Free chapter · Read without an account

CHAPTER 25

by Aisha Sani Abdullahi · 5STARS CHRONICLE Book 1 YEL

("Madame In ba matsala ina son mu hada harkallar kasuwanci tsakanina da naki companin ma,na yi mamaki ace akwai masu fasaha da tunani irin naki duk da kasancewar ki mai kananun shekaru, kin birgeni kuma dukkanin tsarin ki ya birgeni.")

Karaf Farouk ya katse masa magana da, "ba yanzu ba wannan sai munyi tunani."

Dukansu kallon screen din suka yi a tare , ZEEYTER ta ce, "Yes Sir Yadda Farouk din ya ce dai."

Wani irin dogon Numfashi Haiydar ya yi a zuciyarsa yana hamdala , "Alhamdu Lillah na gode Allah da Farouk bai bar wannan mahaukaciyar ta amsa ba."

Zeeyter ta na ji an sake sauti tuni ta tashi tafara rawa, Elon Musk yama ya bita suna yi tare.

"You're such a dazzling angel, you're damn cute, i love your beautiful eyes. Can you be my girl

Friend?"

("Kina da kyau, sosai fa,ke kyakkyawa ce,ina son idanun ki, zaki iya zama Budurwaata?.")

Ya fada yana kallonta.

Gaɓadaya gaban Farouk da Haiydar fara bugawa ya yi cikin sauri.

Murmurshi ZEEYTER tayi azahiri a ranta kuma tana fadin, "bai san cewa wancen sha-shan bane mijina."

Tsabar takaici ya Haiydar ya kasa dannewa zuwa ya yi ya janyo hannunta yana, "Ana son ganinki."

Shi ko Elon Musk yana, "Wait Baby your phone number Please."

Tuni Haiydar ya figeta suka yi waje ,mota yaje ya turata.

Ya kulle kofar shi ma ya shiga.

Ganin yanayinsa ya sauya ko magana bata iya masa ba sai bi da ido.

Ban da maganganun da Elon Musk ya yi ba abun da ke yawo a zuciyar Haiydar, "in ban da son Zuciya mutumin da yake kera motocin wuta ina ruwansa da petur." Bai san lokacin da ya furta hakan a zahiri ba.

Suna zuwa gida cancak ya dauketa bai dire ko ina ba sai akan gado, fara rabata da kayanta ya yi, kasancewar ita ma tana buƙata biye masa tayi nan take suka lula cikin wata duniyar.

Sai da suka yi mai isarsu.

Ta tashi zata tafi kenan ya janyota,ya kara kwanciyar da ita akan kirjinsa.

Duk mutsu-mutsunta sai da ta gaji ta bar shi.

A haka ta kwana suna jin ɗimin jikin juna.....

Da asuba ita ta fara farkawa a hankali ta sabule a jikinsa taje tayi wanka tayi sallah ta dawo bai tashi ba.

Ruwan sanyi ta dibo a fridge ta watsa masa tana, "Sai atashi ayi Sallah ko."

A firgice ya tashi yana kallonta ya yi tsaki .

Ita ma tsakin tayi ta harare shi.

Bangaje juna suka yi,ya nufi toilet ya yi wanka ya yi alwala kafin ya yi sallah.

Jin motsin mutum tayi agidan.

Ta fara duddubawa amman bata ga kowa ba.

Ji tayi kamar an fita, hakan yasata karasawa.

Tana zuwa daidai kofar shiga falon aka buga mata wani katon abu a goshi, nan take ta sume.

Haiydar na fitowa ganinta a kwace ya yi tsaki yana, "Yanzu haukar har da asuba ma tashi take?."

Ya ji shiru.

Kara gyaran Murya ya yi yana, "Ga Kadangare nan ai, Allah sa ya shige miki cikin riga."

Shiru har yanzu ba magana.

Matsowa wajen ya yi yana tunkurinta da kafa, "Kee,keee,dallah tashi."

Ganin ba alamar motsi sai numfashi ya yi saurin matsawa daf da ita.

Gani. Ya yi ta suma,ga kanta jini na fita.

Kallon wayarsa ya yi,karfe shida ne na safe.

Cikin hanzari ya duba number doctor ya kirasa.

Gabadaya ya firgice.

Dagata ya yi ya maida kan gado,kafin ya dauko wani kyalle ya daure mata goshin,amman duk da haka jinin bai daina zuba ba,idanu kawai ya zuba mata yana binta da kallo.

