Free chapter · Read without an account

FREE PAGE-17

by Aisha Sani Abdullahi · AMEEENATOU 'YAR KAKA

Ameenatou ta nufesa tana, "Oyoyo Onkle ka siyo mun rigar Nonon ko?"

Kau da kansa ya yi cike da ɓata rai ya miƙa mata ledar batare da ya jira ta ƙara fadin uffan ba ya shige ɓangaren shi.

Ameenatou kuwa tsalle tasa tana ihu, "Kaka Kin gani Onkle Al-ameen ya siyomun rigar Nonona irin na Antu Naura."

Washe baki Kaka tayi tana faɗin, "to ko kaifa ɗan albarka, in da haka kake kula da ƴar uwar ta ka marainiyar Allah yaushe zan damu, Amma da yake an biyo baƙin halin Uwa shiyasa, tashi muje ɗaki ki gwada muga yanda ya yi na san ma dai zai miki kyau, ƴan baƙin ciki sai dai su mutu." Kaka ta ƙarasa maganar tana hararar Hajiya ƙarama da ta fito daga kicin. "Oh yanzu Al'ameeen saboda rashin aikin yi ne da taya ɓera ɓari ka siyo ma wannan beran yarinyar bereziya har kala goma, tabdijam to ina Nonon da za'a saka abu kaman allon mayu, Allah ya kyauta ƙauyanci irin na ƴan ƙauye kuwa."

Hajiya ƙarama ta ƙarasa maganar tana hayewa sama da sauri, don ta san in har ta tsaya sai kaka tayi mata zagin ƙare dangi.

"Eh lallai wuyar ki ya isa yanka, tabbas za ki ga tijara don kin samu na haƙura ranar ban sa an kaɗaki gidan mai dattin hula ba ko, shiyasa har ni kike zagi bari Audun ya shigo zaki san kin zageni."

Kaka ta ƙarisa maganar ta mai fashewa da kuka. "Kaka kiyi shiru ki barni kawai ni da ita zan miki maganin ta a gidan nan, zata san waye Ameeenatou kaka tabbass." "Yauwa ƴar albarka, shiyasa nake alfahari da ke ai, navsan kevɗin jinina ce ban ce ki ragawa kowa ba gidan nan ehe kowa yayi miki ki mishi."

"Angama Kakan Ameeenatou ikon Allah, tashi muje in gwada rigar nono na kinji."

ASIBITI "Sister Surayya ni abun ya ɗauremun kai, ko dai Dr Al'ameen aure zaiyi,? to in ba aure ba mai zaiyi da breziya, saboda tsaban cin fuska ma ni zai aika in siyo mai bresziyar kayan aure, ni kaina gaba ɗaya ya kulle a lokacin da na ƙarɓi kuɗin saƙon shi."

"Hhhhh sister Rukayya kenan, ke dai kawai ki ce kin ga kuɗi ya ruɗaki kin mance da kishi sai yanzu hankalin ki ya dawo jikin ki, kika sani ko wannan yarinyar da suka zo tare ya siyan ma."

"Yarinyar da ko ƙirgan dangi bata fara ba balle nonuwa."

Cewar Rukayya.

Surayya ta ce, "Ko ma yane dai tunda kin samu rabonki ai shikenan yanzu abani rabona."

Harara Rukayya ta bi ta da shi kan ta tashi tana, "Wannan kudi kam ai ya shiga kuma ba fita Allah sa gobe yazo ya ce asiyo masa pant ma,kuma in sha Allah indai na cika Sunana Rukayya kamar Anyi an gama na Auri Al-ameen."

Ta shige tana rangwaɗa.

Dariya Surayya tai tana, "To ai shikenan Allah ya tabbatar da alkairi."

******Kaf sai da Ameenatou ta gwada breziyoyinnan suna shewa da kaka kai kace sabin kamu ne.

Tana cikin sa kaya taji alamar maganar Hajiya Karama na fitowa.

Ko bari ta karasa sa rigar ba tai ba ta ce, "Kaka ina zuwa."

Da gudu ta nufi kitchen, robar yaji ta ɗauka,ta nufi ɗakin Hajiya Karama sidif sidif ta shige toilet.

Buta ta dauka saida ta ciketa da ruwa dam kan ta juye yajinnan aciki.

Ta fito tana dariya.

Adaidai kofa ta ci karo da Hajiya karama .

"Ke bagidajiya mai kikazo mun aɗaki?"

Ameenatou ta murguɗa baki kan ta ce, "Hassana da Hussaina na zo nema muyi wasa ko da gaba ne?"

"Iyeee Ni kike fadawa hakan da shegen ido kamar na bera." Cewar Hajiya Karama.

Ameenatou ta sheƙe da dariya, "oho dai ni ban da duwawun akuya." Ta zura aguje.

Hajiya karama na shiga ɗaki tana, "Wannan yarinya dole in dau mataki akanta wallahi cikinama ya murɗa bara in shiga toilet in fito kan dai in tafi anguwar nan."

Aiko Hajiya karama ta shiga toilet cikin nishaɗi ta zabga uban kashinta tana nishi.

Tana gamawa ta janyo buta domin tsarki.

**Ameenatou kuwa na can na zabga uban dariya.

Kaka ta ce, "ke wai lafiyanki kuwa?"

"Hhhh Kaka ba za ki gane bane bari bomb din ya fashe ka......

Kan ta karasa suka jiyo karar Hajiya Karama tana.

"Na shiga uku jamaa......

_LITTAFINA NA KUDINE DUK MAI SO ZATA TURO DA KATIN 300 TA WANNAN NUMBER *** SANNAN TA MUN MAGANA AWATSP TA NUMBER KO KUMA ATURA TA ACCOUNT 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Acess Bank, THANK YOU OLL,SHARE& COMMENTS FISABILLAH🥰_

_*Urs Xayyeesherthu[12/8, 1:06 PM] Xayyeesherthou: °°°°°°°°° _*AMEENATOU*_ _('Yar Kaka)_

*NOBLE WRITERS ASSOCIATIONS✍🏼*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

****

_RUBUTAWA_ _*Xayyeesherthul-humaerath*_

_SADAUKARWA_ _*Nura Sada Nasimat, Allah ƙara Daukaka Oga.*_

_*Domin Farincikin ki kawar arziki irin albarka Ameena Abubakar*_

_NOBLE WRITERS ASSOCIATION ABAR ALFAHARI NA,NA GAIDAKU DUKA,SON SO FISABILLAH🤍_

_*LITTAFINA NA KUDINE NAIRA DARI UKU⚠️*_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.