Free chapter · Read without an account
36
by Rufaida Umar · ALWASHI 2
ALWASHI
61
Areef ya murɗa ƙofar falon Laila ya shigo da sallama, Kausar na biye da shi. Gaba ɗaya ƙamshin turarukan da ta kunna ne ya soma ziyartar hancinsu. Kausar da ta ci kwalliyarta ta saka doguwar rigar abaya baƙa, ta bi falon da kallo. Komai a tsare, kujerunta kalar milk da dark brown. Labulayenta ko dark brown ne masu ratsin golden a jiki, babu tarkace amma fa falon ya tsaru ainun. Ga wani show glass dinta na zamani mai O shape an yi jere mai ɗaukar hankali da kyau.
"Bismillah, bari na kira ta." Areef ya furta yana kallon Kausar, lokaci guda yana mata nuni da ta zauna. Ta gyaɗa kai tana mayar masa da martanin murmushin da shi ma yake bin ta da shi.
Zama ta yi a kujerar two sitter mafi kusa da inda take tsaye ta bi bayansa da kallo har ya shige ɗakin Laila. Ajiyar zuciya ta sauke ta riƙe kirjinta take bugu da sauri, ko ya za ta gan ta? Ta dai san tsohuwar mai kitson Mami ce, kasancewar ba ta taɓa sanya ta a ido ba, hakan yasa koda ake cewa kyakkyawa ce ba ta da makusa ba ta wani yarda sosai ba, so take ta gan ta da idanunta.
***
A ɗakin kuwa, Laila na zaune gefen gado ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya suna magana da Haseenah ta waya. Murɗa ƙofar da shigowar Areef ɗauke da sallama bai sa ta dubi ƙofar ba don tun shigowarsu falon ta ji alamar motsinsu sai dai ta fi ba wayar da take muhimmanci a kan ta wani fita tarbar su.
Ya shigo ya tsaya a gefen madubi gami da zuba mata idanunsa. Wani irin yanayi ne karo na farko ya ji a game da ita, kallonta yake from head to toe, daga sadda suka haɗu zuwa yanzu ya gama karantar ita ɗin mace ce mai son ado da kwalliya. Yanda ya kula wato duk yanda zuciyarta ta kai da tsanar mutum, to bai isa domin shi ta fasa gayunta ba. Ya rasa me ya shagaltar da shi wajen kallonta, yanda take futar da zantukanta da harshen larabcinsu na shuwa, ko kuma yanda take wani girgiza ƙafa ne cikin nutsuwa, ko kuwa kwalliyar fuskarta, duka ya rasa gane dalilin dogon kallon da yake bibiyarta da shi.
A ɓangaren Laila, tun tana ba wa banza ajiyarsa tana cigaba da wayarta, har ta gaji da irin kallon ƙurillah da yake mata ta yi wa Haseenah sallama. Dayake hirar zuwan Kausar din suke, Haseenah ke tambayar sun iso ne? Laila ta amsa mata, hakan yasa suka sallama bayan Haseenah ta na ƙara zuga ta wai don Allah ta saki ranta ta kuma ƙara jan aji kar kishiya ta raina ta. Murmushi Laila ta yi, murmushin da ya sa Areef lumshe idanu ya kauda kai.
"Are you done?"
Sai a lokacin ta dube shi tun shigowarsa, fuskarsa a sake kuma cikin yanayin da ba za ta iya fassarawa ba. Ta kauda kai kamar ba ita ta gama waya da sakakken fuska ba.
"Sannu da zuwa." Ta furta ciki ciki, ya jinjina kai.
"Kausar na jiranmu a falo. Ki fito ku gaisa."
"Ok." Ya juya ya koma falon yayin da ita kuma ta bi shi da harara kamar yanda ta saba da jan guntun tsaki. Miƙewa ta yi ta gyara ɗan yafe da ta yi a kafaɗarta ta bi bayansa.
***
Kausar da ke zaune ta gaji har ta soma latsa wayarta, ta ji shigowar mutum falon, koda ta ɗago mijin nata ne. Murmushi ya sakarmata ta mayar da martani gami da maida kanta ƙasa, ƙirjinta na bugu da sauri don a farko ta yi zaton ma Laila din ce.
"Sorry, mun bar ki kina zaman jira."
Ya furta bayan ya zauna a gefenta har cinyoyinsu na gugar juna. Kunya ta sanya ta kasa kallonsa sai furucin 'bakomai' da ta yi.
