Free chapter · Read without an account
The Foyer Echo
by NorthernAngel · His Rose
Galado manor, 8:00am.
Omar ne a tsaye a cikin kitchen dake cikin boys wing da wayarsa a hannu yana dannawa, his brow slightly furrowed in concentration. Zwar yana zaune kan stool ɗin kitchen island ɗin under the soft morning sun. Sanye yake da uniform ɗinsa dake a goge gwanin ban sha'awa, ga ceramic mug a hannunsa yana shan tea. Noor na tsaye gurin cooker tana soye-soye, the rich aroma of breakfast filling the clean kitchen space. Muryar Omar ta tsinta yana faɗin, "Noor, wrap it up. Zwar is practically finished with his tea." Juyawa tayi da sauri ta janyo plate ɗin da ta ajiye tana faɗin, "I'm on it, Yaya. Plating it right now." Seat ɗin ya janyo shi ma ya zauna kusa da Zwar, har lokacin idonsa na kan wayarsa typing rapidly. Da Mu'azzam yake magana inda yake tambayarsa ko yana ganin Baffa zai ce ayi sulhu, ɗan shi bai so Zara ta dawo gidan nan under any circumstance. Shi da yake fatan ma su bar gidan saboda tuni an je an gyare gidansu Zara na Abuja, kawai dai Mu'azzam ne yace su ɗakata su ji me Baffa zai ce tukunna in the Warri meeting. Noor ce ta ƙaraso da plate guda biyu ta ajiye ɗaya gaban Zwar sannan ta ajiyewa Omar ɗaya shi ma. "Merci, Mommy," Zwar ya faɗa yana kallon abincin nasa with a bright smile. Ɗan ɗukawa tayi tana kissing kansa tana faɗin, "Bon appétit, mon ange." Daga haka ta koma gefen Omar ta hau kan island ɗin ta zauna tana facing ɗinsa, yayin da shi kuma ya fara cin abincinsa yana danna waya har lokacin without looking up. Hannu ta sa ta fara zare wayar daga hannunsa slowly, bai mata musu ba ya cika mata wayar gaba ɗaya. Bata ko kalli me yake ba tayi locking wayar ta ajiye a gefenta, her posture relaxed and effortless, duk yana kallonta with a raised eyebrow. Juyowa tayi tana kallonsa ita ma tana shagwaɓe mai fuska beautifully. Ɗan ɗaure fuska yayi, cikin kakkausar murya yace, "Menene kuma?" Kamar zatayi kuka tace, "Zan bi ku, pleaseee." Ya san inda take nufi, amma sai yace, "School ɗin?" Bata rai tayi dan tun ɗazu yake mata irin wannan abun. Ta ɗauke kai, cikin haɗe rai tace, "Warri." Yana cin abincinsa calmly yace, "Saboda gulma?" Da sauri ta juyo ta kallesa, Gulman me kuma, Yaya? For your information, ban san ma bata nan ba sai jiya tukunna da Zwar yake cewa he wants to spend his weekend in Warri with Aunt Zara. That’s how I found out she's away. I just want to check on her and Bubbles, pleeaasee, Yaya." Gyaɗa kai yayi yana kallonta yace, "Toh doctor Nourhane." Sake ɓata rai tayi ta juyawa mai kai. Sighing yayi, cikin soft voice ya tambayeta, "Toh wa zai je Academic Review ɗin Zwar?" Shrugging tayi tana cewa, "Yemma." Nan ma sake girgiza kai yayi da sauri, "The world hardly ever sees her in public, so her rare appearance will turn the school into a massive spectacle. And kinsan fitarta, it requires a level of protocol and security that will completely isolate Zwar from his peers, and you know he values his privacy too much for that." Shiru tayi tana gyaɗa kai cikin yadda da maganarsa, her expression softening in understanding. Zwar baya son attention kam ko kaɗan, shi yasa da ya gwammace na gida ya ɗauko sa daga school ɗin, dan in driver ne toh sai an haɗa da detail, Lamidi kaɗai ake bari ya ɗauko sa shi kaɗai. Muryar Zwar suka tsinta yana cewa, "I really want to pick up Hausa, but it’s just so hard to get a grasp of it. The structure is