Shigowar likitan ne ya dakatar da shi,cikin sauri ya fara mata taimakon gaggawa jinin da ke fita ya tsaya.

Kafin ya mata allure

Kasa fita ya yi kawai ya zauna yana kallonta,ko kofar gida bai je ba bare office din.

Idonshi na kanta duk motsi gani yake zata farka.

A hankali ta fara bude idonta,wani irin radadine ya lullubeta ta dafe kan tana wash.

Da sauri Haiydar ya matso yana, "Lafiya? Sannu koma ki kwanta,me kikeso zaki ci?"

"Bakomai." Kawai ta furta tana kara dafe kanta.

"Aa ba ki ci komai ba tun safe ki fada abun da kikeso zan miki yanzu,me ki ke so? Za ki sha ko custard ne?"

Girgiza kai tayi tana, "Sai dai kamun tuwo."

Zaro ido Haiydar ya yi domin mai'aikin bata nan, shi kuma bai san yadda zaiyi ma ya yi tuwo ba.

Kuka ta fara tana, "Tuwo nake so ni,na ce tuwo nake so."

Babban tashin hankalin Haiydar shine ya ga mutum na kuka, musamman in bai da lafiya

Nan da nan ya kara birkicewa .

Kitchen din ya nufa kawai yana kare masa kallo, ya ma rasa ta ina zai fara can kuma tunanin zahra yaxo masa,nan take ya kirata.

"Madame tuwo nake so a mun hanyar da zanyi ko ince a koya mun inyi." Haiydar ya fada

Dariya Zahra ta yi tana, "Da alama mun samu karuwa kenan."

"Wani karuwa,kukam ai saidai raguwa indai kune, taimaka mun Don Allah."

Zahra tayi dariya ta ce, "Owk Mu shiga App in kiraka ina nunama kana yi."

Shiga sykpee app suka yi duka suna video call zahra na nuna masa komai yana yi

Tuwon semo ya yi, miyar vegetables.

Gabadaya ya yi wujiga-wujiga ban da dariya ba abun da Zahra ke yi, har suka gama .

Zuba mata ya yi a Plate.

Har ta fara barci ya tada ta.

"Dallah ta shi ki ci."ya fada.

Galla masa harara ta yi, tana kokarin tashi amman ta kasa.

Tsaki ya yi ya dafata ta tashi.

Ya ce, "Meya sameki garin ya kika buga kai?"

Kau da kai tayi tana, "Oho Waya sani,jin motsi nayi naje dubawa aka buga mun abu."

Tsaki ya kara yi, "Allah kara,yanzu haka ma garin neman jarabarki ne kika taro wanda yafi karfinki,maganinki, Allah sa gobe ma akuma." Ya fita yana mita.

"Mahaukaciyar Yarinya kawai."

Ta ce, "Eh din naji dai ,ina ruwanka dani,kuma wallahi koma waye sai na rama bara inji sauki."

Tuwon ta fara ci,ba karamin dadi ya mata,duk da cewar Haiydar bai iya tuwo ba,amman yinsa na yau tamkar wanda ya saba yi.

A falo ya zauna.

Tana gama ci taji dan karfi hakan yasata tashi ta fito falon.

Kokarin faduwa take da sauri ya tashi zai tareta ,bigesa tayi ta dafa bango hada ido suka yi tare da sakin tsaki a tare ya shige daki ita kuma tayi hanyar waje.

Zuwa tayi ta zauna a farfajiyar gidan ga goshi duk bandeji,kuma jiki ba kwari Amman hakan bai hanata zuwa ba, kamar ance ta juya bayanta wani katon kadangare sak wanda haiydar yasa mata a gado, bata san lokacin da ta zura aguje ba, daidai da fitowar Haiydar kyam ya kankamesa.

*MUN FARA BIKI ZA ANA MUN HAKURI DON ALLAH,WANNAN MA DUK A TSATTSAYE NA YI WALLAHI*

★★★

Da Mamaki Ya Kalleta Yana , "Lafiya? Mene ne Ya Faru?"

Nuna masa kaɗangaren ta yi da hannu.

Yana kalla ya kyalkyale da dariya, sake shi tayi cikin sauri tana galla masa harara.

