Free chapter · Read without an account
CHAPTER [31
shiru Nawaila yayi kaman bazece komaiba,shikanshi Sadauki yafiddaran jin wani abu daga gareshi,sekuma yaji sautin muryanshi ɗaukeda wani irin nisan taccen yanayi maradaɗi,
"'indasabo yakamata ace nasaba,yanayine dana tashi dashi tun banyi wayauba,
sedai nakasa!wasu lokutan har haushin kaina nakeji,akan meyasa bazan manta dasuba,?meyasa bazan daina buƙatan kulawansu agareniba?
aduk lokacinda naga iyaye da ƴaƴansu se in rinƙa jin wani abu anan ɗina!
yafaɗi yana nuna saitin zuciyanshi,
Dude inada iyaye amma banada maraba da maraya,nida akuyan da aka ajiye agarke bamada maraba,
kasan meyasa!
ye tambayan batareda kuma yatsaya yaji abinda Sadauki zeceba yacigaba,
Dude!inada shekaru 7 mahaifina da mahaifiyata suka rabu,bansan abinda yahaɗasuba amma naji ance wai tun asali mahaifiyan Daddy ne batason auren,shiyasa tasashi yasaki Mommy,
Mommy na kammala idda tai aure abinta,yanzu haka tana abuja,ta tara sabon iyali abinta,
Daddy ma ye aure amma yana zaunane a UK dayike acan yake business ɗinshi,
nikuma inanan tareda masu kuladani,banada matsalan abinci ko abinsha balle kuma kuɗi,
sedai narasa kulawa,suduka bawanda yadamu dani,balle kuma halinda nake ciki,duk shekara nakanyi wayada mahaifiyata sau ɗaya,nakanga mahaifina awasu lokutan dabazan iya ƙayya dewaba,
Dude banason wannan rayuwan,banason duk waɗannan kuɗaɗen da kayayyakin,kulawansu kaɗai nake buƙata,koyayane subani lokacinsu,
yaƙarke hawaye masu zaphi da ciwo nasauka akan fuskanshi,
ko tablet ɗinda kaga inasha bakuwwa yabaniba se ƴar aikin gidanmu,ita takoyamun shaa saboda nagayamata banasamun bacci....,
kukane yaci ƙarfinshi,Sadauki yariƙoshi yana buga bayanshi alaman lallashi,sedaya tabbatar yanatsa da wannan yanayin sannan yaɗagoshi,yaname kallon cikin idanunshi ye magana,
"dagayau bana buƙatan sake ganin waɗannan hawayen,tunda karigada kasamu maganin damuwarka!komai yarigada yawuce"
kallon mekakeson cewa Nawaila yabishi dashi.
"aduniyata mutun 2 nakedashi,kuma kagansu Mamy da Sameera,ayanzu kuma nasameka,don hakazamu raba soyayyan dasukemun atsakaninmu"
"are you sure"
kai Sadauki yajin jinamai alaman tabbatarwa,
"yi sauri kaje kawanko fuskanka kadawo"
bathroom Nawaila yashige,shikuma sadauki yazauna yana dafe kanshi,
***
cikin taimakon Allah suka gama shekarar farko dana biyu,inda ayanzu suke shekarar ƙarke a 2nd tirm,
sannan Sadauki yaƙara wayewa da buɗewan ido,komanshi yasauya saboda gogayya da mu'amala da mutane iri daban daban,
don ayanzu duk makarantan babu wanda baisan Kangiwa ba,wasukuma sukance Michael,saboda iya rawanshi salo salo,aranan social night har fili ake bashi kuwwa yakoma gefe yana kallonshi,
wasu kuma suna sonshine saboda kyawunshi,iya kwalliyanshi,dakuma ajinshi,don ba ƴan makarantan suba hatta ƴan wasu makarantan da Sadauki kezuwa quiz dakuma drama sunsanshi,
