Free chapter · Read without an account
FREE PAGE-6
Bismillahir-Rahmanir-Rahim
Murmushi Ammur ya yi,yana fadin" ba sace ki zan yi ba, nikam ma wai har yanzu ba ka san sunanta bane?" Ya karasa maganar yana kallon Rowan. "E to taya zan sani? Gwanda ma yanzu na ga kamar ta fara fahimtar Hausa a hankali." Ya kalleta kafin ya ci gaba da magana, "ka ga muje tare kawai tunda ta fara maƙe-maƙen nan na san ba zata yarda kuje ba." Miƙa mata hannu ya yi da alamar ta kawo nata ya rike, ta sunkuyar da kai jiki a sanyaye. Sai da ya ce, "ki kawo hannunki mu je." Ka fin ta miƙa suka tafi. Ammur kuwa ban da dariya ba abun da yake,yana, "Lallai wannan shine cakwakiya cikin wata cakwakiyar."
Dakin scanning suka nufa kai tsaye kasancewar Wannan ne fannin Ammur kuma shine shugaba a bangaren gyara na'urar ya yi yana , "Oya ta tazo ta ko ince ka zo ka kwantar da ita."
Nuna mata ya yi ya ce, "Oya jeki kwanta." Tsoro ya bayyana a fuskarta karara domin hatta jijoyin wuyanta sai da suka ƙara bayyana ƙarara. A hankali ta je ta kwanta. Rowan ne ya zare mata hijabi. Ana sa mata abun za ta yi kara kenan suka haɗa ido da rowan tai saurin taushe bakinta da hannu,ɗayan hannun kuma ta kankamesa tare da rufe ido.
Shi ko Ammur me zai yi ban da dariya. Har aka gama bata sani ba. Rowan yanata, "ki sauko an gama, bude idonki." Ina ita kam ta kankame jikinta,kuma ta rike masa hannu gam ga ido a rufe kamar wacce ake kokarin zarewa rai.
Sai da Rowan ya taɓata kan ta firgita cikin sauri ta bude ido Ya mata nuni da ta tashi ,ta tashi tana manna yatsan nan dai na fama a baki.
"Wannan fa mutum na da ita ya huta kallon Tv da bacin rai , Nishaɗi zatana bayarwa kyauta." Ammur ya fada.
Rowan ko kulasa bai ba ya jata suka nufi office.
Ranar ma haka suka wuni a office ko kallon inda yake bata yi, ko sallah ta ga yana yi bata ko motsawa bare alamar tashi yi,har sai ya ce ta je ta yi.
Sai a lokacin kwakwalwar sa ke tuna masa tun ranar da tsinceta da ta yi magana da wani yare bata kara yi ba sai dai ihu, "To ko dai bakinta ya rufe ne bata iya magana yanzu? In ba haka ba meyasa ban ji ta kuma yin magana da yaren ba ko sau ɗaya?Akwai Matsala." ya fada a zahiri yana kallonta.
Ko abincin da aka kawo ranar ma ƙin ci tayi sai da ta ga ya fara zare mata idanu kafin ta ci kadan.
Ji ta yi cikinta na mata wani azababben ciwo amman bata ma san yadda zata furta ba ga tsoron sa da ya gama shiga jikinta.
Dare na yi suka koma gida Bayan sun koma ta ji ciwon yanzu ya nunka na da awanda take ji,domin ta fara fita hayyacinta kamar wasa tana kokarin daga kafarta amman ina ta kasa motsawa ko kadan domin ta rike ,hawaye ne kawai yake sauka daga fuskarta, can kuma ta ji abu na fitowa daga gabanta, kallon da zata yi kawai jini ne gabadaya ya bata mata jikinta ga shi sai kara bulbulo mata yake.
Fitowar Rowan daga kitchen kenan yazo zai miƙa mata Abinci kawai ya ga hawaye a fuskarta ga yanayinta kamar ta kame,zai yi magana kallon kasa sai ga jini na fitowa daga jikinta.
"Subhanallahi ." ya furta a zahiri, cikin sauri ya dauketa ya yi toilet da ita sai da ya wanke mata jiki tas sannan ya tsaya yana tunanin abun da zai sa mata yana tare jinin,domin shi dai ba mace ba bare ace za asamu pad da pant kuma ita da yaje mata siyayya ya manta da batun pant din ma bare kuma pad.