Ƙarasawa ya yi wajen ƙadangaren ya dauka yana kokarin binta, fallawa tayi aguje shi ma ya bita,kan ya karasa har ta kulle kofar fallon.

Kamar wasa taki budewa har dare ya kara yi sosai.

Nocking kofar ya fara yana, "ki bude mun mana, Wannan wani irin wulakanci ne?"

Zeeyter ta ce, "ka shirya kwanan waje shi yafi ma,nikam ma barci zan yi,waya sani ma ko kaine ka turo da asuba akashe ni,don mugunta kawai."

Ba yin da Haiydar baiyi ba,amman sam Zeeyter taki bude kofa,daga karshe ma kida ta sake, tana takar rawa,ta manta da batun rashin lafiya.

Ga ba Keyn dayan bangaren agunsa bare ya bude ya shiga,duk suna ciki, ganin dare ya yi sosai ga sanyi ne,ya sa shi shiga motar dole ya kwanta.

Ita kuwa tana leƙensa ta window tana dariya.

Ba yadda ya iya haka ya kwana a waje.

Asuba na yi ta fito ta bude kofar kan ta koma.

Sai da yaje massalaci ya dawo ya ga kofar abude.

Cikin Ɓacin rai ya shiga yana, "Mahaukaciya kawai."

Ko kulasa ba tayi ba,ta shige daki tana dariya.

Tana shiga ta dau wayarta tana duba sakonni kasancewar ta kwan biyu ba ta hau online.

Sakon Deejerh ta fara gani, "Hi Mrs Haiydar,Ina fatan komai ya tafi daidai wannan kuma dinner gown din tayi miki?"

Murmurshi Zeeyter ta yi sai da ta gyara zama kafin ta fara yi mata reply, "Yes Thank you so much Madame, Kalamai ko furucina sunyi kaɗan wajen yadda zan nuna miki farincikina tare da godiyata, na fahimci abu guda,ko ince na karu da wani abu sanadin,ban damu da ado na kaya ba, bare kuma kwaliya,suturta jiki da Ado ba karamin kankaro daraja gami da ƙima yake ba ga rayuwar 'Ya mace, In kin gyara cikin Kasancewa mai tsaftace wajen ma ko da kuwa ba ko yaushe hakan zai samu ba,shigar kece raini,ta alfarma ba ruwanta da kyawun fuska, godewa Allah da yadda ya yi ki,ki gyara kanki duk muninki in mutane ɗari na kusheki watarana za asamu ɗayan da zai miki yabon da sai ya kore dukkanin masu kushiyar,ba wai na ce hakan da nufin zan dau yabo insa araina wai an yabeni bane aa,amman tabbas ni kaina na ji canji a jikina,kuma na ji dadin hakan,sannan daga yanzu zan fara shiga Mai kyau gami da tsari,ba sai mai tsada ba,iya kudinka iya shagalinka,na yarda da cewa indai zaki Kasance cikin shiga mai kyau babu wanda zai miki kallon wulakanci a duk inda zaki kasance ko da kuwa kin kasance karama cikinsu,ina godiya sosai da kulawar ki gare ni,kin zarce kawa sai dai ince Yaya,Ina sonki da dukkanin numfashi na."

Deejerh ta ce, "Ma sha Allah, Hakan nake fata kuma nake son ji, daga yanzu zanyi kokarin ganin duk na tsara miki irin yanayin kayan da zakina sawa, na wajen taro,dinner har ma da zaman gida."

"Woooo can't love you less, Allah ya bar zumunci na ji dadi Sosai."

Sakon Farouk ta nufa da ya ce, "Hello Friend kwana biyu ko an samu karuwa ne an manta damu?"

. Sai da tayi tsakin nan dai na fama kafin ta ce, "Aa Karni aka samu ba karuwa ba ka ji ko, Taya ma zan haihu da Wannan banzan taɓ."

Dariya ya yi yana, "Adai juri zuwa rafi wataran tulu zai fashe, yanzu dai ince lafiya kwana biyu."

"Ba Lafiya fa in fadama har gida aka zo aka mauje mun goshi sai da na suma,amman wallahi nayi kudirin nemo koma wane ne kuma sai na rama, koma wane ne, Mussamman ina zargin wannan Dpon dana fada ma mai katon ciki."

Dariya sosai Farouk ya yi kafin ya ce, "Ke fa Mazan naki ma da yawa,ga shegen neman jaraba."

Hira suka sha Sosai.

