Free chapter · Read without an account

FREE PAGE 30/31

by Aisha Sani Abdullahi · MATAR POLICE

**************** ************ ******************

Dago glass din Motar ya yi, ya kalleta sannan ya fito.

Ya na fitowa saukar rankwashi kawai Jidda ta ji a kanta, tun kafin ta dago kai ta ga waye ma ta fara, "Allah ya Isa na Wallahi, mugunta kawai."

Dagowa ta yi suka hada ido da KHALEEL ta yi saurin kawar da kai ta na, "Yaron nan fa ya ce min Mamanshi ba tai mai wanka ba shine na Ke mi shi."

KHALEEL ya ce, "Ke din ma kin Iya yiwa kan ki ne bare Dan wasu? Kuma bakya ganin ana sanyi ne? Na Lura Ke kam dai mahaukaciya ce, Shashasha."

"Ni dai ba mahaukaci....

Kan Jidda ta karasa magana sai ga mahaifiyar yaron nan ta fito ta na kumfar masifa.

Banda iskanci A sanyin ki jikamin yaro da ruwa, wannan ai iskancine ba yarinta ba.

Ta na karasowa ta maka wa Jidda Mari afuska, Jidda ta ce, " Mugu Azzaluma kawai."

Nan fa ran MATAR nan ya kara baci hakan ya sa ta saurin harzika tare da Fara jibgar Jidda.

Ban da Ihu ba abin da Jidda Ke yi.

Ta fara , "Yaya Dan Allah ka ce ma ta, ta barni haka Wallahi daga yau bazan kara mi shi wanka ba, ni ba ma ruwana da shi."

Kallonta KHALEEL ya yi,tare da yin dogon tsaki, ko kala bai ce ba ya yi wajen motarshi ya bar wajen nan ta ke.

Mata kuwa sai da ta jibgi Jidda son Ranta kan ta kyaleta, ba shiri da gudu Jidda ta shige gida ta na haki.

Mumy ta ce, "Kakata ina kikaje ne haka tun dazu an gama tuwon Amman an dubaki ba a ganki ba?"

Jidda ta ce, "Umm ni ma ban San inda aka kai ni ba kawai gani nai nadawo."

Ta shi ta yi ko wanke hannu ba tai ba zata fara cin tuwon.

Mumy ta ce, "Aa dai aje awanke hannunku."

Ta shi tayi tana tsallenta ta shige toilet ta wanke kan ta fito ta fara zakar tuwo.

Tunda ta fara cin tuwon nan Mumy Ke ganin ikon Allah har sai da Jidda ta take tuwon nan tsaf abincin da mutane uku za su iya ci Amman ga yarinya nan yar shekara Tara ta cinye tas.

Ta na gamawa Mumy ta ce, "Sannu Fa Jidda, Yawwa Hajiya Iya wai ya maganar yan Jigawane Malam Adamu?"

Iya ta tabe baki , "Yoo ina nasan ma yadda ya ke mutumin da ya manta da mu gabadaya, ina so Ibrahim dai ya zo ya kira min shi asalularsa asanar da shi Maganar Auren Mariya in ya yi niya yazo shi da iyalan na sa."

Mumy ta ce, "Ah yakamata kam ya zo gaskiya."

Malam Adam 'Dana ga yar uwar Hajiya Iya kasancewar Iyayensa sun rasu tun yana yaro hakan ya sa Iya ta Rainasa tare Alhaji Ibrahim,Malam Adam ya na da matukar son abin duniya arayuwarshi ya dage sai ya yi kudi ya zarce Ibrahim, duk da kasancewar shima ya na da rufin asiri dai-dai gwargwado Amman ya fi hange kan na Dan uwansa,hakan ya sa ko waiwayen Hajiya Iya ba ya yi bare kuma Alhaji Ibrahim.

Mama ce ta fito daga daki ta na, 'Yawwa Mumy daman Alhaji ya ce inya dawo daga tafiya za mu je siyayyen kayan bikin, kin ga kwanaki na ta tafiya gashi mu ne dangin Amarya kuma dangin ango."

Mumy ta ce, "Hakane kam Uncle dai kam ai ya yi sa'an uban gida, ya rainesa kuma ya bashi kyautar 'ya, kin ga ai sai mu tafi duka da ni, da Ke, da mariyar, har ma Da Hajiya Iya, kin San yaran yanzu da su ake zuwa siyayyen komai na zamani ya chanja."

Karaf kuwa Iya ta ce, "Ai kuwa dai, ni fa lokacin Aurena, ko Iya hada ido da iyayena ba na iyayi, Amman yanzu Ku tsabar rashin kunya ma naga da yaran kuke shawara, gaskiya duniya ta zo karshe, ko gobe ko jibi sai ku Iya jin ance tashin alkiyama ne."

