Free chapter 路 Read without an account
17
*NANNY...!*
_(Mai Reno..)_
*NA*
*AISHA ALTO馃挒
*JAMILA UMAR (Janafty)*
*HIJABS CORNER BY JANAFTY*
*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, 蓷inki cikin kwarewa da* *mabambanta design, muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan 蓷aya ko sari.*
****, tuntu蓳a ta wannan lambar*
*KADUNA/ZARIA*
*BABI NA GOMA SHA BAKWAI*
Ri茩e 茩ugu Tahir yayi yana Sauke Ajiyar Zuciya, gefe 茒aya kuma Zuciyarsa na Gudu Sosai Saboda Damuwa, Ashe ce Dake gefe Ta 茩arasa Kusa da Goggo Abu Ta Zauna Kusa da Ita Kafin Tace "Goggo..."
Ta fa蓷a Tana kallonta Innaro Dake Tsaye Ta 茒ora Hannu Bisa Ha蓳a Tana Fa蓷in "Wai Hakimi meke Damunshi ne..?Tunda nake Dashi ban ta蓳a ganin yayi irin Wannan Fushin ba.." Tahir ya waigo ya Fara Taku Zuwa Kusa da Goggo Yana Fa蓷in "Ranshi yana 蓳ace...Dole a saurara mai Har ya Sauko Da kanshi.."
Ya fa蓷a yana Zama gefen Ashe, Dayan Hannun ya kama yana Fa蓷in "Goggo Don Allah Kiyi Ha茩uri kibar kukan nan Haka nan Nayi miki al茩awarin Komai zai Daidaita Insha Allahu..." Ya fa蓷a yana Kallonta Goggo Ta Murmusa Tana kallon Tahir da Ashe kafin tace "Bakomai...Allah yayi muku albarka Ku Tashi ku Tafi kubi Umarnin Mahaifinku.." Ta fa蓷a Tana 茩o茩arin 苼oye Hawayen Da Suka Taru acikin 茩wayan Idanuwanta.
Innaro ta saki Numfashi Tana Fa蓷in "Shine kawai magana Don Rashin Tafiyar Naku ma Matsala ne, ku Tashi ku Tafi Insha Allah komai zai zo da Sau茩i, maganar Mufeeda kuma Iya ta Dinga Kula da Ita Saboda yarinya ce..ko Goggo ya kika gani..?" Hannunta Ta zare cikin na Tahir kafin ta saka Hannun ta Share 茦wallarta Tana Fa蓷in "Eh Hakan ma yayi Innaro, Allah ya Sauketa lafiya kabiya ka gaida Fuleran karka manta.."
Gya蓷a kai yayi kafin yace "Insha Allahu.." Har ya Mi茩e Innaro Tace "Ya ita Faridan...? Ina Fatan ba Wata matsala...?" Jinjina kai Yayi kafin yace "Eh Innaro ba Wata Matsala..."
Sauke Numfashi Tayi kafin tace "Masha Allah...Ko jiya naji Mahaifinta suna Waya da Hakimi kan mganar ne, Allah Ubangiji ya kawo mana Komai Da Sau茩i..."..
Gaba 蓷aya Suka amsa da Ameen Kafin Ashe da Tahir suyima su Goggo Sallama Suka Fice Suka barta Tana Share 茦wallah Fita Sukayi Inda yabama Garzali Umarnin ya Shiga da kayan Abinci Zuwa Cikin Gidan Hakimi, A 茩asa Suka Taka Shida Ashe Har Zuwa Gidan Inna Fulera, Wanda Suna Tafe Tahir na Fa蓷ama Ashe Abunda ya Faru da Wanda yake Faruwa yana gaya mata kamar ya Zubar mata Da Hawaye, Cikin Tausayin 茒an'uwanta Take Lallashinsa Take bashi Shawaran karya Damu, kuma ya 茩yale Farida Duk inda Zataje Zata Dawo ne bayan Duniya ta koya mata Hankali ya yarda Da Shawaran Ashe Duk da A lokacin Farida bata da wani Fari Acikin Zuciyarsa.
