Free chapter · Read without an account
Chapter 19
by Amanarcool · SAUTIN KARSHE
SAUTIN ƘARSHE
BY AMANARCOOL
YOTA/021
Under Yota's Amazing Pens
Book 1
Not editing
Page 19
"Subhanallah! Zuhura lafiya?" Ya faɗa yana tasowa da sauri ya iso inda take, muryarta na rawa ta ce "Abbi da gaske ne abin da na ji ka faɗa? Sudais ya yi aure? To waya aura? Abbi ka ce mini bashi da mata, asali ma baya kula mata, to ya za a yi kuma hakan ta faru?" Ta kai ƙarshen maganar jikinta na wata irin tsuma. A hankali Sardauna ya riƙo hannunta ya zaunar da ita bakin gado, ƙare mata kallo ya yi, yaga lokaci ɗaya ta birkice masa ta fita hayyacinta. Ajiyar zuciya ya sauke, ya dube ta da kyau ya ce "Zuhura, da gaske ne Sudais ya yi aure jiya, sai dai shi kansa bai taɓa tunanin zai yi auren a jiya ba, kamar yadda na sanar dake tun farko wanene Sudais, to haka halayyarsa take har a yanzu, wannan auren ma muƙaddari ne daga Allah, kuma ba wata bare ba ce ya aura ƴar uwarsa, saboda ki yi haƙuri, ki cire wannan damuwar da na gani a tattare da ke. Idan Allah ya nufi za ki amsa sunar matarsa zai aure ki."
Cikin kuka Zuhura ta ce "To Abbi." Daga haka ta tashi jiki a sanyaye ta bar ɗakin. Bin bayanta ya yi da kallo, ya yi shiru yana tunanin wane irin sone Zuhura take yi wa yaron nan har haka.
.....
Ƙarfe huɗu da rabi Sudais ya dawo gida, bai tarar da kowa a main falon gidan ba, sama ya haura kai tsaye ɗakin Mammy ya shiga, nan ya tarar da ita zaune saman darduma tana lazimi. Zama ya yi a kusa da ita yana kallonta cike da tsananin so da ƙauna, Mammy ganin Sudais ya shigo ɗakin ne ya sa yin addu'a, sannan ta mayar da dubanta gare shi za ta yi magana kenan ya ce "Barka da yini Mammyna." Murmushi ta yi ta ce "Barka dai yaron Mammy, ka dawo?" Ba ki buɗe Sudais yake kallonta ya ce "Mammy yau kuma ke da kanki kike kirana da yaronki? Ah lallai yau ina cikin alkhairi dumu-dumu." Dariya ta yi ta ce "To na janye, barka dai yaron Uncle."
"Ah haba dai Mammy, ai maganar farko ake ɗauka ko a gaban alƙali." Sudais ya ce yana murmushi, "To shikenan na ji. Ya abubuwan naku ina fatan dai komai yana tafiya daidai babu wata matsala?" Mammy ta tambaya cikin kulawa, ya ce "Eh Mammy Alhamdulillah, sai dai ana fama da jama'a, mutum har ya gaji da zaryar mutune." Mammy ta ce "Ma sha Allah, to ya za ka yi sai haƙuri, da ma duk mai neman halal dole sai ya jure irin wannan, ina Faruk?"
Sudais ya nisa yana faɗin "Haka ne Mammy, Faruk yana can sai zuwa anjima zai dawo, ni ma ba na jin daɗi ne shi ya sa na dawo gida."
"Ko dai kana son ganin ƴata ne ka yi kewarta shi ya sa ka dawo ba?" Ta yi maganar tana dariya
Shiru ya yi yana sosa kansa bai ce komai ba, Mammy ta ce "To ka gaishe ni ai sai ka tashi ka wuce gurin matarka."
"Mammy korata kike yi ne?"
"Eh, tashi ka tafi, nagode da kulawa Allah ya yi ma albarka." Tsam ya miƙe ya bar ɗakin, Mammy ta yi murmushi.
Ko da ya isa part ɗinsa, knoking ya yi tare da buɗe ƙofar ya shiga da sallama, kamar wanda aka yi wa dole ga shiga falon haka ya shiga. Ilham na zaune a falon tare da Zahra, sannu da zuwa suka yi masa, ya ɗaga musu hannu ba tare da ya tsaya falon ba ya wuce bedroom ɗinsa, Zahra ta kalli Ilham ta ce "Tab, aiki ya gano ki Anty Ilham, ni kinga tafiyata" ta yi maganar tana miƙewa tsaye ta fice daga part ɗin. Zahra na fita Ilham ta yi tagumi tana tunanin me ya kamata ta yi masa yanzu. Kamar wadda aka mitsina ta tashi ta nufi bedroom ɗinsa.
