Free chapter · Read without an account

7

by Khadeejarth Sabi'u Yahyah · SHANTYTY: ƘANWAR MANGA

*SHANTYTY💃💕*
_The Little Sister of Manga_
*_(ƘANWAR MANGA)_*

A charming cinematic Hausa comedy-drama that celebrates family, friendship, mischief, and the unforgettable journey of a spirited young girl whose presence changes everyone's life.

Nainarh KD...❤️

Page 7

"Ke kuma daga ina kamar wacce aka hankaɗo ko aka biyo da gudu?."
Sai da ta ƙari sa ta zauna, kusa da Kaka dake zaune, ta gama lazimi ke nan taga yadda Shantyty ta shigo mata ɗin ko sallama babu, ya sa ta faɗa hakan, Shantyty ta taɓe baki tana wani hura hanci ta ce. "Hu'uhmm toni akwai ma wanda zanji tsoronsa ne da har zai biyoni na gudo gida a guje haba ai babu wannan kema dai Kaka kamar kina man ce wacece ni ko?."
Wani duba Kaka ta yi mata sannan ta kauda da kai tana faɗin. "Shikenan fa kin dawo zamu d'aura daga inda muka tsaya, yanzu dai tashi ki fara komawa kiyo sallamar da kika manta sai kace wacce bata zuwa islamiyya."
Turo baki ta yi tana shirin yin mu su ganin Kaka ta ɗaga carbin hannunta kuma tasan hali tsaf zata iya tsafɗa matan hakan ya sa ba shiri ta koma ta yi sallamar tana turo baki.
"Faɗa min daga ina kike da sai yanzu nake ganin kafarki." Cewar Kaka Idonta akanta.
Shantyty ta gyara zama tana ɗan muskutawa ta ce. "Hmmm Kaka ke nan ai in ana sallah ba'a magana, ai dama nasan duk gwaraman da aka sha bakiji ba kina can kina wannan wankan naki kamar zaki sauya fatar jikinki."
"Ni dai ba dogon bayani na tambayeki ba." Cewar Kaka a ɗan kufule dan ta tsani dogon bayani idan tambaya ɗaya ta yi.

"Ni dai ba dogon bayani na tambayeki ba. Daga ina kike?" Kaka ta sake maimaitawa.

Shantyty ta yi shiru na ƴan daƙiƙu tana kallon Kaka, sai kuma ta sauke numfashi ta ce.

"Toh ai daga wajen Karime nake."

"Karime?" Kaka ta tambaya kamar bata gane wacce take nufi ba.

"Eh mana haba kema Kaka kina wani tamabaya kamar bakisan Karime ba ƙawata"

"To me ya kai ki wajenta?"

Shantyty ta ɗan yi murmushi tana yi ma Kaka wani duba sannan cikin zolaya ta ce,  "Hmmm da alama dai rikicin tsufan naki ne ya motsa."

Kaka ta galla mata harara lokaci guda tana ɗaga carbin hannunta take faɗin. "Ki fa kiyayeni Yar nan ni nan har wani tsufa nayi gani da hakorana talatin da biyu curr kike wani kiramin tsufa."

Shantyty ta sheke da dariyar da ya ƙara kufular da Kaka. "Ki ci gaba uwarki zan faɗa ma duk Abin da kikeyimin tun da ni kin rainani." Jin abin da Kaka ta faɗa ne ya sa Shantyty sai ta nutsuwarta ba shiri ta ce. "Haba da wasa fa nakeyi miki Kaka ta abar ƙauna tah ai Bama yar haka dake Dan Allah karki faɗa ma Umma kinji Kakalle tah?." Kaka ta wani taɓe baki tana yi mata kallon ba zakiyimin wayau ba amma sai ta basar ta hanyar fadin. "Yanzu fada min, ina da ina kuke je keda Karimen?."

"Mun fita ne muka je neman magana." Kai tsaye amsar da Shantyty ta bata ke nan.

Da hakan ya sa Kaka ta zaro ido. Tana maimaita kalmar. "Neman magana?"

"Eh mana." Ta amsa mata babu alamar damuwa a tare da ita, "A'ishatuuu!" Kaka ta kira sunanta da karfi.

"Toh Kaka me zan yi? Na kwana biyu ban samu damar neman magana ba, kema fa kin san halin Umma bata bari na fita ko nan da can idan bada kwakwkwaran dalili ba muddin naje gidanta shi ya sa banason zuwa."

"Allah Ya shirya ki. Yanzu to kin dawo daga neman maganar ke nan?" Abin da Kaka ta iya faɗa ke nan hankalinta akanta.

"Hmmm ai Kaka bakisan badaƙalar da aka yi ba ne yau ɗin nan." Cikin son sanin abin da ya faru Kaka ta ce, "Me ya faru?"
Shantyty ta gyara zama, sannan ta fara ba ta labarin abin da ya faru tun daga lokacin da ta fita ta bar gidan zuwa ƙari sawa gidansu Karime da ta yi da sauran al'amuran da suka biyo baya tsakaninta da Gwage bata rage mata komai ba dama kuma haka take ba ruwanta sam bata da boye-boye.