honestly so complicated." Sauri Noor ta kallesa tana kwashewa da dariya, dan in akwai abunda ya tsana shine a ringa Hausa a gabansa musamman in ya san maganarsa ake. Omar na ɗan murmushi ya kallesa yana cewa, "What happened to Rose’s tutorials? I thought you mentioned she was taking you through the basics." Gyaɗa kai yayi yana goge bakinsa da napkin yace, "Yeah, but it’s proving to be quite a challenge. Would you mind not speaking it around me for now?" Omar ya gyaɗa kai, "Of course, buddy." Daga haka ya juya yana kallon Noor yace, "Noor, let’s respect his wishes—Hausa is officially banned around Zwar until he gets a proper grasp of it." Gyaɗa kai tayi tana ɗan tabe baki da murmushi a fuskarta. Mikewa Zwar yayi ya zagayo inda Noor take, his steps smooth and unhurried, ta dauki hannunta yayi kissing lightly like the little gentleman he is, sannan ya kalli babansa yana cewa, "I am going to bid Yemma goodbye real quick." Daga haka ya dauki school bag dinsa yana ratayawa. Omar ya bisa da kallo checking his watch, his dark eyes narrowing slightly, "Be quick, we are approaching eight-thirty." Gyada kai Zwar yayi yana ficewa daga kitchen din with quick steps. Yana fita Omar ya mike, isa yayi gaban Noor ya sa hannu ya ware kafafunta ya shiga tsakiyar, his large hand steady against her hip, sannan ya zagaye dan karamin waist dinta da hannayensa tightly pulling her close. Wani murmushi ne a kwance a fuskar Noor, idonta na bin kitchen din da kallo tana jin wani kunyarsa na lullubeta all of a sudden saboda tunawa da daren jiya da tayi under the sheets, her cheeks flushing a soft rose. Kallonta kawai yake yana jira ta kallesa, amma sam taki out of shyness. Shima kuma dan ya kure ya ringa kallon kyakkyawar fuskarta, yana admiring komai na fuskarta under the soft morning glow—tun daga kan curly dark hair dinta, long arch eyebrows dinta, olive green eyes dinta da long lashes dinta, har zuwa kan long slim pointed nose dints da reddish pink lips dinta. Shi har yau ya kasa yadda she's not the most beautiful thing in the world. So delicate and cute. She's 28 now, but still looking 22; ita haka Allah yayita, bata da jikin girma. Muryata ya tsinta, trying to act nonchalant as she played with his collar, her slender fingers gently tugging the fabric, "I really think this wing suits us best. It’s so cozy." Girgiza kai Omar yayi ba tare da yace mata komai ba saboda zuwa lokacin ya fara gajiya da ce mata NO. Sam taki fahimtar bazai yu ba, duk da tace baza su taba third floor din ba zasu barwa kowa office dinsa, but shi sam bai yadda da su zauna cikin manor din ba. Kuma above anything, bazai yu su tada Ahmad ba yana zaman zamansa in his designated quarters. Hannu yasa ya juyo da fuskarta, cikin sauri tayi kasa da idona tana kin hada ido da shi. Chin dinta ya dago gently to lock her attention, "Hey, look at me." Cikin sauri tace, "No!" tana sake kauda kanta. Yana murmushi yace, "No?" Gyada kai tayi itama tana murmushi, idonta na kallon wani gurin. Kansa ya daura saman kafadar ta, inhaling her soft fragrance as he was leaning in, yana sake rungumota jikinsa, his warm breath lingering on her skin. Shuru suka yi a haka, both enjoying their peace and warmth. Sallama suka ji, kafin su amsa kuma aka fara kiran sunan, "Noori!" sai kuma wata yar karamar murya dake kiran, "Mammy!" Tare Noor da Omar suka sakarwa juna murmushi, their brief bubble bursting. Cikata yayi yana matsawa