Free chapter · Read without an account
10
NAZEEFAH SABO NASHE
FREEđ
***
-10
Sosai Hajja ta sake razana ganin shatu tana nufota, fadâi take â Don Allah kada ku cutar dani ku fadâi mai kuke so nayi? Ni baiwar Allah ce ba ruwa na da kowa a duniya.â Shatu ta âkyaâkyata wata mahaukaciyar dariya â so muke kada ki sake cutar da hadizatu idan kuma kinâki zaki ga sakamakon taurin kai kina ji?.â Da sauri hajja ta dâaga kai â Na bi Allah na biku insha Allah ba zan sake komai baâ shatu ta sake kecewa da dariya bayan jin abinda tace cikin daka tsawa tace â To rufe idonki kuma kada ki sake ki budâe sai nayi nisa da tashi sama.â Da sauri hajja ta rintse idonta gam, shatu da sauri ta fice daga dâakin ta shige dâakinta. Ai cikin azama hajja tana budâe idonta tayi saurin miâkewa ta fice daga dâakin jikinta har makyarkyata yake, A tsakiyar falon ta tsaya ta dinga kwalawa mutanen gidan kira. Yarda muryar tata ta karadâe gidanne yasa dâaukacin mutanen gidan fitowa, suka tarar da ita a durâkushe hankali tashe suke dubanta. Dahda ne yayiâkarfin halin cewa âlafiya hajja?â Hajja ta zuba masa wani irin kallo â ina kuwa lafiya ko da yake yanzu ba zan yi magana ba sai da safe kai ni falonka a can zan kwana kuma kana zaune daga gefe na Yau gamo nayi da aljannu a gidannan.â Dariya ce taso kama Ammar ganin yarda ta haâkiâkiance takeâbuya a bayan dahda. Momma kuwa baki ta taâbe ta juya ta koma ciki bayan tayi wa amaryar mijinta kallo dâaya. Ita kuwa amaryar bin bayan mijinta tayi tana tsinewa hajja a zuciyrta yarda zataâbata mata daren amarci duk da tanadin da ta shirya masa ga turarukan tsubbace tsubbace da ta ambula a jikinta banda wanda ta turara sai da ta kusa samo kan mai gidan sannan wannan tsohuwar zata rusa mata shirinta.
âKarfe bakwai nayi Hajja ta fito babban falon gidan bayan ta tasa âkeyar dahda a gaba â Muje ka hadâo min kaf kan ahalin gidannan ina da magana dasu â cikin tausasa murya yaceâ Hajja da kin bari gari ya âkara wayewa ....â â Naâki Na bari garin ya waye ahmadu nace naâki Na bari manga uba na, saboda ba kai kayi gamo da abinda Na gani ba ko.â Tayi saurin tare shi da sababin fadâa. Shiru kawai yayi yabi bayanta zuciyarsa fal âbacin rai don dai uwa uwa ce da ba wanda ya isa yazo gidansa ya aikata masa haka.
A tsaye suka tarar da momma tana sake gyara cushions dâin main parlour dâin tas ta gyara gidan saiâkamshin turaren wuta gidan yake. Dahda ya bita da kallo ganin yarda tayi kyau sosai cikin wani pink lace duk da fuskarta ba faraâa amma dai bata fasa gaisheshi ba, sannan taâkarasa gefen hajja da take zaune saman kujera âkafa dâaya kan dâaya tana girgiza jiki fuska cike da masifa, muryar mommah a cunkushe itama tace â Hajja barka da safiya an tashi lafiya?â Sai da Ta âkare mata kallo sama da âkasa cikin masifa tace â âkalau sumul na tashi duk da ba haka kika so ba, cikin kiyayewar ubangiji na tashi lafiya, saboda kin san tsaye nake akan âkafafuna wajen ibada, wai ke deejah har tsubbun taki ta kai ki fara turawa mutum aljannu ? Saboda Na saka dâana yayi aure, to albishirinki wannan auren mutu ka raba kuma idan kin tashi yau da daddare ki turo min sarkin rauhanai ma ba aljannu ba , Aljannun naki mai suka isa suyi min sunzo sun baki labarin yarda Na fatattakesu da ayar Allah.â Shatu da sauri ta juya Ta shige kitchen saboda dariyar da Ta ciyota. Hajja Ta cigaba â kuma ni da gidan dâana ba inda zani zama daram.â Mommah shiru tayi tana alâajabin hajja yau kuma gingimemen sharrin da za tayi mata kenan lallai tsanarta da hajja ta girmama. Hajja ta juya gun Dahda â kai kuma manga kana tsaye baka tambayeni baâasi ba, yo ai dai kace hajja mai ya faru kike wannan fadâa da safiya haka tunda kai haka Allah yayi ka kamar dâan fari, to ko Mahmud da yake dâan farin baya abin da kake. Wato kana ji cikin dare matarka tayi min turen jinnu wai suna gargadâi na na rabu da hadizatu kaji fa wai dijah yanzu har tayi shaharar turo min Jinny?â Dahda ya girgiza kai saboda âbacin rai ma kasa magana yayi ya zuba mata ido kawai. Ammar ne cikin dâaure fuska yace â ko dai mafarki kika yi hajja ina mommah taga aljannun da zata turo miki? Mu tunda muke gidannan ba wasu aljannu.â Girgiza kai hajja tayi sai kuma tace â Ba shakka, âkarya nayi maka kenan? To manga ubanka da yake zaune shine maâkaryaci ba ni ba. Raâayal aini yarda nake ganinka haka naga aljannu ina tofa musu adduâa suna ihu da tumami suna fadâin deejah ce ta aiko su, haka Na âkonesu âkurmus ba mamaki idan kuka je dâakin ma kuka ga hayaâkin da tokarsu, yo ni zaâa kawowa zancen banza aljannun me Allah na tubaâ. Ba wanda ya sake mata magana haka ta miâke ta koma dâakinta tana sake bambamin tijara. Shatu da take laâbe a bayan âkofar kitchen ta girgiza kai hadâe da yin âkwafa ta juya ta shige dâakinta .