Ta ci gaba da faɗa mata yadda Antyn Karime taje ta fita neman 'yarta, yadda ta ga Teemah a hannun Gwage, har zuwa lokacin da aka tona asirin abin da ya faru.

Da ta kai wajen yadda ta shiga cikin maganar aka dama da ita har ta saka mutane sukayi ma Gwage duka, ai Kaka sai ta kasa magana ta riƙe haɓa da kyar ta iya faɗin,  "Subhanallah..."

Ta faɗa a hankali tana girgiza kai.

"Toh wannan mutumin... ina hankalinsa yake?" Ta sake faɗa cikin tu'ajjibi Gwage take nufi.

Shantyty ta ɗaga kafada, tana wani taɓe baki ta ce,  "Ni ma ban sani ba Kaka. Amma wallahi na ji haushi sosai. Da farko ma ya ƙi yarda saboda bashi da kunya fa sai ya ƙaryata zargin da ake masa. Amma na faɗa musu abin da na ji tun da farko da hakan ya sa dole ya karba laifinsa."

"Ikon Allah to me kikaji?" Kaka ta tambayeta har lokacin kuma hannunta na kan haɓarta bata dena mamakin al'amarin ba.

"Eh. Tun lokacin da na shiga shagon a d'azu ke nan domin na siya kati da Umma ta aikeni, a lokacin naji kamar kuka amma ya rainamin hankali ta hanyar cewa ba'a shagon bane munafikin."

Kaka ta sauke numfashi. "Allah Ya tona asirin duk mai irin wannan hali. Wannan yarinyar fa ina fata dai lamarin da sauki?"

"Ai an kai ta asibiti." Shantyty ta amsa mata.

"Yanzu tana can asibitin?"

"Eh."

Kaka ta yi shiru na ɗan lokaci, fuskarta tana nuna zallar tausayi da kuma al'ajabin lamarin kafin ta sake furta, "Allah Ya bata lafiya. Allah Ya sa ta samu sauƙi. Yarinyar ƙarama haka gaskiya bai kamata a kyale yaron nan ba sam..."

Wannan karon sai da Shantyty ta ɗan yi shiru. Cikin jimamin abin kafin ta furta, "Ni ma dai Kaka abin ya taɓa ni sosai Wallahi."

Kaka ta ɗan kalle ta. "To ai duk da halinki na neman magana, kina da zuciya mai kyau."

Shantyty ta yi murmushi tana wani gyara zama ta ce "Ai na sani."

"Ba ki da kunya." Cewa Kaka tana taɓe baki.  "Shi ma na sani." Shantyty ta sake faɗa cikin salon neman magana.

Kaka ta girgiza kai tana murmushi ta ce, "Allah Ya shirya ki, jikalleta ya kuma nunamin aurenki."

"Ameen."

Sai kuma Shantyty ta kalli gefe kamar wacce wani abu ya fado mata a rai ta tuna da shi. A fili ta furta, "Au!"

Kaka ta dubeta, tana tambayar, "Mene ne kuma?"

Shantyty ta buga tafin hannunta tana tashi tsaye ta ce,  "Na manta!"

"Kin manta me?"

"Ina wannan kular Umma ta bani na kawo miki!"

Kaka ta taɓe baki cikin ko'in kula ta ce. "Oho ai sai ki nemota."

Shantyty ta kalli hannunta kamar zata ga kular a riƙe sai kuma ta dafe kanta alamun tana nazari.

"Ni kuwa a'ina ma na ajiye kular nan ne?" Sai kuma ta dubi Kaka. "Anya Kaka baki cinye abin da ke cikin kular ba shi ya sa kika wanke kika ɓoye saboda kar na gani."

Kaka ta dafe kai tana faɗin, "Allah Ya kyauta ke ɗin ce zaki sakani wahalar wankewa da ɓoye kula saboda an bani abu na cinye baki sani ba, ai Malama ki saki jiki kawai ki nemo inda kika aje kular nan."

"A'a Kaka, tana nan. Na dai manta inda na ajiye ta ne."
"To ai sai ki nemo." Cewar Kaka tana taɓe baki.

Shantyty mikewa tsaye ta yi da sauri har tana kusan haɗa hanya wurin fita daga Dakin ta ce, "bari dai na nemo tun kafin Umma ta kira kice mata ban danƙa miki kular ba."

Kaka ta girgiza kai ta ce,  "Ke ai dama kin fi tsoron Umman nan taki akan kowa."

Shantyty ta tsaya cak daga fitan ta juya ta duba Kaka ta ce, "Ni fa ba tsoron Umma nake ba kawai ina gudun ɓacin ranta ne."
Kaka ta juya kai gefe alamun maganar bata shige ta ba lokaci guda tana faɗin, "ko kuma kina tsoron kisha duka ba."