"Assalamu alaikum." Jin muryar Laila ya sa Kausar ta ɗago ta amsa. Ƙamshi na musamman ya daki hancinsu kafin ma ta ƙaraso ciki. Kausar ta dube ta, shakka babu kam sai dai hassada da kishi ne kaɗai zai sa mace ƴar uwarta ta kushe kyan halittar da Ubangiji ya ƙera a kanta.
"Sorry Amarya, na bar ki kina jira. Ya gajiya? Allah ya bada zaman lafiya."
Laila ta furta da murmushi saman fuskarta, Areef kuwa kallonta kawai yake ta ƙasan idanu.
"Bakomai, amin Anti. Nagode."
Kausar ta amsa da ƴar rawar murya.
"Bismillah ko, sai mu yi dinner tare. Ko me ka ce?"
Laila ta furta tana watsa idanunta daga kan Kausar zuwa ga Areef din da wani irin salon da bai taɓa gani a wajenta ba. Ji ya yi tsikar jikinsa ya tashi. Daƙyar ya dake ya amsa.
"Ok."
Ta miƙe tana maida kallon na ƴar harara ganin hankalin Kausar na ga wayarta. Shi ko ya murmusa sai dai ba ta ko gani ba don tuni ta yi gaba zuwa kicin. Ya bi bayanta da kallo kana ya shafa kansa.
'Areef control mana!' Ya yi wa kansa wannan faɗan. Kausar kuwa ta lura sarai da yanda yake bin Laila da idanu, ita kanta ba ta san me take dannawa a wayarta ba har dai Laila ta shigo falon dauke da leda babba ta shimfiɗawa a dora abinci. Nan tsakar falon ta shimfiɗa sannan ta ƙarasa gaban dinning dinta ta kwaso kwanukan abincin ta ajiye.
Kausar ta gama fahimtar koda Laila za ta girmeta bai fi da shekara ɗaya ba ma, amma kuma a yau kadai da ta gan ta, ta yarda ta fi ta wayewar kai da daukar gayu. Ita zamanin yanmatancinta ma ba ta wani yin kwalliya, ba ta ma iya ba sai da ta fara son Yaya Areef, ta fara gyara shigarta duk domin idan ya kawo ziyara ya ce yana sonta.
Laila ta dube ta bayan ta zubamata haɗaɗɗen chinese rice din da ta girka da grilled chicken sai ko ɗan sauce da ta yi. Ta ajiye gabanta.
"Bismillah ko?"
Kausar ta yi murmushin yaƙe, ta yi zaton a girki ba za kama ƙafarta ba domin ta iya girki itama daidai gwargwado, sai dai koda ta sanya lomar farko a baki, ta tabbatar nan ma Laila ba kanwar lasa ba ce. Areef kam duban farantin da Laila ta cikamasa yake, yanda ta cika shi ya san da gayya aka mishi. Kar dai irin ka ci ba don halinka dinnan ba. Ya kalle ta sadda take kokarin zuba musu lemun zoɓo a kofuna.
"Ya ban ga kin zuba naki ba? Ko tare zamu ci?"
"No, yanzu zan ɗiba."
Ta fadi tana ajiye masa kofin lemun, sannan ta zuba na Kausar itama ta ajiye sai ko gorar ruwan sanyi a gefen kowannensu.
"Let's share this, ya min yawa."
Ta yi kamar ba ta ji ba, sai da ya ƙara maimaitawa kafin ta yi murmushin yaƙe ta ɗauki serving spoon ta ja faranti ta rage nasa.
"Shikenan ai mun raba ko?" Ta fadi tana dubansa da murmushi lura da ta yi hankalin Kausar na kansu. Areef ya lumshe mata idanu sannan ya buɗe, ta kauda kai.
'Tsohon maye.' Ta furta a ƙasan ranta. Ba ta ƙara magana ba ta soma cin abincinta bayan ta ƙara adadin da ta san za ta cinye, ita ba abin da ya mata zafi da su da har sanadinsu wai za ta kasa cin abinci.
