Free chapter · Read without an account

CHAPTER 47

by Aisha Sani Abdullahi · 5STARS CHRONICLE Book 1 YEL

Tashi tsaye Zeeyter da Haiydar suke yi tare da rugumesa ana tafa masu.

Bayan an gama kuma kowa yaje yasa kayan ruwa za ayi gasa tsakanin Noor da yake a matsayin Haiydar da kuma Miemie da take amatsayin Zeeyter.

Haiydar yaja Noor yana kitsa masa yadda zaiyi, Zeeyter ma ta ja miemie tana mata bayanin yadda za ta yi.

A wannan lokacin Khaleel da Adam ne Alkalai.

Halliru kuma mai duba lokaci.

Sosai Miemie take gudu Noor na cen baya Zeeyter sai murna take.

Kamar anyi walkiya nan take Noor ya wuce Miemie ya isa daidai kan lokaci.

Ihu Haiydar ya yi ya rugumesa suna yi wa Zeeyter gwalo.

Ta galla masu harara tare da fadin, "Ba a gama ba ai za azo wani."

"Oho dai na gaba ya yi gaba,na baya sai labari." Haiydar ya fada yana dariya da gwalo.

Da daddare bayan sun gama ana zaune kowa na hutawa.

Madam Ayshe ta Ammien Haiydar kan ta ce, "Yar Uwa An yi shagali komai ya tafi dadai Alhamdu Lillah kuma mun dau darasin rayuwa sannan munyi farinciki da kasancewa a tare wanda ina tunanin gobe kowa zai koma inda ya fito,mai zai hana ki dan kara tunatar da mu tare da bada wasu shawarwari ga masu auren har ma da wa inda basu yi ba tuxure irin su Farouk."

Ta karasa maganar cikin zolaya.

Dariya suka yi Farouk ya ce, "Very Soon zan baku mamaki, Gimbiyata ta ce za ta aurar dani ko kawar Dole?"

Dariya Zeeyter ta yi ta ce,"Dole na ma abokin dole sarkin basaja."

Ammie ce ta yi gyaran murya tana, "Tabbas Maganarki abun dubawa ce,kuma hakan ya yi daman ance taɓa kidi taɓa karatu,to dukkanmu nan in zabu duba tarihin rayuwar zainab da Aliyu hakan ma kadai babban darasi ne a rayuwarmu, yana da kyau ace kullum mun kasance cikin kyakkyawaan zato tare da kyautata muamularmu ga kowa,wani ma haka kawai ba tare da ka tare mai komai ba zai nuna ya tsaneka, maimakon kai ma ka nuna masa tsanar nuna masa soyayyar ka tsakani da Allah, domin watarana ba asan wa zai taimaki wani ba, masu aure su girmama ra ayin junansu kada ya kasance ana amfani da raunin mace wacen musguna mata,mu tuna cewa kowanni dan adam na da daraja kuma yana da yanci sannan muma mata kada mu wulakanta mazajenmu domin ko ba komai su wani bango ne na rayuwarmu,mu rayu tamkar tsintsiya kuma yan uwa na jini, masu niyar aure kada abi kyau ko wani abu nagarta shine farko tare da kyawawan dabi'u."

Nasiha Sosai Ammie ta masu.

Kafin suka yi godiya kowa yaje ya kwanta.

Washegari kuwa tun sassafe aka fara tafiya.

Bayan sunje sun raka 5stars filin jirgi su Madame Ayshe, Ammiei da Su Adam kowa ya tafi, Haiydar ya koma filin jirgi kai wa Ammie passport dinta data manta.

Zeeyter na jiransa agida.

Dawowaan da zaiyi ya nemeta sama da kasa ya rasa.

Ga wayarta a rotse a falon,mai gadi kuwa kwance a kasa ga dukkan alamu an sumar da shi.

Wata irin kara Haiydar ya sake yana kwallawa Zeeyter kira.

★★

Babu Zeeyter babu labarinta.

Kamar wasa abu har ya kai dare Haiydar da yan sanda na bincike amman babu ko kyallen Zeeyter.

Gaɓadaya ya fice a hayyacinsa ya rasa meke yi masa dadi arai.

Komawa gidan yayi kawai ya zauna abakin get din Yana kallon ikon Allah.