"Ni dai girmamawa nake mata da gudun ɓacin ranta ba wani abu ba." Shantyty ta faɗa tana wani juya ido. Kaka ta yi dariya, "Ai fa girmamawar ne ya sa idan kika ji muryarta a waya sai ki fara neman inda za ki ɓuya?"

Shantyty ta turo baki ta ce, "wai ke Kaka bakya mantuwa ne?"

"Ina fa zan manta kuwa kedai jeki nemo kular." Kaka ta faɗa ba tare da ta kalleta ba.

Ta yi sauri ta nufi inda ta ajiye kayan a waje, tana faɗin:

"Amma idan akwai nama a ciki, Kaka sai dai fa kiyi hakuri domin ni ce zan cinye amma fa karki faɗa ma Umma kinji..."

"Ai kuwa sai na faɗa tun da ita kike tsoro bani ba." Kaka ta amsa mata tun kafin ta rufe baki.

"Ai shi ke nan Ba ma ci zan yi ba.dama tsokanarki nakeyi"

Kaka ta girgiza kai tana dariya ta ce, "ai kuma sai kiyi bani da lokacin ki."

Shantyty ma ta juya tana murmushi ta amsa da, "Ke kuwa kike da lokacina Kaka bari dai na nemo kular nan."

Bayan ɗan lokaci Shantyty ta dawo ɗauke da kular a hannunta. Ta washebaki tana faɗin "Ga ta nan!"

Kaka ta gyara zama ba tare da ta ce komai ba, ita ta yi ma kular kyakkyawan boyo bayan fitan Shantyty daga gidan a dazu sai dai taki sanar da ita ne saboda taga ko zata iya nemowa.

Shantyty ta zauna kusa da ita, ta ajiye kular a gabansu. Kaka ta buɗe murfin a hankali. Nan take ƙamshin abin ciki ya cika ɗakin.

Shantyty ta zaro ido. Tana wani haɗiyar yawu har da lumshe ido lokacin da ta yi arba da abin da ke ciki.

Kaka ma ta ɗan matsa kusa da kular tana faɗin, "ma sha Allah gaskiya 'Yar nan ta kyauta kamar kuwa tasan kwana biyun nan da kwadayi nake kwana na tashi Ubangiji ya yi albarka ya sa ma sana'ar ta albarka ke Shantutuwa mene ma sunan wannan abin daɗin da Ingilishi."

Shantyty dake ta dariyar wannan sambatu da Kaka keyi ta ɗan tsagaita da dariyar tana amsa mata da "Pepper soup ne!" Bata ji haushin kiranta da Shantutuwa da Kaka ta yi ba saboda kayan daɗin dake gabansu amma da da ne da tuni ta fara yima Kaka rigima akan ta ɓata mata suna.

"Kai Kaka! Naman nan da gani an san ya dahu ligif kuma zai yi dad'i a baka bari muji..." Ta ƙare maganar tana daukar ɗaya ta antaya a bakinta har wani lumshe ido ta yi.

Kaka ta yi mata kallon gefen ido ta ce, "wannan shi ake kira ci da wayau ai kya bari ni da aka kawo domin ni na fara ci ko?"

Shantyty da ta sake kai hannu ta ɗauki wani ta ce,  "Ni fa ɗanɗanawa kawai zan yi naji kozai ciyu a bakinki yar tsohuwa."

Ta ƙare maganar tana mai saka naman a  bakinta, ba shiri ta lumshe ido tana muimui da baki kamar yaro ya sama alawa, "Mmm..."

Kaka ta miƙa hannu ta yi gefe da kular naman tana faɗin, "Yanzu ba ki ji kunyar Allah ba?"

"Akan me ke nan?" Shantyty ta tambaya cikin rashin gane inda maganar na Kaka ya dosa. "Kawai a dafa abin da sunana da niyyar ni kaɗai zan ci, amma ki rigani ci haka ake yi to ba zai saɓu ba, Ki dawo min da naman nan."

Shantyty ta yi saurin haɗiye na bakinta tana faɗin,  "An riga an kai shi inda ya dace. Kaka sai dai ki ɗauki na annabawa kuma ai nace miki taste ɗin naji miki."

Maimakon Kaka taji haushi sai ma ta fashe da dariya tana faɗin. "Ke kam Shantyty akwai wayau wannan mijinki ya shiga uku Allah dai ya shirya min ke da wannan taƙadirin yayan naki da ya je can Lengas (Lagos) ya manta da mu."

"A'a Kaka. Pepper soup ne fa. Yana da kyau a sha da yawa domin ƙarin lafiya, kuma da kike batun Yaya Manga ya manta damu ai kin faɗa san ranki ne domin a yanzu ma zaki iya ganin ya kira, sannan ma ki dena min maganar miji kwana kusan nan wai ma kin manta sai na zama Farfesa a jami'ar Akzfad dake america sannan ne zan yi aure."
(Shantyty bata san cewa Oxford da take kira Akzfad a england yake ba'a America ba ita dai burinta ɗaya shi ne ta zama Farfesa a jami'ar Akzfad (Oxford), to Bara mu gani Burin nata zai cika ko kuwa.....😆✨✍️)

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.