Sai bayan an kammala Kausar ta taimaka mata suka tattara komai. Kafin bayan dawowarsu Areef ya ɗan musu nasiha da nuna musu kowacce yana sonta ya auro ta, don haka su girmama juna. Sannan Laila ta riƙe girmanta matsayinta na babba, haka Kausar ta ba ta girmanta. Ita dai Laila jin sa kawai take, a karshe dai suka yi mata sallama ya wuce takawa Kausar zuwa nata ɓangaren. Har ƙofa Laila ta mata rakiya gami da godiya, daga nan ta koma ciki. Ba ta jira komai ba ta dauki abin da duk za ta buƙata a falon ta rage fitilu ta yi ɗakinta ta ƙulle da muƙulli. Dalilin barin falon a buɗe bai wuce ganin ya bar wayoyinsa a ajiye ba. Shi ma koda ya dawo ya ya fahimci ta shige ɗakin kuma ya sani ba za ta yi gangancin barinsa a buɗe ba, murmushi kawai ya yi ya dauki wayoyinsa ya fice zuwa nasa bangaren.
***
Zaune take a falon Mami ita ɗaya sai wayarta da ke taya ta hira, chatting suke da Zakiyya tana faɗamata ta kai mintuna ashirin zaune a falon, tare suka zo gidan da Kausar bisa alfarmar da Areef ya roƙa a wurinta na ta bi su da Kausar din su shiga ta gaida Mami da mutan gidan. Suna zuwa kuwa Kausar ta nuna ita ta gida ce ta shige ciki ta bar ta nan zaune a falon.
Can sai ta ji sallama daga ƙofar shigowa falon, Benazir ce ta shigo hannunta riƙe da ledar da ta sha gam ta ko'ina, ga dukkan alamu saƙo ta karɓo. Laila ta amsa sallamarta, Benazir ta ƙaraso cikin sakin fuska ta na fadin.
"Lah, Sis Laila sannu da zuwa. Ina wuni."
Laila ta amsa fuskarta a sake. Tun haɗuwar da ta yi da ita sadda ta je gidanta, babu wani abu da yarinyar ta nuna mata na ƙyama ko makamancinsa.
"Ke kaɗai? Afrah ko ta fita ne? Mami fa?"
Duka tambayar a lokaci guda Benazir ta jero tana waige.
"I think suna tare da Kausar."
Amsar da kawai Laila ta ba ta kenan. Benazir ta ɗan ji ba dadi, sai ta waske da fadin.
"Anya kuwa? Mami nasan ba ta san tare kuke ba, ko kun gaisa? Bari dai na mata magana."
Ba ta jira amsa ba a wannan karon ta kinkimi kayan da ta shigo da shi ta nufi ciki. Laila ta yi murmushi, wato a duk inda aka haɗa mutane marasa kirki da sanin darajar ɗan adam, sai an samu wanda ya fita zakkah a cikinsu. Ta lura da hakan a kan Benazir da ma Adda Mardiyya. Kawai dai ita a wurinta laifin iyayensu ne ya shafe su.
***
Koda ta shiga ɗakin Mami, ta iske Mamin zaune a gefen gado ga Kausar da Afrah sun sanya ta tsakiya suna hira abin su da harshen fulatanci. Mamaki ya bayyana ƙarara saman fuskar Benazir. Ba ta zaci haka ba, ta fi tunanin Mami na banɗaki ko tana wani uzurin, Kausar kuma ƙila tana ɗakinsu wurin Afrah da ta riga ta sani zai wahala ta fito falon saboda wata Laila.
"Ah, yaushe kika dawo?" Mamin ta tambaya.
Benazir a sanyaye ta amsa.
"Yanzu na dawo Mami, na iske Sis Laila ita kaɗai a falo babu kowa, Sis Kausar ba ki ce tare kuke ba?"
Kausar za ta yi magana Mami ta riga ta.
"To idan ta faɗi mene ne? Ko dole ne sai na fita a sadda aka sanar min? Ki kiyaye ni fa!"
"Allah ya huci zuciyarki Mami, amma na ga ko Hamma ne ya shigo ba zai ji dadi ba. Ke fa mutum ce mai karrama baƙonki Mami."
Mami ta yi shiru ranta a haɗe sai kuma ta ja tsaki.
"Sai ki je ki ce mata ta shigo tunda ba hana ta shigowa aka yi ba ko? Ba zan iya zuwa falon saboda ita ba."
Kausar ta saci kallon Mami kafin ta kauda kai, zuciyarta fari ƙal, ita tun sadda ta ci karo da Laila ta ke jin haushinta. Kishinta take ko ta ina, tana fatan Allah ya dauwamar da wannan ƙiyayya nata a wurin Mamin da su Afrah. A gefe guda kuma ranta ya sosu da ganin damuwar Benazir kan Laila, za ta fi kaunar kowa cikinsu ya kasance ita kaɗai yake so. Ta bi Benazir da kallo har ta fice domin kiran Laila zuwa ɗakin.
