Free chapter · Read without an account

63.

by HADIZA IBRAHIM D AUTA · UMARNIN ZUCIYA.

*UZ.*
*Page63.*
*11/7/2026.*

       Cikin soron gidan ya ja tsaya ba tare da mun fita harabar gidan ba. Ni ma tsaya nesa da shi na lafe jikin bango ina kallon gefe hannuwa harɗe a ƙirjina. Ganin mun ja minti biyu a haka babu wanda ya ce da wani komai, na motsa tare da ƙoƙarin juyawa na koma ciki. Muryarsa da na tsinkayo yana faɗin, 

    "Sallama nake so mu yi, gobe zan koma Abuja kuma zan yi wata ban dawo ba." 

Hakan da na ji, babu shiri na isa gabansa ina cewa, "Ni dai ka tafi da ni don Allah." 

Wani siririn kallo ya yi mini kafin ya faɗaɗa fuskarsa da murmushi ya ce, "Kina cikin idda zan kwashe ki mu je Abuja? Ni fa wurin aiki zan je, kwanaki da yawa ana ta jajen na yi likimo na ƙi komaw...." 

    "Ni ma aikin zan je." 
Na yi maganar ina tura baki kamar wata ƙaramar yarinya. 

"Aiki kike yi da ma?" 

"Eh!" Na faɗa ina wasa da yan yatsuna. 

"Kin gan ki, ba kya jin magana. Yau shagaɓar ta motsa kuma a kaina za sauke lodi. Bayan ko rakiyar ma sai da aka koro ki kika biyo ni. To, na fasa so, ki koma can ku ƙarata ke da Hajja. Amma ki sani batun da muka fara ina so ki sanar da ni gaskiya, saboda duk abin da ya shafi dokokin Allah da hukunce-hukuncensa ba wasa da shi. Idan har kin san wani abu ya shiga tsakaninku a lokacin da kika yi masa kome, haramun ne neman aure cikin idda, idan kuma babu komai ɗin kamar yadda na ji labari, sai mu ci gaba fafatawa har zuwa ganin tabbatuwar alƙawarin Allah." 

"Fatatawa, tabbatuwa, alƙawarin duka a kan mene ne?" 

    " A kan abin da na sa gabana yanzu." 

Wani kallo na yi masa fara'a ɗauke a kan fuskata na ce, " Me ya sa ka faye zaurance yayin magana. Ka sanar da ni ko ma mene ne, saboda abokin kuka ba a ɓoye masa mutuwa." 

    "Kuma fa haka ne, amma ko ma mene ne, zan sanar da ke idan na dawo, in sha Allah."

    "Hummmm!" Na sauke wata gwauruwar ajiyar zuciya, saboda ganin ya ƙura mini kallo tun ina iya juriyar haɗa ido da shi na janye nawa ina cizon a kaifa." 

"Ya Bash." Na kira sunansa a hankali ina kallon 'yan yatsuna. 
Ya ce "Mene ne?"
Sai da na kalli gefena sannan na ce masa,

    "Idan ka koma, na san za ka je gidan Baba Hassan ko?" 

    "In sha Allah." Ya tabbatar mini da hakan, "Yawwa to, don Allah idan ka je, ka ce a nuna maka Samira." 

    "Akwai saƙon da za a karɓo miki ne?" 

Ina ƙoƙarin ba shi amsa muka jiyo sautin Hajja tana nufo soron tana faɗa. 
    Da sauri na juya ina yi masa Allah Ya kiyaye hanya. Kiciɓis na yi da Hajja ina gaf da shiga ita kuma ta doso kai za ta fito. 

     "Wayyo! Yi haƙuri Hajja." 

   " Ai dole ki ba ni haƙuri, kin fito ba kya so amma kin maƙale yaron mutane kin hana shi zuwa wurin matars..." 

    "Innalillahi Hajja! Yaushe na maƙale shi ni? Har da zan hana shi zuwa wurin matars...." 

    "Yi mini shiru mara kunya! Shi kuma ya yi wani sakato baki ya ƙi rufuwa don ya samu sake. Kai ma wuce ka tafi tun dare bai yi maka ba, tafiya a gabanka ka tsaya biye mata tana ɓata maka lokaci."

   " Tafiyar da sai gobe za a yi ta Hajja, saurin me nake yi tun yanzu?" 

    "Eh, na ji, tafi kawai gida za mu rufewa." 

    "Duk hanzarin ungozoma sai ta jira an haihu. Don ɗakin Baba Isihu a rufe yake har yanzu bai zo gadin ba ballantana ya rufe muku gidan." 