Yana shiga ɗakin wani irin dadaɗan ƙamshi ne ya tarbe shi, lumshe idanunsa ya yi ya sake buɗe su yana bin ɗakin da kallo, an gyara ɗakin ko ina ya yi tsaf da shi, sai yaga duk gyaran da yake yi wa ɗakin bai taɓa gyaruwa kamar na yau ba, rage kayan jikinsa ya yi. Ya ɗakko towel ya ɗaura a ƙungunsa, ji ya yi an buɗe ƙofar ɗakin, kanta a ƙasa ta shigo da sallamarta. Juyowa ya yi yana kallonta, "Lafiya dai kika shigo mini ɗaki?" Ɗago da kanta ta yi da zumar yi masa magana, babu shiri ta runtse idanunta ta ja da baya tana manna jikinta a jikin ƙofa. "Magana nake yi miki?" Da ƙyar ta buɗa baki ta ce "Babu komai."
"Babu komai ne za ki shigo mini ɗaki?"
"Ka yi haƙuri Yaya."
"Ki na jina?" Ta gyaɗa masa kai alamar eh, ya ce "Daga yanzu idan ba ni na kira ki ba ka da ki sake shigo mini ɗaki idan ina ciki." Jinjina kai ta yi. "Magana za ki yi mini ba na son wannan kaɗa kan kamar wani ƙadangare." Ta ce "To Yaya" ta yi maganar tana ƙara takurewa, ƙare mata kallo ya yi, doguwar riga ce a jikinta, wadda ta kame ta sosai ta fito da surar jikinta. Wani abu ya ji yana ta so masa yana bin dukkan ilahirin jikinsa, ya lumshe idonsa ya buɗe su, ƙirjinta yake kallo yadda suka ciko, Ilham jin shiru ya sa ta ɗago da kanta ta kalle shi, ganin irin kallon da yake yi mata ne ya sa ta runtse idonta. Sudais ji ya yi lissafi na ƙoƙarin ƙwace masa, ya ɗago hannunsa kamar zai taɓa ƙirjinta sai kuma ya fasa ya ce "Fita na ce." Ai babu shiri ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice da gudu.
Tana fita ya sauke wani gwauron numfashi, ya koma ya kwanta saman gadon ya yi rub da ciki.
Ilham na fita ɗakinta ta shige, ita ma kwanciyar ta yi tana mayar da numfashi, a fili ta ce "Na shiga uku ni Ilham, amma na auna arziki yau da Yaya bai rufe ni da wannan faɗan na shi ba, to wai ma me ya kai ni ɗakinsa? Kodayake ai mijina ne ina da damar shiga ɗakinsa." Haka dai ta ci gaba da surutanta ita kaɗai tana murmushi.
Sudais ya daɗe kwance a gurin ƙwaƙwaran motsi ya kasa yi, da ƙyar ya miƙe ya shiga toilet ya sakarwa kan shi ruwa, ya daɗe ruwan na sauka a jikinsa, sannan ya yi wanka ya fito. Jalabiyarsa ya saka, bai damu da ya nemi abinci ba ya ɗakko laptop ɗinsa ya zauna ya fara aikinsa da ita, sai dai duk da haka idan ya tuna yadda yaga Ilham sai ya ji yana ƙoƙarin rasa natsuwarsa, bai taɓa tunanin yana da irin wannan lafiyar a jikinsa ba sai yau. Duba da yadda sam sha'anin mata baya gabansa. Yana nan zaune har aka yi kiran sallar magriba, tashi ya yi ya ɗauro alwala ya fice masallaci.
.....
"Inna Lantana"
Lantana ta ce "Na'am ƴar albarka"
"Yanzu shikenan ƴan ta'addan da suka yi ɓarna a hanyar ƙauyen garin nan sun ci bulus ko?" Inna Lantana ta yi murmushi mai ciwo ta ce "Zaliha kenan, zan iya cewa kam sun ci bulus tunda ba a san ko su waye ba, sannan ana kyautata zaton ba ƴan garkuwa da mutane ba ne, domin da sune ai tafiya za su yi da su sai in an hana su kuɗi ne sannan za su yi kashe su." Cikin damuwa Zaliha ta ce "Sun ci bulus fa? In sha Allah ba su ci bulus ba sai Allah ya toni asirinsu, mutane sam babu Allah a ransu, kowa abin da yaga dama yake yi, zalunci ya yi yawa a ƙasa, Allah ya saka mana ba zamu taɓa yafewa ba."