baya sannan ya daga cak ya sauko da ita akan kafafunta onto the floor. Dai-dai lokacin Imaan ta shigo kitchen din tana rike da hannun Mezyan dake faman kwala kiran mamansa. Yana ganin ta ya tafi da gudu cikin murna ya kire kafafunta. Itama cikin sauri ta sunkuya ta daukesa yana cillasa sama tana mai wasa making him giggle loudly. Imaan ta karaso inda suke tana gaida Omar a hankali, ya amsa mata coolly, sannan ta kalli Noor tana gaya mata Yemma tace tayiwa Mezyan wanka su shirya su fito breakfast. Daga haka ta mika mata baby bag din da ta sako kayansa aciki, her hands brushing against Noor's purposely cike da tsonaka, sannan ta juya ta fice daga kitchen din. Daman sunje wing din Baffa basu ganta ba, shine Baffa yace su dubata kila tayo nan saboda shi duk a tunaninsa tana dakinta bai san tun daren jiya ta fice ta wing dinsu Yusrah ba. Omar ne yasa hannu ya karbi Mezyan shima yana mai wasa for a while, tossing him gently, a subtle grin softening his stern features, kafin ya mika mata shi saboda Zwar daya leko yana ce masa su tafi. Kissing kan Noor yayi tare da Mezyan kafin ya juya yana ce mata sai sun dawo, saboda daga school din airport zai wuce su hade dasu Baffa acan saboda tafiyan su Warri. Binsa tayi har bakin kofa sannan suka sakeyin sallama, her eyes following him out into the hall, yana mata tunin taje school dinsu Zwar akan lokaci for the Academic Review…
Karfe goma na safiya Zara ta tashi daga bacci, tana zaune akan gadonta ita kadai, staring blankly at the wall, her frame completely still. Tayi nisa cikin tunanin abunda ya faru jiya, addua kawai take acikin zuciyarta Allah yasa karya Tifah takeyi. Tama kasa komai tun jiyan, her mind completely scrambled, tama rasa tunanin da zatayi. Dan ta tabbatar kafin ta kwanta sai da ta kira J-wire tasa ya bincika mata gaskiyar maganar, amma sai tace masa ya kira ta da safe ya bata amsa. Dalilin da tayi hakan shine, tana tsoron gaskiyar ta hanata bacci, she wanted one last night of peace inma hakan ne. Ai kuwa tunawa da ta saka J-wire bincike yasa ta janyo wayarta, her hand trembling slightly as she reached out, inda tana dubawa kuwa taga ya mata missed call daya ten minutes ago. Number sa ta fara dialing, gabanta na dukan uku-uku saboda tsoron abunda zata ji. After few rings J-wire ya daga yana fadin, "Queen, good morning o." Cikin muryar bacci ta amsa, "Morning J, how far?" Kai tsaye J-wire ya fara magana, "Ah, Queen, na raw fact oo. Dem load am around 7:20pm. The BMW no match any Galado name or tag for body, but the guy wey show face pick am up na your husby errand boy." Shuru Zara tayi tana sauraron J-wire har ya gama bayaninsa. Babu wani much clue sai gayen da yake jan motar ya tabbatar mata badan kasar nan bane, and he operates under the radar shiyasa babu wanda yasan sa, kuma yayi bincike ya gano Zafar yakewa aiki tuntuni. Zuwa lokacin da ya gama mata bayani Zara bata ko iya magana, her throat completely dry, da kyar tace masa, "Thank you," sannan ta kashe wayarta. Hannu tasa ta dafe goshinta saboda wani jiri da take gani daga zaune, gabanta na wani irin dukan uku-uku tana ji kamar numfashinta zai dauke, the oxygen leaving her lungs, her posture slumping under the sudden weight of the betrayal. Kusan 10 minutes tana zaune, kamar an tsikareta kuma ta mike tana wata dariya ita kadai. Bathroom ta shiga ta fada wanka trying to wash off the cold sweat, bayan ta gama ta hau skincare routine dinta. Ko