Free chapter · Read without an account
CHAPTER 35
Sai da ya ci ya koshi tana gyara daining din yazo ya rike mata hannu tare da rufe mata ido da ɗayan hannun.
Sai da suka je filin gidan kafin ya bude mata ido yana, "Surprise."
Mota ce Sabuwar ƙira , wacce ya kasa haɗa bangarenta ta haɗa mai ranar.
Hakan yasa ya fara fito da biyu na shi da nata.
Bude baki Zeeyter tayi cikin yanayin mamaki tana, "Sunshine na waye ne wannan motar? Ta mun kyau sosai."
"Just For yhu My Bright Eye, I said Just For yhu, kiyi yadda kike so da ita." Haiydar ya fada yana mika mata keyn.
Kin karban keyn tayi ta ce, "Amman ni.......
Kafin ta yi magana ya rufe mata bakin da kiss, "Ki yi shiru bana son musun nan naki, na san kina da kudin siya Amman wannan kyauta ce daga gareni ban damu ba don kince ba za ki hau ba,amman motar nan da sunanki nayi kuma da sunanki zata kasance, kin ga cen?."
Ya fada yana nuna mata motar da hannu
Kafin ya ci gaba da Magana.
"Sunanki ne jiki, kamar yadda ɗayar tawa take dauke da sunana, karo na farko ki karbi kyauta daga gare ni ko zan ji dadi araina duk da cewa ban san ko kina sona kamar yadda nake sonki ba, kuma ba ki taɓa nuna hakan ba,amman Please ka da kice zaki maida mun wannan kyautar ina son kasancewar ki da ita,ki duba wayarki na tura miki App din Software din da za ki yi amfani da shi wajen driving."
"Sunshine." Abun da Zeeyter ta furta kenan da ya dakarta da shi daga shiga motar.
Da gudu ta karasa ta rungumesa tana fadin, "I love you, I mean I Really Love You, U mean D world to me,
How can I explain my feelings to you. Its pain, its numbness, its like I can see only one thing, hear one thing and think about one thing. That is you.
You know what?
U are the one who i can open up to. I feel so compotable in ur presence. And
Ban yi karyar cewa ba zan rayu ba in babu kai, amman ina so kasani cewa rayuwata ba za ta taba samun
walwala ba har sai da kai cikinta, ka rayu dani har ƙarshen numfashinka,daga yau gobe,anjima har ma da kullum kasa aranka cewa nima ina sonka."
Wani irin hamshakin Murmurshi Haiydar ya yi tare da saukar wani sanyi a zuciyarsa.
Ya kara rungumeta yana, "Love Yhu More Bright Eye,But Just Remember You Mine,Mine Only, ki kula mun da kanki, byee byee."
Ya kara sauke mata kiss a goshi Yana kokarin shiga mota.
Zeeyter ta yi Murmurshi tana , "Adawo lafiya, amman ka dawo fa sai munyi lissafi na biyaka kudin motarka ehee, kuma in zaɓa ma gun parking kowa ya dunga yi agunsa."
Dariya Haiydar ya yi yana, "Ciwon ya dawo kenan Ok what Ever bari in dawo ina daidai da kowani irin yanayinki ai kin sani."
Dariya tayi ta shige ciki tana, "Oho dai."
Driving yake amman gabadaya tunano maganar Zeeyter yake yana sake Murmurshi.
Ita ma din kamar haka har ta koma ta gama shiri inta tuna shi kawai sai dai tayi dariya.
"Mamaki nake,wai nice na fada tarkon soyayya? Imagine,ina son shi sosai fiye da zato ko tsammani na, rayuwa ke nan."
Sai da ta gyara gidan tsaf kafin ta nufi gidan mai.
Tana zuwa ba jimawa sai ga Halliru ya shigo tare da sanar mata cewa tayi baki.
Bada izini tayi kan cewa su shigo.
Maman Yusuf ce da wasu mata su biyu.
Ba karamin kyau tayi ba da ƙiba kana ganinta kasan cewa tana cin na kanta kuma zaune take cikin kwance hankali.