Zahra kuwa sakon barka da jiki ta mata,tare da bata shawarwarin kalan abincin da ya kamata tana ci domin lafiyarta.

Group din su ne Farouk ya yi messeges da.

"Hi Guys ku fito, ina da magana fa, na ce ina da magana a marmatso."

Sai da ya tabbatar dukansu sun fito kafin ya ce, "Eheen ganin cewa Haiydar ya yi aure,mun karu sannan nasan cewa dukkaninmu gaba kowa zai iya yi, hakan yasa na yanke shawarar yi mana zanen gidajen da zamu tsara kowanne yadda duk inda zamu kasance muna da wadataccen wajen sauka kamar gidan Haiydar ba tare da munje hotel ba, kai tsaye muna kasancewa anamu a kowacce kasa."

Khaleel ne ya fara magana, "Bravo! Tabbas na ji dadin wannan hangen naka, kuma ya yi matukar gaske muna da bukatar waddataccen wajen zama a kowacce kasa zamu kasance, hangenka ya yi, nikam ina marhabun da shi."

Deejerh ta ce, "Ma sha Allah Aboki nima dai ina baya 💯."

"Nima gaskiya na ji dadin hakan." Cewar Zahra.

Haiydar ya ce, "Wait! ku dakata fa,wai hakan na nufin ni baza amun wani sabo bane?"

Dariya suka yi dukansu kafin Farouk ya ce, "Oh kai da tamu daban ina so muyi magana amman ba yanzu ba tukun,And Deejerh zan turo miki komai da komai ki duba kiga kudaden da Yakamata mu kashe a kowanne duka, sannan ki turawa Khaleel da Zahra suyi Aproving."

"Owk Sir." Cewar Deejerh

Haiydar ya ce, "ni fa ban yarda ba da sake."

Sai a lokacin tsilif Zeeyter ta yi tagging kan maganar Haiydar, "Gaskiya ba mu yarda ba fa,muma amana sabon gida."

Dariya suka yi Khaleel ya ce, "Iyee wato abun taron dangi ne kin shigarwa mijinki."

Zeeyter ta ce , "Eheen He Is My Sunshine."

Karaf Haiydar ya ce, "Yes Bright Eye."

Tsokanarsu Su Deejerh da Zahra suka fara.

Sunata kare juna kamar masu soyayyar gaskiya da arzik ana gama chatting kowa ya fito zai tafi office suna haɗa ido suka gallawa juna harara tare da sakin tsaki,kamar kullum harda bangaje juna.

Fita suka yi shi ya hau motarshi,ita kuma ta ɗane kekenta,kowa ya kama hanyarsa.

Tana tafiya tana kalle-kalle sai jinta tayi tim a ƙasa, da sauri ta tashi ta karkade jikinta kafin ta ci gaba da tafiya.

Ba inda ta nufa sai Police station

Tana zuwa ta wuce wajen Dpo.

Rike kwankwaso ta yi tana, "Wallahi wallahi wallahi ka ji sau uku na rantse ko? To in baka fita a harkata ba sai nayi sanadin barinka aiki, banza kawai,wawa mai katon ciki."

Wani kofir ne da ke wajen ya daga hannu da niyar dakatar da ita.

Tsawa Dpo ya masa yana, "Get Out,I said Get Out."

Ya karasa maganar yana nuna mai hanyar fita.

Matsowa ya yi daf da ita yana

"Tu seras surpris si dey c'était moi."

(Za ki sha mamaki in dai nine muje zuwa)

"Entre moi et toi on verra celui qui sera surpris."

("Tsakanin ni da kai ai za aga wanda zai ba da mamaki.") Karasa maganar tayi tana yin tsaki ta fice.

Binta ya yi da wata irin Dariyar mugunta har ta fice.

Cikin Bobiel ta wuce kai tsaye Makaranta sai da aka gama masu karatu kafin ta je gidan Marayu suka gaisa da Madame Ayshe da yaran kafin ta nufi gidan mai.

Tana zuwa Halliru ya ce, "Barka da zuwa Madame, Une bonne nouvelle (ga labari mai dadi)"

Da Murmurshi ta karasa tana, "Ma sha Allah, Tun da naga fara'a sosai a fuskarka na tabbata kam akwai labari me dadi meya faru?"

Halliru ya ce, "Mun cike Form din Humanitarian Award da za a gudanar a singafur kuma mun samu damar tsallakewa a takaice dai ana bukatar kasancewar mu a singafur."

