafar ya janyo hannunta ya juyar da ita. Ghost shima yayi turning cikin sauri yana binsu suka nufi inda motarsa take a private parking space ɗinsa. Yana isa, ya buɗe mata front seat yana nuna mata ta shiga ba tare da ya kalleta ba. Wani dogon tsaki Zara ta ja ganin yanda ya wani haɗe rai yana shan ƙamshi. Shiga tayi cikin motar ta rufo ƙofar da ƙarfi slamming it hard, inda shi kuma yayi ƙwafa yana gyada kansa in disbelief at her attitude. Backseat ya buɗe, Ghost ya shiga cikin sauri, sannan ya rufo ya zagaya ya shiga driver's seat. Ya rufo ƙofar, ya tada motar, revving the engine as he sped out of the Nexus premises. Throughout the ride babu wanda yace uffan, the heavy silence suffocating the entire space. Zara dai ko a jikinta, sai video take a wayarta, tana magana tana hasko Ghost dake manne da seat ɗinta. Can dai ta gama video ɗin ta ajiye wayar, sannan ta juya ta kalli Zafar da mamaki, "Where are we going?" Ta tambaya ne saboda ganin ba hanyar gida suka nufa ba; hasali ma ya nutsa cikin gari ne weaving through the Lagos traffic. Banza yayi mata, idonsa na kan hanya babu alamar ma yasan tana yi. Gyada kanta tayi bitterly kafin ta ƙara cewa, "You know, if you have a problem with this marriage, just say it. Seriously, I am always the one who gets wronged in our marital problems, yet you always act like you're the one who is suffering." Daga haka ta canza sautinta, inda ta fara magana da ƙarfi, her voice echoing within the car: "And why the hell would you report me to Daddy? Look at all the things you do in this marriage—do I ever broadcast your behavior to anyone? For all the insults you hurl at me constantly, have I ever exposed you to a single soul? If you need sex this badly, you have another wife—go to her, am I blocking you? Have you heard me complaining to Baffa about anything again? At this point, Zafar, you should realize that I am just protecting my peace. So please, stay out of my business the same way I stay out of yours. You don’t see me reporting your flaws to your parents, so stop running to mine. Bana so, bana so! I absolutely loathe it. If you are this exhausted with me, then just let me go. It is not mandatory for you to remain in this marriage with me." Ta ƙarasa maganar tana huci, tana goge hawayen dake zuba a fuskarta ba ƙauƙautawa. Zafar kam kamar da dutse take magana, don har yanzu bai ma nuna alamar yasan da ita yake ba, his expression completely blank and detached. Bayan kusan tafiyar awa ɗaya, Zafar yasa kwanar wani layi, inda ita dai Zara kawai kallon hanyar take tana goge hawayenta. Parking yayi a daidai ƙofar gidan ba tare da yayi horn ba, alamar ba shiga zai yi ba. Ba tare da ya kalleta ba, yayi magana cikin wata calm, low voice that sent a chill through the air: "Get out." A bazata taji maganar tasa, wanda yasa ta saurin juyawa tana kallonsa. Da mamaki tace, "What?! What are we doing here?" Juyowa yayi yana mata wani banzan kallo with absolute coldness yace, "Do I really have to tell you what you are doing in your father's house? Fitar mun a motata, malama. Just get out." Frowning tayi tana kallonsa, her brain completely scrambling, yana gaza mata processing abun da ya faɗa. Cikin gajeren haƙuri yaja tsaki yana jijjiga ƙafa, hannunsa na tapping steering wheel impatiently. Zara dake kallonsa ta buɗe bakinta dake rawa, amma sai ta ƙasa magana. Sai kawai ta rufe bakin tana haɗiye wani abu mai ɗaci da ya tsaya mata a maƙogoronta. Gyaɗa kanta tayi tana cewa, "Okay," cikin wata shaƙaƙƙiyar murya choking on her own tears. Daga haka ta buɗe motar ta sauka a hankali, saboda jirin da take gani her vision momentarily blurring. Bayan ta saukan ma, sai da ta ɗan dakata tana riƙe da ƙofar saboda jirin sosai take ganinsa. Sai bayan kusan minti ɗaya sannan ta iya motsawa, ta rufe motar a hankali sannan ta nufi gate ɗin gidansu na Oduduwa Crescent dake nan cikin Ikeja GRA. Bata ƙarasa shiga gidan ba taji ya tada motarsa ya juya ya bar layin tare da Ghost a cikin motar, leaving her completely stranded. Security ɗin da ke zaune a gurin, tuni suka miƙe suna mata sannu da zuwa, duk sun cika da mamakin ganin yanayinta kamar ba ta da lafiya, her pale face instantly giving her away. Da ƙyar Zara ta ƙarasa cikin gidan, inda ta tura ƙofar ta shiga cikin foyer. Ko ina shuru, da alama ba kowa a ƙasa. Kitchen ta shiga kai tsaye, inda ta buɗe built-in fridge ta ɗauki ruwa mai sanyi, ta ɓalle marfin ta kai baki. Ba ta cire ba har sai da ta shanye ruwan tass, sannan ta sauke robar daga bakinta tana faman sauke nannauyan numfashi, feeling the cold water rush through her heated body. Zama tayi kan seat ɗin kitchen island ta kifa kanta tana sauke numfashi. Kusan 30 minutes ta ɗauka a zaune a gurin tana hutawa, sannan ta miƙe ta fito daga kitchen ɗin. Ɗankwalinta ta cire ta jefar a gefe, sannan ta faɗa kan sofa ta kwanta. Nan da nan baccin wahala ya fara ɗaukarta, amma tunawa da ba tayi azahar ba, gashi la'asar ta kusa, yasa ta miƙe da ƙyar. Sama ta nufa, inda tana fara hawa matakala ta hango Mommy dake saukowa. Cak Mommy ta tsaya tana kallonta cikin tsantsar shock, kallo ta ringa bin Zara da shi har ta ƙaraso kusa da ita. Cikin mamaki tace, "Ha'ah, Ada! What are you doing here? What happened?" Zara ta wuce Mommy, cikin muryar bacci take cewa, "Well, if anyone actually checked the ground floor, they'd know I've been here for an hour, Mommy. Good afternoon, I’m happy to see you too." Mommy ta juya ta bi bayanta tana kallonta suspiciously tace, "And why are you here?" Zara dake turo baki ta ci gaba da tafiya ba tare da ta cewa Mommy komai ba. Cikin masifa Mommy dake binta tace, "Ada, am I speaking to the wall? What is your mission coming to this house this afternoon?" Ta buɗe ƙofar ɗakinta kenan ta tsaya, sannan ta juyo tana kallon Mommy. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke, kafin cikin sanyin jiki da wata irin muryar da ta rasa kuzari tace, "Ọ gbala m alụkwaghịm." Wani irin zaro ido Mommy tayi tana kallon Zara, her entire world suddenly tilting on its axis, kafin a hankali ta zame ta zauna a ƙasa dirshen, staring into space cikin wani pure horror and utter disbelief...
NorthernAngel🪽