"Barka dai Madame kwana biyu ashe bakya kasar inata zuwa sai ace bakya nan sai jiya Yusuf yake sanar mun ai kin dawo."
Murmurshi Zeeyter ta yi ta ce, "eh wallahi mun dawo,ga waje nan ku zauna mana Bismillah."
Ta karasa maganar tana nuna masu wajen zama.
Bayan sun zauna an kawo masu ruwa sun sha zeeyter ta ce, "Ya kike? Ya sana'a ya kuma Baban Yusuf."
"Alhamdu Lillah Madame muna lafiya ya ma ce agaida ki shi ma yana nan tafe yi miki barka da dawowa yanzu ma kawaye na ne na rako Aminatou da Aishatou ."
Kallon su tayi tana, "Barkan ku dai Ameenatou da Mamana Ayshatou me ne ne matsalar ku? Allah sa ina da hali ko ikon Taimakawa."
Dukansu suka ce, "Barka dai Madame."
Kafin Ameenatou ta fara magana, "Matsala ce tsakanina da mai gida na dana fadawa maman Yusuf shi ne ta ce zata kawo mu gunki domin ita kam tunda kika bata shawara matsalar zamantakewar su ta kau kuma mu kanmu mun ga zahiri har sun zam abun kwatance a gare mu."
Zeeyter ta numfasa tana, "Alhamdu Lillah ina jin ki."
Ameenatou ta ci gaba da fadin, "Tunda na Aure shi bai fi wata gudu kacal bane muka yi rayuwar farinciki ta aure tun daga lokacin da abubuwan da iyayena suka kaini da shi suka kara komai ya sauya, komai a wulakanci kuma komai cikin tozarci,ya maidani tamkar baiwa sai dai yazo ya kwanta dani kawai ba batun wata soyayya domin har ma na manta da yadda ake yinta, sannan maganar abinci kuma kullum a Wulaƙance zai bamu kuma da wadatacce ba daga ni sai yarona karami shekarar mu ɗaya da aure amman komai a ƙaiyade yake ban isa in taba abu ya wuce kima ba,hatta magin da zansa a abinci guda biyune , Shinkafa kuwa rabin gwangwani ni da yarona,abun karyawa naira hamsin ne a kullum, ban isa in kusance shi da magana mai dadi ba,kullum cikin fada da hantara muke,in ina son abu sai dai in dau wani abu na kayan in saida,inna kai kara gida kuma sai dai ace in ci gaba da hakuri haka rayuwar aure ta gada,a kullum maganar kenan." Ta karasa maganar tana fashewa da kuka.
Cikin yanayin tausayi Zeeyter ta ce, "ba kukq zaki yi ba,kiyi shiru in sha Allah komai ya kau kuma komai ya wuce indai zaki bi shawarar da zan baki."
Ta kalli Ayshatou ta ce, "Saura ke ina sauraren ki Mamana."
Numfasawa Ayshatou ta yi kafin ta ce, "To nidai Alhamdu Lillah a bangaren tufatarwa da kuma ciyarwa, zai bani komai a wadace aurenmu Wata Bakwai kenan amman indai zai fita yaga kaya masu kyau ko amai tallah zai siyo mun,sannan abinci ma kan ya kare ya kawo wasu, inda gizon yake saƙa shine sam baya iya gamsar dani kuma ba zai taɓa yarda ya yi wasa dani kafin saduwa ba sai ya ce shi bai iya ba,kuma bai san wannan ba,sai dai kawai ya biya bukatarshi ya tashi bai damu da nawa biyan bukantan na gamsu ko aa ba, kawai dai kansa ko nace masa ni inada bukata sai ya ce ya gaji,wannan ce babbar matsalar zamantakewar gidan aurena."
