Free chapter 路 Read without an account

Page 29/30

by Ummu~Fadeela 路 MARYAMA

馃挮MARYAMA馃挮

                     29/30

                 BY

            Ummu Fadeela



Bayanta yake shafawa gently. Da sanyin murya mai nuna halin da ya ke ciki ya ce, "What happened pretty? ki daina kukan haka kar kan ki ya yi ciwo,..." kamar wadda ya ce ta 茩ara karfin kukan ta bu蓷e murya tana kuka mai cike da shagwa蓳a, ha蓷e da bubbuga 茩afafu a 茩asa, wani irin yamutsawa jinin Jabeer ke yi sakamakon ta蓳arar da ta ke masa yayin da yake jin 茩afafunsa suna 茩o茩arin gaza 蓷aukarsa, da sha茩a茩茩iyar murya ya ce, "me ya sameki ne MARYAMA? akwai abin da ya faru bayan fitata ne? yi shiru ki fa蓷a min mene ne?"

Da kuka ta ce, "ba kai ne ba ka tafi ka barni kuma kasan inajin tsoro ni ka蓷ai,"

Baya baya ya koma da ita ya zauna saman kujera ya ajiyeta saman cinyarsa. Still holding her tightly ya ce, "Sorry wife gani nan na dawo daga yanzu ban 茩ara fita ko ina idan dare ya kusa kin yi ha茩urin?" Ya fa蓷a saitin kunnena. kaina na kifa saman kirjinsa saboda wani irin kunya da na ke ji, hakan da nayi kuwa ba 茩aramin 茩ara birkita shi ya yi ba, amma yayi 茩arfin halin cewa "Ohk idan har kinyi ha茩uri then wipe your tears and smile ina da wani labari mai da蓷in gaske da zan baki".

Da sauri na 蓷ago kaina ina jin wani irin excitement dan na gama sawa a raina cewa maganar makaranta ta zai min dan yanzu shi ne ka蓷ai labarin da zan 茩irashi mai da蓷i a wajena.

Shi ya sa hannunsa duka biyu ya goge min hawayen kana ya ri茩e duk kumatuna ya ce, "Bani son 茩ara ganin wa蓷annan hawaye masu tsadar da sukafi gold daraja a wajena, ki daina zubar min su a banza kinji hayatie na?" Ba tare da na ce komai ba ya ci gaba da magana.

Yana kallon cikin idanuna still bai sake min kumatu ba ya ce, "Albishir!".

Cike da annuri da ke kwance saman fuskata da kuma za茩uwa na son jin abin da zai fa蓷a na ce "Goro"

茒an chukling 蓷ina ya yi a gefen ciki, ta ke na fara dariya, ya ce, " yawwa ko kefa amma da kin ha蓷e rai kamar wacce zanyiwa albishir 蓷in kishiya,...Murmushi na yi wannan karon har dimples nawa suka lo蓳a, 蓷an yatsarshi ya 蓷aura saman dimples 蓷in gami da fa蓷in, "tha's my wife"....

(Nasan mai karatu zaiyi mamakin yadda ni Maryama na sake da Hamma Jay wato ya yi bala'in sanin makamar 拼a mace a cikin zuciyata ba ni son abin da ya ke min, amma gangar jikina ya kasa janyewa daga gareshi, wannan wani sirrine dake tattare dashi da ba kowanne 蓷a namiji Allah ya bawa ba.)

Still looking into my eyes,ya ce, "Albishir!", turo baki na yi gaba na ce, "kai dai hamma jay ba na ce goro ba,"

Jabeer bai gajiya da kallon kyakkyawar baby face na ta dake cike da shagwa蓳a, yana jin wasu abubuwa suna bijiro mashi cikin kai...Iska ya hura min a kunne ganin yadda na kafeshi da idanu ba tare da nasan nayi hakan ba.Da sauri na rufe idon ban ankara ba naji saukan wani sassanyan kiss saman idanu na, da sauri na kuma bi蓷ewa ina 茩o茩arin tashi amma bai bani dama ba.

Cikin low voice ya ce, "Na samu aiki pretty!".

Wani irin mi茩ewa na yi da sauri na tsaya ha蓷i da 蓷aura hannayena duka biyu saman bakina, tsabar murna na ma rasa abin da zance.Tashi yayi shima ya rungumeni ta baya gami da zuro kanshi ta saman kafa蓷ata ya ce, "Kina farin ciki ko pretty?,....nima ina farin cikin cewa na samu aiki yanzu zan iya 蓷aukan nauyin karatunki dan ganin kin cika burinki,.

