Free chapter · Read without an account
FREE PAGE-10
Bismillahir-Rahmanir-Rahim
Free pages na daf da karewa In Sha Allah daman na ce ba zan yi da yawa ba.
*Payment Still On Going...*
Pay Into 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Access Bank
Evidence of Payment To *** In Kuma Kati ne ma Transfer Or Message ***
★★★
"Waye ne? Waye a wannan bangaren kuma?" Ta karasa maganar tana tura kofar. Rowan ma na jikin kofar tana rike da shi. Kafin Ummu ta karasa tura kofar da sauri ya turata baya. Tsayuwar mamaki Ummu tai ganin Rowan ta bude baki tana, "Kai ne daman,yaushe ka dawo,kuma ba wanda ya sani?"
Alamar rashin gaskiya ta gama bayyana a fuskar Rowan karfin hali ya yi yana kokarin fitowa tare da maida kofar ya ce, "Um Ummu jiya da daddare na so inyi surprising dinku ne, yanzu daman nake shirin zuwa bangarenku mu gaisa."
"Anya kuwa Rowan? Lafiya , kana Lafiya kuma?" Ta fada.
"Lafiya lau kawai dai ban bi jirgin safe bane sai na yamma." Ya karasa maganar yana bin bayanta.
Babban bangaren suka nufa inda ya fara cin karo da , Kakarsu wacce suke kira da Granny. Teɓe baki tayi tana fadin, "Wannan da ya manta danin kuma daga ina haka da sassafe kamar an korosa daga inda yake?"
Dariya Ummu tai tana, "Aikuwa mijin da ya jefar da matarsa ba ,da alama kam korosa akai,kin gansa ba zato ba tsammani ya dira kawai."
Karasawa ya yi ya rungumeta yana, "ta ma za ayi in manta da kyakkyawar zuƙekiyar mata ta? Hakan ma ba mai yiwuwa bane baby granny." Sunan da yake kiranta da shi kenan na zolaya
Kara taɓe baki tai tana, "yo na nawa kuma? Wayasani ma ko wata ka samo acen." Cikin dariya ya zauna daf da ita yana wasa da yan yatsunta. "Taya ma idanuna zasu iya kallon wata ne bayan ke? Ke fa ta musamman ce cikin mutane na musamman dinma shiyasa Kullum nake kara sonki,kin ga yadda kika kara kyau baby granny na ji haushi da GranFa ya rigani aureki."
Daga masa hannu Granny tai suka tafa tana jin dadi,domin kaf cikin jikokinta ba wanda take bala'in so sama da Rowan kasancewar shine jikan fari,sai ya zam tamkar abokinta, gata tsohuwa tukuf har haƙora sun zube amman gaye da daukan wanka kai kace karamar yarinya 'Yar Shekara sha biyar dake tashen budurci,kullum cikin gaye take,aduk inda take zaune ba arasa camb, madubi da jan baki bata da aikin da ya zarce wannan.
"Umm ka ga Bara na ci gaba da gyaran gashi nan kafin su hada mana abun karyawa." Karban comb din Rowan ya yi yana gani indai gyara miki.
Suna cikin haka sai ga Ammy Matar kanin babbansu,babbar munafuka kuma makirar da ke kulla makirci ba wanda ta tsana irin Rowan saboda ta lura da cewa gabadaya dangin anfi ji da shi kuma duk abun da ya zartar a gidan shine daidai sabanin yaronta da baya iya tsinana komai shi ko karatun ma bai tsaya ya yi ba.
"Good Morning Ammy."
Wani irin kallon tai masa tana ,"Morning yaushe ka zo ba ko sanar wa ko haka rayuwar yan Nigerian take zuwaan baƙo ba notice."
Murmushi kawai ya yi ya ce, "Jiya da daddare."
"Umm." Kawai ta furta tare da hardewa kan kujera tana danna wayar da ke hannunta.
Budurwar yarinyata ce ta shigo tana , "what am I seeing? Shiyasa na ji gidan nata kamshi yanayinsa ya canja ashe my favorite bro ne ya zo,no wonder." Ta karasa maganar tana rumgumesa fuska fal dauke da murmushi.
Magana yake yana ja mata hanci, "Asmy ba za dai ki bar zolaya ba ko?"
"Kai ma kasan gaskiya ne,yayana na musamman ne wanda yafi kowanni namiji kyau a duniya kuma yake fidda kamshi na musamman aduk inda ya kasance." Ta karasa maganar tana ko ba haka ba granny. Kallonta tai tana kallon madubi da shafa janbaki ta ce, "Kwaraikwarai kuwa kin san shi gadona ya yi a kyau amman kin ganki gadon uwarki kikai da hanci kamar takalmin wada." Granny ta karasa maganar tana harar Ammy da ke sam basa shiri ko kadan.
Dariya Asmy tai tana , "Jealousy kina jin tsoro zan kwace miki miji dai."
Ita ko Ammy taɓewa kaka baki tai ta gyara zama tana danna wayarta.
Ana kawo abinci kuwa sai ga Rashden babban yaron Ammy kenan wanda bai da damuwar data zarce masa cin abinci da neman mata. Gabadaya family din sun hadu a draining area Domin cin abincin safe duk sun gaisa da Rowan tare da farincikin ganinsa Musamman Samra da samir yaran kanwarsa Monah twins ne shekarar su uku cif a duniya basa ji ko kadan ba wanda suka bari a gidan musamman granny kullum cikin takura mata suke , Ummu kadai suke dan shakka don ko Ammy ma basu bari ba.