Zeeyter ta numfasa kafin ta ce, "Tabbas tunda kuka kawo kukanku gare ni kun yarda kuma kun aminta da cewa zan iya magance maku matsala ne, Alhamdu Lillah zan yi iya bakin gwagwadon iyawata, abu na farko da nake so ku fahimta shine 'YA MACE BA BAIWA BA CE KUMA BA BOLAR ZUBAR DA SHARA BA CE,MUTUM CE KAMAR KOWA, gudun saki ko tsoron rabuwa da miji ba naki bane don inganta rayuwarki, zawarci ba tozarci bane, kada ku taba sa hakan aranku wai kuna gudun miji ya rabu da ku baza ku iya rayuwa ba, Ameenatou matsalar ki bangare biyu ce amman babbar masahar ta guda ɗaya ce, shi ne ki tashi ki kama sana'a ki dogara da kanki,nuna masa cewa ko ya baki ko bai baki ba za ki iya kuma za ki inda hali ma har shi ki kyautata masa,tsaya da kafafunki za ki ga canji arayuwar gidanki ba zai taɓa tunanin wulaƙanta ki ba ko nuna miki halin ko oho atakaice ma za ki ga tarairaya da soyayya fiye da zato ko tsammaninki, sannan ki cire tsoro ko shakkar sa abu mafi girma shine ki guji abun da zai iya janyo maku matsala a tsakani amman daga nan kada ki taɓa yarda ya takaki kan gaskiyar ki, fito da asalin ke wace ce, kasancewar ki mace ba shi ke nufin za a tauye miki hakki kiyi shiru bane, fi karfin kanki da bukatun ki ba wanda ya isa ya taka ki,in makaranta ce ma ba kiyi ba koma kiyi , in Kasuwanci ne baki da jarin yi zan baki gwagwadon iyawata in sha Allah na miki wannan alƙawarin."
Ta numfasa ka fin ta dubi Ayshatou ta ce, "Aishatou matsalar ki babba ce amman kuma karama ce awani bangaren ko addinance ba a haramta neman saki ga wanda baya samun bukatar aure yadda ya dace ba, Amman kafin nan zauna da shi ku fahimci juna ,cire tsoro fito a yadda kike kuma a yadda kike son kasancewa, nuna masa hanya mafi bullewa domin inganta rayuwarku, in yaki fahimta ba dole ba kashe kai, nemi takardar saki,in yaki kai shi kara daga nan Allah zai baki wanda zai iya dake,domin muddin bai canja ba,kuma kika ci gaba da zama da shi a haka watarana neman wasu mazan zaki fara, kuyi magana ta fahimta ku fahimci juna, sannan dukanku ina so ku rike wannan ba batun cewa zaman aure zaman hakuri ne,komai ma na duniya sai anyi hakuri ai amman kada ka yi hakuri agun da za a tauye ma hakki sam! Wannan ba yi bane kashe kanki za ki yi a banza,ba wai nace karku nunawa mazajenku soyayya bane aa in lokacin soyayya yazo ayi amman in an kauce hanya nuna masa cewa da kai ko ba kai zanyi rayuwa kuma mai inganci da yardar Ubangiji,wani zubin nuna soyayya fiye da kima kan janyo mana wasu matsalolin, ina fatan kun fahimta kuma kun aminta da zantukana."
Ameenatou ce ta fara girgiza kai tana, "Hakane Madame na yarda da batun ki ɗari bisa ɗari kuma zan yi amfani da su in sha Allah, Allah saka da alkairy."
"Nima na Aminta kuma na fahimci dalilai da dama dake sawa maza ke wulakanta mu a rayuwa da ace za mu cire tsoro kuma mu dogara da kanmu ba abin da zaifi karfinmu, mun gode sosai Allah ya saka da alkairy." Cewar Ayshatou.
Maman Yusuf ma ta ce, "Mun Gode Madame Allah biya bukatu na alkairy duniya da lahira , Allah ba da 'Ya'ya na gari."
Murmurshi Zeeyter tayi tana fadin, "ba komai, Allah ba mu ikon aikata alkairi."
Daga nan ta kira Halliru ya ba da Ayshatou da Ameenatou 50000f
(Cinquante mille francs) domin su ja jari.
Gaɓadaya cikin farinciki suka rabu.
Sai da Zeeyter ta raka su har bakin get suka tafi kafin ta dawo.
Su Harira da Hurera na lekenta.
