Free chapter · Read without an account
FREE PAGE-7
Bismillahir-Rahmanir-Rahim
Kullum kara takurewa take maimakon sake duk da cewa yana kokarin sake mata fuska yanzu amman duk da hakan a takure take. A hankali ta fara sabawa da kallon Tv da ya fahimci hakan in zai tafi Office sai ya kunna mata , aikuwa har yaje ya dawo zai tarar tana kallo ne,in ta gaji kuma wani lokacin ta yi barci.
Ya manta shaf da maganar Period dinta bare batun yin wankan tsark da Sallah kwana Bakwai kenan a lissafin da ya yi. Hakan yasa yana dawowa daga office a ranar ya jeta toilet yana dubawa kuwa ya ga Jinin ya tsaya har ma alamar gamawanta ya bayyana.
Wankan tsarki ya mata da kansa sannan ya ce tai alwala ta zo ta yi sallah.
★★★BAYAN SATI ƊAYA
Result din scanning da duk gwaje-gwajen da akai mata sun fito hakan yasa Ammur kaiwa Rowan Office dinsa yana, "Ga Result din 'Yar ka zan ce ne ko mutuniyarka oho dai, duba ka gani sai in kara ma bayani."
Karɓa ya yi,yana dubawa ya dago yana kallon Ammur, "ban gane ba"
"Abun ne da ban mamaki kwakwalarta na lafiya lau amman abu yana daf da taɓata,ga dukkan alamu a nazarina tana fama da cutar damuwa sosai wanda a karancin shekarunta babbar illa ne hakan, a kalla in za a raba shekarunta biyu to za a iya hasashen cewa daga rabin matsalar ta fara samo asali a lokacin da ta fara gane komai da kowa, akwai matsala babba wanda in ba a tashi tsaye ba za a iya fuskantar babban kaluben da ƙwaƙwalwarta zata taɓu kuma taɓuwa ba kadan ba, domin ta yi karama da kasancewa a wannan halin babba ma ya aka ji da shi da cutar damuwa bare yarinya karamar da bazata zarce shekara goma ba? Tana bukatar kulawa sosai,ja ajiki, wasa da dariya da duk wani abu da zai iya sa ta farinciki kuma ya kawar mata da tunani." Cewar Ammur
Rowan ya gyara zama yana, "Imagine! She's too young ta samu Wannan matsalar , atakaice ma ni ban taba zato ko tunanin za asamu irin wannan matsalar ga kananun yara ba, How?" Ya karasa maganar cikin yanayin mamaki da takaici.
Ammur ya ce, "Eheen wannan fa abu mai sauki ne a wasu kasasahen har ma sa Nigeria walau yaro ya rasa iyayensa an rasa me tallafa mai ko kuma yaran da ake haifa a yasar ,har ma wa inda yan boko haram ke rabasu da iyayensu, ka ga kuwa duk yaron da aka dakile masa rayuwa a daidai lokacin da ya fara ginata hakan zai zauna masa arai da zuciyane tamkar zanen Dutse,ko da nata baya cikin lissafin nan dai a arasa mai kamanceceniya da wani ba ."
Rowan ya ce, "Amman dai kam Allah ya kyauta,akwai babbar matsala a rayuwar Dan Adam wanda in ba mu gyara ba watarana za mu danasani mara dalili."
"Amin dai kam,ka ga yanzu dole ka jata a jiki sosai ta saba da kai ka zama abokinta ma inda hali,kuna wasa da dariya Sosai,ka ga inta shagala da wannan komai zai warware cikin sauki daga nan ina ga a iya samun mafitar da za a mikata ga ahalinta." Ammur ya fada.
Girgiza kai Rowan ya yi,yana jin jina abun aransa domin bai san ta ina zai bullowa lamarin ba,shi da tun yana karami baya shiga cikin yara sa'aninsa wasa bare yanzu, baya zama ya yi hira da kowa illa tattaunawa mai mahimmanci in ta tashi kan sa ne ya fara masa ciwo ya dafe yana fadin, "Ammur Please in da kwai sauran Drinks (giya) dinnan ka bani in sha ko zan ji daidai."
Dariya Ammur ya yi , "Aiko ba zan baka ba,ka kwanta kawai,kar ka manta fa kai ka hanani sha a cikin asibitin nan ka ce koma miye muyi a waje so bana zuwa da komai kuma kaima Dole ka yi hakuri,in kanka ke ciwo ka sha magani ka kwanta kawai zai fi ma."
Ko kulasa bai ba ya sake tsaki kawai.
Ji yayi kawai gwanda ya tafi gida ya kwanta hakan yasa shi tashi ba tare da ya cewa Rowan komai ba ya dau keyn motarsa ya nufi gida.
Ya shiga motar kenan sai ga kiran Mahaifiyarsa da suke mata lakabi da Ummu . Cikin bacin rai take magana , "Rowan wai kai baka da lokacin hutu ne a Nigerin gabadaya? Kwanakin nan ka kira ka ji lafiyarmu ma ya gagara? Me kake son zama ne? Duk aikin da kake komin girman koma mene ne ina umarta da ka tawo Malaysia cikin sati guda."
Kara ji ya yi kansa yana sarawa tare da fara kallon dishi-dishi.
Domin ya Tabbatar da cewa in bai je Malaysia ba akwai matsala don kuwa Ummu ta fi Abbu dinsu zafin zuciya da zafin rai in ta kafe kan abu duk rintsi ba za ta canja ba.
Ya kasa jurewa,ga Zancen Ummu ga na waccer Yar Tsintuwar ga ma maganar asibiti da suke tsaka da aiki sosai, figar motar yayi kawai ya nufi shagon da Ammur ya saba siya masu giya yaje ya siya ya fara sha kawai ba kakkautawa.
Kwance take akan kujeru ganin shigowar sa cikin wani yanayine ya bala'in razanata ta tashi tana kame jikinta da sa hannu a baki
Kwanciya yayi a kasan falon jikinsa ba kwari gabadaya can kuma sai barci ya kara kwashesa tana tsaye tana kallonsa har ya yi barci.
Karasawa ta yi a hankali ta zare masa takalman ta aje a gefe sannan ta dunga jansa har kan kafet din falon,ta dauko filo ta daga kansa ta sa masa zama tayi tana tagumi dayan hannun kuma na gado aka maka shi a baki tana kura masa ido.
Urs Xayyeesherthuo ***
TALLAH *🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝* *MTN* . *Airtel* 1GB = ₦300. 1GB = ₦300 2GB = ₦600. 2GB = ₦600 3GB = ₦900. 3GB = ₦900 4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200 5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500
*GLO* . *9MOBILE* 1GB = ₦350. 500Mb ₦500 2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100 3GB = ₦1050. 2GB ₦1600 4GB = ₦1400. 3GB ₦2000 5GB = ₦1750. 4GB ₦2500
*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH* For cable subscription or sell recharge card Call this number or whatsapp 👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 *🪀**** [2/20, 10:12 AM] Xayyeesherthul-Humaerath: *BOƊƊIYA*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
****
RUBUTAWA Aisha Sani Abdullahi *(Xayyeesherthul-humaerath)*
_Hi,Hello,Fans😍Gani na dawo da wani labari mai ɗauke da nishadantarwa, ilimantarwa ....... ba ma sai na ce komai ba,ku kun sani kuma zaku bada labari, Kafin in ci gaba da Series din Yel na ce bari mu taɓa wanan,kada ku bari a baku labari domin labarin na musamman cikin musamman dinma na daban ne_