Kara yaji wayarsa nayi dubawan da zaiyi ya ga su Zahra ne suka kira video call ta Sykpee.

Kamar ba zai dauka ba sai kuma ya dauka.

Gaɓadayansu kowa ya sauka a masaukinsa.

Deejerh ce ta fara magana, "Hi Friends mun kowa ya sauka lafiya?".

Khalil ne ya dakatar da ita ganin yanayin Haiydar ba walwala ga idanunsa sunyi ja ya ce, "Haiydar meya ke faruwa? Fada mana don Allah."

Farouk ya gyara zama yana, "Fuskar ka ta nuna akwai matsala sanar mana Please."

Zahra da Deejerh ma suka ce, "Please Haiydar."

"Zeeyter ban ganta ba."

Haiydar ya fada ya kawar da kansa.

A firgice Farouk ya tashi tsaye.

"What? Me kake nufi? Kidnapping dinta aka yi ko me? Kar ka ce mun an kasheta ko an mata wani abu."

Tsabar rikicewa deejerh ta kasa magana sai kuka.

Khaleel ya ce, "Garin yaya?"

"Dawowa nayi daga kai wa ammier passport babu ita sai wayarta akashe mai gadi kuma an sumar da shi."

Zahra ta ce, "Innallillahi wa inna illar raji un, Allah ka dubemu."

Farouk ya ce, "Ka jirani yanzu ina zuwa ka jirani."

Khaleel ma ya ce, "Nima zan tawo yanzu in sha Allah ka zauna acikin gidan kar ka je ko ina gamu nan dawowa."

"Nima gaskiya ba zan iya zama ba gani nan kawai." Zahra ta fada cikin yanayin damuwa.

Deejerh ma cikin kuka ta ce, "Nima yanzu zan tawo."

Kan kace miye har Farouk ya fice.

Khaleel ya ce, "Aa ku, ku zauna,wannan aikin namune kuma zamu magance in sha Allah ku zauna kun ji, kada ya kasance kun samu cikin wata damuwar mu rasa wacce zamu fuskanta."

Da kyar khaleelr ya lallaɓa su suka yarda kafin shi ma ya biyo jirgin dare ya tawo nijar

Farouk na zuwa airport ya rasa jirgi.

Dafa kai ya yi yana tunanin ina mafita.

ASHIRIN DA TARA

Kwatsam yaga saukar wani Private jet.

Bayan wani mutum ya fito sai da ta kai jirgin hanger sai fa zoe ta fito

Hada ido suka yi.

Da mamaki ta ƙarasa gabansa tana, "Ah You."

Farouk ya ce, "Yap kin shigo wajenmu yau kenan."

Zoe ta ce, "Yes Na shigo Wallahi ina tunani ma kwana zan yi da safe sai na wuce amman meyasa na ga u Look some how, like kana cikin Matsala me ya faru?"

Dafa kai Farouk ya yi yana, "Zeeyter an rasa ta about 10hours akwai bukatar in tafi nijar cikin daren nan kuma babu jet."

Bude baki zoe ta yi, "What? Zeeyter? I so much Like that gurl oh oh gaskiya ban ji dadi ba amman taya zan iya taimakonka?"

Farouk ya ce, "If possible ki kai ni mana amman za mu biya Uk mu dauki Khaleel saboda na san shi ma zai yi matukar wahala in ya samu jirgi "

"Oh Yes Bara inyi signing komawa yanzu sai mu tafi."

Zoe ta fada tana tafiya.

Sai da taje tayi signing ta biya kudin tukun ta dauko jirgin a hanger kafin ta dawo suka tafi.

Farouk ya kira Khaleel kan cewa yaji airport ya jirasu.

★★Haiydar na zaune a falon ya rasa meke yi masa dadi.

Kamar daga sama sai da Deedarth ya shigo dake ya koma Skul baya nan amman tunda yaji labari cikin daren ya fito.

"Yaya Ina Antyna? Wai basu kira ba? Yaya Don Allah kar abar su mata komai.

Kallonsa Haiydar kawai ke yi ya ma kasa yin magana domin shi kadai yasan raɗaɗi da kunar da yake ji a cikin zuciyarsa.