Hurera ta ce, "Ikon Allah ina jin wannan fa ba za ta taɓa karaya ba,da kamar bata nan tayi sanyi amman kuma yanzu ta kuma dawowa da karfinta,ina mamakin shin wace iri ce Zeeyter."
Tsaki Harira ta yi tana, "Aljana mana,in ba Aljana ba wa zai iya hakan ni ki bar ma mun maganarta wallahi takaici nake ji inna ganta sai inji kamar in kasheta."
Hurera ta ce, "nikam tun ranar da ta kaini asibiti ta fara birge ni Wallahi ita muka ma Amman ya koma kaina kuma karshe ta taimakeni wanda da ba ita Shikenan sai dai inyi rayuwa ba kafa don nasan ruɓewa zata yi kuma ba mai kudin kaini asibiti."
Wani irin tsaki Harira ta kara tana, "kyaji da shi dai, kima sota ba birgewa ba."
Ta fada tana tafiya cikin sauri.
Zeeyter kuwa na komawa office ta yi tagumi ban da tunano matsalolin rayuwar auren da su Ameenatou suka fada mata ba abun da ke yawo akanta.
Jiki a sanyaye ta koma gida, afalo ta kwanta kawai tana kallon sama,har haiydar ya shigo ya yi sallama ba ta ma ji ba,bare ta lura da zuwan shi.
"Madame I'm back , I'm Back oh oh, ba za amun maraba da dawowa bane?"
Ina Zeeyter ko jin sautin muryarshi ba ta yi ba ta jima da nisa cikin duniyar tunaninta.
A hankali ya ƙarasa kunnenta cikin raɗa ya ce, "Sunshine I'm back."
Da Murmurshi ta juyo tare da tashi tana, "Welcome yaushe ka shigo."
Zaunar da ita ya yi,shi ma ya zauna yana, "Aa, Is Something Wrong?,Meya ke faruwa? Gaɓadaya fuskarki ba walwala bare annuri ba yadda kika saba kasancewa ba,na shigo ina ta sallama da magana ba ki ji ba har sai da nazo kunnenki fa,mene ne yake faruwa? Just Let Me Know Please da ganin Murmushin fuskar ki na san na boye damuwa ne ba asalin wanda kika saba ba."
Jiki a sanyaye Zeeyter ta ma haiydar bayanin komai da su Ameenatou suka sanar da ita.
Girgiza kai ya yi, yana, "Maddallah da mata da gari yadda kika shi ne dai-dai ,zan yi alfahari da ke aduk inda za ki kasance And kuma in baban Yusuf ya zo ki ce ina nemanshi akwai bukatar mu tattauna da mazajen nasu suma, ina so muyi magana akwai abun da dole sai namiji da dan uwansa na miji kamar yadda kuma kuka yi magana muma za mu yi in sha Allah komai zai daidaita ki daina damuwa kin ji, yanzu ki mun asalin Murmurshi bana bogi ba."
"Thank you,Thank you so much,a kullum kana bayana kuma kana karfafa mun gwiwa ban san ya rayuwata zata kasance in babu kai ba, i can't love you less Sunshine, amman fa ba zan yi Murmushin nan ba yau I'm hungry kuma kai nake so kamun girki irin tuwon ranar sai inyi Murmushin har ma da dariya."ta karasa maganar tana taɓe baki.
Tashi Haiydar ya yi yana daga hannu kamar dan sanda yana, "As You wish Madame."
Shiga daki ya yi ya cire kayan ya dauko kananu yasa sannan ya daura rigar girki asama ya shiga kitchen yana, "Ki bani mintuna kadan yanzu zan cika miki ciki,har sai kin gaji."
Cikin minti talatin ya mata tuwon semo din da miyar vegetable.
Ajiyewa ya yi a daining table , kan ya dawo ya rike hannunta yana, "Komai ya kammala."
Zaunar da ita ya yi,yana kokarin diba ya bata abaki.
Dariya tayi ta karba tana, "Thank you, zan ci da kaina yanzu kam sai aikin yama yawa ai, je ka yi wankanka sai ka dawo kai ma ka ci."
Har ya tafi ya dawo.
Kin tabbata ba abun da za a kuma miki.
