Free chapter · Read without an account

CHAPTER 33

by Aisha Sani Abdullahi · 5STARS CHRONICLE Book 1 YEL

Dariya Deejerh ta yi tana, "What Ever,ni birgeni Aboki yake if he didn't show her Love and care then wa kuke so ya nunawa? I wish Abokin Rayuwata ya kasance mai tarairaiya dani, girmama ni,tare da mutuntani Like D way friend is doing."

Zahra ta katse maganar tana , "Love, Love,Love kun isheni da zancen soyayya fa,mu fara wasa kowa ya shirya."

Haiydar ya ce, "Yess Mu za mu cinye In sha Allah." Ya karasa maganar yana tafawa da su Anushka.

Noor ma ya kalli Zeeyter yana, "We Are The winners ko Aunt?"

"Yesss In sha Allah My Dear." Zeeyter ta fada ita ma tana mika mai hannu.

Nan take suka fara basket ball din

Kowa burinsa ya cinye, kamar wasa kuwa aka tashi 4/3

Team din su Zeeyter sun cinye 4

Su Haiydar na da 3

Suna haɗa ido ban da gwalo ba abun da take mai.

Noor ma sai rawa da murna kawai yake sun cinye yanama su Anushka gwalo.

Nan take zeeyter ta sake sauti agun ita da Noor, Khalil da Frouk sai tikan rawansu suke yi.

Da su zahra suka ga abun ba yi suma shigewa suka yi harda Haiydar suna cashewa.

Hotuna suka yi sosai na farinciki kowanne fuska fal dariya.

Tukun suka koma cikin gida,ranar Zahra da Zeeyter ne suka hada masu Lunch noodles soup da jack fruit dragon suka yi.

Tunda Zeeyter ta fara shirya abincin akan daining gaba-daya hankalin su ya karkato nan Mussamman Haiydar ko bari agama shiryawa bai ba ya je ya zauna yana Tsokanar Zeeyter, "Yau big Madame an shiga kitchen,Let Me See za mu iya cin jagwal din ko kuwa?"

Kallon shi tayi ta galla masa harara.

"Ko da zaiyi ma kowa dadi ai ni ban so ya yi ma,i wish ma ka kasa ci."

Ta karasa maganar tana komawa kitchen.

Deejerh ce tazo tai zuba ma kowa.

Haiydar na ta zura abinci ko magana ya kasa Deejerh ta ce, "Yau Food Master ko magana ma an kasa fa, Sisters kuna son zauta mun aboki da girkin ku."

Haiydar ya dago yana dariya, "Yoo ba dole in kasa magana ba yau fa harda hanun bright Eye a ciki i can't Express How I Feel oh oh d test is so Sweet or should i said to much sweet?"

Ya fada yana kallon Zeeyter.

Murmurshi ta yi kawai tana, "Na U sabi."

Farouk ya ce, "Ko ni fa yau na ruɗe da girkin nan bare kuma Oga,tun tuni cikina ya cika amman bakina ya kasa koshi."

"To sai ka bari ya fashe ai ka hakura da ci dole."

Zeeyter ta fada tana dariya.

Khalil ya ce, "Umm ni kam na ce anjima za a iya kara mana girkinnan?" Ya fada yana kara kai loma.

Dariya suka yi duka Zahra na fadin, "Ashe dai ba Abokina bane kadai acici da aka sa mun shi agaba yau lambar kowa ma ta fito."

Ci gaba da cin abincin su suka yi cikin nishadi da nuna kaunar juna.

An gama cin abinci Zeeyter na tattara Plate kenan ta bige akasa kafarta ta fashe sai jini.

Gaɓadaya Haiydar ya gigice ya ma rasa me zaiyi.

Daukanta ya yi kamar wata jaririya a ruɗe yana, "Sorry zai daina jini Khaleel kai mu asibiti Yanzu Don Allah tana zubar da jini Sosai fa."

Su ma gabadaya sun birkice ganin yadda radadi ya hana Zeeyter magana sai hawaye kawai.

Goge mata hawayen yake yana sambatu.

Cikin sauri Zahra ta dauko first aid box dinta za ta fara mata Treating wajen kan suje asibiti.

Haiydar ya fisge kawai ya fara yi mata.

Yana yi a hankali yana kallonta , "Sorry zai daina zafi, yanzu za mu tafi asibiti abaki magani."