hakan yasa duk wani wanda yakeda taro na biki,kona birthday,kona party to seya gayyaci Sadauki,dagashi kuma har Nawaila basa wuce tayi,sedai duk wannan bidirin da'akeyi betaɓa yarda Mamy tasanda wannan ɓangaren nashiba,
@@@
matashin saurayine ɗan kimanin shekaru 15 tsaye agaban madubi,dogone sosai,kuma fari,fari ba irinna africans ba,fari irinna asalinsa wato fulani,
yanada dara daran idanu da dogon hanci,mai yawan gashin ido dana gira gazar-gazar,ga sumansa ta asali wato fulani takwanta akansa tai luph,
cikin askin high fade,ga kuma razor part agefe,kamannin fuskarsa sune suke bayyanarda asalinsa na hausa fulani,irinshi ake kirada end of discussion,
wani irin kyau gareshi meban mamaki,da ɗaukar hankalin me kallonsa,tiraren hannunshi ya ajiye,yana sanyane da ƙananun kaya dasuka fito daga companyn Gucci,
yaɗauki school bag ɗinshi dake gefe,tun last week aka koma makarantan amma yaƙi komawa,sanadiyyan haka har faɗa sukayida Nawaila,bakuma don yanada wani uzuriba,
cikin takunsa na ƙasaita,izza dakuma aji yafito palon,akwance yaga Mamy akan kujera,yaƙarisa kusada ita yazauna,
hannunta yakamo seyajishi yaɗau zafi,bece komaiba yakai hannunshi kan wuyanta,zafinda yaji ajikinnata yatabbatar maida batada lafiya,
"Mamy bakyada lafiya,"
cikeda kulawa ye maganan yana kallon ƙwayan idonta,
tai murmushi tace,
"karkadamu bawani ciwobane,idannasha paracetamol zan warware"
tunda tafara magana yake kallonta,yasan halin Mamy,batason zuwa asibiti da shan magani,
hakan yasanyashi cewa,
"tashi muje asibiti"
yaƙarke yana miƙewa daniyyan ɗaukomata mayafinta,shiru Mamy tayi tasan halinshi kome zata faɗa baji zaiyiba,
shida kanshi yasan yamata hijjab ɗinda yaɗauko mata,tana miƙewa jiri yaɗibeta,ye saurin riƙota yana mitan yanda batadamuda lafiyantaba,
tun kafin su'isa asibitin yakira doctor Mu'azzam yagayamai suna hanya,don haka suna zuwa suka wuce office ɗinshi,
bayan yagama dubata yasanar dashi gado za'abata saboda jinintane yahau kuma ga zazzaɓi,
wayanshi yaɗauka yakira Sameera yagayamata tasanarda sauran mutanen gidan ankwantarda Mamy a asibiti,
ko mintina 30 ba'ayiba segasu sunzo,sedai doctor yahana shiga saboda anmata alluran bacci don haka tana buƙatan hutu,
Sadauki nazaune akujeran dake gaban gadon idanunshi tsaye ƙyam akan Mamy,ahankali yaga tabuɗe idanunta,
"sannu Mamy"
yafaɗi yanakai hannunshi saman goshinta,domin yaji ko zazzaɓin yasauka,
"kai nafaji sauƙi dama bawani ciwobane"
"Mamy wannan ne baciwoba?koda bari kiwarke faɗa zamuyi dake sosai"
ye maganan muryanshi dake asanyaye nafitarda ɓacin ranshi,
"bari inje inkira doctor"
yace yana ƙoƙarin miƙewa,Mamy tariƙoshi tanacewa,
"dawo kazauna akwai maganan dana keson muyi"
dawowan yayi yazauna,
"Sadauki akwai abubbuwan danakeson inroƙeka amma bazan faɗaba sekaimun alƙwari,"
ye shiru yaname sunkui dakanshi ƙasa,haka kawai yakejin gabanshi na faɗuwa,haka kawai yaji bayaso jin koma meye zata faɗa,