Wata irin dariya Zeeyter tayi tana, "Eheen je ka yi wankanka Ni dai na san wannan ladabin ba a banza ba da biyune."
Dariya ya yi ,ya tafi yana waƙa.
Wayarsa da ke kan daining din ne ta fara ringing,lekawan da za ta yi ta ga Meenoh ce ke kira.
Tsaki tayi ta ci gaba da cin abincinta.
Ganin kiran yaƙi ci bare cinyewa yasata katsewa.
Ta ci gaba da kiran, cikin ɓacin rai Zeeyter ta dauka tare da kasawa a kunne...
"Hello Darling, Wato ka manta dani ko? Wai me matarka take da shi ban da shi ne? Ni fara ce, kyakkyawaa kuma doguwa sabanin ita baka ga muni, Haba Don Allah kasan fa ina sonka,ka amince muyi aure ni na yarda zan yi zaman kishi da ita."
ASHIRIN DA UKU
Wani irin takaici ne ya dunguri Zeeyter a Zuciya, sai da ta ja numfashi kafin ta ce, "Tabbas bai zama lallai in Kasance miki mai kyau afili ba,amman ina fata tare da burin a kullum in ingata zuciyata ta kasance mai kyawun da bai misaltuwa,. Sannan kuma maganar Haiydar in baki fita harkar shi ba zan baki mamaki, miji na ne mallakina,ban hana ki aure shi ba inda hali Bismillah ba zan yi fada dake ba domin ban ga abun yin fadan ba, ina kara jaddada miki dai ki fita sabgata har ma da tashi."
Meenoh ta yi wani Hamshakin tsaki tana dariya, "Yoo wai har business Marriage din ya samu wani mahimmin wajen zama da har xakiyi tutiyar shi naki ne?banxa wawiya mara galihu yar kan titi, balagaza mara asali, Ni na rasa ma in ba kaddara ba ai ko a hanya kika ga Dear ba ki kai ki kula shi ba bare har auratayya ta shiga tsakani,ki kwana da sanin cewa indai ina raye sai kin bar giddannan da kafafunki kuma bari na har abada."
Dariya Zeeyter ta yi sosai tana, "Faɗawa sakarai wanda bai san Allah ba,ba ki isa mun abun da Allah bai mun ba,domin kafinki dubunki sunyi ko ince suna kai, but bazan ce miki komai ba fatan Nasara muje zuwa."
Tana karasa maganar sai ga Haiydar ya fito cikin sauri ya fisge wayar yana ganin Meenoh ce ya daga murya tare da fadin, "wai ke wace irin wawiya jaka ce wacce bata san kanta ba? In kina son zaman lafiya ki fita cikin rayuwata kamar yadda na fita a taki,kaddara ce ta hada kuma ta raba." Tsaki ya yi yana katse kiran ba tare da ya jira amsarta ba.
Kallo ɗaya Zeeyter ta masa ta kau da kai tare da tashi zata shiga daki.
Rike mata hannu ya yi ta fisge tare da sakin tsaki ta tafi daki tare da kulle kofar.
Nocking kofar Haiydar ya fara yana, "Kiyi Hakuri Don Allah ki gafarceni, Dans tes yeux, tu as vu et tu sais que j'ai cessé de faire quoi que ce soit qui puisse t'offenser. Se pas moi qui l'a appelé tu vois. S'il te plaît, sois patient. Toutes les décisions que tu as prises, sauf d'être avec moi, s'il te plaît." ("A idon ki kin gani kuma kin sani na daina duk wani abu da zai bakanta miki,bani na kirata ba kin gani,kiyi Hakuri,duk hukuncin da zaki mun kiyi amman ban da na kasancewa da ke Don Allah."
Shiru tayi ba tare da ta ce komai ba,tana kokarin kwanciya har ta kwanta kuma sai wata zuciyar ta ce mata ta bude kofar.
Tana budewa ta gan shi zaune abakin kofar kawai yayi tagumi.
Tana budewa ta koma ta kwanta.
Ya bita yana, "na ce kiyi hakuri,shin ba zaki tausaya mun ba? Me kikeso inyi ne?"