Sai da ya bata taimakon gaggawa kafin Khalil ya dauko mota suka nufi asibiti.

Noor da su Anushka ban da kuka ba abun da suke.

Hakan yasa aka bar deejerh a gida domin ta lura da su.

Suna zuwa aka ba Zeeyter gado domin ta bugu Sosai ba za ta iya taka kafar bama.

Ana kokarin mata dreesing wajen ance Haiydar ya fita fir yaƙi ya zauna.

Ana yi tana ƙanƙamesa tana ihu.

Da tayi wata kara a fusace ya cewa Nurse din, "Yee Yhu Madame ba ki da imani ne? Ki na mata a hankali mana,wannan ai mugunta ne,kina gani yadda kafar take amman ba za ki mata a hankali ba,ni bana son mugunta wallahi."

Tsayawa kallon shi Zeeyter kawai tayi tana ganin ikon Allah.

Ita ko Nurse din ta ce, "Am sorry Sir."

Ka fin ta ci gaba da aikinta.

Bayan ta gama ya gyarawa Zeeyter kwanciya, dake an bata magani da allura tuni wani gigitaccen barci ya yi gaba da ita kanta na cinyarsa.

Waya ya dauko ya fara yi masu hoto tana barci.

Shigowar su zahra ne ya dakatar da shi, "Ah ka ce ma har ta samu barci? Ma sha Allah."

Ya dago yana, "Eh Wallahi ta samu barci yanzu ina ga allurar da aka mata ne ."

Farouk ya ce, "ma sha Allah, Allah sa dai su sallamemu yau mu koma gida."

"Anya kuwa? Don ban ga alamun hakan ba,kuma ma banjin cewa za ta iya taka kafar a kasa."Haiydar ya fada.

Khalil ya ce, "What Ever mu ai lafiyarta ya fi mana komai,in ma sati za ayi indai zata samu sauki ai Shikenan."

"Tabbas Allah dai ya kawo sauki." Deejerh ta fada.

Dukansu suka amsa da Ameeen.

Sai da Zeeyter tayi kwana uku kafin aka sallameta duk kwanakin nan Haiydar na tare da ita a asibitin yake kwana, kan ta furta tana son abu ya yi mata,ko abincine abaki yake bata, wanka kuwa in za tayi shi yake kaita toilet din da kasan ya cire mata kaya tayi , inta gama ya sa mata wasu sannan ya maidata kan gadon,don wankanma shi ason ransa ya mata amman saboda taurin kai Zeeyter sai ta ce zata yi abun ta ai za ta iya.

Zasu koma gida Khaleel ya zo daukan su,Dakyar take iya daga kafar hakan yasa ya tallafeta ta kafaɗa.

Bigesa tayi tana un uni, "ni ba gurguwa ba ce,sake ni in tafi abuna da kaina."

Zata daga kafar taji ta kasa,bata daddara ba ta kara dagawa,bata san lokacin da ta riƙo shi ba tana ihu.

Haiydar da Khaleel me za suyi ban da dariya.

Tsaki tayi ta fiske tana bata rai.

Haka ya riƙeta sai da ya kaita mota.

Suna zuwa da gudu Noor da Anushka suka zo suna rungumeta.

"Oyoyoooo Aunt We Miss You."

ASHIRIN DA BIYU

Murmurshi Zeeyter tayi tana, "Oyoyo my babies I Miss You More."

Zahra ta tare su tana, "kun ga kafar Aunt da ciwo karku fama mata tayi kuka kuje ku zauna Uncle ya shigo da ita."

Tamkar jaririya a hankali ya zaunar da ita kan kujerar,suna hada ido zaiyi dariya sai ta galla masa harara.

"Aunty Jaruma."

Ya fada yana Kallonta.

Farouk ne ya shigo yana, "Ma sha Allah yanzu gidan zai dawo dadi da bakya nan ba dadi gidan sam ya yi duhu ba haske, Gaɓadaya komai ba dadi, we really really miss you,welcome Gimbiyata ya jikin?" Ya karasa yana zama kusa da ita.

Murmurshi ta yi tana, "Alhamdu Lillah I'm Feeling better Now."

Kallonta ya yi yana kokarin sa hannunsa a kafar yana, "in taɓa inji? Nifa ina son ganin kukanki kyau kike yi, Mussamman in idonnan ya kara ja sai kyansa ya kara fitowa kamar a kwace a gudu."