Rowan na gama gaida Abu ya ce shi yana so ya koma daki ya karya domin yana da meeting video call. Wanda a zuciyarsa kuwa ba wacce yake tunani illa Wacce ya bari a daki yasan in ya ci gaba da zama zai iya fara jiyo ihunta.
Haka ya tafi mai aikin gidan ta hada masa kayan karyawan ta bi bayansa da shi, tsayawa ya yi ta karaso ya karba domin baya son ta shige masa bangaren. Yana shiga kuwa ya tarar da ita tsugune bayan kofar da ya ɓoyeta tana ta shashsheƙar kuka.
Share mata hawaye ya yi,ya durkusa yana kama kunnensa, "Sorry,kiyi hakuri kinji, bana so ki gansu su taɓaki kuma ki ji tsoro, kina jin yunwa ko?."
Ta girgiza kai. "Tom ga abinci nan mai dadi nazo miki da shi oya bude bakin in baki."
Ko ci bai yi ba sai da ya tabbatar da ta ƙoshi sannan ya ci sauran.
Bayan sun gama ci ya kara gyara labulayen dakin ya rufe lungu da sako yadda ba mai fahimtar cewa da mutum a ciki in ba wai an shigo ba,ya ce, "Oya ki zauna kinji kar ki leka ko ina zanje in dawo ne,in kina jin barci ki hau gado kiyi kinji."
Ta amsa masa da kai.
Fita ya yi, ya koma cikin gidan ba don yana son hakan ba illa don yasan in bai fita ba za a iya shigowa.
Yana shiga kuwa Ummu ya fara tatarwa zaune tana aikin dubu sarkoki a falo ta ce, "Maddallah daman yanzu nake son turawa a kiraka,kasan dai ban da buri da wuce ace yau ka yi aure ko? Kai kuma a kullum na lura baka da kalmar da ka tsana fiye da cewa ta Auren ba,Rowan wannan karan ba zan taba sarara maka ba sai na tabbatar da cewa an daura aurenka da Asmy kafin ka bar kasar nan in ma zaka tafi da ita ko zaka barta anan bai dameni ba amman ka tabbatar da cewa babu fashi don a halin yanzu ma an riga da ansa rana shirye-shiryen biki kuwa daga gobe nake sa ran cewa In Sha Allah zamu fara."
Gaban Rowan ne ya fara rawa kan sa na kasa ba tare da ya dago ba ya ce, "duk yadds kika ce ya yi Ummu In Sha Allah ba zan taba bijire miki ba."
Ammy ce tazo dauke da wata kalanda a hannunta tana, "Yawwa ni fa har na zaɓa mana babban dakin taron da za ayi shagalin bikin nan don ni bana son karanta,so nake bikin 'Yata ya karade kafatanin garin Malaysia suji ya amsa."
Karfa Ummu tai tana, "ba matsala ya yi ai asamo contact din su kawai kuyi magana ko kisa Rashden yaje ya kama mana kan lokaci.
Rowan kuwa dakin granny ya wuce kai tsaye ya bar Ummu Ammy na faman kai kawo.
"Ah! Ya haka ne? Na ganka ba fara'a jiki duk a sanyaye me ya faru?" Granny ta fada. Karasawa yayi ya kwanta a cinyarta yana, "Me yasa kukeso sai nayi aure ne?"
Sai a lokacin ta harbo jirgin ta ce, "Eheen daman don haka ne kaketa kumbura kana batsewa na gulma kar mu ce kana so? Na fa na san kana son auren nan sarai wayancewa kake kawai irin abun da mahaifinka ya yi, da kyar ya amince da zaiyi aure amman abun mamakin shine ana aure wata biyu bai cika ba sai ga mahaifiyarka da ciki,yoo wanda bai son aure ya sankamawa mace ciki? Kai ma na tabbata haka za kai."
Dariya Rowan ya yi yana, "to ni ba ina da ke ba, ni ba sai anmun wani aure ba ke kadai kin isheni.....
Yanzu aka fara......
A yi mun afwa cikina ciwo yake na so in karkare free pages ayau amman ba dama watakila zai kai 12 ko 13 kafin mu shiga paid pages.
Thanks Oll ***
Urs Xayyeesherthuo
*🤝 SDEENDTM DATA SERVICES🤝* *MTN* . *Airtel* 1GB = ₦300. 1GB = ₦300 2GB = ₦600. 2GB = ₦600 3GB = ₦900. 3GB = ₦900 4GB = ₦1200. 4GB = ₦1200 5GB = ₦1500. 5GB = ₦1500
*GLO* . *9MOBILE* 1GB = ₦350. 500Mb ₦500 2GB = ₦700. 1.5GB ₦1100 3GB = ₦1050. 2GB ₦1600 4GB = ₦1400. 3GB ₦2000 5GB = ₦1750. 4GB ₦2500
*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH* For cable subscription or sell recharge card Call this number or whatsapp 👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽 *🪀**** [2/20, 10:13 AM] Xayyeesherthul-Humaerath: *BOƊƊIYA*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION✍🏼*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° ```Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.``` °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
****
RUBUTAWA Aisha Sani Abdullahi *(Xayyeesherthul-humaerath)*
_Hi,Hello,Fans😍Gani na dawo da wani labari mai ɗauke da nishadantarwa, ilimantarwa ....... ba ma sai na ce komai ba,ku kun sani kuma zaku bada labari, Kafin in ci gaba da Series din Yel na ce bari mu taɓa wanan,kada ku bari a baku labari domin labarin na musamman cikin musamman dinma na daban ne_