Free chapter 路 Read without an account

Page 35

by Ummu~Fadeela 路 MARYAMA

馃挮MARYAMA馃挮

EPISODE/35

      By

   UMMU FADEELA.



***



Babana kana tare da ni kuwa?".
cewar Innarmu jin Jabeer ya yi shiru bai ce komai ba. "kana jina?" ta kuma tambaya.

Da 茩yar Jabeer ya yi 茩undunbalar cewa, "am ehm dama Innarmu dama ita ce",

"Jabeer 茩alau kake kuwa mai ke faruwa na tambayeka amma ka cika ni da In'ina"

"Innarmu ita ce bata da lafiya tun jiya kuma yau ko tsayawa bata iya yi, plsss Innarmu kizo ki ganta dan Allah" ya 茩are maganar da 蓷an karaya a muryarshi.

"Subhanalla! mai ya sameta haka?" Inna ta kuma jefo mishi tambayar da ya kuma rikita shi.

Haka kawai fa Innarmu haka kawai ta kasa tashi da kanta ba abin da ya sameta.

"To sai kuje asibiti ai, ni mai zan zo in maku a gida?" cewar Inna tana yanke kiran.

Wani irin murmushi yana bayyana saman fuskarta, ba tun yanzu ba tasan itace mutum na farko da Jabeer ke fara tunkara da damuwarshi tun yana yaro, kuma wannan shine tarbiyar da ta bashi na cewa duk abin da ya sameka ko ya shige maka duhu ka fara tuntu蓳ar iyayenka kamun wasu suji, kuma Alhmdllh Jabeer ya 蓷au wannan tarbiyar sai dai batai zaton har a irin wannan al'amarin zai iya sanar mata ba, dan sarai ta fahimci abin da ya faru, and she's happy da Allah ya nuna musu wannan lokacin murmushi ta kuma yi har ha茩waranta na bayyana.

"Ah'ah na shiga uku ni jikar mutum hu蓷u, wai ba magana nake miki bane Dijah amma kin min shiru kamar wata shashasha".cewar Daada da ta ajiye kayan da take ta aijin na蓷ewa tun bayan da Innarmu ta amsa 茩ira ta zuba mata idanu.

"Ayya kiyi ha茩uri Daada ban jiki bane ba".

"Yo ina zaki ji ni dama gaba 蓷aya kin ru蓷e kin firgice, me ya samu takwarar nawa na ji kina ambaton sunan asibiti da safiyar nan?" ta tambaye ta tun bata dire maganar ba.

Murmushi ta kuma yi. a'a ba maganar murmushi bane Dijah fa蓷a min abin da ke faruwa, kar dai ace rashin ha茩urin yaran zamanin ya nuna ya turmushe mana 拼a ba tare da ya dubi 茩an茩antar ta ba?" murmushi Inna ta kuma yi ta sinne kai 茩asa, ita tana rasa gane kan daada, komai ya zo bakin ta fa蓷a take tana manta cewar ita surkarta ce kodan su 蓷in yan uwane?

A firgice ta 蓷ago kanta tana zare ido sakamakon wani irin salatin da Daada ta rabka, ha蓷i da kiran sunan" lami, lami"

Har tana tuntu蓳e Inna lami ta shigo 蓷akin tana tambayar "lafiya Daada"?

"Inafa lafiya 拼annan, Jabeeru dai ya cika tantirin mara kunya lamba 蓷aya, Ina fa蓷a miki lamba 蓷aya na bugawa a jarida shafin farko yanzu inba rashin kunya ba bazai jira mu koma ba tukunna ya ida rashin kunyar tashi. Yau ni naga jaraba da farar safiyar nan? amma ko zuwa ganin 蓷aki bamuyi ba ace yaron nan ya turmushe yar mutane daren jiya kuma tsabar rashin ta ido yanzu ya 茩ira uwar wai yar bata da lafiya? tir wannan zamani da ya yara basa girmama 茩imar mata, mu a lokacinmu basai yarinya tayi shekaru uku a 蓷aki ba tare da mijin ya ri茩e ko dan yatsanta ba, amma jiba ki gani daga kai mashi yar kwana biyu har ya hai茩e mata."fa蓷a daada keyi ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba.

