Free chapter · Read without an account

Chapter[5

by Hindatu Auwal · ZAREN KADDARA

*KANO*

Washe gari.suka shirya sukaje gidan sheik Ubaid Maaleek sukaimai godiya.

ananne yakegayamusu akwai walima dayahaɗamusu amma acikin makarantan za'ayi.

nanmadai godiya sukaimishi,sannan suka dawo.

sebayan sallahn isha'i suna zaune suna hira Alh.Zanna yakirashi yasanardashi tafiyansu jibi inAllah yayarda.

"tom"

kawai yace dashi don bayada yanda zeyi dashi,yaso yazauna daɗiyarshi datai shekaru bata aƙasar sedai betaɓamai gardamaba hasalima be'iya gardamanba.

washe garin ranan Asma'u taima Hamrah rakiya zuwa asibiti wanda Omar ne yakaisu.

scaining akaimata doctor tadubata ananne takesanar da'ita insha Allah asatinnan zatahaifi twins dinta kaman yanda E.D.D.dinta yanuna.

awannan ranan daga Asma'u har Omar basuda wani zance sena haihuwan.

Itadai Hamrah hakakawai takejinta wani iri jikinta yesanyi ƙalau hakama zuciynta,tinaninta dakomai nata baya cikin duniyan damuke ciki.itakanta bazatace ga'inda tinaninnata yakeba.

Omar da Asma'u sam basuluraba saboda yanda tazubamusu ido.dama hankali kegani ba'ido gululun banzaba.

"Nury wani suna kikeso asama yaran"

jintayi shiru yasa Omar huramata iska akunni,fuskanshi ɗaukeda murmushi yace

"hala yau ƴan miskilancin sunmotsone?!tunɗazu munata magana bakice komaiba"

maganan dayayine yasanyata dawowa cikin hayyacinta,numfashi tasauke fuskanta ɗaukeda tattausan murmushi.

dayike Asma'u akwai tazara atsakaninsu,Omar kuma message dinda akaturomai yaɗaukemai hankali shiyasa suduka bawanda yaji ajiyan zuciyan datasauke meƙunsheda ma'anoni mabanbanta.

"Noury please wani suna kikeson sanyama ƴan 2nki."

"Nadr da Nadarah"

"wow"

faɗin Asma'u.

"kaji suna masu daɗi hala larabawa zakihaifanmana"

Omar yafaɗa idanunshi akanta.

sanyayyiyar murmushi tasaki banda Asma'u datai dariya mesauti.

"nikam atinanina Falalu da Falmata za'asamusu."

cewar Omar cikin sigan tsokana.Hamrah takwabe fuska kaman zatai amai kamun murmushi yamaye gurbinshi.sakamakon dariyan da uba da ƴan sukayi cikin nishadi.

"Nury meye abinƙi acikin sunan da Abba yazabarmusu."

"ganemunhanya daga faɗi tayi kaman zatai amai f..."

"'idan kasake faɗin waɗannan sunayen zanyi amai."

dariya tabasu aikam sukasaki kayansu.sosai yanayin yakemusu dadi sunajin inama zasu tabbata ahaka.

"dare yayi kije kikwanta seda safe kikulada Addua."

tai maganan cikin sigan bada umarni.tana kallon agogon palon dayake nuna10:00pm"

"'insha Allah Nury seda safenku"

Asma'u tafaɗi tana wucewa ɗakinta,

"Zaki'iya tashi kosena dagaki"

hannunta tamikamai yaɗagota tamike akan kafafunta cikinta yasumabata yace,

"nagode da kyawawan yaranda kikebani,ei-nace yara saboda ƴaƴana dasuke cikinki thank you very much."

murmushi tayi domin magan-ganunshi sunyimata dadi.idanunta cikin nashi fuskanta daukeda murmushi

"nagode dakazama adalin miji agareni,sedai inason tinatardakai kyawawan badaganibane dagakaine,sakamakom fitarwa kadai nakeyi kaine engineern"

yemagana yanasaƙalo hannunshi cikinnata,

"nufinki Husna dani takekama kenan"

"aybama iya kamanba hadda surutun."

"oh!dama surutune dani?!"

yamaidamata damartanin maganan yana kashemata Sexy and Sleepy eyes nashi masu yalwan girmada haske kaman madara.

gani batada niyyan amsashi se murmushin datakeyi meƙayatarwa yasanyashi cewa.

"muje ciki kimun bayani"

baiya itakaɗaiba harshi dayemaganan sedayayi dariya,kayan wutan palon suka kashe atare bayan sunkulle ko ina sannan yadauketa itada cikinnata yanata setaimishi bayani.