Zama Deedarth ya yi agun kawai yana kallon haiydar sai kuka.

Ganin ba sarki sai Allah yasa haiydar yin alwala tare da fara salloli yana mai rokon Allah ya bayyana Zeeyter aduk inda take kuma ya kubutar da ita.

Shi ma Deedarth alwalar ya dauro yana sallah yana kuka.

Madame Ayshe ma na jin labarin kaf ta tashi yaran bata sanar da su abun da ke faruwa ba amman ta ce Antynsu ce take buƙatar addu'ar su su ta shi suyi sallah

Haka kuwa suka hadu suna salla masu karatu nayi.

Ranar gaba-daya ba wanda ya runtsu sallah da addu'o'i kawai ake.

Misalin karfe 6 na safe su Farouk suka isa Nijar, kasa hakuri zoe ta yi ta koma tana ajiye jirgin ta biyo su Farouk aka nufi Pleatau.

Suna shiga Farouk ya ce, "Har yanzu shiru wai yan sandannan suna aikin da ya kamata kuwa?"

"Suna yin iya nasu amman in da kidnapping ne ya ci ace sun kira sun fada bukatarsu wannan zainab suke son dauka ba wai kudinmu ba." Haiydar ya fada.

Zoe ta ce, "Ayyah Sorry Ko za ta dawo ko ma ina take."

Khaleel ya ce, "Ok ina tunanin akwai bukatar shigo da Xavier abokina cikin case dinnan MI6 ne zai iya taimaka mana ina ga ta wani fannin ko ba yanzu ba,amman akwai bukatar in sanar da shi."

Khaleel ya karasa maganar yana kiran Xavier.

Bayani ya yi masa Sosai sannan Xavier ya ce ba matsala in anji labari ko anganta amasa magana,sannan a turo masa number dan sandan da ya tsaya kan case din sannan duk sanda suke buƙatar taimakonsa a shirye yake.

★A hankali take bude idanunta kasancewar har yanzu abun da suka sheƙe mata bai gama sakinta ba.

Cikin magagi take Addu'a, "Alhamdulillahil-lazi Ahyana ba'adama Amatana wa ilaihir nushur."

Kokarin tashin ta fara amman ta kasa saboda ciwon da ke kanta.

Ji tayi gabadaya jikinta amace ta kasa motsawa.

Sautin Muryar wani matashi ta ji yana, "Usman,Sani ku zo ta farka fa ta tashi."

Cikin sauri suka karaso.

Dakyar Zeeyter ta iya daga idanunta .

Wasu matasa ta gani reras a gabanta su uku .

Usman dinne ya fara magana, "Maddalla daga yau aikinmu ya kammala mu,Sani ka kirashi ya zo mana da kudin aikinmu ya dau kayansa,kai kuma Habu ka je ka nemo mata wani abu ta sa baki tunda kwananta biyu tana barci kuma bata ci komai ba."

Cikin karfin hali Zeeyter ta ce, "Ku su waye? Waye ya turo ku? Meyasa za ku kawo ni nan? Baku da hankali ne?"

Cikin zafin Rai Usman dinnan ya daga hannu zai mareta.

Sani ya rike masa yana, "Ke ki iya bakinki sannan ki adana duk wasu tarkacen tambayoyinki ki jira shi wanda yasa a dauko ki ya zo sai ki mai,mu mun gama namu."

Duk da cewa tana kwance amman bakinta bai mutu ba,tsaki tayi tana fadin, "Wawaye kawai da ka bar shi ya marenin ai ,aikin banza kawai."

A fusace Usman ya kara nufanta da mari Sani ya kara rikeshi yana, "Dalla kar ka biye mata,mu fa namu abiya mu ne,ina ruwanmu da ita koma me zata ce ta ce ba damuwarmu bane."

Can anjima wajen awa ɗaya habu ya kawo mata wani irin daskararren tuwo ko kallonsa ba tai ba bare niyar ci.

Kamar da wasa ta miƙe tana kokarin fita.

Tsawa Sani ya mata yana, "Ke dallah dawo ki zauna ina zaki je?"

Zeeyter ta ce, "fita zanyi amman kafin nan in tambayeka ma mana, me ya kawo ku wannan aikin har ku rasa abun da za kuyi sai dai asaku satan mutane a biyaku."