"Hmmm, ai lamarin wannan ƙasa tamu da jama'ar cikinta sai dai mu ce Innalillahi wa inna ilaihim raji'un."
"Inna Lantana kin san wani abu?"
"A'a sai kin faɗa."
Zaliha ta yi shiru kafin ta ce "Mutane ba sa tsoron Allah wallahi, sam ba su tunanin mutuwarsu, kin san gidan da muke zaune ni da wannan yaron Amir?" Inna ta girgiza mata kai alamar a'a, Zaliha ta ce "Daga ni har shi bamu san iyayenmu ba, a gidan marayu muka tashi."
Zaro ido waje Inna ta yi, ta ce "Ikon Allah, a gidan marayu? To ya aka yi kuma Malam ya ce a hanya ya tsinto ku? Kuma yanayin yadda ya zo daku gidan nan ya nuna kuna cikin tashin hankali."
Zaliha ta ce "A nan cikin garin Abuja, a gidan marayu muka taso, gida ne mai cike da tsafta da natsuwa, gida ne da aka san muhimmancin ɗan Adam, kuma ake kiyaye duk wani haƙƙi na shi, ba na gwamnati ba ne, gida ne da wani bawan Allah ya gina domin inganta rayuwar marayu, tunda na ta so na yi wayo a gidan ban taɓa ganin mutum mai tausayi da jin ƙan al'umma kamar Baba Sardauna ba, mutum ne mai dattako da natsuwa. Dukiyarsa sam ba ta gabansa, kullum burinsa ya ga ya yi abin da zai inganta rayuwarmu. Duk da haka ya kasance yana bayar da yara ga waɗanda Allah bai nufe su da samun haihuwa ba, amma kafin ya bayar da yaran sai an bi duk wani tsarin da ya dace, wanda aka tabbatar da yaran za su zauna a hannun mutanen ƙwarai ne, kwatsam wata rana wasu bayin Allah mace da namiji suka zo gidan, kallo ɗaya za ka yi musu kasan cewar akwai natsuwa a tattare da su, nan suka nuna suna buƙatarmu ni da Amir. Bayan an gudanar da komai kamar yadda aka saba ne aka ba su mu, sosai na ji kewar barina gidan, ashe mutanen azzalumi ne, gurin wani Alhaji suka kai mu suka sayar masa da mu, sosai na yi mamakin abin da bawan Allahn nan daya karɓo a gidan marayu ya yi, babu imani Alhajin da aka sai da masa da mu ya keta mini haddina, ya mayar da ni tamkar matarsa, Amir kuma suka yi ƙoƙarin hallaka shi Allah bai basu iko ba, wata rana Allah ya ba ni sa'a na ɓalla tagar ɗakin da nake ciki, na ɗaura ɗankwalin a ƙugun Amir na fitar da shi ta tagar, kasancewar ba ni da jiki ni ma ban sha wahala ba na bi ta gurin na fita, da ƙyar na samu na tsira a hannun na ƙaraso bakin titi, a nan ne Allah ya haɗa ni da Baba." Ta kai ƙarshen maganar tana wani irin kuka mai tsuma zuciya. Inna Lantana ma hawaye take yi na tausayinsu, ta dinga rarrashinta da ƙyar ta samu ta yi shiru, ta ce "Ki yi haƙuri Zaliha in sha Allah Allah zai saka muku, shi kuma wanda ya kula da ku tun farko Allah ya biya shi ya saka masa da alkhairi."
Zakiha ta ce "Inna don Allah ina son in koma gidan da nake da zama, in sabar da su halin da na shiga, kuma in gaya wa Baba Sardauna a daina karɓar yara a gidan." Inna Lantana ta ce "To shikenan za ki koma in sha Allah, amma dai ki bari ki ƙara samun nutsuwa tukuna, sai Malam ya raka ki. Duk da baya son zuwa garin Abuja."
"Saboda me baya son zuwa Abuja Inna?"
Inna ta ce "Saboda ya zauna a farko bai ji daɗin zaman garin ba, daga ƙarshe da ƙyar ya samu ya tsira da rayuwarsa har ya dawo gida." Shiru Zaliha ta yi tana sauke ajiyar zuciya, Inna ta ci gaba da rarrashinta.
......
Zuhura tunda ta shige ɗakinta ta kulle kanta ba ta fito ba, ban da kuka babu abin da take yi, sosai take jin kishin a ranta na auren da Sudais ya yi, nan ta ɗauki alwashin ko ta halin ƙaƙa sai ta aure shi, kuma sai ta raba shi da matar da ya aura. Wayarta ta ɗakko ta kira shi.