"Sadauki kaimun alƙwari"
Mamy takatsemai tinani tana kamo hannunshi,ayanayin dayake ciki bayajin koya buɗe bakinshi sautin muryanshi zata fito,don haka seya gyaɗamata kai,
"Sadauki inason kaimun alƙwarin duk yanda rayuwa zatayi dakai,duk wani kallo da ƙaddara zataima,bazaka sauyadaga yanda kake ayanzuba,bazaka rabuda komai danabakaba"
setai shiru tana kallonshi,hakan yasanyashi buɗe bakinshi,muryanshi tafito can ƙasan maƙoshi,
"Mamy naimiki alƙawari"
"Sadauki burina ɗayane aduniya shine inga rananda iyayenka da ƴan uwanka zasu tashi daga zaman son zuciyan dasukeyi,rananda zasu amshi kusa kurensu,
sedai bansaniba ko ubangiji zemun wannan tsawon ran,amma inada tabbaci akanka,inada cikakken yaƙini akan abinda zefito daga bakinka,
Sadauki kaimun alƙwari zaka koma hannun iyayenka aduk lokacinda suka buƙaci hakan"
dasauri yaɗago ƙwayan idonshi yasauke akan Mamy,seadai kallonda Mamyn taimishi cikeda roƙo yasanyashi jinjina kanshi batareda yasaniba,
Mamy tai murmushi tana lumshe idanunta,doctor mu'azzam ne yashigo kallo ɗaya yema Mamy yaji gabanshi yafaɗi,hakan yasanyashi ƙarasowa bakin gadon dasauri,
Sadauki dake zaune yamiƙe ganin Mamy takoma bacci,bece komaiba yafice abinshi,me adai daita yanima yakaishi gida,
***
su Sheik Usman nazaune 'a VIP reception Doctor Mu'azzam yashigo,
"Doctor yajikinnata"
suduka suka tambaya,ya sunkuyarda kanshi ƙasa yaname basu amsada,
"mejiki tawarke"
"zamu iya shiga kenan"
Muhammad yafaɗi yaname miƙewa,
becemai komaiba yakalli Sheik Usman yace,
"Sheik ɗanzo mui magana "
bamusu yamiƙe,can gefe suka koma,Doctor Mu'azzam yakalleshi yace,
"Sheik sefa haƙuri,Allah yarigada yayima hajiya rasuwa"
*SADAUKI*
zaune yake acikin palon,yana duba wani project da'aka turomai daga Ɗanƙasa Building And Construction Company,dayike ayanzu shine wanda yakemusu duk wani zane zane dasuke buƙata,
Ƙaran ambulance yaji,yaɗan dakata da abinda yakeyi sakamakon hayaniyan dayaji,
kusan mintuna 20,segasu sunshigo tareda gawan mamy,
tunda suka shigo yatsaya ƙyam yana kallonsu,jiyakeyi kaman ankafeshi,kokawa yakeyi da numfashin shi dake neman ɗaukewa,
daƙyar ya'iya kai hannu yabuɗe fuskanta,yana kallon yanda Sameera data shigo take kuka kaman ranta zefita,
wani irin ciwo zuciyanshi takemasa,ƙirjinsa yamasa nauyi,
Masu karatu kuya haƙuri mutsaya anan semun hadu a chapter 32
Dfatan dai labarin yaƙayatar daku,wannan littafin gaba dayanshi kyautane agareku masoya,kudai kui mana comment,kununamana reaction dinku,sannan kui sharing a group group naku.
Taku Hindatu Auwal
Se anjima............
*ZAREN KADDARA*
*حبلاالقدر
®By Hindatu Auwal
*HIKAYA WRITERS ASSOCIATION*
ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN
FACE BOOK:Littafan Hausa Novel Only
WhatsApp:
AREWA BOOK:Hindatu Auwal
PHONE NUMBER:***
_______________________________________