Da sauri ita da Haiydar har suna karo wajen bige masa hannu.

A tare suka dago suna kallon juna...

★★★

Dukansu basu san sanda suka tintsire da dariya ba.

Farouk ya ce, "Alright anata nuna mun bambanci dai wato Oga harda kai abige hannuna kar in taɓa Gimbiyata,What Ever Allah karo sauki dai , yanzu tunda kika dawo gidanma zai dawo dadi."

Haiydar ya ce, "You Know What? In ka fama ciwon nan jikinta ne amman ni ke jin raɗaɗin so kar ma ka soma,yoo dole kayi murna mana tunda abokiyar shirmen ka ta dawo."

Zahra ta ce, "aikuwa rabon da ya zauna a falon nan tun ranar da kuka tafi asibiti sai yau,kullum kawai aiki yake adaki."

Noor ne ya katse masu magana yana rike hannun Zeeyter, "Aunt zaki tafi dani kasarku?"

Zeeyter ta lakace masa hanci, "Da gudu ma kuwa,ka cewa Dad ya bani kai mu tafi."

Dariya Khaleel ya yi yana, "na yi alƙawari In sha Allah duk sanda za mu kara zuwa Nijar zan tawo miki da shi."

Anushka da Anitha ma suka kalli Zahra, "Mom mu fa? Za ki je da mu muma?"

Murmurshi tayi, "Why Not? Za ku je ku gaida Aunt In sha Allah."

Tsalle suka fara Dukansu suna murna ance za a kaisu Nijar.

★cikin kwana biyu Zeeyter ta ware hakan yasa dukanninsu kowa suka fara shirye-shiryen komawa ƙasashen .

Ranar da zasu tafi dakyar aka raba Zeeyter da su Noor.

Da Rana suka isa Nijar kasancewar da wuri suka tawo, sannan suka hau wani jirgin da zai kaisu Niemey daga nan su wuce bobiel.

Madame Ayshe da su Baby na jin zuwan su suka fito bakin get,ba karamin dadi suka ji ba ganin yadda walwala ta mamaye fuskar Zeeyter sabanin yadda take lokacin da zasu tafi Indonesia.

Da gudu su meme suka rungumeta.

"Oyoyoo Aunty,Munyi kewarki sosai,ba za ki kara tafiya ki barmu ba?"

Karamin Wanda take kira Baby ya yi maganar cikin Shagwaba.

Murmurshi Zeeyter ta yi tana, "In sha Allah Babyna na ko na kuma tafiya zan dawo,kasan ina sonka ko?"

Ya girgiza kai, "Eh Anty nima kin san ina sonki ko?"

Mika masa hannu tayi suka tafa.

Madame Ayshe ta ce, "Barka da zuwa,Sannu Da Hanya Yarona,shige ciki abinka in ka biye ta yaran nan da Antynsu sai ka ji da kallon rigima."

Murmurshi ya yi,har azuciyarsa birgesa suka yi, yanayin yadda yaran suke da Zeeyter da ka gansu zaka san akwai tsantsar kauna game da shakuwa a tsakani.

Zeeyter ta nuna masu Haiydar tana, "Oya baku ma Uncle barka da zuwa ba."

Da gudu suka je gunsa suna, "Oyoyoooo Uncle."

"thank you,amman nima kuna sona kamar yadda kukewa Antynku?"

Kallon Zeeyter suka yi tana dariya suka juyo tare da girgiza masa kai alamar Eh.

Haiydar ya bude baki, "Eyee? Wato kunfi son Antynku dani? Zan yi kuka fa."

Da sauri Miemie ta rike masa hannu tana, "Sorry Uncle Muna sonka sosai da yawa amman bai kai na Anty ba fa,amman kuma kar ka yi kuka kaji,Anty ma na sonka dukanmu muna sonka da yawa sosai,kayi Murmurshi Anty ta ce kullum muna yin Murmurshi kada mu bar fuskarmu a ɓace,duk mai ɓata rai muni yake."

Booboo ya ce, "Eh Uncle ka ji,kuma ka taimakawa duk mai neman taimako ko da makiyinka ne, ni har cikin barci Murmurshi nake Anty ta ce ina kyau sosai."

