Free chapter · Read without an account

CHAPTER 31

by Aisha Sani Abdullahi · 5STARS CHRONICLE Book 1 YEL

"Ai ko ba mai taɓa Anushka da Anitha ina gidannan." Deejerh ta fada.

Dariya suka yi dukansu.

Zahra ta dubi agogon hannunta, "Na san yanzu jirgin su Haiydar ya kusa sauka,kuma yana zuwa food Master zai fara maganar abinci bara in tafi kitchen byee."

Sai alokacin Farouk ya yi magana, "Umm wato mutuminki kadai zaki ma girki mu da muka zo ai sawa kikai aka mana,mun ga bambanci zamu rama."

Zahra tayi dariya tana, "eheeen abokina na musamman ne, zanyi komai domin shi."

"Eheen ni fa?" Khalil ya fada

Dariya tayi kawai ta wuce kitchen din tana shiga.

NASI GORENG

Indonesian Fried rice.

Oil ta fara sawa a a tukunyarta da ya soyu ta dauko kwai kwaya ɗaya ba tare da ta kwaɓa ba ta zuba yana soyuwa ta cire shi Gaɓadaya ba ta juya ba kuma bata bari ƙoduwar ta samu matsala ba,ta cire ta sa shi agefe cikin Plate.

Kafin ta dawo da sauran mangyadan cikin ta zuba galic,ta juya kafin tasa Red chili da onion sai da ta juya su sun dauko soyuwa kafin ta dauko tafassshiyen neman kazanta (chicken) wanda aka yayyakan shi ta zuba aciki,ta ci gaba da juyawa sai da ya dauko soyuwa kafin tasa kecap manis ta kara juyawa tukun ta dauko tafassshiyir shinkafarta ta zuba aciki,ta kara zuwa kecap manis tukun ta juya su a tare ta zuba shrimp paste tukun ta sauke ta dauko yankakken Schallits da tumatur, da pepe ta zuba akai.

Wannan soyayyan kwan ta dauki shi ma ta ɗaura akai.

A fili ta ce, "Ma sha Allah am done with my nasi goreng."

Ba karamin kyau shinkafar tayi azahiri ba bare kuma in ankai baki.

Tana kammalwa daidai da saukan jirgin su Zeeyter a Jakarta Indonesia kafin suka hau jirgin Balikpapan.

Suna isa Direct mai taxin da zahra ta aiko ya daukesu.

Tun daga wajen gidan Zeeyter na hango su Noor Anitha Da Anushka suna wasa ta cilawa Haiydar jakar hannunta ta nufi gunsu.

Tsaki ya yi kawai ya shige jiki

Tana zuwa ta ce, "Hi Friends nima zan iya shigowa ayi wasan dani."

Noor ne ya fara washe baki yana Kallonta , "Why Not Ant?"

Haiydar ya shiga ciki dauke da jakar Zeeyter mai Farouk da deejerh za su yi ban da dariya.

"Wai har abun ya kai ga haka ne? Ina gimbiyar tawa naga sai jakarta." Cewar Farouk.

Haiydar ya bisa da harara ba tare da ya ce komai ba.

Khaleel ya dubesa yana, "Welcome Aboki."

Mika masa hannu ya yi suka gaisa kafin ya kalli Zahra yana shafa ciki.

Kan ya yi magana dukansu suka hada baki, "Food."

Dariya duka suka kwashe, deejerh na , "Nikam barin je gun Kawata."

Ta karasa maganar tana fita.

Zahra ma da ta kawo masa abincin ta bi deejerh.

Wasan su suke sosai cikin nishadi.

Deejerh na zuwa Zeeyter ta rugumeta.

Zahra ma tazo suka rugume juna suna yi mata Barka da zuwa.

Zasu shiga ciki Anushka ta bata rai, "Mom kin dauke mana Anty muna wasa."

Murmurshi Zeeyter ta yi tana, "Sorry Babyna i will be back ku ci gaba ina zuwa ko? Zan dawo muyi wani wasan."

Haiydar ya ƙafe ban da zura abinci ba abun da yake.

Zeeyter na zuwa ta dauke Plate din.....

A fusace Haiydar ya dago yana kallonta.

"Meye hakan? Ki bani abinci na naci am hungry ho."

Zama tayi akan daining din ta fara cin na san.

Tsaki ya yi ya tashi zai fisge.

