Free chapter · Read without an account

FREE PAGE-13

by Aisha Sani Abdullahi · AMEEENATOU 'YAR KAKA

*MY GROUP XAYYEESHERTHOU FANS CLUB TABBAS INA YINKU OVER🥰🔥TEAM AMEENATOU ANTIES MASU SHARHI BAN DA GOGGOS YAN ƊUMAMA GROUP*

______

Mai zai gani?

Bra ce sanye a kirjin Ameenatou tana nuna masa.

"Onkul ka siyamun nima wannan ka ji, ka ga ya mun kyau ina so nima in fara sawa."

Wani irin hamshakin Tsaki Al-ameen ya yi bai san lokacin da ya figi Ameenatou ya jafa waje tare da kulle kofarsa ba.

Dafa kan sa ya yi, "Oh My God, Na tsani yarinyar nan amman tana neman takurawa rayuwata."

Ameenatou kuwa bajewa tai tana bori da ihu, "Onkul wallahi ka fita sai ka siyamun aradun Allah ba inda zanje in baka siyamun ba, Kaka ki zo ki ce Onkul ya siyamun abun saka Nono nima zan sa nawa." Tuni kurarin Ameenatou ya baza gidan aka firfito.

Kaka ce ta fara karasawa tana, "Meya Faru kuma Ameenatou kar dai waccen Zulai Mayyar ba ta barki ba har yanzu?"

Kuka ta fara tana, "Kaka Onkul wai naje ina nuna masa ya siyamun wannan abun saka nonon shine ya koroni waje kuma ya kulle kofa, Kaka ki ce ya bude kuma ya siyamun ni."

Kaka ta tashi tsaye da rike kugu kai ka ce Budurwa ƙauye, "Iyeee ai lallai Ameenu ka isa lallai ne tashen balagar tsuntsayen naka har ya kai haka da zaka jefomin Jika waje ba gaira ba dalili to ni da kai ne maza ka bude kofar nan kuma ka ɗauke ta kuje ku siyo in ba haka ba sai na tsinewa shegen goshinnan naka mai kama da albasar turawa."

Nauwara ce ta karaso ta dafa Ameenatou tana, "Ameenatou ina wannan kikeso? To na bar miki kuma Uncle zai fito ya siyo miki wasu ma akasuwa amman yanzu ki fara sa wannan tashi ki daina kukan kinji."

Share hawayen "tau Antu Naura kuma ki ce ya siyamun masu kyau."

Hajiya Karama ta kallesu ta ce, "Oh Allah Gidadanci da ƙauyenci dai bai yi ba Arayuwa, ina brest din da za asawa bran ma kirji kamar kan giginya." Ta na karasa maganar ta juya ta tafi abun ta.

Kaka ta ce, "Nace kinyi da Uwar gyatumarki mai kashin kwance da mijin ta mai ruɓaɓɓiyar kaciya kinji ko."

Ameenatou ta ce, ,"Kaka ki barta na san haushi tana ji Antu Naura bata, ba ta irin nawa bane kuma yasin zan yi maganinta ai a agidannan haa haa."

Ameenatou ta tashi tana tsalle ta shige daki.

Ɗauko tsimmokaran dankwalinta ta yi tasa acikin brar kan ta sa ajikinta ta maida riga .

In ka ganta kai kace wata falfela kirji ya tsaya jak kamar tumatur.

Fitowan da zata yi suka ci karo da Al-ameen.

"Onkul ka ga Antu Naura ta ban nata kafin ka siyomun ya mun kyau ko?"

Wani bakin ciki ne ya kara turnike zuciyar Al-ameen da sauri zai wuce sai ga Kaka tayi charaf.

"Kai Amenu maza ka dau Yar Uwarka kuje kasuwa ka siya mata rigar Mama kana ji na ko?"

Ba tare da ya yi magana ba kawai ya fice Kaka na ganin Dady ta fara kuka, "Wai ni zan ma Ameenu magana ya harareni ya mun tsaki sannan kuma ya fice ya barni." Ta face majina da gefen zanin ana kuka wiwi.

Da sauri Dady ya karaso, "Subhannallah Inna meya faru?"

Kara fashewa tai da kuka.

"Fisabillahi dan anga Malam baya duniya sai anemi wulakanta mu ni da Ameenatou a gidannan,yoo wai ni Al-ameen ni zai zaga ya ce mun Bakina kamar duwawun bera? Har ni zai kalla ya harara." Ta kara fashewa da kuka.

"Dan kawai na ce ya dau yar uwarsa suje kasuwa asiyo mata rigar Mama kenan ni ban isa da shi ba ko? Ban isa ba ko." Face majinar ta kara kan ta kuma fashewa da kuka.

"Shikenan, na ce shikenan daman na san ni ba kowa ba ce koma ban isa ince ayi komai agidannan ba."

Dady ya ce, "kiyi hakuri Inna zai zo ya dauke ta suje kiyi hakuri dan Allah bana so kina kukannan haka kin riga kin tsufa yanzu ciwo zai iya rufeki dan Allah kiyi hakuri."

Hajiya Babba ya kwalawa kira kan cewa ta kirawo Al-ameen nan take kuwa sai gashi.

Da gudu Ameenatou taje ta dane cinyarsa ba yadda ya iya ba abun ya motsa ba Kaka ta fara suffar masifa.

Ita ko Ameenatou sai lilo take mai ajiki minti ƙadan sai mintsini tun yana yi kamar bai ji ba har ya fara motsi.

Ita ko ban da dariya ba abun da take masa takaici kamar ya haɗiye kansa.

Dady ya ce, "Ka dau Ameenatou kuje kasuwa duk abun da take so asiyo mata komai da komai na bukata, maganar skul din ta ma zakuje ranar Monday in Allah ya kai mu."

Al-ameen ya ce, "Dady Office zan tafi mai zai hana driver ya Kaita."

Karaf Kaka ta ce, "Ka ci gidanku na ce ka ci gidanku ungo nan ba drevon da zai kaita da kai zaku eher mutum da yar uwarsa amman yana gudunta dan bakin hali, ansha a nonon gyatuma."

Dady ya ce, "Hakuri za ka yi ka dau excuse in kun dawo kaje yanzu kam tun da anyi break kuje kawai i think yanzu 10:pm ma ta wuce."

Ba yadda Al-ameen ya iya haka ya tashi babban tashin hankalin sa shine maganar siyo bra a kasuwa bai ma san ta yadda xai kwatanta ba ga kuma wannan aljanar yarinyar abun da kunya anganshi yaje siyan bra kuma da ita.

"Onkul jirani insa takalmi na , "ta fada tana washe baki.

Kaka ta ce, "Yawwa ka kulamun da ita kuma axaɓo mata bra mai Bala'in kyau ehee."

Tun da ta shiga motsr nan ban tabe tabe da tambayoyi ba abun da take yiwa Al-ameen bai kulata ba ita ko ko ajikinta ta ci gaba kamar ana zugata, "Onkul yaushe za ka yi aure? Ka haihu kana daukan jinjiraye zannsma yaranka wanka da kaina aradu na iya har kai ma zan iya ma fa ko kashi kayi zan ma tsarki."

Daidai da isowarsu kasuwar kenan ya yi paking tuni ta fito kamar an jefota.......

*Me kuke tunanin zai faru?*

*Zan ci gaba in sha Allah in ga ruwan comments*

_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER *** SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_

_*Urs Xayyeesherthuo🤍*_ [12/1, 4:28 PM] ***: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

****

_RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_

_SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_

_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_

_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_

_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.