Free chapter · Read without an account

CHAPTER 3

by Aisha Sani Abdullahi · 5STARS CHRONICLE Book 1 YEL

Details din Zeeyter Oil And Gas ya tura masu duka kowa ya karanta cikin Mamaki Khaleel ya ce, "Gaskiya kam wannan abun mamakine da kuma farinciki, wannan shine silar hadin kanmu domin bayyanar da masu boyayyun baiwa tare da tallafa masu."

"Wooo."

Cewar Deejerh.

,"Ni na rasa ma abun fadi."Zahra ta fada tana bude baki.

Kaf ciki Farouq ne kawai baiyi magana ba kuma yana online.

Haiydar ya ce, "Farouq ya dai na ji shiru kowa na magana ban da kai,kuma kana buɗe sakonninmu?"

"Bai mun ba,ban ma yarda da companin ba,in ban da rainin wayo taya ma za ace wai ana hada Petrol da shara? Wannan shirme ne da rainin hankali." Cewar Farouq.

Zahra ta ce, "What! Me ka ke nufi?"

"Wannan ma ai iskanci ne, taya har za su iya turo mana jawaban bogi?"cewar Khaleel.

"Hmm."kawai Deejerh ta ce.

Ganin abun na son zama rikice gare su Farouq ya ce, "Kawai mu bar batun yanzu kowa ya je ya yi tunanin duk shawarar da aka yanke sai mu kara zama."

Kasancewar basa taɓa yanke hukunci ba tare da amincewar waninsu ba, ko da mutum ɗayane bai amince da abu ba to baya taɓa yuhuwa,wannan damar Farouq ya yi amfani da ita domin cimma manufarsa da take boyayya.

Da haka suka rabu Haiydar fal zuciyarsa da tunani yadda lamarin zai karƙe.

★

Bobiel

Wata irin kara Zeeyter ta sake wacce sai da ta karade kafatanin gidajen da ke yankin.

Hawaye ne ya fara zuba daga idanunta.

Cikin sauri Madame Ayshe ta tawo domin tallafa mata,amman ina ba alamun motsa ta kame awajen kyam.

Laure da Harira na gefe suna ƙyalƙyala dariya.

"Tu vios (kin gani) ai na fada miki indai muka je gun Malam Dule an gama magana ,ita da ƙara wata tafiya ko wani abun arziki sai dai ta ga ana yi." Harira ta faɗa tana kunshe baki.

Hurera ta ce, "ni babbar damuwata mu kwace gidan man cen da ma gidan abincin muje muyi kane-kane Allah sa bakinta ya rufu kamar yadda kafar ta kame,ai wallahi kadan ta fara gani,in abun ya citura sai mun kaita har lahira ma kowa ya huta." Tafawa sukai suna ƙara leƙawa tare da kunshe baki.

"Kin ga mu je harkar gabanmu aikin gama ya gama yanzu kam." Cewar hurera tana jan hannun Harira.

Tafiya suke suna waƙa da ka gansu ka san sun ƙula ƙulalliya

Anyi anyi kafar Zeeyter ta motsa amman ina har ta fara ficewa a hayyacinta.

Madame Ayshe ba abun da take ban da adduoi daga karshe ma sai da aka kira babban malamin da ke anguwar.

Tun yana karatun zalla har ya dawo wanke mata kafar da ruwan magani....

Rufe idanun da zata yi ta fara hango..........

Kan kace miye Zeeyter ta sake shi tim a ƙasa.

Jini ya fara zuba ta kai da baki.

Nan take Polisawa suka baibaye wajen aka kamata shi kuma aka tafi da shi asibiti domin yi masa taimakon gaggawa.

Ta bada bayanin komai tare da bayyana yadda yake son keta mata haddi cikin jama'a amman ina dake babban mutum ne ba wanda ya yarda da hakan a karshe ma maida lamarin sukai kan cewa ita ce take nemansa cikin mutane ganin cewa ya yaƙi amincewa ne yasata neman hanyar illata shi.

Mamaki fal a idanun Zeeyter ta dubi sifeton tana fadin, "Me zan nema agun wannan? Ban ga abun so a tattare da shi ba,in inada bukata da kudina nake wannan ba wai zuwa bin mazan kantiti ba Allah ya kyauta ya tsare ni."