Murmurshi ya yi mai dauke da dariya, "Shikenan nima ina sonku na yi Murmurshi harda dariya ma Ko?."

Aransa yake jin kaunar yaran domin duk da kasancewar su yara amman suna tashi ne da ɗabi'u kyakkyawaa kuma na Zeeyter.

Shiga ciki suka yi,sai da suka rakasu bangarensu kafin Madame Ayshe ta tattara su,suka koma nasu bangaren.

Haiydar ya shiga wanka kan ya fito har Zeeyter ta fice.

Gidan mai ta wuce da mamakin ta an gyara komai an maida komai yadda yake harma da wasu kare-karen da aka yi .

Tana shiga ciki kuwa aiki akeyi kan tsari yadda ya kamata Halliru na lura da komai.

"Barka da dawowa Madame yanzu na ji labarin saukarku nake shirin zuwa gidan."cewar Halliru.

"Barkanmu Halliru Fatan kuna lafiya? In ce ba matsala dai ko? Ko da yake muje office mu tattauna."

Ta karasa maganar tana shigewa.

Tana shiga office ma'aikatan suka fara zuwa gaisheta,bayan sun gama gaisawa .

Halliru ya zauna yana yi mata bayanin komai tare da nuna mata takardun komai na tafiya a tsari sannan an samu ci gaba sosai.

Zeeyter ta ce, "Ma sha Allah na ji dadin hakan sosai, yanzu bangaren ma'aikata fa? Ka tabbatar kowa bai da matsala? Ina so ka bincika duk wani mai Matsala a sanar dani, sannan a magance masa indai bai fi karfinmu ba,kada ka manta da wannan tsarin ma'aikatan mu tamkar danginmu ne,damuwarsu ta mu ce,haka matsalar su ta mu ce,a tabbatar kowa bai da damuwa domin yin aiki mai inganci cikin sauki."

"Yes Madame ban manta da wannan tsarin ba, domin duk wanda ya taso karskashinki dole ya karanci hakan, na kan tambayesu duk wani mai Matsala kuma ina magancewa kamar yadda kika saba akwai bayanan komai acikin wancen file din,dake kanune matsalolin yasa ban saki ciki amman indai da babba dole sai na sanar miki kafin yanke kowanni hukunci."

"Owk to Shikenan Allah yasa mu dace." Zeeyter ta fada tana tashi.

Haiydar na fitowa wanka ya duba ko ina bai ga Zeeyter ba.

"Oh My God,ko yaushe Yarinyar nan zata gama hankali tana nutsuwa oho, Shikenan tunda ta dawo seti ai na shigai abun da ba ayi da ba ma za a fara,Mutum ya dawo daga tafiya ta tsaya tayi wanka ta hutu ma aa bare kuma batun cin abinci,oho dai ita ta sani Let Me take my Food." Ya fada yana ƙarasawa wajen daining.

Sai da cikinsa ya ci yaji ya ƙoshi tukun ya dau wayarsa ya fara dannawa.

Zeeyter kuwa na fitowa daga kamfani ta shige cikin anguwar gani tayi duk anyi ruwa ya taru ga shara ta cika waje Cebur ta dauko tana jan ledojin da suka hana ruwan tafiya.

"Maddalla An dawo kenan,ni a tunani ma kin mutu ne ashe da sauran kwana,da na ji labarin gobara a gidan manki ai a tunani na harda ke cikin wa inda suka rasa ransu."

Dagowa tayi cikin mamaki tana kallon Dpo dake tsaye fuskarshi fal walwala.

Dariya ta yi kafin ta ce, "Ayyah ka san cewa mutum baya taɓa barin duniya ba tare da kwanansa ya ƙare ba,ko da za ata hankaɗasa kabari sai Allah ya nufa,gani kam da raina Alhamdu Lillah ina numfashi kamar kowa."

Wata irin dariyar Mugunta ya yi yana faɗin, "maddalla na ji dadin ganinki araye domin kuwa har yanzu burina bai cika ba,amman fa na miki murna kasancewar kubutar da kika yi matuka wannan ai babbar nasara ce, And ina kara miki murna karo na uku bisa kara gyara miki gidan mai da aka yi,tabbas kin samu miji ko ince kin samu kudi,hakan ya matukar birgeni."

"Godiya nake sosai,miji kam na samu mai jin kai da goyon bayana, Alhamdu Lillah, ko zaka iya ƙarawa gaba?."