Wani irin tsalle Zeeyter ta yi tana, "Me ma zan ce ne? Lokaci na farko da zan fita cikin kasata kuma sanadin nasarata, tabbas Allah baya barci,kuma maji rokon bawansa ne aduk inda zai kasance, Alhamdu Lillah, Halliru Allah kara basira da hazaka,ina jin dadin kasancewa da kai matukar gaske,babu hassada bare kyashi alamuranka,abubuwa da yawa sai dai inji labari daga baya ka aikata ba tare da sanina ba,in sha Allah indai ina numfashi bazaka zubda tawayen takaici ba sai dai na dadi."

Office din Haiydar ta shiga ta fara duba takardu.

Tunawa tayi kamar ranar taron nan ta bar takarda a Office dinsa.

Hakan yasata daukan kekenta ta nufi company.

Tana zuwa ta fara gaisawa da masu gadi tana Murmurshi

Suko sai kallon keken suke suna mamaki.

Office din Haiydar ta wuce kai tsaye zata shige,wani matashi ya yi saurin dakatar da ita.

"Excuse Mah, ki dakata ba a bada izinin shiga ba, a takaice ma yau ban jin cewa Oga na da wani ko wata bakuwa."

Ya fada.

Kallon shi tayi sama da kasa tana, "ko ba Ogan ba? Na ce ko ba Oga ba? Na bi Oga da gudu ba takalmi, dalla matsamun in wuce kana nan da kai kamar kwallon giginya."

Ta karasa maganar tana janye shi daga kofar.

Shima fara kokarin tureta ya yi yana, "Ke baki da hankali ne? Ba ki ji me na ce ba?"

Jin hayaniyar tayi yawane ya sa Haiydar fitowa.

Daidai lokacin da Zeeyter ta makawa wannan matashin mari.

Ya daga hannu zai rama kenan cikin zafin rai Haiydar ya rike masa hannun yana, "Wawa kawai."

Jan hannun Zeeyter ya yi,ya shigar da ita ciki sai da ya kulle kofa kafin ya fara ruwan bala'i, "me zai sa ki tsaya cacar baki da shi? Ba za ki kirani kice kina zuwa ba ko kinzo sai kin nuna halin naki kin bani kunya cikin mutane? Wai ke mahaukaciyar ina ne?"

Tsaki tayi tana fisge hannunta agunsa tana, "Mahaukaciyar gidanka mana,in ba ta gidanka ba ta ina ce,ko ince dukanmu ai mahaukatan ne."

Takardun ta fara daukowa tana dubawa .

Haiydar ya ce, "Ga Keyn Office dinki nan kije can ki gama dubawa kar ki takuramun anan ni."

Murguda masa baki tayi tana, "Ba zan fitan ba,anan zanyi,in ka gaji kai ka je nawan kayi."

Tsaki ya yi ya ci gaba da aikinsa a system kawai.

Tana aiki tana kallonsa, can ta ga ya yi tagumi yana zufa.

Maganar zuci ta fito fili, "Oh Allah kusan wata kenan ina kokarin haɗa part din motar nan amman na kasa kash."

Bai san maganarsa ta fito ba sai ji ya yi Zeeyter na, "Mu gani."

Tsaki ya yi afili yana, "Dalla matsa mun ni da gani me zaki iya."

Bata kula shi ba ta fisge Laptop din tana dubawa ta hada mai bangaren da ya kasa kafin ta ajiye masa.

Da mamaki yaga tayi aikin da ya kasa yi awata guda amman ita cikin minti ɗaya tayi ta gama, kallonta ya tsaya yi can kuma ya kawar da kai yana kara jin mamaki.

Ita kuwa takardun ta hada waje guda, har taje kofa zata fita,ta dawo mintsilinsa tayi kafin ta fice da gudu shima ya bita.

Ya ma manta ba a gida suke ba, sai da sukaje tsakiyan compaynin suna guda kafin ya ankare ganin an fara kallonsa.

Kunya yaje ya koma office.

Ita kuwa Dariya tayi tana, "Ai da kazo Wallahi."

Gidan mai ta koma,ta samu Halliru zai je masu visan tafiya singafur saboda za su tafi da wuri ana saura kwana biyu ko ɗaya kan taron domin tsara yadda Shagalin zai kasance.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.