"Ke fa daman ba isasshiyen hankalin gare ki ba, Impoli (mara kunya)yau ko zan baki mamaki a sel za ki kwana,tunda ada kina tunƙahon ana baki damar beli ne."

Tsaki tai ta tashi, ta sa hannu a jaka , ta ce, "Idot. (Wawa)dubu ɗaya ta ciro ta hurga masa ta fice aguje.

Da gudu suka bita amman ina ta tsare,gudu take tamkar fanka ta samu wutar lantarki.

Haka har ta isa gida, abun mamaki tasa kafarta ke nan da niyar shiga gidan ta maƙale,ko motsi bata iya yi bare ta iya takawa.

★

Zaune yake akan tanƙashesshen gadonsa yana danna computer, saƙone suka fara shigowa rututu na kamfanonin da ke neman tallafi.

Har ya gama tattarawa wani ya shigo.

Zeeyter Oil And Gas, tsayawa ya yi domin ya duba.

Ganin bayanan sai da ya ƙara gyara Gilashin da ke fuskar shi,

"Haɗa man Petrol? Kuma anan Niger? Sannan da robobi? Wonder shall never end, akwai masu fasaha sosai a duniyar nan,lallai ina da bukatar kasancewar wannan Companin karkashin nawa ko dan inganta Petrol din da za ana sanyawa motocin da zamu fitar."

Duniyar tunani ya fada,amman babban abun da ya fi bashi mamaki ganin cewa mace ce shugabar companin kuma Bahaushiya

Janyo Wayarasa ya yi cikin sauri, WhatsApp Discussion group din su ya shiga

"Hey Friends ,I need Ur Attention Please! (Barka dau Abokai!Ina buƙatar nutsuwarku) na ga abun mamaki yau."

Zahra ce ta fara magana, "Here we are (ga mu nan) ga dukkan alamu abun ya taɓaka da yawa ba mu, mu sha I done gyara my glasses." Ta ƙarasa maganar tana sa emojin dariya.

Farouq ne ya katse ta da fadin, "Aboki na zaƙu fa ba mu bayani."

"Kunnuwana har rawa suka fara oh oh." Haiydar ya turo da emojin kunne tare da dariya.

Deejerh ta ce, "Oh Haiydar na gaji da shirun fa."

Sai a lokacin Haiydar ya ƙara magana , "Oh calm down Friends, (ku kwantar da hankali abokai) yanzu za ku ga abun mamaki kowa ya tabbatar ya zauna da kyau " shi ma ya ƙara she maganar yana dariya.

Details din Zeeyter Oil And Gas ya tura masu duka kowa ya karanta.

Haiydar ne ya ƙara ce wa, "Gaskiya kam wannan abun mamakine da kuma farinciki, wannan shine silar hadin kanmu domin bayyanar da masu boyayyun baiwa tare da tallafa masu."

"Wooo." Cewar Deejerh.

,"Ni na rasa ma abun fadi."Zahra ta fada tana bude baki. Kaf ciki Farouq ne kawai baiyi magana ba kuma yana online.

Haiydar ya ce, "Farouq ya dai na ji shiru kowa na magana ban da kai,kuma kana buɗe sakonninmu?"

"Bai mun ba,ban ma yarda da companin ba,in ban da rainin wayo taya ma za ace wai ana hada Petrol da shara? Wannan shirme ne da rainin hankali." Cewar Farouq.

Zahra ta ce, "What! Me ka ke nufi?"

"Wannan ma ai iskanci ne, taya har za su iya turo mana jawaban bogi?"cewar Khaleel.

"Hmm." Kawai Deejerh ta ce.

Ganin abun na son zama rikice gare su Farouq ya ce, "Kawai mu bar batun yanzu kowa ya je ya yi tunanin duk shawarar da aka yanke sai mu kara zama."

Kasancewar basa taɓa yanke hukunci ba tare da amincewar waninsu ba, ko da mutum ɗayane bai amince da abu ba to baya taɓa yuhuwa,wannan damar Farouq ya yi amfani da ita domin cimma manufarsa da take boyayya.

Da haka suka rabu Haiydar fal zuciyarsa da tunani yadda lamarin zai karƙe.