"Yanzu ni abin da ban gane anan ba daada shine, laifine dan Jabeer ya ha蓷a shimfi蓷a da matarsa? Ina ce takanas kika taso daga nijar dan shaida 蓷aurin aurensu amma kin zo kina ta bambamin fa蓷a dan kawai ya aikata abin da yake na halal. kinata wani ha蓷a zamaninku da ake da karancin wayewa da wannan zamanin" cewar Inna lami da maganganun daada ya tunzurata.

"To dama nasan ba kirki ne dake ba ai lami, yanzu sai ki iya kawo min duka, wuce muje muga mai ya aikata mata, wata茩ila ma ciwo dan banzan ya ji mata ya kuma kasa gasata."

"Kin wuce ne ko sai na 蓷auke ki a ka?".inji daada ganin inna lami na tsaye 茩i茩am. Daada ya za'ayi mu wani je gid....."

Wani kallon da innarmu ta watsa mata ne yasa ta yin shiru ba dan ta so ba, "kuje kawai lami wata茩ila akwai abin da zaki taimaka mata dashi ga can abin karinsu da Fati zata kai idan anjima dama ki 蓷auka" 

Ba don taso ba ta yafa mayafi ha蓷i da bin bayan daada wacce har tayi nisa tana ta sababi, ita a ganinta wannan sirrinsu ne bai kamata wani ya sani ba.

Turus daada ta tsaya a tsakar gidan tana 茩arewa babban zanin gadon dake shanye tsakar gidan yana ta 蓷igar ruwa kallo juyowa tayi ha蓷i da kallon inna lami da ta ja tunga ta tsaya itama tace, "Lami kin gani ko?" munafu茩in har ya wanke zanin gado"

Murmushi kawai Inna lami tayi tana bawa zuciyarta tabbacin dole fa daada tana bukatar uzuri dan shekaru sun ja, dan ma dai akwai karfin jiki.

                   ************

Zama Jabeer ya yi bakin gadon ha蓷i da dafe kanshi cike da rashin sanin abun yi lokacin da Innarmu ta yanke wayar, ya da蓷e a haka ba tare da yasan what next ba.

"Ya Allah" ya furta ya dafe kanshi dake sara mashi gami da juya kanta jin wani irin hucin zazza蓳in da take fitarwa ga kukan da take amma baya fita.

Kanta ya tallafo zuwa kan cinyarshi ya kwantar gami da fara shafa dogon gashinta zuwa saman kumburarriyar fuskarta, "Sorry pretty" kawai Jabeer ke fa蓷a idanunshi sun ka蓷a jajur dasu....a wannan yanayin ne kuma ya fara jiyo magana kamar daada a tsakar gida,bai gama tantancewa ba yajiyo sallamar inna lami a bakin 茩ofar 蓷akin.

A hankali ya sau茩e kan Maryama da yai mata matashi da cinyarshi zuwa kan pillow sannan ya mi茩e yana gyara mata kwanciya,ha蓷i da shafa kyakkyawar fuskarta da ta kumbura tayi haske fayau.Sannan ya fita.

"Haan ya kika tsaya daga waje baki shiga ba?gidan ba茩onki ne ko dai shi jabeerun ne ya kafa allon sanarwar kar wanda ya shiga mishi 蓷aki".?

"Eh musamman ma idan wanda ya zo 蓷in ban gaiyyace shi ba."Cewar Jabeer da ya ji maganar da daada take yi lokacin da ya ke fitowa.Risinar da kai ya yi 茩asa ya ce, "Barka da zuwa Inna"

 Da murmushi Inna lami ta ce, "yauwa barka ka dai ango,ya 蓷iyata 蓷in Innarku ta ce bata ji da蓷i ba".

Yana shafa kanshi ba tare da ya ce komai ba, daada da ta 蓷aure fuska tamau ta ce, "kaga ja'iri mara kunya zaka bamu hanya ne ko yaya?."

茒an matsawa yayi fuuu ta shige 蓷akin ba tare da ta kalleshi ba,蓷an dariya ka蓷an Inna Lami tayi tana kallon Jabeer da still kanshi ke kasa ta ce, "Daada yanzu sai an ha蓷a mata da uzuri,dariyan yayi shima yana gya蓷a kai da fa蓷in "haka ne kam".

Sosai sukayi mamakin halin da suka tadda Maryama da zuwa lokacin jijinta ya 茩ara yin tsami dan rashin amfani da ruwan zafin da basu yi ba tun asuba 蓷in, "dama nasan za'ayi haka,inba rashin imani irin ma alhassan da dijah ba ina Jabeer lutete dashi 茩iran samudawa ina maryama da take yar firit da ita? ai kowa yasan daman cutar ta kawai za'ayi to gashin nan dai tun ba'aje ko ina ba kun fara gani".