Idea ce tazo masa,ya kira mai gadi awaya ya ce ya je ya siyo masa pad da pant cikin gaggawa.
Sannan ita kuma ya dau wata rigarsa ya sa mata agabanta duka yadda zai tsare jinin. Allurar rage radadi ya fara mata sannan ya nufi kitchen ya dafa mata Cinimon da citta kadan ya dibo a kofi ya bata, duk da cewa shi likita ne amman ya fi shawartar masu fama da ciwon mara yayin period amfani da ruwan cinimon da citta fiye da shan maganin bature ,yakan tanade su kuma domin dafa shayinsa a kullum don ya san amfani da darajarsu a jikin Dan Adam.
Cikin ikon Allah kuwa ya lafa mata tuni ta samu barci. Cike da Tausayi yake kallonta yana aiwatawa aransa, "daman yarinyar da ko balaga ba tai ba aka ma fyaɗe? Wannan kuwa wani jahilin ne? Allah dai ya kyauta."
Sai can dare ta farka a hankali take bude idanunta tana tuna abun da ya faru. Ita dai tasan a duniyarsu ranar da mace ta fara ganin wannan jinin aranar ake daura mata aure,amman daga nan kuma bata san shi kansa mene ne jinin ba bare kuma dalilin Zuwansa.
Ganin ta tashi ya zo yana mika mata pad din da pant ,ganin yadda ta zura masu ido ya sa shi kara tabbatar da cewa bata san ma yadda ake amfani da su ba.
Haka ya ciro pad din daya ya manna jikin pad din sannan ya ce ta daga kafafunta ya cire mata ta tashi,cire mata towel din ya yi tare da jan pant din har sama yana fadin, 'haka ake kin gani dai ko?" Girgiza masa kai tayi a dole ta fahimta. Daga nan ya dauko mata kayan barcinta ya miƙa mata, duk da cewa daman darene su zata sa,amman yana da kyau ma a kowanni lokaci in mace na al'ada ta kasance cikin sa kaya marasa nauyi, musamman ga masu fama da matsanancin ciwon mara. Karban kayan tayi tasa sannan ya bata ruwan Tea da snacks ya ce ta ci. Da kyar ta samu ta iya shan tean sannan ta ci gaba da barci.
Zuwa ya yi, ya kara yin wanka kafin ya sha tean shi ma ya yi nafila kafin ya kwanta.
Yana tashi da asuba ita ma kuwa ta tashi tsamo ta zauna suna hada ido zata sunkuyar da kai, tana jira ya yi salla ita ma ya bata umarni tayi.
Kallonta ya yi, yadda take rarraba ido tana kara taune hanunta yasa shi fahimtar jira take ya ce tai sallah.
Bayani ya fara mata da hannu da baki, karfi da yaji dai ya zama kurman dole.
"Ba za ki yi salla ba har sai wannan jinin ya daina fitar miki,kinyi wanka sai ki ci gaba da sallah, yanzu tashi zakiyi ki wanke jikinki sai ki canja wata audugar."
Haka dai ya ta faman mata bayani daidai gwargwadon iyawarsa ta fahimci wanda ta fahimta, ta bar masa wa inda bata fahimta ba.
Tashi ta yi tai wanka ta dauro alwalarta ,sai da ta fito sannan ta cire pad din ta ajiye masa akan gado. Tana kokarin sa wani.
Cikin sauri ya kalleta yana, "wai ke gidahumar ina ce? " A hasale ya ja hannunta da pad din ya nuna mata toilet yasa ta zuba sannan ya yi floshin yana"haka ake yi a yarda wannan,haba ke wai komai sai an nuna miki ne? Ina mamakin daga wacce irin kasa kika fito haka."
Ita dai idonta na kasa kawai tana jinsa. Suka fito ta dau sabon wani pant din da pad tasa kamar yadda ya nuna mata jiya.
Yana ajiyar zuciya kenan sai gani ya yi taje kan sallaya za tai sallah.
"Kee!! Kee! Allah na gode ma, wannan dai ina ga asalinki ba musulma ba ce a ko ina ma kike."
Zaunar da ita ya yi kawai yana ."Aa"
Tare da kara dafa kai zuciyarsa na masa sake-sake daban daban.
Zama tayi yadda ya ajiye ta na sunkuyar da kai.