★

Bobiel

Wata irin kara Zeeyter ta sake wacce sai da ta karade kafatanin gidajen da ke yankin.

Hawaye ne ya fara zuba daga idanunta.

Cikin sauri Madame Ayshe ta tawo domin tallafa mata,amman ina ba alamun motsa ta kame awajen kyam. Laure da Harira na gefe suna ƙyalƙyala dariya.

"Tu vios (kin gani) ai na fada miki indai muka je gun Malam Dule an gama magana ,ita da ƙara wata tafiya ko wani abun arziki sai dai ta ga ana yi." Harira ta faɗa tana kunshe baki.

Hurera ta ce, "ni babbar damuwata mu kwace gidan man cen da ma gidan abincin muje muyi kane-kane Allah sa bakinta ya rufu kamar yadda kafar ta kame,ai wallahi kadan ta fara gani,in abun ya citura sai mun kaita har lahira ma kowa ya huta." Tafawa sukai suna ƙara leƙawa tare da kunshe baki.

"Kin ga mu je harkar gabanmu aikin gama ya gama yanzu kam." Cewar hurera tana jan hannun Harira.

Tafiya suke suna waƙa da ka gansu ka san sun ƙula ƙulalliya

Anyi anyi kafar Zeeyter ta motsa amman ina har ta fara ficewa a hayyacinta.

Madame Ayshe ba abun da take ban da adduoi daga karshe ma sai da aka kira babban malamin da ke anguwar.

Tun yana karatun zalla har ya dawo wanke mata kafar da ruwan magani. Rufe idanun da zata yi ta fara hango Wani irin tsuntsu addu'a take azuciya har tsuntsun ya iso inda take daf wajen kafarta ya shafa da fuka-fukinsa . Nan take ta furta, "Alhamdu Lillah."

Tana jan kafar kuwa ta motsa.

Madame Ayshe ta ce, "Ma sha Allah amman dai ba kya jin komai yanzu ko?."

Ban da nisha ba abun da Zeeyter keyi tana gumi, Murmurshi ta yi abayyane tare da fadin, "Allah ka maidawa mai sharri, sharrin sa."

Tare suka shige cikin gidan.

★Madame Ayshe tamkar uwa take ga Zeeyter ba ma Zeeyter kadai ba uwa ce ga dukkanin wani maraya da ke rayuwa a cikin gidan marayu na bobiel, kasancewar ta shugaba kuma mu'assasar gidan.

Kuma ita ce ke kokarin karfafawa Zeeyter gwiwa a kullum ko da ta fara kokarin karaya.

Haiydar na zaune a office yana aiki sai ga kiran Khaleel. Bayan sun gaisa Khaleel ya fara da, "Na ga jiya kun tattauna ina off sai da zahra ta kirani ta mun bayani,amman Meyasa kuka biyewa Farouq? Baka taɓa kawo bangare ka ce kana so a dauka ba da wannan karan ka nemi alfarma laifine? Ko ma mene ne zai faru bai dameni ba, ka turomun details din komai zan bincika inyi accepting."

Murmushi kawai Haiydar ya yi2.FFRafin ya ce, "Bana so mu rushe tafiyar shekaru da shekaru a kwana guda,so abarsa ya kawo dalilinsa cikakke inya karɓu kawai sai a hakura."

"Aa fa na gama magana da shi And na fahimtar da shi wasu abubuwan da nake ganin bai fahimta ba,sauran ya rage na shi, Deejerh ta fara shirye-shiryen zuwan mu Niger In sha Allah acikin satinnan."Khaleel ya faɗa yana gyara zama.

"Owk duk yadda ku ka ce zanyi farinciki da hakan,fatan alkairi."

"Alright fatan alkairi."Khaleel ya fada yana katse wayar.

★

Tunda su Harira suka ji labarin cewa kafar Zeeyter tayi tafiya ba abun da ya sameta hankalinsu ya tashi matuka har sai da suka koma gun bokan wanda acewar shi ai abun ya lafa ne amman inya tashi dawowa bata isa ta iya koda motsa hannunta bane bare kuma kafar,hakan ne yasa hankalin su har ya fara kwanciya.

Dare ya yi sosai Zeeyter ce kadai a Zeeyter Oil And Gas duk ma'aikata sun tashi kamar yadda aka saba ita ce ke zama sai 2am take tashi.