"Ina ruwanki? Wannan ba damuwarki ba ce kuma ba rayuwar ki ba ce."

Karaf Usman ya furta.

Zeeyter ta ce, "Don Allah ku fada mun ko kadanne ina da bukatar jin dalilin da ya kawoku wannan sana'ar domin na tabbata akwai dalili."

Zama suka yi duka.

Sani ya ce, "Ina so inyi rayuwa kamar kowa,inji dadi kamar kowa amman ba hali govnati da masu kudi sun rike kowanni fanni na jin dadin Rayuwar mu sun gatange an maida talakawa abun banza, na yi wahala ba irin wahalar da ban sha ba arayuwa wajen neman ilimi har dako nayi da girmana babu wani aiki da banyi ba duk dan in rufawa kaina da iyayena asiri wajen ganin nayi karatu na samu aiki amman a banza domin dana gama kwalin ba abunda ya tsinanamun neman aiki ko ina kaje ba za a dauka ba in dai baka da hanya kuma kai talaka ne baka da cin hancin da zaka mika adaukeka, nafi shekara daya ina yawon neman aiki amman ko da wasa ban taba samu ba,a lokacin na fahimci ace wahalar da kaina nake abanza na kudiri niyar musgunawa duk wasu masu kudi da suke mantawa da talakawansu tare da govnati ba ta damuwa damu bare rayuwarmu."

Numfasawa Zeeyter ta yi.

Habu ya ce, "Naka mai sauki ne ma tunda har kayi karatun ai ni fa tunda na taso kullum cikin tsine mun da zagina mahaifina da Mahaifiyata ke mun saboda na taso tun ina yaro bana jin magana,ko makaranta basu sani ba wai ni dan iska ne ko naje ba xan iya ba karatu ba,ni ko dana girma naga ba amfanin ci gaba da rayuwa cikinsu ana hantararta da zagina na zabi zuwa in kwamushe mutane a biyani kudi inji dadin rayuwa ta."

Tsaki habu ya yi ya ce, "To ku kunada iyayen ni ban san su ba,ban san kowa nawa ba , a anguwa dai ana kira da dan cikin shege ba mai shiga harkata bare damuwa da damuwata wannan sanaar ita ce kawai farincikina."

Zeeyter ta numfasa kafin ta ce, "To za mu taimaki juna in kun yarda amman zan taimake ku kuma nima za ku taimake ni, kai Sani da kake neman aiki ka kawo takardunka in sha Allah zan nema ma aiki ako ina na fadin duniyar nan kake so da ikon Allah,kai kuma Habu zan baka jarin da zaka dogara da kanka tunda baka yi karatu ba,amman inma kanason aikin akwai na compyanin gidan mai na muna da bangaren da zamu iya ajiye kowa, kai ma Usman ka fada abun da kakeso ba zai gagareni ba in sha Allah,sharadin dayane zaku taimaka mun wajen gano wanda yasa ku satoni da yake bibiyar rayuwata."

Sani ne ya fara washe baki yana, "Tabbas da naji dadi araina da ace aduniya za ana samun irinku da talaka bai wulakanta ba, bare har ya yi tunanin aikata ta'addanci ba, In sha Allah bana da matsala a bangare na."

Habu ma ya ce, "Tabbas nima ban da Matsala kin gama mun komai."

Usman ne ya dakatar da su da fadin, "Wannan ai iskanci ne da cin amana ni dai ban aminci ba kuma ban yarda ba,ba ma zan taɓa lamunta ba,nina gaba nine oga kuma na ce ban yarda ba."

Habu ya ce, "Ba zai sabu ba fa daman cen mu munsan kuskure muke aikatawa kaddarace kawai tasa muke rufe idonmu muna aikata wannan munnan aikin, yanzu kuma mafita ta zo baza mu ƙi ba."

"Ahto mu dai mu muka kawo kanmu kuma munce mun daina." habu ya fada yana tashi tsaye.

A fusace Usman ya tashi yana kokarin danna waya, "Yanzu zan kira shi in sanar da shi daga ku din har ita sai dai wasu bayanku, sai na ga bayanku."

Wani katon icce habu ya dauko ya makawa Usman akai nan take ya samu.