A haka suka isa Gidan Inna Fulera, Ashe ce Ta fara shiga Suka Gaisa da Inna Fulera da Maman Lantana kafin tace musu Tahir zai Shigo Cikin Sauri Maman Lantana ta gyara Tabarma Tahir ya Shigo ganin Maman Lantana ne Awajen yasaka Daga Ashe Har Tahir ba Wanda ya Tada maganar Illah Sunkuyar da kai Da Tahir Yayi kunyar kansa na 茦ara kamashi ganin yadda Inna Fulera ta Rame Lokaci bayan Lokaci Tana Share 茦wallah...
Basu Wani Da蓷e ba Tahir ya Mi茩e zai Tafi bayan ya bama Ashe 30k yace Tabama Inna Fulera, Ashe na Bata ta茩i kar蓳a Sai Ta Fashe da Kuka Lokaci 茒aya Ta 茒ago ido Tana kallon Tahir bayan ta 茒ago Daga Kwancen Datake Maman Lantana Tana gyara Mata Filon Kanta Saboda Taji Da蓷in Zaman Sosai.
Cikin Muryan Ciwo da Kuka Inna Fulera tace "Alhaji....."Ta fa蓷a Muryanta na Sar茩ewa, cikin Sanyin Jiki Tahir ya Tsaya cak kafin ya Waigo Zuciyarsa na Tsinkewa Sosai Cikin Muryan Sanyi da Ro茩o tace "Bana Bu茩atar Ku蓷inka Alhaji Abu 茒aya Nake da Bu茩ata Awajenka.." jikinsa na Rawa ya Dawo ya Du茩e agaban Inna Fulera yana Fa蓷in "Ki Fa蓷i Abunda Kike Bu茩ata komai kike Bu茩ata matu茩ar na Mallakeshi zan baki Shi Inna.." Ya fa蓷a Cikin Karaya..
Muskutawa Tayi kafin tace "Ba komai nake Bukata ba Illah ka Ri茩e min Mufeeda Tsakani ga Allah...Ka zama gatanta..!kaji 茩anta..! Ka jibanci lamarinta...! Ka zama garkuwa a gareta Alhaji Domin Duk Duniya Mufeeda bata da Wani gata bayan kai..Don Allah kar ka barta tayi kukan maraici In kamin Wannan Abun Ka gamamin komai kuma Bana Bu茩atar Wani ku蓷i ko Kawan Duniya Farin cikin Mufeeda ka蓷ai Shine Burina Alhaji.." Ta fa蓷a Tana Rushewa da Kuka, Maman Lantana Dake gefe kanta ya 茒aure amma bata kawo komai ba sai ta barshi a 茩ila zafin Ciwo ne ke Damun Inna Fuleran.
茦uri Tahir yama Inna Fulera da Ido kafin ya maida kallonshi kan Ashe Wacce Idanuwanta Suka Cika da 茦wallan Tausayin Inna Fulera Iska mai Zafi ya Furzar kafin yace "Girman al茩awari Inna Ba Abu bane mai Sau茩i, Amma Duk Da Haka Nayi miki Al茩awarin zama Gatan Mufeeda, Nayi miki alkawarin bazan bari Mufeeda Ta 茩ara kukan Wani Abu ba...Sai na zama Silan Murmushinta anan gaba.." Ya fa蓷i Haka Idanuwansa Sun kawo Ruwa kafin ya mi茩e da Sauri ya Fice Saboda Yadda Inna Fulera Ke kuka Tana Godiya sai yaga Kamar Bazata Tashi ba, Lokaci 茒aya kuma Kunyar Abunda ya aikata ke Dawo mai Har Ashe ta Fito yana Tsaye yana Maida Hawayen Idanuwanshi Haka Suka Jero Har Zuwa gidan Hakimi ba Wanda ya 茩ara magana, bai koma Cikin gidan ba Ashe ya umarta data cema su Basma Su Fito Tare Suka Fito Dasu Laila sama sama yayi ma Hakimi sallama suka Shiga mota Har da Ashe Har gidanta Suka kaita Kafin su Sauketa ita dasu Muda da Tsarabansu 20k yabama Muda da Laila ita kuma Ashe ya kara mata 10k ta 茩ara Da Wanda ya bama Inna Fulera Ta茩i kar蓳a Haka Motarsu Ta 茒aga Ashe Ita da 'ya'yanta Suna Daga maSu Hannu Har Suka 蓳ace ma ganinsu.