Daada kenan ke ta sababi ganin Maryama sai ma茩yar茩yata take tamkar an ji茩a kyanwa.shigowar Inna Lami ya sata yin shiru.

Ruwan zafi Innan ta ha蓷a daidai zaman mutum cikin baho sannan ta kama Maryama da dambe da komai ta tsoma ta ciki, ihu ta ke yi tana 茩an茩ameta,duk da ta fahimci irin azabar da take ci hakan bai sa ta barta ba don shine gatan da zata mata.a hankali ta fara jin ruwan yana mata da蓷i har da lumshe idanu ganin haka inna lami ta fita ta barta a bayin....

..........................*******...........................

                       GOMBE

Tsabar do茩i Khadija kasa bacci tayi a ranar sai juyi kawai take a kan gado,茩iran sallar farko a kunnenta dan haka ta tashi ta fito a hankali ta kama handle 蓷in kofar ta bu蓷e without making any sound,sau茩a ta fara yi daga stairs 蓷in cikin san蓷a dan kar Mommy ta jiyota,saura baifi steps uku ba ta gama sau茩a taja ta tsaya tana turo baki gaba gami da kama bakin rigar baccinta tana wasa dashi.

Mommy ce zaune downstairs idanunta sanye da glasses tana operating laptop dake gabanta...蓷an sauke madubin idon ka蓷an tayi zuwa 茩asa tana kallon Khadija da ta茩i gaba ta茩i baya.Hannu Mommy ta sa ta yafitota ha蓷i da nuna mata gefenta, da sauri ta gama sau茩owa tazo ta zauna gefenta 蓷in tana mata side hug "morning Mommy".

"Morning dear, ina zakije yanzun nan ko Salla ba'ayi ba?".

"Mommy zan ji茩a rice 蓷in da zan wa yaya girki dashi ne, kin san fa ya ce morning flight zai bi, and ba wani nisa tsakanin port da nan" ta kare maganar cike da shagwaba, shafa kanta Mommy ta yi ta ce, " God bless you dear, je ki ji茩a but be fast kar jam'in salla ya wuce ki."

"Thank you my momm" ta fa蓷a tana bawa mommy peck a hannu ta shige kitchen 蓷in da 蓷an gudunta. Iya tsaruwa wannan kitchen 蓷in ya tsaru, babu ce kawai babu a cikinta, store 蓷in dake manna cikin kitchen 蓷in ta shiga bayan ta dauki mazubi mai 蓷an girma ka蓷an,farar shinkafa ta 蓷iba kofi biyu ta fito ta kunna tap ta zuba ruwa akan shinkafar sannan ta ajiye a gefe ta fita.

Lokacin da ta fito babu mom a palon ta haura sama, dan haka itama hayewa ta yi ta shige 蓷akinta direct toilet ta shiga ta 蓷auro alwala babban hijab har kasa ta 蓷aura saman riga da wandon baccinta ta gabatar da rak'atal fajr, tana zaune bisa pray mat 蓷in da qur'an a hannunta har aka tada sallar asubahi, da ta kammala yau ko azkar batayi ba ta yaye hijab din gami da linke shi ta ajiye saman bedside drawer. Gashinta ta na蓷e cikin hula sannan ta sau茩o kasa, babu kowa palon har yanzu kuma gari da 蓷an duhu dulum dulum,kitchen 蓷in ta koma ta janyo apron ta 蓷aura akan pyjamas nata ta fara aiki.Ruwa ta jona a kettle sannan Shinkafar ta duba ganin ya mata yadda ta ke so ta wanke shi ya fita tas ta juye cikin blender ha蓷i da marka蓷a shi yayi lu茩ui,wasu glass bowl babba da 茩arami ta 蓷auko ta juye a cikin babban ta ajiye blender 蓷in cikin sink.

