Free chapter · Read without an account

CHAPTER [45

by Hindatu Auwal · ZAREN KADDARA

"Iname baki haƙuri akan magan ganun dazasu fito daga bakina,nasan babu ko kalma ɗaya daze miki daɗi,to amma nima banida yanda zanyine,dabazan gayamikiba.

Asma'u iyayena sunce basu aminta da aurena dakeba,idan kuma har inasonki bazan iya rabuwa dakeba to sedai nanimi wasu iyayen su ɗauramun aure dake,bakuma don komaiba sedon bakyada iyaye.

Wannan dalilin yasa naƙi ɗaukan wayanki saboda ba maganan waya bace,tayu kafin nagama miki bayani kikatse wayan"

"Ai nafahimci magan ganunka Kabir,kuma iyayenka sunada gaskiya,kawai dai mui addu'an Allah yahaɗa kuwwa da rabonshi"

"Asma'u hakan bayana nufin mun rabubane"

"Kabir yakakeso muyi,a maganan pha dakayi yana nunida indai har kamatsa seka aureni to sedai kabijirema maganan iyayenka,nikuma kasan bazan taɓa amincewa ka aikata hakanba."

"Asma'u don Allah kitina,kisake tinawa ko zaki iya tina wani abu agameda danginki"

Kanta ta girgiza hawaye naƙara gudu akan fuskanta,cikin sheshsheƙan kukan da takeyi tafurta,

"Bazan iyaba"

"Yarabh!!!"

Yace cikin rashin sanin madafa,balle kuma makama.

Ganin haka yasata cewa,

"karka damu Kabir,wata ƙila daidai dani zezo wanda shima bayida dangi kamarni,kaga semui aurenmu"

"Asma'u"!

"kaga Kabir kawai kayahaƙuri seda safenmu"

Tana kaiwa nan tajuya abinta duk da kiran sunanta dayakeyi,

Tana shiga palon sukai kaciɓiss da Ummah dazataje sashin Abba.

"Ke inata kiranki kizo intam..."

Sauran maganan natane yamaƙale amaƙo gwaronta,ganin fuskan Asma'u sharkaf da hawaye,

"Asma'u lafiya meyafaru"

Ummah tafaɗi cikeda damuwa,tana kamota tazaunar,

"Bakomai"

Asma'un tace tana ƙoƙarin share hawayenta da suka kasa daina zubanmata,

Mardy tace,

"ai naɗauka zaki samu natsuwa da kwanciyan hankali tunda Kabir ɗin yazo"

"Wallahi Ukty dama bezoba"

"Wai meyafaɗa mikine"

Ummah ta tambaya.

Asma'u ta amsata cikin kuka,

"yafaɗi cewa iyayensa sunƙi amincewa ya aureni saboda banida iyaye hasalima banida kuwwa"

"Yanzu tsakanida Allah akwai wanda yakamata namiji ya'aura wacce tafiki?

Akwai macenda yakamata ahaɗa zuri'a da ita samadake?wai meyasa mutane basada tinanine balle hankali"

"A'a Ummah kada kifaɗi haka,kuma ni aganina sunada gaskiyansu,kwata kwata banga laifinsu awannan al'amarinba"

"Kinsan menene yakamata muje musamu Abbanku mugayamai"

"A'a Ummah kibarshi kawai dare yayi"

"Shikenan Asma'u zan kwana taredaku"

"A'a Ummah kije kawai abinki,ba'abinda zefaru kuma ga Mardy ma,imma don wannan kukan dakikaga inayine inayine badon komaiba sedon iyayena danarasa"

Dukda Ummah taji abinda tace ƙinyarda tayi,sanin bataci komaiba yasa Mardy haɗamata tea mekauri,taɗaukomata snacks ɗinda sukanyi su ajiye.

Ganin yanda duk suka tada hankalinsu yasanyata karɓan cup ɗin tashanye,

Washegari suna zaune apalo Abba yashigo,zamewa sukayi dagakan kujeran da suke zaune suka gaidashi,

"Lafiya ƙalau_yajikinnaki"

Yakarke,yana maida akalan maganan zuwaga Asma'u,

Asma'u tace,

"dasauƙi"

"Asma'u naji duk abinda yafaru abakin Ummahnku,don haka inaso kiyahaƙuri,kirungumi ƙaddara,insha Allah mijina nanan zuwa,wanda yadace dake,kuma irin wanda kikeso insha Allah,wani hanin ga Allah baiwane"

"To Abba"

Mahmud yace,

"senadawo"

"Tom adawo lafiya"

Suduka suka faɗi,

*UMMAR*

Da sallama yashigo cikin ɗakin,Jameela da fitowanta kenan daga cikin bathroom ta'amsamai tana zama abakin gadonsu,shima zaman yayi akusada ita.