Sai yamma Suka Shigo Kaduna Tahir na Sauri Ko Gida bai Shiga ba Garzali ya Juya Dashi kamfani ya samu Kiran gaggawa bai Dawo ba sai Dare Lokacin kowa yayi barci iya ka蓷ai ya Tarar Farke, Mufeeda Ita da Naila Sun Da蓷e da yin barci gaisawa sukayi sama sama, kafin ya Haura Zuwa 茒akinsa Ransa Duk babu Da蓷i ko yayi Wani Motsi sai ya Tuna da Al茩awarin Inna Fulera wanda Maganar da Suka gama Tattaunawa da Ishaq kenan kafin Su Rabu gaba daya Abubuwa sun mai yawa yanzu Farida bata gabanshi Matsala Goggo ce Sai Tausayin Mufeeda Daya 茩i barinshi Su sukafi Zama Cikin Ranshi Suka Hanashi Sukuni.
****
Farida kuwa Tana gidan Bilkisu Wajen Kwananta Uku amma basu ci karo da Mijin Bilkisu ba mai Suna Aliyu Saboda Tun Safe yake Fita kuma sai Dare yake Dawowa, Sai ya Fita Farida ke Fitowa Haka Kuma kafin ya Dawo Bilkisu zata san yadda Tayi Ta Hillaceta ta koma 茒aki Abunda ke bama Farida Mamaki yadda Bilkisu ke Rawan Jiki da Abban su Walida in ya Dawo Haka zata Tsala Wanka, Taci Gayu Tana Kwakwarsa, In ko Ta mata sallama bata 茩ara sakata a ido sai Washegari bayan ya Fita, Amma kuma Tana Daga Cikin masu bata Shawara ko Acikin group 蓷insu na makaranta Kan Mace ta Daina sakarma Namiji amma Ita gashi Bata Iya Ha蓷a komai da Mijinta.
Wani Abunda baima Farida Da蓷i ba Shine yadda Bilkisu Ta Dinga ya蓷a Abunda ya Faru Wajen Sauran 茦awayensu Wa蓷anda basu san Meke Faruwa ba Haka Suka Ha蓷u agroup 蓷insu na Classic Ladies Sukayi Ta Tsinema Tahir Aciki Harda masu bata Shawaran Takaishi 茩ara Kotu, ya茩e kawai Farida Keyi amma Bata jin Da蓷in yadda Billy ta Fallasasu A duniya ba Ko ba komai Tana Son Tahir Kuma Har gobe yana Matsayin Uban 'ya'yanta ne, Kuma Mijinta.
苼angaren su Umma kuwa basu san Abunda ke Faruwa ba Don Daga Faridan Har Tahir 蓷in ba Wanda basa Waya Dashi amma ba Wanda yace ga wani Abu, Ita Farida Tsoron Su Umma ne Domin Tasan Ranta sai ya 蓳aci Balle Abba dayayi Fushi da Ita don Musamman ya Kirata ya Zageta Tas, Balle kuma tace Ta Baro Gidan Tahir ai kila sai Abba ya Kusa Tsine mata, Shiko Tahir Faridan ne Kwata Kwata bata gabanshi Baya Fatan ya 茩ara Bu蓷an baki ya Fa蓷i Wani Abu Daya Danganceta ya Ratayeta Gefe ne Domin Ahalin Da yake Ciki yafin Jin Tsananta da Haushinta Fiye da Kanshi Shiyasa Ko Umma ta tambayeshi Suna Zaune lafiya yake cema ta ba wata matsala Domin Kaucema Duk Abunda zai Dawo Da Farida Yamafi Jin Da蓷i da bata nan Ko ba komai bayasan Abunda zai Dinga Takura Mufeeda.