Da gudu ta tashi, tana gudu yana binta.

Su Zahra sun zama yan kallo da dariya.

Su Noor ma biye masu suka yi suka dunga gudu suna zagaya gidan, sai dai suka gama galabaita Haiydar kafin ta tsaya tana haki, "Acici Mala'ikun tauna ga shi."

Tsaki ya yi ya karba yana, "Zan kamaki u wil explain."

Zahra ta ce, "ba za dai a fasa halin ba."

"Tom And Jerry ba za mu kunna Tv agiddanan ba har mu bari tunda kuna nan kallo za mu na yi kyauta."Khalil ya fada.

Dukansu suna dariya.

Zubo mata nata abincin Zahra tayi tana, "sai abar abokina ya yi kiɓa kowa ya ci nasa."

Zeeyter ta ce, "Indai abinci zai sa abokin ki kiɓa ai da tuni ya dade da yi har mun kasa daukansa ma."

Haiydar ya dago ya kalleta yana, "eh anji ai gwanda mutum ya zauna dan daidai ba kato kamar biredi ba,kika sa wasa sai na sace ki inga da kibar da zaki na taƙama."

Zeeyter ta yi shewa, "Osheeey mu gani a ƙasa."

Cin abinci suka yi duka cikin nishadi kafin suka shiga daki domin yin wanka suyi sallah.

Haiydar na idar da sallah ya fita Falo.

Deejerh ta shiga ɗakin domin ba Zeeyter kayanta.

Riga da wando ta duba aciki tasa, ba karamin kyau ya yi mata ba.

Sai da ta feshe jikinta da turare kafin ta fita falon.

Tana fita duka suka zuba mata ido.

Farouk kasa hakura ya yi,ya taso yana, "Wooo Gimbiyata U Look So Cute,kin kalli kanki kuwa kafin ki fito."

Tsaki Haiydar ya sake yana kau da kai.

Suna hadu ido da Zeeyter ta masa sigina ka fin ta ce, "Thank You So Much Darling, Nawa ka sai wankan?"

Farouk ya ce, "Umm nawa kike so?"

"Aa ai kai zaka fada in baiyi ba sai in fada ayi ciniki." Ta fada tana kara kallon haiydar cikin yanayin zolaya.

Farouk ya ce, "To ai ni ban ma da kudin iya siyan wankanki don yafi karfin ko nawa zan ce,amman kin saida a 1hundred Dollar?"

Kafin Zeeyter tayi magana karaf Haiydar ya ce, "ni kuma na siya a 3hundred Dollars."

Dariya duka dakin suka yi Zeeyter taje ta rungumi Haiydar tana, "Thank you Sunshine."

Ta mintsinesa kafin ta sake shi tana dariya.

Tauna baki ya yi irin zaki gamu dani dinnan.

Khalil ya ce, "To Farouk ka gani dai ? Ogan gimbiya ya kwace abarsa ya siye Kwalliyar tunda daman tasa ce, sai ayi zuciya a nemo asalin gimbiya."

Dariya Farouk ya yi kafin ya ce, "Eheen ko ma wace ce zata zo ai bazata taba amsa sunan Gimbiyata ba, Gimbiyata ta Mussamman ce all over d world."

Hira suka yi sosai Zeeyter na tare da su Anitha suna ta hira ita ma tana basu labarai suna hira.

Dare ya yi Haiydar na so su tafi daki Zeeyter kuwa fir taki sai kara jan su Noor take da hira suna dariya.

Suna haɗa ido da haiydar ya mata alamar su tafi sai ta ce aa domin ta gane take-takensa.

Daga karshe ta ce, "Oga na ga kamar barci kake ji kaje ka kwanta mana."

Tsaki ya yi yana galla mata harara, "ni na ce miki ina jin barci?"

Khalil ya tashi yana miki, "What Ever ni dai barci nake ji,kun san ban cika juran zaman nan ba,gudnyt Friends, gudnyt Anushka,Noor And Anitha kuma dare ya yi aje ayi sleep."

Karaf Noor ya kankame Zeeyter yana, "Dad ni agun Anty zan kwana."

Wani irin takaici Haiydar ya ji kaman ya falla masa mari.

Khalil ya ce, "Aa Kabar Anty da Uncle su huta ka je dakinku maza ku kwanta."

"Oh oh ka bar shi zamu kwana tare da babyna." Zeeyter ta fada tana kallon haiydar.