Sudais na zaune a danning ya gama cin abinci tare da su Mammy, don tunda ya fita sallar magriba bai dawo ba sai da ya yi sallar isha. Shi ne yana shigowa falon ya ga su Mammy a dinning shi ma ya je aka zuba masa abincin ya ci. Duk da Mammy nata tsokanarsa da cewar "Ya je gurin matarsa ya ci." Kira ne ya shigo wayarsa, ko da ya duba yaga Zuhura ce, sai ya tashi ya yi wa Mammy sallama ya tafi, yana isa part ɗinsa a falo ya tarar da Ilham zaune da kofi a hannunta tana kurɓar tea, ƙananun kaya ne a jikinta riga da wando sun ɗame ta sosai. Ilham sam ba ta son saka manyan kaya sai dole, tafi son saka ƙananun kaya. Zama ya yi a falon yana satar kallonta, "Sannu da zuwa Yaya." Ya ta faɗa tana kallonsa.
"Yawwa sannu" ya amsa mata yana ƙoƙarin ɗaga kiran Zuhura da ya sake shigowa wayarsa. Rangaɗau muryar Zuhura ta fito tana faɗin "Assalamu alaikum masoyi." Gaban Ilham ne ya yi mummunar faɗuwa jin muryar mace. Amma sai ta daure ta yi kamar ba ta ji ba.
"Wa'alaikissalam" ya amsa
Zuhura ta ce "Barka da dare, ina fatan ka na cikin ƙoshin lafiya?" Ya ce "Yawwa barka dai, Alhamdulillah."
Ɗan shiru ta yi, sannan ta ce "Masoyi sai na ji labarin ka yi aure" ta faɗi maganar tana runtse idonta. Ɗan kallon Ilham ya yi, yaga yadda ta yi kicin-kicin da fuska ya ce "Eh"
Hawaye ne suka sake zubo mata, ta ce "Ma sha Allah, Allah ya sanya alkhairi." Ya amsa da "Amin". Har zai kashe wayar ya ji ta ce "Ashe dai Allah bai nufi ni ce zan fara zuwa ta farko ba, yanzu kam sai dai na zo matsayin ta biyu." Sudais ya ce "Eh haka Allah ya nufa." Daga haka ya kashe wayarsa yana kallon Ilham da ta tashi fuuuu ta bar falon.
Murmushi ya yi ya girgiza kai, sannan ya tashi ya shige ɗakinsa. Ilham na shiga ɗakinta ta fashe da kuka, "Wato ashe ma har budurwa yake da ita? Ko da yake nuna babu ruwansa da mata, shi ne za ta kira shi yanzu bayan ta san yana da aure, hadda wani kashe murya tana ce masa baby." Ta kai ƙarshen maganar tana faɗawa saman gadon ta ci gaba da kukanta. Baccin da ta ji ya fara ɗaukarta ne ya sa ta tashi ta cire kayan jikinta ta saka rigar bacci, ta feshi jikinta da turare ta kashe wutar ɗakin ta kwanta ba tare da ta rufe ƙofa ba.
Sudais na ɗakinsa sanye da kayan bacci, sai dai baccin ya gagare sa, gabaɗaya surar jikin Ilham da ya gani ɗazu da kuma yanzu ta hana shi suku ni. Kwance yake yana jin yadda mararsa ta yi masa tsauri, da ƙyar yake iya fitar da numfashi, ganin da ya yi yana ƙoƙarin hallaka kansa akan abin da yake da iko da shi ya sa ya tashi a hankali nufi ɗakinta. Ilham tana kwance har ta fara bacci, ba ta ji ƙarar buɗe ƙofa sai ji ta yi an hauro saman gadon. Kasancewar ba ta nauyin bacci ya sa ta farka da sauri ta ce "Waye?" Tana lalubin inda makunnin wutar ɗakin yake ta kunna. Hannunsa ya sa ya janyo ta jikinsa ba tare da ya ba ta damar kunna wutar ba, ƙamshin turarensa ne da ta ji ya tabbatar mata da ko waye, ƙoƙarin janye jikinta ta yi saboda wani irin tsoro da ta ji ya ziyar ce amma yaƙi ba ta damar yin hakan, babu za to ta ji ya zura hannunsa cikin rigarta yana yawo da shi a hankali. Tsikar jikinta ce ta fara tashi, ta ƙanƙame jikinta, ci gaba ya yi da yawo da hannunsa cikin rigarta har zuwa cibiyarta, daga bisa ni ya yi ƙasa da shi gabaɗaya. Ƙanƙame shi ta yi za ta yi magana ya haɗe bakinsu guri ɗaya.
Amanarcool
***