Sai Ranar Data Kwana A cikin Gidan Kana Suka Ci karo da Abban su Walida, Ranar bai Fita ba Kwata kwata yana gida, Lokacin Daya ga Farida yayi Mamaki sosai nan yake Tambayanta Yaushe tazo..? Sai tace mai ta kwana biyu ma..Ido ya Zaro yana kallon Billy Wacce Tayi Fi茩i Fi茩i da Ido Zuciyarta na Tsananta Bugu Wani kallo yabi Farida Dashi bai dai yi magana ba Amma Acikin Ranshi yana Tunanin Wani Shirme kenan Mace da Gidan Mijinta Kuma Tazo Gidanshi Ta tare, Ina bazai 茒auki Wannan Iskancin ba.
Bai mata magana ba sai da Suka Shiga Cikin Bedroom 茒insu kana ya Tsareta da Ido yana Fa蓷in "Da wani Dalili Farida Tazo nan gidan Harta kwana uku ban sani ba..? Ke dama wani Manufa Matar Da take da Mijinta..?"
Ya fa蓷a yana Hararanta Sanin Halinta na Shanshanci Shi bai Sake mata ba Shiyasa Duk yadda Billy taso tayi Iskanci bata samu Dama ba, Cikin Rawan Murya tace "Dama..Dama..Umh..." Tsawa Ya Daka mata yana Fa蓷in "Dama Menene..? Baki zaki Bu蓷e kiman magana Yadda zan Fahimceki kinsan bana son Raini ko....?"
Kai ta gya蓷a kafin tace "Matsala suka samu da Abban su Basma..." Kallonta yayi A 蓷age kafin yace "Matsala..?" Ya maimata da Sigan Tambaya kai Ta gya蓷a mai alamar Hakane, Cikin Dariyan karki Raina min Wayau yace "Kuma Shikenan Don Sun samu Sa蓳ani ita da Tahir sai kuma akace tazo gidan Aurenki ta tare ko..? Ke gaki Uwarta ko kuma Mai bata Shawaran karta koma gidan Mijinta ta cigaba da zama agidan naki Mijin..?" Ya fa蓷a yana kallonta Cikin 蓳acin Rai..
Jikin Billy na Rawa Ta Ri茩o Hannunshi Tana Fa蓷in "Don Allah ka Tsaya ka Saurare Abban Walida Wallahi Tahir ya chanchanci Farida Data barshi Amanarta fa yaci Shida yarinyar Datake mata Renon Naila.." Ta fa蓷a Lokaci 茒aya Tana Zaunar Dashi gefe 茒aya Kafin ta Fara Rattaba mai yadda Akayi Billy Saboda Sharri Harda 茩ari kamar Agabanta Akayi
Haba Aliyu ya ri茩e Kafin yace "Ke Bilkisu bana son 茦arya fa..? Shi Tahir 蓷in..? Haba Don Allah ya za'ayi mutum mai Daraja ya aikata Haka, Tahir fa Yana da Kima Sosai a idanuwan Wa蓷anda Suka sansa.." Ya fa蓷a yana Tantama Rantsuwa Billy Ta fara Jera mai, Domin ya yarda Da Ita, Bai yarda ba Mi茩ewa yayi yana Fa蓷in muje naga Faridan, Jiki na Rawa Tamai Jagora Zuwa 茒akin data Sauke Farida, Cikin Tsare gida yake Tambayanta gaskiyan lamarin Cikin Kuka Farida ke labarta mai Hadda Hukuncin da Iyayenshi Da nata Suka bashi goyon Baya.
Tana Fa蓷a tana Share 茦wallah, Jinjina kai Aliyu yayi kafin yace "Lallai ba Shakka In ko Hakane Tahir bai kyautama kanshi ba ya Cuci kanshi kuma ya Tozarta iyayensa Da kuma Zuri'arsa..Ya bani kunya Sosai, kuma sai na kirashi na mai magana.." Da Sauri Farida tace "Don Allah Abban Walida ka 茩yaleshi ko kayi mai magana bazai Saurareka ba baya ganin Abunda ya Aikata amatsayin laifi Tunda Haryana Ikirarin data bar gidan Gwara ni na Fita na bar mai gida.."