Tsaki ya yi ya tashi ya tafi daki don takaici.

Khalil ya ce, "Ok gudnyt Oll duk yadda kuka yi ma daidaine." Ya fada yana shigewa ɗaki.

ASHIRIN DA DAYA

Zahra ce ta dauko kayan barcinsu duka ta sa masu,kafin Zeeyter ta dauki Noor suka tafi ɗakin.

Haiydar na jin shigowarsu ya yi lum kamar ya yi barci, Zeeyter ta kwantar da Noor tayi addu'a ta shafa masu duka kafin ita ma ta kwanta.

Can Haiydar ya fara laluben taɓo Zeeyter.

Noor ya fara, "Aunt, Aunt....

Kunshe dariya Zeeyter tayi tana, "Mene ne Babyna?"

Haiydar ya kara wani shahararren tsaki ya juya.

Gaɓadaya a takure ya yi wannan barcin domin yana sa hannu da niyar taɓa Zeeyter Noor zai motsa ita kuwa me za ta yi ban da dariya.

Asuba nayi ya tashi fuska a murtuke, suna haɗa ido da Zeeyter sai dariya.

Ko da suka zo breakfast suna hada ido sai ya galla mata harara.

Deejerh ta lura da hakan ta ce, "Wai yau Love din na harara da dariya ne? "

Zeeyter ta ce, "Kin san in mutum bai samu ya yi barci ba komai zai iya yi, watakila rashin barcin ya kawo ciwon harara ko Sunshine?" Ta fada tana kallon shi.

Tsaki ya yi yana, "koma miye ina ruwanki?"

"a'ah fa abar batun nan naga abokina ba sauki yau, ba ku ga ko Kula kowa baiyi ba yau sai zura food yake aciki."Khaleel ya fada yana dariya.

Farouk ya ce, "Gimbiyata say Sorry to food Master,in ba haka ba yau mun shigai da ɓata rai da tsaki."

Dariya Zeeyter tayi ta daura hannu a kunne

A sanyaye ta ce, "Am so Sorry Sunshine."

Ko kulata baiyi ba ya tashi zai koma falo ya zauna.

Sai da ta bari yaje ya zaune taje tana masa cakul-kulu dariya ya fara ba ƙaƙƙautawa , "Ki bari Don Allah ki bari bana so."

Zeeyter ta ce, "In ka ga na bari to ka ce ka daina fushi."

Cikin dariyar ya ce, "Na daina Stop it please bright Eye."

Tukun Zeeyter ta daina.

Sai da suka gama break duka kafin suka fara shirin tafiya office domin tattauna da companin da zasu tallafawa.

Zeeyter ta ce ita ba za ta je ba zata zauna agida Anushka.

Har bakin get ta raka su tana masu byeebyee zasu shiga mota, Haiydar har zai shiga ya dawo ya mata kiss ita ma kiss din ta mai tana, "Thank you Sunshine,Byee byee Adawo lafiya."

Daga nesa Farouk ya ce, "Gimbiyata ni fa? Wato an fara mana wariyar launin fata, dole mu rufe ido muyi aure."

Murmurshi Zeeyter tayi ta ce, "Byeebyeer My Dear Adawo lafiya kai ma ko,amman The Kiss Is Just For My Sunshine."

"Hakan ya mun kyau Gwanda ya yi zuciya shi ma." Khalil ya fada yana dariya.

Deejerh ma ta ce, "Nah Love."

Zahra kuwa dariya kawai take har suka shiga mota kafin suka dau hanya.

Zahra da Khaleel mota ɗaya

Deejerh, Farouk, Haiydar ma mota ɗaya.

Kwana biyu suna tafiya office sai dai abar Zeeyter da su Noor sai da suka kammala komai kan suka shirya fita shaƙatawa.

Gaɓadayan matan irin shiga ɗaya suka fito harda su Anushka da Anitha .

Noor ma nasu iri ɗaya da na su Haiydar.

An fito za a tafi Haiydar ya riƙe hanun Zeeyter da gudu Noor yaje ya bige yana, "Uncle Aunt na ne,ba naka ba,ka bar mun Antyna."

Haiydar na dariya ya ce, "Oh Allah Noor ina ganin karfin hali, Shikenan na bar maka Antyn ka."

Suna fita suka nufi water falls.

Anan suka wuni suna shaƙatawa tare da zagaye wajen gwanin ban sha'awa.