Horn aka mata da sauri ta bude tare da duban waye.

Masu siyan Petrol din ne cikin fara'a ta ce, "Barka dai yallaɓai."

"Barkanmu dai Madame."

"Na nawa kake so?"

"Jaka biyar."

Karban kudin tai tare da sawa cikin jakarta ta shige ciki domin sallamarsa,amman abun mamaki ganin ta bar jakar awajen yasa shi zuwa ya dauke kudin har ma dana sauran kudin jakar,jin motsinta yasa shi saurin komawa gefe.

Kamar yadda ta tafi da fara'a haka ta dawo cikin fara'a ta sallame shi kafin ta rufe get din ta koma ciki.

Sai da tazo lissafi ta ga ba kudi babu alamun su,maimakon kuka Murmushi ne ya bayyana afuskarta, maimakon zagi addu'a tai aranta, "Allah na gode ma, Allah ka bani wanda ya fi su, Allah kar ka sa mun hassada bare kyashi ga duk wani mahaluki na fadin duniya." Daga karshe ma tashi tai tayi sallah kafin ta shige gida ta kwanta.

Ko barci Zeeyter take ba za ka taɓa ganin fuskarta ba Murmurshi ba daga farkon kwanciyar ta har wayewar gari,in ko salon fuskarta ya canja to ankaita maƙura.

Washegari da misalin karfe 12:00pm zaune take tasa wani Iron gaba tana gyarawa, Halliru ya shigo cikin fara a yake magana, "Madame Je le promets? (Albashirinki)."

"Goro meya samu ne haka?."cewar Zeeyter tana goge zufar da ke fito mata.

"Yanzu-yanzu na samu saƙo awayata 5stars Expensive company na bukatar mu domin tantancewa nan da mako guda."

Da sauri ta tashi tsaye tana fadin, "Dieu merci (Alhamdu Lillah) yanzu sai afara shirye-shiryen yadda zaman zai kasance." Karasa maganar tai tana duban agogon hannunta

"Ina ga lokacin zuwan Malama ya yi bara inje muyi karatu da dare karasa maganar."

Ana cikin karatu ta dauki wayarta tare da kiran wata number da ke sama. A ɗaya ɓangaren cikin sauri ya amsa yana, "Madame akwai bukata ke nan."

"Eh." Kawai ta furta

Sannan ta karbi uzuri wajen Malamar, tana fita ba inda ta faɗa sai toilet sai da ta wanke jikinta fes kafin ta fito sanye da wani ƙaramin towel.

Tana fitowa yana ƙarasowa, Murmurshi yake yana suɗe baki tamkar wanda ya ga nama,ko bari ya ƙaraso batai ba tai saurin ƙarasawa tana kissing dinsa.

Tsareta ya yi da idanunshi yana mata wani munnan kallo da karfi ta fisge hanayenta tana masa kallon wulakanci ta ce "Ba shi ka ke bina ne malam da za ka rike min hannu?" Farouk ya yi mata wani kayataccen murmushi me fassararori ya ce "Sannunki Gimbiya?" Kallon sama da kasa ta masa duk da kasancewarsa kyakyawan gaske sam bai mata ba ta tabe baki ta ce "Da ganinka baka da ishasshen seti, kana nan da baki kamar famfo ina ma garga'di ko da wasa ka da ka kuskura ka sake gwada taba jikina ba tare da izini na ba, idan ba haka ba wallahi ran ka zai yi mumunan baci."

tayi tsaki ta juya dan shigewa shagon sa ke rike mata hannu ya yi "Dakata mana Gimbiyata ki saurareni magana nake so muyi dake Please."

A fusace ta juyo ta ce "Tu es fou quoi? tu comprends pas tout ce que je te dit." ( Kana hauka ne ko me? baka gane duk abin da na fada maka bane?)

Ganin hankalin mutanen kasuwar ya fara dawowa kansu yasa Farouk sakar mata hannu tare da cewa "Tabbas na haukace a kan ki kuma zan iya jure ko wane irin wulakanci daga gareki domin kina cikin irin matan da nake so a duniya."