    Ina tsaye bakin ƙofar shigar ina kallon su da sauraron musayar yawun da suke yi har na ji ƙarar tayar da motarsa da tafiyarsa. 
Da sassarfa na koma cikin gidan na shige ɗaki, kwance na yi a kan gado ina jin raina ya yi babu daɗi, domin ban san me ya sa na ji ba na son rabuwa da Ya Bash ba, duk da ba wani shirin kirki muke yi ba. Amma dai da za a yi mini yadda nake so, da bai je ko'ina ba ya zauna mun yi ta rikicin da muke yi. Sai ga shi zuciya ta kwaɓe ni ganin ina ƙoƙarin manta wace ce ni.

   'Ki dawo hayyacinki Lubna, a yanzu Bashir ya wuce ajinki.' 

     "Uhum, ba wani nan. Ni ma ina da capasity." A take na yi zancen saboda ƙarfafa kaina da kaina. Amma kuma ni da kaina na san kalaman nawa iya baki ne kawai, saboda babu yadda za a yi na bari a yi masa rufa-rufa a aura masa ni a yadda nake. Allah ma ba zai yafe mini ba idan har na sake cutar da rayuwarsa, bayan ƙalubalen da yake ciki tsawon lokaci a sanadina. Da wannan nazarin na tuƙe zancen rashin son ta tafiyarsa a raina, na yi wa kaina faɗa tare da saƙa wa zuciyata sadaukarwa domin nuna tsantsar ƙauna ta domin Allah. Ko da zan rama masa halaccin da ya yi mini a rayuwa. 
    Ina jin motsin Hajja na gyara kwanciya kamar mai barci, ko da ta leƙo ba ta gano idona biyu ba. Ina ji tana cewa,

    "Ita wannan har yanzu da sauran gajiyar jinya a jikinta, har ta yi barci." 

Tana gama faɗar maganar ta fice tare da rufe mini ƙofa a hankali. Ai kuwa ban yi don motsi ba, daga haka barcin gaske ya kwashe ni. 
Da safe ni da Inna Uwani muka haɗa abin kari, muna ta hira tana ba ni labari. Kafin na baro ta kitchen ɗin ganin 'yan dubiya sun fara zarya a gidan, don wasu asibitin suke zuwa, daga can ake sanar da su an sallame mu su zarto gidan. 
     Abin mamaki, Mama Amina ma tana cikin tawagar masu zuba Allah Ya ƙara lafiya. Farida a bayanta tare da da sauran facalolinta biyu da 'ya'yansu biye da su. 
Gida ya cika da jama'a, ni kam kallo ɗaya na yi wa Mama Amina na shige ɗakina. Don gaishe ta da na yi cikin ɗar-ɗar ta amsa babu yabo babu fallasa, saboda Hajja ma tana ganin su ta canza fuska. Ko gaisuwar da suka yi mata a daƙile ta amsa musu duka, yaransu ma babu wanda ta kalla. Har sai da babban ɗan Farida ya isa inda take yana cewa,
   
    "Hajja ina kwana?" 

Sannan na ga ta ɗan saki ranta tana amsa masa. Tare da tambayar ina Babansu, kamar ba ta san ya koma ba. Yaron ya ce da ita tun da safe ya koma wurin aiki, shi ma yana barci bai samu ganin sa ba kafin ya tafi.
      "Allah Ya ƙara lafiya." Mama Amina ta faɗa cikin ciki. Na amsa da "Amin." Sannan na bar musu falon, don da ma can a takure nake tun da na yi ido biyu da su. 
    
     Tsintar kaina na yi da tura masa saƙon Allah Ya kai shi lafiya. Mintuna a tsakani kiransa ya shigo, kamar kada na ɗaga, wata zuciyar ta ce ɗaga ki ji me zai faɗa. 
   Babu ɓata lokaci na ɗauka ba tare da na ce komai ba. "Ranki ya daɗe abin babu magana?" 
     "Kai da ka tafi ba ka yi mini sallama ba." 
   Na yi maganar ina jin hawaye ya cika idona nan take. "Ya Ilahi! Sallama nawa kike so mu yi bayan wadda muka yi?" 

    "Goma, goma za ka yi. Kai ashirin ma ai ba laifi ba n...." 

    "To, to, na ji, kada ki kuskura ki yi kukan nan, don na ji kina shirin kashe mini dodon kunne. In dai sallamar ce damuwa zan sake yi miki yanzu." 
Na yi wani irin kallo kamar a gabansa tsabar jin daɗin yadda yake mutum mai sauƙin kai. 

   "Princess Lubna, zan tafi Abuja, ga ni ma a kan hanya har na kusa shiga cikin garin." 

    Murmushi na ji ya suɓuce mini babu shiri na rufe bakina. Kafin na saita kaina na ce, "Allah Ya kiyaye hanya." 

   "Amin, shikenan ko?" 
   Na ce masa "Eh." 

"To, a gafarce ni."
   Ya yi maganar cikin wata kalar murya, wadda ta sa na ji tsikar jikina ta tashi yarr, na shiga juyi a kan gadon ina cewa, 

   "An yafe maka, amma kada ka kom..." 