Suka zo zasu shiga ruwa Deejerh ta ba kowa kayan ruwansa, na Zeeyter daban saboda yanayin jikinta amman ba karamin kyau ya yi ba.

Karba suka yi duka kowa yaje zai sa kayan, ban da Khaleel da bai iya ruwa ba,kallonsu kawai yake yana dariya.

Zeeyter da Haiydar suka ja gefe zasu canja kaya dake ba mutane sosai agun.

Zeeyter na cire kaya Haiydar ya firgice ganin surar jikinta gabadaya a bayyane kuma azahiri ga shi daman yana hannu kwana biyu.

kokarin riketa ya fara yana romance da jikinta.

Zeeyter ta ce, "Mene ne hakan? Ka bar ni insa rigar nan mana,awaje muke fa, Please ka bari bana so."

Ina Haiydar yasan tana yi ya dage Gaɓadaya ya susuce.

Dakyar ta samu ta zame jikinta ta sa rigar,tukun shi ma yasa ,gaba ta fara yi kafin ya dawo har ta shige ruwan.

Abun mamaki duk tafiso iya ruwan, ita da Farouk ne gaba domin shima ya mugun iya ruwa.

Gaɓadaya sai ɗaukin wajen suke saboda yadda ya tseru, musamman yadda ruwa ke gudu.

Sai dare suka nufi night market.

Suka shiga Batavia Restaurant Cafe.

Suna shiga Haiydar ya fara washe baki yana zuba abinci, soto bandung,fried fish, chicken wings,teh poci,beef rending Off, prown crackers with weet soya sauce, tegallahang rice terrace duk a ya hada a Plate guda sannan yaje gun Sea Food ya gasa shi ma ya dibo.

Su ko Gaɓadaya daga tegallahang rice sai chicken wings,da prawn crackers with sweet soya sauce suka sa.

Deejerh ta kelleshi ta ce, "Food Master." Tana dariya.

Haiydar ya ce, "Zahra kin san me yake birgeni da kasar nan taku?"

Zahra ta ce, "a'a sai ka fada."

Ya ce, "Baku da tsadan abinci sam,ko ya kudin mutum yake zai ci abinci hankalinsa kwance."

"Ba dai santi ba kadai ci abinci." Khalil ya fada.

Zeeyter na kallonsa zai ci sea Food ta bude baki, "Oh wannan ma ci ake? Dama nima zan iya ci mana."

Karaf Farouk ya ce, "Me zai hana,nama ne ai kici da dadi,kina zaune da Food Master kuwa ya ci ace kin iya cin komai."

Dariya suka yi Haiydar ya dauko yana kokarin sawa Zeeyter abaki.

Bige masa hannu tayi tana hararar sa.

"Kai dai ka ci da ka saba NIkam ba zan iya ba."

Ranar sai cikin dare suka koma gida.

Suna komawa Haiydar na ganin Noor ya yi barci yaje ya kaisa ɗakinsu da kanshi.

Zeeyter tana lure da shi tana dariya.

Suna shigewa daki ya fara fuskar tausayi, "Please bright Eye Allah da matsala in yau ma kika ce zaki gwarani,ko ma miye ki fada zan miki ina cikin bukata kuma nasan kema kin sani sarai Help Me Please."

Zeeyter ta bata rai, "Ni ban san kana cikin wata bukata ba, Amman ko ma miye ma You have to do something before."

Haiydar ya jura mata ido, "Like?"

Tayi masa sigina kafin ta ce, "Goyani za ka yi mu za ga gidan nan."

Haiydar ya bude baki yana kallonta.

"Eheen If Yhu can't just leave me,let me sleep joor."

Haka Haiydar ya durkusa ba yadda ya iya ya goyata,abun mamaki ba ta yi nauyin da yake tsammani ba.

Haiydar ya tsaya yana, "har yanzu goyon baiyi bane?"

Zeeyter ta yi dariya, "Oyaa kaini ɗaki tom."

Yana direta kan gadon nan take ya fara aika mata da wasu zafafan saƙonni ba tare da ya jira ba.

Washegari

Kowa ya fito amman ban da Haiydar.

Zahra harta kammala breakfast

Khalil ya ce, "Wai yau meke damun mutanen nan ne? Su da suke riga kowa tashi su addabi mutane Amman yau shiru?"