Cike da mamaki Zeeyter ta ce "Dube ka dan Allah ni ko a kyauta a ka ban kai ai sai dai na zubar a shara, idan kana ganin kana da kyau ne to ni kyau ba zai burgeni ba, dan haka sai ka kara gaba can inda ka fito."

Farouk ya yi murmushi kawai ita kuma ta shige shagon tayi siyayyarta sai da ta gama sannan ta fito.

Farouk na tsaye har ta kamalla ta fice bin bayanta ya yi har suka yi nisa daga kasuwar juyawar da za ta yi ta gan shi yana binta tsayawa ta yi ta ce "Pourquoi tu me suis ?" ( Me yasa ka ke bina?)

Farouk ya shafa gashin kan shi ya ce "Parceque je t'aime et je peux tout faire pour t'avoir." ( Soboda ina sonki kuma zan iya yin komai dan na sameki."

Zeeyter ta gyara tsayuwarta ta ce "Idan ka ga ka sameni ni to sai idan ba a hayacina nake ba."

Farouk ya matsa kusa da ita ya yi kasa da muryar tare da kai hannunsa yana kokarin taba mata baya.

ta rike da sauri.

ya nuna da yatsa yana "Wannan surar taki tawa ce ko kin ki ko kin so mu zuba mu gani."

Tsabar takaici sakar masa hannu tayi kawai tai tafiyarta shi ma ya kama gabansa ban da kule-kule ba abun da yake azuciya.

Yana komawa masaukinsu ya zube akan lafiyayyun kujerun da aka kawata falon dasu Deejarth ce ta ce "Farouk daga ina haka daga zuwanka ba hutu sai ka shiga gari."

Haiydar ya yi hanzarinta ya ce "Ai kin san sa baya son zama guri daya kullun shi ne nan shi ne can,kamar mai sabuwar basir."

Zahra ta ce "Ni fa bana ganin laifin shi nima dazun da ya fita dan ina a gajiye ne da ba abin da zai hanani bin bayanshi."

Dukanin su suka yi Dariya.

Farouk ya ce "Rabu dasu Zahra ai zama guri daya bashi da anfani ga Da namiji to yau fitar da nayi ba karamin kamu nayi ba." Ya karasa maganar yana gyara zama.

Haiydar ya ce "Haba dai bamu labari mu sha." Duk suka gyara zamansu Khaleel ma da yake daining yana cin abinci ya ajiye ya taso da sauri ya ce "Bari nima na matso kusa ayi dani."

Ran Zeeyter a bace ta isa kamfani duk kayan da ta siyo ta ba ma'aikatanta ta shige offishinta ranta a bace ya ke da abin da Farouk ya aikata mata,duk da cewa wani Ɗa namiji bai taba nuna mata soyayya ba Amman wadda ya nuna mata maimakon ta ji dadi sai tarin takaici da ya cika mata zuciya.

Tashi ta yi tare da cewa "Allah ya hadani da kai wata rana sai ka sha mamaki zan nuna ma ni ba Kanwar lasa ba ce ."

Fita tayi daga offishin

ta shiga gidan marayu sai da ta tabbatar komai na tafiya daidai kafin ta shige gida، wanka tayi ta shirya cikin wata yagallaliyar doguwar riga da taji jiki iyaka gwiwa ta fito tsakar gidan kennan sai ga Harira da lemo a hannunta ta ce "Zeeyter ga lemo da na hada dazun kowa yasha shi ne na ajiye miki rabonki."

Zeeyter ta karba tare da sakin Murmurshi ta ce "To na gode Harira Allah ya bar zumunci."

Da "Ameen." Ta amsa tare da sakin wani munafukin Murmurshi kafin ta fice.

★★

Faruk ya basu labarin haduwarshi da Zeeyter duk sun zuba ido suna sauraren shi, Deejarth ta ce "To da ka barta ta tafi ba tare da ka samu adireshinta ba ko number wayarta ya za ka yi kenan?"

Ya ce "Ai kar ki damu ina ji a jikina zamu sake haduwa nan ba da jimawa ba,ita din ta Mussamman ce ga wanda ya fahimta kadai just na yarda ne da abun da idanun suka gani ."

Khaleel ya ce "Yanzu duk akan wannan ne ka samu cikin zumudi haka ." Yaja tsaki ya tashi ya bar gurin.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.