âKarfe biyu daidai baâkin Abuja suka sauka. âKannen mommah ne hisham da hafsa sai nahnah. Kyawawa dasu farare tas kamar su innaji da mommah. Shatu tana zaune tana lesson driver ya dawo dagaâdaukosu dâaya bayan dâaya suke bin ta da kallo ita ma tana kallonsu, Hisham ne ya budâe mata alamar ta taho ya dube ta kafin yace If I guessed It right youâre shatu ?na canka shatu ce ko?â Da sauri ta dâaga kai hisham da su nahna suka rungumeta da ihu cikin tsananin farin ciki suna murnar ganinta hakanne Yasa Ammar da mommah da imran saurin fitowa suna murnar ganinsu , kasancewar sun dadâe basu zo hutu ba nahna da hafsa suna turkey, shi kuwa hisham mate dâin Ammar ne tare suka gama makaranta a egypt, Imran ne yayi oxford university england. Murna da hayaniyar da suke ce a main parlour ta fito da mutanen gidan har Hajja da ta fito tana dogara sandarta da yake tana da âkiba ciwonâkafa ya sata a gaba.
âDaya bayanâdaya take hurga musu kallo tana amsa gaisuwarsu a gatsine â Ba shakka dijah kin ci gida kin mallake manga kin mallake dukiyarsa ga âyan uwanki ma sun zo sun taru a gida, kai Allah wadaran naka ya lalace su kuma wadâannan gandâan-gandâan âyan matan daga ina?â Nahna fuska a dâaure za tayi magana mommah ta girgiza mata kai â Donât say any word here ku shiga part dâina am coming.â Kasancewar akwai tarbiyya hakan yasa basu shiga ba suka ja hannun shatu su kayi gaba su imran ma suka bi bayansu. Mommah ba tace da hajja komai ba ta miâke zata wuce. Cikin masifa Hajja tace â la shakka ga âyar iska wato kin bawa banza ajiyata nayi tayi ko? To kinyi da gyatumarki mai kama da sadakar yallar nan kuma da ni kike zancen yau yau zasu juya su koma, kuma kaf jakunkunansu sai nazo Na caje don yanzu haka wani tsubbun suka kawo miki an ji anyi miki kishiya azo a koreta ko? Kuma idan zasu tafi ki tattara har bararojinnan su tafi da ita shaidâanun banza kawai.â Momma wani abu Ta hadâiya kawai ta juya ta shige part dâinta zuciyarta na tafarfasa, itama fa mutum ce ba dutse ba dole zuciyarta zata dinga zafi da irin cin kashin da hajja take mata amma ya zata yi dole ta girmamata tunda dâanta take aure. Sai da Ta share hawayen fuskarta sannan taâkaâkalo faraâar dole ta budâeâkofar falonta.
A zazzaune ta samesu tuni sun watsar da lamarin hajja sun saka shatu a tsakiya, sai fito mata da tsarabar kayayyaki suke wanda suka siyo mata a turkey da wanda kakanninta suka bata, sai nuna mata tsananin soyayya suke, hakan yasa faraâar fuskar shatu ta kasa âboyuwa kowa nuna mata âkauna yake ashe ba zata yi maraiciba bayan mutuwar innaji, ashe yanzu ne zata fara fuskantar farin ciki a rayuwa. Ta lura kowa sonta yake idan ka d'auke Imran da yake gefe yana harararta âkasa-âkasa. Hisham ya dubi Mommah kafin yace â Hope dai by now an yi mata register a school ?â Momma ta girgiza kai â so muke brain dâinta ya daân budâe before taking her to school insha Allahâ Imran ya taâbe baki cikin takaici yace â Allah wahala kawai kuke wannan yarinyar she will never be socialized kamar yarda kuke so , rayuwar daji fa tayi ai sai a slow kawai dama kun daina wahalar da kudâinku kawai don wasting time dinku zaku yi ji fa wasu tarkace a hannunta â ya fadâa yana nuna hannunnata, gaba dâaya gurin shiru kawai su kayi zuciyarsu kowa da mamakin imran. Hisham ne ya katse shirun yana dafa Imran yace â Amma son banyi expecting hakan daga wajenka ko bakomai she is your bloody sister da nake fatan mu nuna mata soyayya mu kuma bata jin dadâin da ta rasa.â Tsaki yayi Hasfa ganin yarda mommah ta damu sai ta sako wasa cikin zancen â Rabu dashi Yaya hisham bayan ma bai san yarda rana zata fadâi ba â da sauri ya zaro ido â wa? God forbid wallahi insha Allah rana a gabas zata fadâi ko don ba kiga babban kamun da nayi ba classy baby ga good hygiene ga kyau ga ladabi.â Tsakin da mommah ta zabga ne yasa yin shiru duk gurin kuma aka saka dariya ban da shatu da imran ya riga ya âbata mata rai. Miâkewa tayi zata shige ciki taji Nahna tana cewa â Mhmn Allah ya kaimu lokacin da zaka zo kanaâyar murya â ya miâke yana fadâin â ai ko a âkafa aka dâaura min wallahi sai na cire na yar â Mommah kwafa tayi tana nuna musu dinning â Hisham close the chapter kuyi taking shower ku ci abinci duk da dai tafiyar dadâi kuka yi tafiya a jirgiâ Nahna tace â Yo wa zai zo kano from Abuja a mota.â