茒an ajiyar zuciya ya sau茩e sannan ya cigaba da cewa, "amma baki tambaye ni wani irin aiki na samu ba? bai jira na bashi amsa ba ya ci gaba da fa蓷in, 

"Na samu aikin koyarwa a makarantar firamare, Insha Allah duk wata zamuke samun naira dubu talatin da uku kinga ai ba kananan ku蓷i bane wannan ne abin da muka yini yi tare da Baffanmu a yau kuma alhmdllhi mun kammala komai,". ya 茩are da murmushi yana shafa fuskata zuwa saman wuyana.....

A hankali na fara jin wani abu mai kama da zare yana kwancewa daga cikin 茩wa茩walwata yana bin jikina har zuwa tsakar kafata..."aikin karantarwa a firamare? dubu talatin da uku ne hamma jay ke kira da manyan ku蓷a蓷e a hakan ma sai yayi wata 蓷aya cur sannan ya same su? 33k ai ko monthly allowances da nake fatan mijina zai ke bani bai kai ba.....A cikin kunnena ya ra蓷a min, "hmmm kinyi shiru baki ce komai ba,"..

Gyara tsayuwa nayi da niyyar matsawa daga wajen, hakan ya bashi daman juyowa yana shigar da idanunsa da suka sauya kamanni cikin nawa, zaro ido nayi da sauri kirjina na bugawa ganin abin da hamma jay ya fara.......

  ************--------------------************

Wannan dare dai Sadeeq a cikin ru蓷ani ya yishi, duk yadda ya so daure wa kasawa yayi a autoreadialling yasa layin Maryama sai kira yake duk kuwa da cewa matar nan ta MTN tana tabbatar mishi layin da yake nema a kashe take zama yayi a 茩asan rug dake bakin gadonsa ya ri茩e kanshi da hannu biyu, "What's happen to me? meke damu na ne?" ya yiwa kanshi tambayar kome ya tuna kuma ya yi saurin sau茩e hannunshi yana katse 茩iran da yake ta zuba wa Maryama kana ya juya akalan 茩iran zuwa kan wani layi ya 蓷aura saman kunnenshi ha蓷i da lumshe idanu kamar mai bacci.

____________***********______________

     FEDERAL LOWCOAST GOMBE.

         
                 GOMBE STATE.

Cikin 蓷aya daga jerin gidaje na alfarma dake sha茩e a anguwar mai 蓷auke da tsarin zamani na shiga 

Daga compound 蓷in gidan zaka iya fahimtar mamallakin wannan gida ya samu na duniya kam saidai yayi harin lahira. gida ne na alfarma mai 蓷auke da bene hawa 蓷aya, sai wani babban duplex shima mai kama da aljannar duniya a gefen hagun babban building 蓷in, daga inda kake kana iya hango boysquarter's a can karshen gidan bayan su garden swimming pool da kuma wawaken parking space,kutsa kai na yi cikin gidan bayan na bu蓷e kofar palon,tsayawa fa蓷an ha蓷uwar wannan palo dai 蓳ata lokaci ne A kalla paluka ukune cikin downstair 蓷in da kuma kitchen da store da sauran bedrooms.

Zaune ta ke bisa stool dake gaban dressing mirror a 蓷aya daga ciki kyawawan 蓷akuna kuma mafi girma dake upstair,tana 蓷aure da babban towel da ya kai har guiwanta tum daga kirji,gashin kanta mai wal茩iyar da kallo 蓷aya zaka mishi ka san ba 茩aramin laushi zai yi ba a baje har saman kafadunta,hannunta 蓷auke da handrayer tana busar da gashin,duk da a zaune ta ke amma zaka iya fahimtar bata cika tsawo ba kuma baza'a 茩irata da gajera ba,kai tsaye zamu iya 茩iranta ba茩a amma ba 茩irin ba dan da gani skin nata yana samun kulawa ta musamman sakamakon shining dim da ya ke yi,idanunta farare tas da 蓷an madaidaicin baki mai 蓷auke da cikakkun lips irin mai tsoka 蓷innan kana da jerarrun ha茩ora farare tas masu dau茩e da babban wushirya a tsakiyarsu,she's just a black beauty, a 茩alla zata kai shekaru ashirin a duniya,tana gyara kanta amma fuskarta cike da annuri da ganinta zata yi fara'a, bayan ta gama ta shafa mashi mayuka masu da蓷in kamshi sannan ta 蓷aure gashin da band hot red kana ta kama jelar ta kitsa shi ya sau茩o har gadon bayanta ya kwanta lib gwanin sha'awa, hair spray ta fesawa gashin sannan ta 蓷aga container 蓷in lotions dake wajen ta fara dubawa, duk ajiyewa tayi dan ba wanda ya mata ta 蓷auki body spray ta yiwa jikinta wanka dashi kana ta 蓷au wani kwalban humra ta dinga bin lungu lungu a jikinta tana gogawa, take 蓷akin ya 蓷au wani irin kamshi har yana hawa kai amma ita ko a jikinta kamar ma hakan wani nisha蓷i yake bata. Tana tsaka da goge gogen turarukarne wayar dake zaune kan mirror 蓷in ya 蓷au 茩ara. Dagawa tayi dan ganin mai 茩iran a wannan lokacin Imoji 蓷in love guda biyu da ta gani fuskar wayar ne ya sata picking cikin gaggawa tana fa蓷a蓷a fara'ar dake fuskarta.