Sani ya ce, "Yawwa abokina kayi kyan aiki, yanzu kafin ya dawo hayyacinsa ya kamata mu gama aiwatar da komai."

Ficewa suka yi agidan gaba-daya harda Zeeyter.

Sai da suka yi nisa Sosai kafin Zeeyter ta karbi wayar sani.

★★suna zaune sai kiran Haiydar ake amman yaki dauka daga karshe ma tsaki ya yi ya kashe wayar.

Can kuma sai gashi an kira wayar Deedarth kamar shi ma ba zai amsa ba sai ya dauka.

Karawan da zaiyi a kunne kawai ji Muryar Zeeyter.

Ta shi ya yi tsaye yana, "Anty kina ina? Kina ina?"

Gaɓadaya Dukansu hankalinsu ya dawo kan Deedarth cikin sauri Haiydar ya fisge wayar yana, "Kina lafiya dai ko? Ba abun da ya sameki ko? Kina ina ne in zo in daukeki kar ki ce mun wani mummunan abu ya faru da ke." Gaɓadaya ya rasa abun fada sai kame kame yake.

Murmurshi Zeeyter ta yi ta ce, "Sunshine ka nutsu ina lafiya,amman gani cikin kauyen ƙure azo adauke ni, in ba hakan ba ci gaba da tafiyar mu akwai matsala."

Ko amsa Haiydar bai bata ba ya fice.

Binsa suka yi duka kowa ya dau mota.

Farouk ya kira police dinma ya bi su.

Suna isa Haiydar ya yi parking agigice yaje ya rungume Zeeyter.

Ita ma kankamesa tayi tana kuka.

"Me yasa zaki tafi ki barni ina kika je waya dauke ki? Kin san cewa ba zan iya rayuwa babu kai ba kuwa."

"Uhum Sunshine nima bazan iya ba,kaddarace ta so raba mu amman gani nan ai ko,ina sonka."

Ta fada tare da kara ƙanƙamesa.

Khaleel ne ya katse su tare da fadin, "Oh ya isa ko bamu da time anan yanzu muje gida koma Miye ayi."

Nan take suka shiga mota harda su sani da habu.

Bobiel suka wuce domin Haiydar yaƙi yarda aje Pleatau.

Suna zuwa...

★★★

Suna zuwa da gudu su baby suka fito suna rungume Zeeyter.

Miemie ta ce, "Anty ina ki ka je kwana biyu inata kewarki."

"Umm Anty nayi kewarki,kinki ki dawo ko."

Baby ya fada.

Murmurshi Zeeyter tayi ta rugumesu duka tana masu kiss tare da fadin, "Wani aiki naje kunji, ga shi na dawo yanzu ai."

Ciki suka shiga nan take zeeyter tasa aka kawo ma su Sani Abinci daga free food restaurants sai da suka ci duka suka yi sallah, Haiydar na biye da Zeeyter duk inda tayi ji yake kamar za a kara dauke mai ita .

Farouk ya ce, "Malam ka nemi guri ka zauna ko ba fi mu sonta kayi ba fa ehee muma ai ta mu ce."

Dariya Khaleel ya yi yana, "Yoo ina ruwanka,kasan yanzu ba komai zai na ganewa ba."

Zoe ma tayi dariya , "Wai mutum da matarshi ka ce ka fi shi sonta wannan ai wasa ce."

Shi ma dariya Farouk din ya yi kafin ya ce, "Yoo Gimbiyata ce fa tamkar jinin jikina take ehee."

Zeeyter na idar da sallah ta ce, "Yap Abokin Dole na, bari ma anjima akwai gulmar Sunshine."

Sai alokacin Haiydar ya yi dariya yana, "Inda sabo ai wannan kam daman kun saba."

Khaleel ne ya katse su yana fadin, "Ma sha Allah ga officer ya zo sai ku nutsu ayi abun da ya dace."

Karasowa police din ya yi tare da yin sallama.

Nan Zeeyter ta fara masa jawabin komai duk abun da ya fara daga nan su habu ma suka yi bayanin cewa sa su aka yi wanda ya kasance shi ne ogansu tun Asali.

A lokacin folis din ya tsara masu komai yadda za ayi har a kama ogan nasu .

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.