    Ban ƙarasa zancen ba na ji an turo ƙofar ɗakin an shigo. Na yi saurin tashi zaune ina kallon Hanif da babban yaron Ya Bash, cikin hanzari na daƙile kiran cike da fargaban su ji muryarsa su je su faɗa, wani sabon ɓalli ya sake tashi. 

   "Hanif yaushe kuka zo?" 

   "Yanzun nan tare da Mummyn Aslam, na duba ban gan ki ba na ce bari na zo nan na gani."

   " Oya, ku zo, ku zo."

Na yi maganar cikin sakin fuska ina miƙa musu hannu alamun su ƙaraso. Zaunar da su na yi a bakin gadon ina faɗin,

    "Kai ya sunanka?" Na yi maganar ina nuna yaron Ya Bash.

   "Mubarak." Ya faɗa yana yi mini wani kallo. 
     " Woww! Sunanka da daɗi Mubarak, amma ai kana zuwa makaranta ko?" 

   "Eh, primary 4 nake." 

"Ma sha Allah! Ga shi kuma kamar kai ne kake ɗauko na ɗaya a cikin ajin, haka ne ko?" 
     Ya kalli Hanif tare da rufe bakinsa yana 'yar dariya, Hanif ya yi caraf da zancen yana cewa, "Ai ko ta goma bai taɓa zuwa ba, wannan shekarar ma an ce shi ne ya kulle ajins..."

   Faff! Shi ne ƙarar dukan da ya kai wa Hanif a gefen baki, kafin ka ce me dambe ya kacame a tsakaninsu. Domin alamunsa ya nuna bai ji daɗin asirinsa da Hanif ya tona ba, na zabura cikin tashin hankali ina ta fama rabon kokawar, amma na kasa. Saboda sun iya damben kowa naushi yake kai wa ɗan'uwa, kaf-kaf kawai ke tashi. Dole na zare USB na ɗaga da niyyar kai musu duka cike da barazana sannan suka saki juna.
     Huci suka dinga yi suna kallon juna tamkar wasu zakuna. Hannun Mubarak na ja tare da kai shi bakin ƙofa ina cewa shi ya tafi, Hanif ya tsaya kada su sake yin wani faɗan kuma. Ai kuwa fitarsa babu jimawa, na fara jin sautin maganganu suna tashi kamar ana faɗa.
Ina yi wa Hanif faɗa dole na dakata na kasa kunne, ina sauraron maganganun Mama Maryam da Farida suke faɗa. 

   "Ni fa shi kansa Hanif na fara zargin ya koyi munafurcin uwarsa. Tun ranar da muka zo gidan nan ya fara ganin Lubna ya dinga shige mata. Ita kuma don raba ɗaya biyu shi ne za ta koro Mubarak daga ɗakin tun da Hanif ɗin ya fi shi cikin gidan." 

    "Uban da ya aike shi zuwa ɗakin ai! Duk abin da aka yi masa shi ne ya kai kansa." 

Zantukan nasu ya sa na ce da Hanif shi ma ya tafi na tashi na rufe ɗakin da key, na dawo na kwanta ina ci gaba da sauraron su sama-sama. Duk da ƙoƙarin toshe kunnuwana da nake yi, don ba na son jin duk abin da zai dagula mini lissafi. Tun ina jin surutan nasu ƙasa-ƙasa har na koma jin abin ya koma wani babban abu. Har da kuka na dinga jin yana tashi bayan tsinuwa da zage-zagen da na ji a bakin Hajja da talatin Mama Amina. Cikin sauri na yunƙura da zummar tashi na ji me ke faruwa, kafin na isa ƙofar na ji an fara dukan ƙofar da maganganun Farida tana a bakin ɗakin,

   "Baƙar munafuka ki fito, kin haɗa bala'i kin yi likimo kamar ba ki san ana yi ba. Tun da kin jawo Hajja ta ci mutuncin Mama a kanki, ki fito ki zuba ruwa ƙasa ki sha, burinki ya cika, bokanki ya farraƙa tsakanin uwa da ɗiyarta."
       
      Sai da na gayyato jarumta sannan na buɗe ƙofar. Ganin babu kowa cikin falon sai ita kaɗai, hakan ya sa na gyara tsayuwata ina yi mata kallon sama da ƙasa, kafin na ce, 

     "Wai ke wace cikin daƙiƙiya ce a cikin mahaukatan mutane? A nan gidan ma rashin hankalin za ki sake nunawa? To, na rantse da Allah ba zan raga miki ba, ko da farcen susa." 

Wataƙila mamaki na ba ta, don baki ta sake tana kallo na riƙe da ƙugu ko motsi ta kasa yi. Babu aune na ji shaƙa a wuyana, cikin zafin nama na ɓanɓare hannuwanta na harɗe su wuri ɗaya na matse gam. Kafin na sake ta na sa hannu biyu na ingiza ta baya ta faɗi ƙasa tim. 




D. Auta✍🏼

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.