Cike da 蓷okin murna mara misaltuwa ta ce, "Yayaaaa!".

A 蓷aya bangaren Sadeeq ya 蓷an muskuta daga zaunen da ya ke kasan rug 蓷in ya yi murmushi 茩a蓷an wanda baisan ma yayi ba yace, "Lilsis kin manta da yaya ko?".

Wannan karon turo baki tayi ta ce, "Ba wani nan yayaa so kake kar inyi korafin ka manta dani, amma sau nawa ina 茩iranka ko amsa wayata ma bakayi"

"Ohhh sorry my lil, kinsan yayannaki lebura ne so ba ko da yaushe nake da lokacin kaina ba,"

Cikin fara'ar da yake 蓷abi'arta ta ce, "To yayaa Allah ya bada sa'a amma....sai kuma tayi shiru"

"Amma me?" ya tambayeta duk da ya san abin da zata fa蓷a...."Just to told you munyi missing naka" ta fa蓷a da sanyin murya.

"Where's Mom?" ya tambayeta ba tare da ya bi ta kan maganar da ta fa蓷a ba. Mom tana side 蓷in Abbu ba ta jima da fita ba. In kai mata wayar ne?".

"No ki barta, kawai idan ta shigo kice mata am on my way tomorrow morning bala yaje ya 蓷auko ni a airport, ohk?" wani irin da蓷i ne ya ratsa zuciyarta da sauri ta mi茩e har towel nata na kwancewa ta ce,"Da gaske kake yayaaa".

"Da wasa nake lilsis" ya kwaikwayi abinda ta fa蓷a da irin muryarta, dariya ta kumayi ta ce, "Allah ko kayi suprising namu bari inje in fa蓷awa Mom byeeee" .

Ba tare da ta jira jin abin da zai ce ba ta yanke wayar ta nufi 茩ofa da 蓷an gudunta...karo suka ci da wata dattijuwar mata fara sol kai da ganinta kasan ba 茩aramin kyau ta yi lokacin kuruciya ba,baya ta dawo tana ha茩i kamar wacce tayi gudu mai nisa.

"Wai sai yaushe zaki girma ne KHADIJA? kullum kina girma kinacin 茩asa. yanzu me ya ha蓷aki da gudu haka?"kafun budurwar da aka 茩ira khadija tace wani abu mom ta gama shigowa 蓷akin tana bubbu蓷e hancinta.

"Me nake ji haka khadija? yanzu perfumes nawa ne kika bulbular a jikinki kamar mara lissafi ko?.'

Rungumeta khadija tayi cike da farin ciki ta ce, "Sorry Mommy,!bazan sake ba, "bata bawa mom daman magana ba ta ci gaba da fa蓷in, "Albishir Mommy,yanzu yayaa ya 茩ira wayarki na 蓷auka ya ce min yau in sanar dake gobe zai zo da safe, bala ya je ya 蓷auko shi a airport plsss mommy ni zan je 蓷aukoshi karki fa蓷a mishi plsss plssss plssss Mommm." ta 茩are tana 蓷an bubbuga 茩afa a 茩asa...

Sake baki kawai Mommy tayi tana kallonta, "say something mana mom".

"To Allah ya kaimu zaki jira goben ya yi ai ko,? irin wannan rawar kan da kike yiwa MAN shi yake sa shi yana basar dake ke kuma baki gane ba".

"Nidai ki barni kawai mom, ta fa蓷a tana turo baki...yauwa bari inje in fara ha蓷a masa favourite nashi kamun ya iso."

" Na shiga uku ni Hauwa mutumin da sai gobe zai zo ne kike 茩o茩arin shiga kitchen tun yanzu?"

"Ahhhh na manta ne mom"cewar khadija tana dawowa bakin gado ta zauna.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.