Tsaki ya yi ya ce, "Hakan ya mun kuma zai ci gaba da mun amman ki jira wani lamarin da zai afku anan gaba,walwala,karfin gwiwarki da duk wata jarumta sai an nemeta an rasa bare kuma jajircewa."

Ya ƙarasa maganar yana kokarin sa hannu a jikinta.

Riƙon da aka masa ne ya sa shi saurin juyawa.

Haiydar ne cikin zafin nama yake magana, "da ka bari hannunka ya taɓata da kayi babban dana sani wanda baka taɓa ba arayuwa, MATATACE, tawa ce, Alhakina ce kuma rayuwata ce, kada ka kuskura ka yi kokarin shiga gonar da ba taka ba,ban san me ya hadaku ba amman ina mai kara sanar maka cewa ka tsaya iya matsyinka."

Fisge hannunsa ya yi yana, "Kasan ni wane ne da za ka zo kana fada mun magana son ranka? Na ce kasan ni wane ne? Kuma ma maganar ba akan kowa ba sai akan wannan watsattsiyar Yar Tasha mara gilihu yar Lingo? Ga dukkan alamu baka.....

Bai karasa ba sai jin saukar mari ya yi da duka ta ko ina.

Cikin fada Haiydar ke magana, "Zan iya hakuri ni a za geni in kyale,kuma zan iya hakuri ni aci zarafina in bari, zan kau da kai ko da dukana za ayi amman kada ka kuskura kai kokarin taɓata ko cin zarafinta ka nemawa rayuwarka salama ta hanyar kaucewa duk wata hanya da zai kasance ka kuntata mata." Ya fada yana nuna Zeeyter da hannu.

Dakyar Dpo ya samu ya tsare aguje,ko takalmi babu sai jiki na rawa kamar mai naguda amman duk da haka bai daddara ba yana gudu yana fadin, "Wallahi sai ka sha mamaki indai ina raye za ku sha mamaki sai na jefa rayuwarta cikin garari zan ga yadda za ka yi."

Tsaki Haiydar ya yi.

Zeeyter tayi kokarin ƙarasawa garesa tana rikosa bigeta ya yi ya wuce yana wuce kamar bijimin sa,tana mai magana ko ya tanka, direct ya je ya shige motarsa tare da yi mata wani irin figa ya tafi.

Mamaki ne ya kama Zeeyter ta tsaya kawai tana kallon ikon Allah,daga karshe ta shiga cikin gida, wayarta ta dauka ta kira Numbersa,amman sam yaƙi dagawa.

In yaga kiran ma tsaki yake ya kashe.

Tafiya yake cikin sauri ba abun da yake ganowa a idonsa sai Dpo dake kokarin sanya hannunsa jikin Zeeyter.

Da karfi yake maganar yana, "Me ya haɗata da shi? Me yasa take kula shi,har hannunsa a jikinta? Ba zan jure ba, sam ba zan jure hakan ba, Meyasa za ta bashi damar hakan?"

Tafiya yake kawai ba tare da yasan inda yake nufa ba.

Saura kadan ya yi accident ya tsaya.

Ganin dare ya yi Haiydar bai dawo ba yasa Zeeyter tayi wanka ta sa wasu fitattun kayan barci da Deejerh ta aiko mata.

Ba karamin kyau ya yi ba tare da fito mata da yanayin jikinta.

Tana zaune tana duban agogo har karfe 12 na dare ba Haiydar ba labarinsa.

Ta shi tayi tana kokarin shigewa ɗaki buɗe kofar da ta ji anyi ne ya dakatar da ita.

Haiydar ne dauke da kwalbar giya a hannunsa.

Kallo ɗaya ya mata ya kauda da kai,tare da zama kan kujera yana kokarin bude giyar.

Cikin fushi ta karaso ta kwace tare da fara yi masa kiss.

Sai da ta gama kashe masa jiki kafin ta ja shi, suka koma daki.

Nan take Haiydar ya manta da wani batun ɓacin rai tare da lulawa wata Duniyar.

Sai da suka farantawa ransu rai a wannan daren yadda ya kamata kuma ya dace.

Washegari

Haiydar ya gama shiri tsaf Zeeyter ta hada masu break da kanta.

Ci yake yana santi tare da yin godiya.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.