Mi茩ewa Aliyu yayi Daga kan Sofa yana Fa蓷in "maganar banza kenan Har office 蓷inshi Zani Wallahi..Sai na gaya mai gaskiya sai dai ko karyaji Da蓷i.." Daga Haka ya Fice Daga 茒akin Cike da Mamakin Tahir 蓷in Duk da ba wani Kusanci Suke da Juna sosai ba, amma Suna Ta蓳a Juna Lokaci bayan Lokaci Saboda 茩awancen Matansu Da ba yanzu yake ba, Yana Fita Farida Ta Mi茩e zatama Billy magana tayi Saurin Dakatar da Ita tana Fa蓷in "Kinga Farida Bar maganar nan sai gobe..Yanzu lokacin Abban Walida ne kada mu Shiga Hakkinshi Nasan, Halin yan kaya na.." Daga Haka ta Fice Ta bar Farida Ri茩e da baki Tana Binta da Kallo.
****
Washegari kuwa Da Misalin 茦arfe 3:00pm na Rana Aliyu ya 茩wan茩wasa 茦ofar Office d'in Tahir inda ya bashi Umarnin Shigowa Suna Tare da Ishaq lokacin Suna Wani Lissafi ganin Aliyun sai da yayi mgana Cikin Fara'a Ya Tarbeshi yamai iso Zuwa Kujeran Dake office d'in Ruwa ya kawo mai Ya Zuba mai ya Mika mai ya kar蓳a yana Mai Godiya sai da yasha Ruwan ne ya Mi茩awa Ishaq hannu suka gaisa Cikin Sakin Fuska ya kalli Tahir yana Fa蓷in "Alhaji Tahir Wajen ka nazo, Wata maganace mai Muhimmanci ke Tafe dani.."
Shiru Tahir yayi kafin yace "Allah Sarki ba komai ina Jinka.." Ya fa蓷a Cike da Mamaki Lokaci 茒aya yana zama agefensa, Kallonsa Aliyu yayi kafin ya maida kallonshi kan Ishaq, Tun kafin yayi magana Tahir yace "Karka damu ka fa蓷i maganar Ishaq Tamkar 茒an'uwa yake a gareni.." Zaku蓷a kafa蓷a Aliyu yayi kafin yace "Kana da Labarin Matarka Farida na gidana Tun Ranar data bar gidanka..?"
Tahir ya 茒ago ya kalli Ishaq shima ya kalleshi kafin Duka su maida Hankalinsu kan Aliyu Lokaci 茒aya Tahir yace "Ah...Ina zan Sani kuwa Alhaji Aliyu.." Ya fa蓷a Cikin Halin Rashin Damuwa, Gyara zama yayi kafin yace "Toh Tana gidana nima bansani ba sai jiya na sani Shine na Turke Ita Bilkisun Shine Take Sanar dani Wani Labari mara Da蓷in Ji ban yarda ba sai da Na Kira ita Faridan Na 茩arajin Ta bakinta Wai Alhaji Da gaske ne Maganar da Suka Fa蓷a min..?"
Mi茩ewa Tahir yayi yana Kallon Aliyu kafin yace "Wata magana kenan..?" Ya fa蓷a Jijiyoyin kansa Sun Fara Tashi Saboda 苼acin Rai Cikin Jimami Aliyu yace "Na kama yarinyar Da kuka 茒auko Daga Garinku tana muku Rainon Naila Ciki.." Ya fa蓷a yana Sakarma Tahir ido, Runtse ido Tahir yayi Zuciyarsa na Tafasa kamar tayi Bindiga Haka Shima Ishaq yana Tsinema Farida ne a Cikin Ranshi, shi Wallahi ko Zahra bai yarda ya bata wannan Labarin ba balle ke ace Mijinki amma baki da Buri sai na Tona mai Asiri ki tozartashi.
Taku Tahir yayi Zuwa bakin Window Office 蓷inshi ya yaye labulen Wajen Cikin Juya baya yace "Eh Da gaske ne Aliyu..Nama Mufeeda Ciki, amma Duka Abunda ya Faru ba laifina bane Laifin Farida ne Ita ce Sanadiyar Jefani Cikin Halaka amma Wallahi bayan Matata Farida ban ta蓳a Keta Gonar da ba Tawa ba sai akan Mufeeda Wacce 茦addara ta Hau kanmu.." Ya 茩arashe Fa蓷a Cikin Muryan Kuka, Mi茩ewa Aliyu yayi yana Fa蓷in "Ashsha Kaji ko..? Abu baiyi Da蓷i ba.."