Deejerh ta ce, "Aikuwa Food Master ya yi lum yau ba jin yunwa."

Farouk ya tashi yana,"bara in katse shakku inje in duba su.....

★★★

Yana zuwa ko nocking kofar baiyi ba ya tura kawai.

Zeeyter kwance ajikin Haiydar suna manne da juna barcin su suke hani'an cikin kwanciyar hankali.

Har aransa ji yake dama ace shine ya kasance da Zeeyter mana, ya siɗe bakin takaici ya fita ya ja kofar kafin ya masu nocking, "Mutanen daƙin nan suna nan ince ko sun mutu ne?"

Zeeyter ce ta fara farkawa jin sautin Farouk a kunnenta .

Kallon haiydar tayi wanda ya kankameta tamkar wadda za a kwace masa ita,tunda suka yi wanka suka yi sallah da suka koma barci ya riƙeta ƙyem.

Murmurshi tayi ta masa kiss ta ji ya kara ƙanƙameta yana numfasawa.

Farouk ne ya ƙara nocking yana, "Ina ga yau fa sai mun buge kofar nan."

Zeeyter ta mitsini Haiydar nan take ya bude ido yana hararta tare da kara kankameta , "Sleep Jor."

"Na bi sleep da gudu sai nocking kofa ake ka tashi muje wannan barcin fa,ba ka ga yadda gari ya yi haske bane ko yunwa baka ji yau."

Tashi ya yi ya zauna yana shafa cikinsa, "Kuma ina jin yunwar fa,amman in dai ina tare da ke ai komai mai sauki ne."

Murmurshi tayi tana kokarin tashi ya janyota ta zauna a kunne ya raɗa mata, "I love you."

Yana kokarin fara kissing dinta.

Ya fara fitar da ita a hayyacinta jikinta duk ya mutu ban da tsigar jikin ba abun da ke tashi.

Shigowar Farouk ne ya katse su yana, "Oh My God ko dai yau aka daura maku aurennan ne?"

Zinbir Haiydar ya miƙe yana sosa ƙeya

Zeeyter kuwa mai za ta yi ban da dariya.

Fita Farouk ya yi yana, "Ina ganin sabon salo a kasar nan in ban yi aure ba ina ga wa innan za su kashe ni da takaici."

Zeeyter zata fita Haiydar ya riko hannunta suka fita tare.

Suna zuwa da gudu Noor yaje ya rungumeta yana, "Aunt kar ki bari Uncle ya kwace ki fa,na fiki son shi."

Dariya Haiydar ya yi yana, "Eheen Wato kafi son Aunt dani? Shikenan na bar ma ita zan dau Anushka da Anitha yau fita muyi wasa sosai ban da kai ko my babies?"

Ya fada yana kallon su tare da mika masu hannu su tafa.

Zeeyter ta ce, "Duk inda zaku mu sai muje inda ya fi nan ko my Dear? Kuma shi bai iya goyo ba ai."

Dariya suka yi duka kafin aka fara breakfast din.

Gaɓadaya ko motsi kadan Zeeyter tayi Haiydar na lure da ita,ko ina tayi idonsa na kanta,ko kyakkyawan motsi tayi sai ya ce, "Mene ne? Me kike so?"

Su Zahra da Farouk sun tsaya kallon ikon Allah Haiydar ya canja tamkar ba shi ba.

Ranar agida zasu wuni hakan yasa Zahra ta hada masu wasanni na Shaƙatawa harda basket ball.

Team biyune.

Zeeyter, Khaleel, Farouk sai Noor. A team A.

Team B kuma Haiydar, Deejerh Zahra,Anushka da Anitha.

Gabadayansu kayan sport iri ɗaya suka sa wanda deejerh ta tsara,ba karamin kyau suka yi ba, Haiydar ban da satan kallon Zeeyter ba abun da yake.

Khalil ya ce, "Oga ni fa ban gane maka ba yau, anya kuwa? Madame Oya Tell Me yau me kika ma abokina ya zuzuce ne it seems ba zai bar mu,mu yi basket ball dinnan yadda ya dace ba indai yana kallonki."

Cikin dariya Zeeyter ta ce, "Ask Him Oh Oh nima ban sani ba, haka na gan shi."

"Duk abunnan ni nafi kowa jin zafi ai, Gimbiyata dole ki nemo mun mata ki aura mun, kuna kara samun shaukin son aure." Farouk ya faɗa

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.