Babban cokalin miya ta 蓷auka ta debi marka蓷a蓷蓷en shinkafar ludayi daya da ka蓷an ta zuba cikin karamin bowl 蓷in sannan ta koma kan kettle nata da zuwa lokacin ruwan ciki ya tafasa kashewa tayi ta 蓷aga ta zuba tafasashshen ruwan akan 茩ulli ludayi daya da ka蓷an 蓷in da ta zubawa karamin bowl 蓷in, take ya ha蓷e ya zama tamkar kunu,juyashi ta dinga yi har yayi sanyi 茩alau da yake sauri take yi,bayan yayi sanyi ta hadesu da sauran 蓷anyen 茩ullin ta juyasu suka hade jikinsu sannan ta zuba yeast daidai ta zuba baking powder shima daidai da 茩ullin ta kana sugar (according to your taste) sai gishiri 蓷an ka蓷an.,ta juyasu sosai ta rufe da babban marfi ta barshi a wajen.

Gaban frizer taje ta bu蓷e ta fara tunanin da mai zata ha蓷a miyar kifi ne ko gajeren 茩ashi or peppe chicken.murmushi tayi har babban wushiryarta na bayyan tuna irin amincin dake tsakanin yayan nata da kaza,thou SINASIR da jajjagen danyen kifi yafi da蓷i amma bari tai masa peppe chicken 蓷in kawai.

Wata dakwalar kazar gidan gona ta 蓳an蓳aro kasancewar ta das茩are, cikin ruwa ta jefa ta barshi ya yi melting ta koma kan kayan miya ta jajjaga attaruhu da tattasai mai 蓷an yawa kana ta dau plate ta daura curry powder da maggi thyme garlic and ginger powder tumeric soysource da sauran kayan spices da take bukata gyara kazar tayi bayan tayi melting ta yayyanka su into peaces sannan ta wanke ta zuba kayan kamshi da albasa ta 蓷aura kan gas wani albasar tayiwa yankan slice mai 蓷an yawa shima ta ajiye gefe, da sauri sauri take aikin.fry pan ta fitar ta 蓷aura bisa gas, wata tukunyar ta kuma zubawa ruwa ha蓷i da mint leaf ginger cinnamon da sauran kayan shayi ta daura a gefe, sannan ta koma kan 茩ullinta da zuwa lokacin ya taso yayi kyau, fry pan ta 蓷aura saman gas shima ta shafa mai ta fara suyan sinasir 蓷in ta, take gidan ya ba蓷e da kamshin abubuwa kala kala, cikin 茩an茩anin lokaci ta gama soyawa ta zuba cikin food warmer mai dan karen kyau shima tea 蓷in dake ta tashin 茩amshi ta juye a tea flask da sauri sauri ta soya kazar ta ta ha蓷a peppe chicken that look so mouth watering kasancewar ya samu kala mai kyau. shima ta juye a warmer duka ta fitar ta jere saman dining, sai a lokacin cooks na gidan suka shigo dan fara aikin breakfast.

A gurguje ta fa蓷a wanka ganin karfe takwas ya wuce,tsawon minti talatin ta kwashe tana dirzar jikinta sannan ta fito tana goge jikinnata mai 蓷an karen sul蓳i da towel, duk da kasancewarta ba茩a, amma tana da glowing skin,da shike ita ma'abociyar kamshi ce nan ta fara bulbilawa kanta turare kala kala daga na jiki na hammata, na bayan kunne, na gashi ko ina khadija tana da turarenshi na mussamman, sai da ta gama sannan ta fara shafa ha蓷a蓷蓷en manta wanda shima ke cike da 茩amshi,
(瞥ar uwa ki kasance mai yawan amfani da turare, domin mace mai 茩amshi darajarta da 茩imarta daban yake.)

Kasancewarta ba ma'abociyar kwalliya ba a take ta gama shirinta cikin wani tsadadden abaya ash colour ta yane kanta da mayafin abayar sannan ta 茩ara feshe jikinta da wani turaren ta 蓷auki jakarta 茩irar channel ta rataya ta sanya wasu takalma sau ciki suma na kamfanin channel 蓷in ta zari wayarta ta kama hanyar fita tana duba agogon dake tsintsiyar hannunta,zaro ido tayi ganin lokaci ya tafi ashe bata ankara ba.

Da sauri har tana tuntu蓳e ta fa蓷a 蓷akin mommy, amma bata sameta ba, dan haka ta fita tana zumburo baki ta nufi side na abbu.still tayi a wajen tana lumshe idanu ri茩e da hannun 茩ofa bayan ta shiga 蓳angaren abbu 蓷in sakamakon 茩amshin turaren da ta sha茩a cikin hancinta ..

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.