da ta fito wurin karfe sha daya na safe ne. Wani black satin palazzo pants tasaka tare da black crop top. Gashinta daya sha gyara ta hau packing sannan bayan ta gama ta dauki turare ta fesa sama-sama sannan tasa flip flops wedges dinta ta juya ta fito daga cikin closet din, tana ta kokarin maida kukan da ke neman taso mata, biting her inner cheek, her jaw clenching with forced restraint. Kasa ta nufa da wayarta a hannu tana dannawa, tun kafin ta karasa sauka daga benen taji muryar mutane na tashi daga parlourn, the echoes reaching the stairs, wanda aciki muryar Ya M dinta kawai ta dago. Dan frowning tayi tana tunanin ba dai tafiya da ita suka zo yi ba. Tana gama saukowa kuma ta dakata saboda muryar Baffa da taji, kallon kanta tayi taga bazai yu ta shiga ba da bump dinta a bude in her cropped top. Juyawa kawai tayi ta nufi bayan staircase din inda akwai kofar fita ta nan, her flip flops steps making small sound against the marble. Tana fita cikin compound ɗin ta zagayo, ta gaban entrance ɗin ta ga biyu daga cikin ƴaran maids ɗin a zaune suna ta karatu abunsu with their notebooks open, their shoulders hunched over their books in silent focus. Daman ita Mommy tana son ɗaukar ƴara ƙanƙana aiki, mostly waɗanda suka gama secondary school; idan ta ɗaukesu kuma tana basu ɗaman zuwa higher institution su yi karatu, giving them a better life and a chance at a bright future. Amfaninsu kawai a gidan shine su ringa zuwa aiken nan da chan da kuma taya asalin ƴan aikin gidan aiki, mostly aikin kitchen. Daya daga cikinsu Zara ta aika akan taje kitchen ta dauko mata coconut water mai sanyi to soothe her throat. Da sauri yarinyar da suke kiran da Chichi ta tashi ta shiga ciki. Bin bayanta Zara tayi amma sai ta tsaya a foyer, ta samu guri can single couch din gurin ta zauna jiran ta tana danna wayarta, her fingers trembling slightly on the screen, her dark lashes lowering to mask the turmoil in her eyes. Chichi kuwa koda ta shiga ciki bata kalli tsakiyar gurin ba inda nan ne kowa ke zaune, dake gurin yana da girma so akwai distance tsakanin hanyar kitchen din da tsakar parlourn shiyasa ba lallai ma kaji me ake cewa ba sai dai ka tsinki mutum daga nesa. Acikin parlourn kuwa Baffa ne a zaune da yayansa maza su duka, sai kuma Daddy, Mommy da Brother Obi. Hira ake cikin masha'a yayin da Zafar kam duk inda hankalinsa yake ya tashi saboda jin Baffa yace wa Daddy babu abunda ya kawosa sai gaisuwar mutuwar da akayi mai. Wato ashe ba zuwa yayi dan ayi wani silhu tsakanin sa da Zara ba? Omar ne ya sauko daga sama yana danna wayarsa, ya dan dago yana kallon Mommy yace, "She's not in her room, Let me try calling her phone again." Da mamaki Mommy tayi frowning, toh ko ta shiga bathroom? Sai kuma ta kalli Omar tana cewa, "Have you checked Vicky's room? She's probably there, or maybe she's in the bath." Omar dai bai ce mata komai ba kawai ya zauna, his posture completely unbothered, dan shi bazai iya duba dakin Vicky ba kuma bai ma san wannene ba. Wayar Zaran yaci gaba da kira amma tana shiga busy, alaman tasa wayar a DND mode kenan. Cike da rashin yadda Zafar ke kallon Omar, his eyes narrowing in deep suspicion, yana zargin kila ma zuwa yayi yace mata ta boye karta fito. Yana cikin wannan tunanin, idonsa ya fada kan yarinyar data fito daga kitchen, hannunta rike da barta fresh coconut water exactly irin wanda Zara ke sha, sannan ga straw a hannun ta kuma Zara ke shansa da