Free chapter 路 Read without an account
04
*SHANTYTY馃拑馃挄*
_The Little Sister of Manga_
*_(茦ANWAR MANGA)_*
A charming cinematic Hausa comedy-drama that celebrates family, friendship, mischief, and the unforgettable journey of a spirited young girl whose presence changes everyone's life.
Page 4
Kunya taji ya 蓷an kamata domin koba komai aka ce ido da kunya, bare kuma tana shirin dakar masa 蓷a a gabansa duk da bata ganshi ba a farko amma taji kunya na ha蓷a idon da suka yi koba komai shi蓷in bai ta蓳a nuna mata wani banbanci tsakaninta da yaransa ba duk da tana a matsayin 'yar matarsa amma kullum buri da kokarinsa shi ne ya kyautata mata.
"Ashe kana ciki Babanmu sannu da hutawa."
Ta fadi tana wani 茩asa da kai kamar ta Allah.
Bai nuna alamun komai a fuskarsa ba domin fuskarsa a sake yake dubanta lokacin da ya tashi tare da mi茩ewa tsaye yana mi茩a ya ce.
"Yawwa Mamana har an fito ke nan wato duk kin bi kin kosa ki tafi shi ne ko tsayawa a gama girki bakiyi ba ko?"
Ya 茩are maganar ta sigar zolaya lokacin da yake kokarin janyo wasu kaya a leda.
Sosa kanta ta yi da murmushin ya茩e domin har lokacin bata wani saki jiki ba duk da taga bai nuna komai ba ta ce. "Na kosa naga Kakata ne shi ya sa."
"To madallah ga wannan idan kin je ki gaisheta da kyau da kyau."
Ya 茩are maganar tare da mi茩a mata ledar bakko. Sai da ta sa hannu ta kar蓳a sannan ta amsa masa tana kuma 茩are ma ledar kallo a wayance, so take taga abin da ke ciki, sai ta tsinkayo Muryarsa ya ci gaba.
"Kayan makaranta ne a ciki ranar litini idan Allah ya kaimu zaku fara zuwa makarantar birni keda Safiyyah in Allah ya kaimu..."
Tun da ya soma maganar ta saki baki tana dubansa cike da tsananin mamaki ha蓷e da farin ciki ai batasan lokacin da ta 茩ara kankame ledar bakkon ba a 茩irjinta 茩am! Bata ma jira ya 茩ari sa maganar ba ta kwala ihun murna da ya sa Idrissa sakin baki yana dubanta.
"Wayyo Allah na, Wayyo da蓷i amma gaskiya Babanmu ka kyauta kai 蓷in nan 蓷an aljanna ne in sha Allah, yadda ka faranta mini rai 'yar marainiyar Allah jikar kakanta, yar lele a wurin 拼a拼anta Manga, Shantyty ta 茩auye, Allah Ubangiji ya saka maka da mafificin alkhairi, Wayyo iyyeni nima shikenan zan zama city girl zan fara zuwa makarantar birni wihuhuhu...."
Ta 茩are maganar da godiya har da wani karkace wa ta yi irin yadda Yan daba suke yi idan abu na farin ciki ya samu.
A zuciyar Idrissa ya ce. "Ba karya ai idan baki yi hakan ba baki cika 茦anwar Manga 蓷an daba ba."
"Yi a hankali mana godiyar ai ta isa haka kuma ki dena gode min kinji domin duk abin da uba zai yi ma yarsa shi zan yi miki a matsayi 蓷aya na ajeku ke da 拼a拼an da na haifa."
Cewar Baba yana dubanta da murmushi a fuskarsa.
茦ara washe baki ta yi bata kuma dena yi masa godiya ba a haka har ta bar shagon cike da farin ciki kai tsaye ta far ma gidan Kaka cike da farin ciki da annashuwa.
"Wayyo Kakata kina ina ki fito ga 'yar jikallenki ta dawo!"
Maimakon sallama da fa蓷in hakan ta shiga gidan a guje kamar wacce aka kora bata tsaya ba ta ci gaba da kwalawa Kaka kira.
"Oyoyo oyoyo 'yar jikalleta marainiyar Allah sannu da zuwa sannu da zuwa 茩ari so nan yar 茦anwar Yayanta mai son ta."
Wata tsohuwa tukuf da kana ganinta kasan shekaru sun tura amma kuma da kuzarin ta, ita ce ta fito daga band'aki tana fa蓷in hakan cikin farin ciki da jin da蓷in dawowar jikar nata tana tafe zanen da ta yayo ta d'aura a 茩irji yana 茩o茩arin kwancewa tana 茩ara riko sa ga jikinta nan duk kumfa da alama ma wanka take ta fito.
Da gudu Shantyty ta 茩ari sa wurinta ba kuma tare da bata lokaci ba ta saki kayan hannunta bata duba jikin tsufa na Kaka ba ta fa蓷a jikinta tana dariya da murna take fadin.
"Kakata nayi kewarki sosai."
Gwalalo ido kawai Kaka take tana so ta yi magana amma ta kasa domin rungumar da Shantyty ta yi mata ji take tamkar shake mata wuya aka yi da kyar ta fizgo maganar da fa蓷in.