***
Laila dake zaune tana shawarar kawai ta miƙe ta bar gidan, ta tsinci muryar Benazir na faɗin wai ta shigo ciki inji Mami ai an zama ɗaya. Ta san kawai kwaskwarima Benazir ta yiwa zancen, ta cije ta amsa da toh kafin ta bi bayanta zuwa ciki. Karon farko da suka yi tozali da Mami, kaf rayuwar Laila sai a hoto ta ke ganin matar, a yanzun da ta ƙaremata kallo kuwa, sai ta ga kamar Areef ta ke kallo tsabar yanda suka yi kamanni. Mami ta ƙara ɗaure fuska tana mai jinjina tsageranci da rashin kunyar Sameera, wato har kallon ƙurilla take bin ta da shi, kallo na rashin kunya.
"Afrah, ku ɗan bamu waje zan yi magana da Sameera."
Jin haka Afrah suka miƙe tare da Kausar har Benazir suka fita, sai a lokacin Laila da ke tsaye ta nemi wuri a saman tattausan kafet din dake shimfiɗe a gaban gadon Mamin ta zauna.
"Barka da rana." Ta faɗi daƙyar tana jin wani zafi da tsanar Mamin na taso mata a rai.
Mami kanta ji take kamar ta tashi ta ƙarasa ta kwashe ta da mari.
"Sameera zan kira ki ko Laila?"
Murmushi Laila ta yi ta ɗago ta dube ta tsakar idanu.
"Duk ɗaya ne Mami."
Mami ta yi kwafa.
"Dama ai tatacciyar mara kunya ce, ni na sani ko can baya rashin samun fuska ne da za ki baje hajarki a ƙwarya ya sa ki ka yi mana lulluɓin biri. Toh ki sani Sameera, yanda kika shigo gidan nan haka za ki fita domin wallahi na tsane ki! Ba zan taɓa sonki ba! A kanki ɗana ya taɓa kusantar zina! Duk da ya yi zaman Turai, ban taɓa samun labarin ya haiƙewa ɗiyar wani ba sai da lamarinku ya afku! Ba ki bar shi haka ba sai da kika gama yawonki na ta zubar kika rasa mashinshini kika saɗaɗo kika yaudare shi har ya aureki ko? Wannan baƙin naci har ina! Idan kuɗi kike buƙata ki lissafa adadin da kike buƙata ki gani idan ba mu damƙa maki ba mana!"
Duk da irin baƙaƙen maganganun da Mami ta fesa mata, kawai sai ta saka dariya, dariyar da ta yi mugun shaƙar da Mami. Idanun Mamin suka kaɗa, ta rantse da ace wani bawa na da ikon kashe ran wani bawan kawai saboda tsana kuma babu abin da shari'a za ta yi masa, to a yau dinnan za ta gama da rayuwar Laila ta huta. Ta sani musabbin tsanar da ta yiwa Sameera ba wai don kasancewarta talaka ba, ita ba ta ƙyamar talaka, kawai dai tsana ce da ta samo asali da fahimtar abubuwa da yawa da ta yi kan lamarinta da ɗanta wanda a gaba take da tabbacin zai haifar da matsaloli tunda a yanzun ma an fara.
"Hajiya Salma."
Sunanta da Laila ta ambata kai tsaye ne ya sa da sauri ta dube ta, kanta har wata sarawa ta yi, da rawar baki ta nanata. Laila ta miƙe tsaye ta ƙarasa ta zauna gefenta a saman gadon. Mami kallon Laila kawai take da tsantsar mamaki har da ɗan ja baya saboda ganin irin kallon da Lailar ke bin ta da shi da jajayen idanunta.
"Na yi zaton abu na farko da za ki fara tambaya shi ne batun jikarki ko jikanki da na haifa."
Wata irin zabura Mami ta yi ta miƙe tsaye, cikinta har wani ƙullewa ya yi, ƙirjinta ya hau dukan tara-tara.
Laila ta yi baya da tafukan hannayenta ta tokare su a gadon ta dora ƙafa ɗaya kan ɗaya tana duban Mamin da murmushi saman fuskarta a wannan karon.
"Me...me..ki..ke..nufi?"
Mamin ta tambaya da rawar baki, ita kuwa Laila ta yi ƴar dariya.
"Yes, abin da kika ji na ce. Ko kin manta sadda kuka yi min korar kare da cikin ɗanku a jikina?"
Zufa ta ketowa Mami, ta yi ɗif kamar ruwa ya cinye ta.
©Rufaida Umar