Tahir bai bashi Zarafin 茩ara magana ba, ya Shiga bashi Labarin irin zaman Wula茩ancin Dayayi da Farida da yadda ta banzatar da Rayuwarsa da 茦o茩arinsa na 茩ara Aure da yadda Goggo Take Dakatar dashi har Zuwa Faruwan komai Ya 茩arashe yana Fa蓷in "Wallahi Tallahi..Farida Ta Cutar dani Cutar da Allah ne ka蓷ai zai sakamin, Sai Farida tayi Wata Hu蓷u bata kalleni A shimfi蓷a ba, Ku gayamin Ni Dutse ne ko Gunki da bazan Bu茩aci mace ba..?" Ya fa蓷a lokaci 茒aya yana Juyo da Fuskarsa Wacce Hawaye suka Wanke mishi ita.
Daga Ishaq Har Aliyu Jikinsu yayi Sanyi Sosai Aliyu ne ya 茩arasa Kusa Dashi ya Dafa Kafa蓷arshi yana Fa蓷in "Cool Down Ka daina Kuka, Ha茩i茩a Wannan Abun da ya faru 茩addara ne ko Kuma nace Darasi ne ga Farida da Goggo, Amma fa maganar gaskiya kana da babban Laifi Tahir na yarda kabar Farida ta Rainaka take yarda taga Dama bayan Kai kake Aurenta aiko Min gatan da iyayenta Suka bata Tunda tabar Gabansu Ta Dawo 茩ar茩ashin Ikonka ya kamata ka Nuna mata 茩wanjinka na Mulkinka Amatsayinka na Namiji mai Cikakken Iko Agidanshi.. Maganar gaskiya kayi Kuskure.." Ya fa蓷a yana Murza Kafa蓷arsa.
Numfashi Tahir ya Sauke kafin yace "Tabbas maganarka Hakane... Ha茩urina da girman Iyayenta Danake gani Da kuma Nasihan Goggo Akaina da Kuma 'ya'yan Dake Tsakanina da Farida yasanya Bana iya Mata Wani abu, In tayi ba Daidai ba Shine Kuskure na barta ta saba da Komai tayi Daidai ne Tabbas nima ina da Laifi ba komai Ake ma Ha茩uri ba Gashi Ha茩urina yajamin naje na Afkama Marainiyar Allah Daga 茦arshe na zama Abun Ya蓷aWar Farida Kamar bamu Ha蓷a komai da Ita ba, ba komai...Haka Allah ya Tsara min.." Ya fa蓷a yana Share Hanci kamar Wani yaro.
Kafa蓷arsa Aliyu ya Daka kafin yace "Kazama namiji Abokina ka ganni nan bana ma Bilkisu da Wasa Tunda na Lura tana da Rawar kai Ubanta Nakeci tasan Halina ko yanzu 蓷in ma ina komawa zan Koro Faridan Dole ta Dawo Tunda bata da Wajen Zuwa..."
Da Sauri Tahir yace "No..no plz ka 茩yaleta Ka barta ta Zauna Da kanta zata Dawo ba sai kamata magana ba ai zataga Abunda sa蓳anin Shi Suke gaya mata zata ma kanta Fa蓷a Tun kafin Wani ya mata.." Ishaq yace "Shawara mai kyau Tahir..."
Aliyu ya Saki Hannu yana Fa蓷in "While Tunda kace Haka zan saka musu ido.. Amma True Tak, Yarinyar nan ta Haihu ka Aureta Wallahi Sweet Sixtyn suna da Da蓷in Sha'ani, Tuni Farida zata Rena kanta Ta Dawo Tana begenka Lokacin Da ka mata Nisa.." Dariya Ishaq ya saka kafin yace "Shawara mai kyau..Dama Shi ya Chanchanta yayi Wuf da Ita.." Hararanshi Tahir yayi Bai yi Magana ba, Shima Aliyu Dariya yake kafin su Cigaba da Tattauna maganar Tare Suka Fito Sai da Sukayi sallar La'asar Cikin Jam'i kana suka Rako Aliyu ya Hau Motarsa Zuwa gida, su kuma suka koma Office d'in Tahir Ishaq bai Dawo da Maganar ba ganin Tahir ya basar da Zancen ya 茒auko Lissafinsu suka cigaba dayi amma Cikin Ran Tahir Tsanar Farida ce ke 茩ara Ninkuwa in ya Tuna Tana chan tana Yawo Dashi Acikin Duniya kamar babu Igiyan Aurenshi Akanta.