"Sa kar ni 'yar nan sakeni haka karki 茩ari sani banga aurenki keda yayanki ba bare naga yayanku sakarni Yar nan karki 茩ari sani."
Dariya Shantyty ta yi tana sakin nata 蓷in ta tura baki tana fa蓷in. "Gaskiya ke Kaka fa matsalar ki ke nan baki iya abu irin na Yan birni ba yanzu fisabilillah har guda nawa nake da zaki ce zan 茩ari sa ki."
Ri茩e baki Kaka ta yi bata ma bari Shantyty ta kai aya ba ta ce. "Aw haba yanzu duk wannan uban girman naki kike fa蓷in nawa kike wai hala ma bakisan kin isa aure ba ne ko 'yar nan?."
Shantyty ta katse ta da fa蓷in.
"Hmmm Kaka ke nan ai ni kam Aure ba yanzu ba dan duk mazan 茩auyen nan babu wanda ya yi min karatu ma zan yi sai na zama Farfesa a jami'ar Akzfad (Oxford) dake can America kin san burina ke nan."
Ta fa蓷a cike da neman magana dan tasan abin da Kaka ta tsana ke nan ta ce ba zata yi aure ba sai karatu idan kana so kaga fushin Kaka ka ce mata Burin Shantyty shi ne zama Farfesa a jami'ar 茩asar waje.
"Ai shikenan kuma Allah ya yi kin dawo zamu d'aura daga inda muka tsaya ko to ni dai ba zan kulaki ba yanzu."
Kaka ta yi maganar tana kama Hanyar komawa bayi.
"Kakata ke nan da wasa fa nakeyi miki ai nayi kewarki Dan Allah ki hakura da wankan nan dan nasan zaki iya kaiwa bayan isha'i ma baki fito ba indai wankan ki ne."
茦are maganar da Shantyty ta yi ya yi daidai da 茩ari sawa da ta yi ta baya ta 蓷ane bayan Kaka tana dariya. "Yawwa Kakata 蓷an goyani mana da gaske fa nayi kewarki cikin carbi sau goma." Cewar Shantyty cike da sha茩iyanci.
"Yau naga Lili ban ga A'isha ba yanzu fisabilillah wannan go蓷ai-go蓷ai dake 蓷in ne zaki kalla tsohuwa kama na, ki ce na goyaki, an ya kuwa 茦anwar Yayanta akwai adalci a lamarin nan, a'a wannan ba kewata kikayi ba kin dawo ne kawai ki 茩ari sa ni."
Shantyty ta kwashe da dariya tana sauka daga Bayan Kaka ta ce. "Allah kuwa duk a cikin kewarki da nayi ne yanzu dai ba wannan ba ga sako nan a kula Umma ta ce na kawo miki kila ma wannan dambun naman mai da蓷i ne a ciki ta gai ce kar na bude shi ya sa ban bu蓷e ba amma da na biye ma zuciyata da tuni na bu蓷e kafin na 茩ari so nan."
Kaka ta girgiza kai tana fa蓷in. "Zaki aika kuwa na sani to ita kuma wannan ledan bakkon fa mene a ciki?"
Sai da Shantyty ta washe baki kafin ta ce. "Kayan makaranta ne Babanmu ya 蓷inka min kuma ya ce jibi Litini zamu fara zuwa tare da Safiyyah makarantar fa a birni take Wayyo ni Shantyty 茦anwar Yayanta nima zan zama City girl."
Ta 茩are maganar har da rawa da juyi ita kam Kaka ri茩e ha蓳a ta yi tana kallon ikon Allah kafin ta jinjina kai. "Ah lallai ba shakka yo ke wannan kikaje makarantar birnin nan ai an kai musu jafa'i bama bala'i ba. Domin na san halinki na neman magana zaki gwada musu acan kuma idan kika yi ba kyaleki za'a yi ba sannan idan aka yi miki hukunci kizo ki fa蓷a ma wannan Yayan naki daga nan nasan a yadda yake son ki ma da rashin son abin da zai ta蓳a ki har 茩ona Makarantar ma zai iya yi"
Cewar Kaka iya gaskiyarta.
Shantyty ta ta蓳e baki tana wani dira-diren 茩afa ta ce. "Tohm shikenan kuma kin fara ko Kaka? Yanzu wai ma yabonmu ni da Yaya Manga 蓷in kike ko zaginmu?."
Ta蓳e baki Kaka ta yi ta ce. "Ko daya kawai dai gaskiya na fa蓷a."
"To ki ri茩e kayanki yanzu dai muje bayin na tayaki kiyi wankan domin na kosa a bude kular nan naga abin da ke ciki, tun d'azu sai ha蓷iyar yawu nake kuma nasan halinki ba zaki bu蓷e ba sai kin yi wanka kin shirya sannan kiyi zama na musamman domin bu蓷e wa zuwa lokacin kuwa wata kila na gaza hakura na bu蓷e."
Free Book ne amma idan kun bada ha蓷in kai ta hanyar like 馃憤 comments 鉂わ笍 and share it 馃 thank you
Nainarh KD