_***_

Tsaye suke abakin motanshi suduka expression iriɗayane akan fuskokinsu shine basason rabuwa dajuna.

haka kawai emotions and impulse ɗindake aiki ajikkunansu adaidai wannan lokacin kesanyasu jin kaman sunrabu dajuna kenan,bazasu kara ganin junaba shiyasa idanuwansu kefitarda saƙon bankwana bataredasu-sun saniba.

"kikulamun dakanki don Allah,dakinji wani'abu ki flashing ɗina."

yanda yemaganan araunane yasanyata jin rauninta datakeda dannewa yanatasowa,hawayenda sukeneman taranmata tashanye.

"Allah yakiyaye hanya"

motan yashiga kaman yanda Asma'u tashiga sakamakon seyafara sauketa amakarantasu sannan zewuce gidan Alh.Zanna,amemakon yaja motan seyatsaya yanamata kallon bankwana.

Hamrah tazaromai ido cikin yanayin dayake ƙaramata kyau,kaman hadin baki sautikan muryoyinsu yaratsa masarrafan jinsu lokaci guda

"kikulamun dakanki,kakulamun da kanka"

sekuma sukai shiru suna kallon juna.ringing din wayanshi yakatse wannan kallon me daukeda dinbin sakonni masugirman gaske.

Ganin Alh.Zanna ne yasanyashi dauka cikeda girmamawa yasanardashi yanahanya,dukda batacemai komaiba yakaranci sakon insonka acikin kwayannin idanunta.

sanin kantane idan har tacigabada tsayuwa to shima tsayawa zetayi bazetafiba,se kawai tai juyawanta zuwa cikin gidan.

seda yaga shigewanta sannan yasauke numfashinda duk tsayin wannan lokacin besan yanariƙedashiba.

wannan shine karo nafarko da Asma'u da Omar suke zaune awuri ɗaya amma basacewa komai sesautin karatun alqur'ani dayake tashi ahankali,ahaka suka ƙariso harcikin makarantan.

kofa tabude tafito kaman yanda shima Omar ɗin yafito.rungumeshi tayi tsam ajikinta ahakan take cewa

"haka kawai nakejin kaman inkatafi bazaka dawoba don Allah kacemun zakadawo cikin koshin lafiya."

zuciyanshine takarye maganganunta suntaɓashi takowani fanni,baze'iya tare hawayanshiba.

"bazan iya miki alƙawarin dabanada tabbaci akaiba sbd banina halicci kainaba,tafiyana da dawowana suna wurin Allah,ahadussamadu,mekowwa,mekomai,meyanda yaso alokacinda yaso.

kedai kikasance me haƙuri da juriya,merunguman ƙaddara akowani irin yanayi."

"Abba don Allah ka daina magana haka"

tafaɗi asanda takeƙara cusakanta acikin kirjinshi.

"shikenan insha Allah zandawo gareki cikin koshin lafiya"

dayasan yanda takematuƙar buƙatan jin waɗannan kalman dazeyi tamaimaitawa harse tasamu daidaito aciki dawajen duniyanta,ɗagowa tayi tana kallon fuskanshi atsanake.

fiyeda kodayaushe tahango tsantsan kamanninta damahaifinnata,laɓɓan mahaifiyanta da jikinta kawai taɗauko amma har ƙwayannin idanunta kalanna Omar ne.

"sekadawo Allah yatsaremanakai daga sharrin mutum da aljan da karfe kowace irice."

sosai addu'o'inta sukaimai daɗi,hakanan sukai sallama badon zuciyoyinsu nasoba sedon basuda yanda zasuyi.

*ZARIA*

Awannan yanayin Adam yashigo bakinshi daukeda sallama,jin ba'a'amsaba yasanyashi zama akan kujera.

ajikinshi yafarajin Ummahnshi batacikin farinciki.

sosai zuciyanshi takebugawa tana bijiromai dasaƙon Ummah nabuƙatanshi hakan yasanyashi miƙewa yanakiran sunan ta cikeda kulawa.

Masu karatu kuyahakuri mutsaya anan semun hadu a chapter 6

Dafatan dai labarin yaƙayatar daku,wannan littafin gaba dayanshi kyautane agareku masoya,don Allah kuimana coment sannan kuimana sharing a group group naku.

Taku Hindatu Auwal

Seanjima

*ZAREN KADDARA*

*حبلاالقدر*

® By Hindatu Auwal

HIKAYA WRITERS ASSOCIATION

ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN

FACE BOOK:

WhatsApp:

AREWA BOOKS:

PHONE NUMBER:***

_______________________________________

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.