******
*BAYAN SATI 茒AYA*
Lokacin Tuni Har Su Basma Sun koma Makaranta Hadda Itama Mufeedan Don Da Tahir ya nuna kamar Ta Ha茩ura da Karatun Saboda Gujema idon Mutane sai Ta Fara Share 茦wallah Shi kuma 茩wallar Mufeeda kamar dalma yake Acikin Ranshi, dole ya barta ta cigaba da Zuwa Makaranta amma bayan yaje yama Shugaban makarantan Bayanin Cewa Mufeeda matar Aure ce, Kuma tana 茒auke da Juna biyu So School Authority Su kula da Ita, basu Tsaya Tambayan Waye Mijin Ba Illah Suka yarda da maganar Tahir Suka kuma Rubuta Cikin Record Book.
Hatta da Islamiyya ta koma Abunta kamar ba Ita ba, sai dai Tayi Ki蓳a Sosai, Ta 茩ara Fari ta Cika ta Ko'ina Saboda tana samun Abunda Take so Abincinta Dama Shine Faten Wake, sai 茩osai da Koko sai kayan kwa蓷ayi Irinsu Goriba, yalo Sai Ice cream Wanda In Mufeeda bata Sha ba kamar Cikin zai 蓳are, Shiyasa Tahir kullum zai Dawo sai ya Shigo mata Dashi, Ba laifi Iya na Kula da Ita sosai su Basma ba'a barsu Abaya ba Lokaci ka蓷an Mufeedan Ta Saki Ranta sai dai Tunanin Innarta Dayaki barin Ranta.
苼angaren Su Goggo Abu kuwa ba Wani Cigaba, Tahir Sau 茒aya ya Kira Baba Hakimi Awaya Tunda yaji ya fara mai maganan Goggo Abu ya Datse Kiran, Tun daga Ranar ko ya Kirashi baya 茒auka Dole ya Ha茩ura sai dai yana Kiran Goggo Akai akai Yana 茩ara bata Ha茩uri amma ya 苼oye mata Shima Saboda Ita Baba Hakimi ya Daina 蓷aga Wayarsa sai dai ya Dinga Nuna mata ta kwantar da Hankali komai xai Daidaita.
*******
Yana Toilet yana Wanka, Akayi ta Kiran Wayarsa bai ji ba sai da ya gama Wanka ya 蓷auro Alwala ya Fito 茒aure da Towel A 茩ungunsa 茦aramin na Saman kansa yana Tsane Ruwan Jikinsa, Yaji Kiran Wayarsa Cikin Sassarfa ya isa Kusa da Wayar, Abunda ya bashi tsoro ganin Kiran Baba Hakimi, Da Asuban Fari Domin Lokacin Wajen 茩arfe 4:43am ne.
Cikin Firgici Da Tsoro ya 蓷aga Kiran yana Fa蓷in "Salamu Alaikum Baba..?" Ya fa蓷a Cikin Rawan Murya banji me akace ba Sai dai naji Tahir ya saki Salati yana Fa蓷in "Innalillahi Wa'inna Alaihirraju'un..Allah ya Ji茩anta da Rahma Allah yasa ta Huta..."
Ya fa蓷a kafin ya 茒auke Wayar A kunnensa Cikin Mutuwar Jiki ya Fa蓷a gefen gado yana Dafe kanshi Ko'ina na Jikinsa na Rawa, lokaci 蓷aya Yaji Hawaye Sun Cika mai ido Har Sun Fara gangarowa.
Nanny(me reno) Free book ne amma ga wa蓷anda ba za su iya jira ba akwai completed documemt 1k ne ku tura ta wannan acct 蓷in 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK ko tuntu蓳ar wa蓷annam lambobin ***
***.
*Janafty*
*Aisha Alto*