Kana kallonshi zaka shaida farinckin dayake ciki,hannunta dayasha jan lalli yakamo yana cewa,

"Albishirinki"

"Goro faritass!"

Jameela tabashi amsa fuskanta nacikada murmushi,duk da batasan farincikin dayake cikiba.

Omar yace,

"ina contract ɗinda nace miki munanima"

"Eyyy"

Ta'amsashi dasauri,

"Shine aka kirani yanzu aka sanardani munsamu,gobema zanje aimana signing"

Rungumeshi tayi tana cewa,

"Alhamdulillah!Allah mun godemaka"

"Aifa Allah shine abin godiya,don banyi zaton zamu samu contract ɗinnanba saboda manema sunyi yawa"

***

Washe gari 10:00pm Omar yashiga garin kano,garinda rabonshi da ita shekaru biyar kenan,

Garinda yashigo cikeda farinciki,yafice cikin yanayi meciwo,ciwonda zezauna ataredashi har ƙarshen rayuwanshi.

Yana packing yafito,kai tsaye ciki yashiga,sectary ɗinda ke zaune agun yashigar dashi,nan danan yasamai hannnu bayan yemai congratulation,

Wayanshice tahau ruri asanda yake fitowa daga office ɗin,sunan Wifey daya bayyana yasanyashi ɗauka yana murmushi,

"Mijina"

"Na'am matar mijinta"

Ya'amsata,yanajin dariyanda tayi,tukun tacigabada magana,

"Ka'isa lafiya"

"Lafiya...

"Omar....."

Sunanshi da'aka kira yakatse maganan dazeyi,

Ido huɗu sukayida Alh.Zanna dake nesa dashi kaɗan,Omar ye tsaye yana murmushi kaman yanda Alh.Zanna ke dokamai murmushi,

"Ashe rai kanga rai"

Cewan Alh.Zanna asanda yaƙariso gaban Omar,

Omar yafaɗaɗa murmushin shi yana miƙamai hannu sukai musabiha,tsayawa sukayi suka taɓa hiran yaushe gamo,sannan sukai musayen number kafin su rabu.

*MARDY*

Tana fitowa daga adai-dai tan tanufi gida,yau ɗinnan agajiye take komai yafita daga kanta,ba'abinda take bumata samada taji haƙar-ƙarinta akatifa,

Sadauki tahango atsaye,yajingina dagaru,hannunshi riƙeda wayanshi yana dannawa,

Kananun kayane ajikinshi dasukai matuƙar dacewa da ƙerarren jikinshi me tafiya da ƴanmata.

Duka wannan kallon taimaine aƙasada daƙiƙu biyar kuma lokaci guda taɗauke kanta,ɓacinrai na ziyartanta wanda yanuna har akan fuskanta,data ɗaureshi tamau tamkar batataɓa dariya ba 'aduniyannan tamaliki yaumiddini.

"Mardy don Allah kitsaya ki saurareni"

Sadauki yafaɗi cikeda magiya,yana shan gabanta,ganin tana ƙoƙarin wuceshi tamkar batasanda wanzuwanshi agunba.

Batace komaiba seɗauke kai datayi taraɓashi daniyyan wuceshi,

Yaƙara shan gabanta,kaucewa tasakeyi,sekawai yasa hannunshi yadafe garun gate ɗin,

Motsawa tayi daniyyan wucewa taɗanyan ɓarayin,ye saurin maida ɗay an hannun nashi,seya zamana yasakata atsakiyan hannayenshi,

Masu karatu kuya hakuri mutsaya anan semun hadu a chapter 46

Dafatan dai labarin yakayatar daku,wannan littafin gaba dayanshi kyautane agareku masoya,kudai kui min comment,kununa min reaction dinku,sannan kui min sharing a group group naku.

Taku Hindatu Auwal

Se anjima.....

*ZAREN KADDARA*

*حبلاالقدر

*By Hindatu Auwal*

*HIKAYA WRITERS ASSOCIATION*

*ZAKUIYA SAMUN WANNAN LITTAFIN*

FACE BOOK:Littafan Hausa Novel Only

WhatsApp:

AREWA BOOK:Hindatu Auwal

PHONE NUMBER:***

___________________________________

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.