straw. Yarinyar yabi da kallo yana hangota har ta wuce ta nufi kofar fita. Mikewa yayi cikin sauri yana sa waya a kunne yayi muttering "Excuse me," daga haka ya bar gurin ya nufi hanyar fita cikin sauri kar yarinyar ta bace masa, his pulse quickening with every step. Yana zuwa bakin kofa ya bude, ya ga yarinyar a tsaye a cikin foyer din, ga Zara ta mike tsaye dake kan kujerar tana kokarin karbar drink din da aka kawo mata. Kallon ta ya tsaya yi, ta fada, ta kuma kara haske tayi kyau sosai ba kadan ba. Yanzu kam za'a iya cewa she is heavily pregnant, cikinta yana 6 months ne da two weeks. Gashinan sai sheki yake, fatarta cikinta so flawless sai glowing take kamar sauran skin dinta. Yarinyar dake mikawa Zara drink din ajiyewa tayi ganin hankalin Zara baya kanta yana kan Zafar, bayan ta ajiye mata ta juya ta fice. Zafar ma kallon ta yake kamar yanda take kallonsa, his gaze locked onto her figure, sai dai ita wani kallon tsana da takaici take watsa mai. Karasowa yayi gabanta cikin sauri, his hands reaching out slightly before pulling back, in a greeting form yace, "Princess," Sake hade rai tayi tana aika masa wani kallo, her chest heaving with restrained anger, da wata low voice da kaji kasan danne fushinta take tace, "Get out of my face. What the fuck are you even doing here, you son of a bitch?" Cak ya tsaya daga kokarin rikota da yake, his hand frozen mid-air, completely taken aback and shocked. Da wani irin mamaki yace, "Zara?" Har ta bude baki zata sake zaginsa kuma sai ta rufe. Girgiza kai tayi ta juya ta dauki drink dinta, her knuckles white around the bottle, tana fadin, "Engaging with someone as disgusting as you is a waste of time. Just stay out of my way, please." Daga haka ta juya ta nufi hanyar fita. Tana kokarin bude kofa yayi saurin rikota a rikice, his fingers clamping around her wrist, yana cewa, "Zara, listen to—"
Tassss!
Karar data karade ko ina kenan inda dukkan tazarar dake parlour da foyer din sai da aka jiyo. Wani irin mari ne da ko iyayensa da suka haifesa basu taba masa shi ba. He's been slapped, yes! Especially akan case din Zara lokacin da yake ganiyar matsuwa ya aureta musamman daya ganta a taron ta da Roman, tabbas Yemma ta mare sa a lokacin. Da kuma lokacin da tasan Noor nada ciki, shima nan sai da ta maresa saboda tana ganin sakacinsa ne yaja hakan, ace har cikin Noor yakai wata shida bai sani ba. Wannan shi kadai ne lokacin da yake tuna mahaifiyarsa ta maresa. Baffa ya taba marinsa? Yes! Baffa ya taba marinsa yana yaro baifi shekara 12 ba suka yi fada shida Muazzam yayi wa Muazzam gorin Baffa ba babansu bane. Nan ne Baffa yayi masa maruka kusan biyar masu kyau Hajiya Mama ce kadai ta iya kwatarsa da kyar. Bacin wadannan baya tuna wani mari daya taba sha a rayuwarsa sai yau da matarsa tayi masa marin da yafi dukkan wanda ya taba sha zafi. Babu karya, Allah ya hore mata zafin hannu da zafin rai. Tuni dusky skin dinsa yayi ja, shatin yatsunta ya kwanta akan kyakkyawar fuskarta, his head snapped to the side from the sheer force, olive eyes dinsa kuwa tuni suka kada suka yi jajir kamar wanda aka watsawa barkono aciki. Muryarta ya tsinka ringing inside his burning ear, her posture rigid with lethal coldness, "Don't you dare lay your hands on me! Those same filthy hands you spent all night wrapping around your cheap mistress in private fleshpots? Like I said—stay. Out. Of. My. Way!" Daga haka ta juya ta nufi kofar fita...