Mumy ta ce, "Hajiya Iya gobe talata jibi laraba fa kuma ai Ran juma'a ne za ai tashin alkiyama."

Iya ta ce, "Au ki na so ki cemin ba ma juma'an ba ne yanzu? Lallai to ni azatona ma ai yau juma'an ne duniyarce duk kun bi kun rikitata."

Dariya Mumy ta yi ta tashi ta na fadin , "Wai yaushe ne Alhajin zai dawo?"

Mama ta ce, "Ina jin gobe ma insha Allah."

"To Allah ya kai mu, bara kiga na huce gida nasan su Amira kadai ne agida sai dije mai aiki." Cewar Mumy da ke kokarin fita daga gidan kenan.

Mama Ta tashi za ta bi ta Iya ma ta tashi za aje ayi munafurcin ba to muje tare kanwa uwar gami.

*******WASHE GARI

Dassafe Mama ta sa Jidda ta shirya domin driven su Amira na hanya zai zo ya kai su skul.

Sabon uniform din da aka dinka ma ta,ta kalla kawai sai ta fara kuka , "Ni Wallahi bazan sa wannan dangalallen guntun sket din ba, ai ni ba yar iska ba ce, Wallahi bazan sa ba."

Iya ta ce, "Ina bayanki walle Dan haka ke ba yar iska ba ce ba Wanda ya isa ya saki ki sa wannan danalallen skilen kamar mai tallan jikinta, kalan ma ki fita ace mi ki karuwa, to Wallahi ahir din ki Zainabu Jidda ba za ta sa ba ah to na dai Fada mi ki, ki ma fice min da gani tun kan na tsine mi ki na tsinewa kankan kakarki."

Ba yadda Mama ta iya da Hajiya Iya haka ta fita, sai wata shawarar ta zo ma ta, ta kira Baba ta sanar da shi, ya ce ta kai wa Jidda wayar.

Da ke Mama tasan halin Iya ta na shiga ta ce, "Hajiya wai Gashi za Ku gaisa da babansu."

Da sauri ta fizge wayar ba ni naji Dana.

Ta kafa ta akunne kamar zata manne awajen Baba ya gaisheta ta amsa sai washe baki ake, ya ce, "Ah ya na ji kamar muryar Jidda ne ko ba ta je makaranta ba ne yau."

Iya ta ce, "Ina fa zataje makaranta bayan ankawo ma ta kaya wani irin na yan iskan zamanin fir'auna."

Baba ya ce, "Ayya Iya Kiyi hakuri ta sa ba kayan yan iska bane uniform ne, na yara kuma haka ake yin sa, Amman inna dawo za asan yadda za ayi."

Iya ta ce, "To shikenan ba ra dai mu gani."

Ta mikawa Mama wayar, Mama na fita.

Iya ta ce, "ai in sun San wata ba su San wata ba, ni dai bazan barki da shigar iskanci ba dauko ki sa ki ga wani Abu."

Da Jidda ta sa uniform din nan ba karamin kyau ya ma ta ba tamkar Dan jikinta akayi.

Nan ta ke Iya ta dauko wani tsohon zanin leshinta ta ce, "Yawwa matso nan in daura mi ki, tunda su yan iska ne ai mu ba ma biye ma su ba."

Haka Jidda ta fito ga uniform ga zani daurin kirji, zama ta yi ta zabga uban kwalliya kamar me tafiya tashi, sannan aka sa sandal da safa, tafiya ta farayi kamar wadda kwai ya fashewa aciki adole ita ta yi kyau.

Mama na ganin Jidda daga sama har kasa Dan takaici bata San lokacin da ta fara dariya ba, Mariya ma na fitowa ta fara zabga dariya harda rikye ciki.

Iya ta ce, "Iskancin banza iskanci wofi, mu za agayawa iskanci ai mun nuna ma Ku mun fi Ku iyawa ne."

Mama dai tai tsit.

Mariya ta ce, "Dimple Queen ina zuwa haka? Kamar mai zuwa tashe Amman dai ba makaranta za ki ba ko?"

Jidda ta murguda wannan bakin da ya sha Dan Jan baki kamar manja ta cigaba da tafiya ta na rankwasa ta ce, "Makaranta ma na ai ni ba yar iska ba ce."

Ta na fita sai ga driven ya zo, shi kan shi sai da yayi dariya ganin shigar da Jidda ta yi, Amir da Amira ma ban da dariya ba abin da su ke.

Ita kuwa Jidda ko ajikinta ga ni ta ke ta yi shiga tare da kwalliyar kera sa'a.

Suna shiga Makaranta ban da kallon Jidda ba abin da ake ana dariya Amman ita hakan fa ko ajikinta, malamai sun yiwa Principal magana Amman ya ce abarta.

Fita break aka yi Jidda da Amira su ka fito waje suna cin abinci.

Wata yarinya ta zo wucewa kawai ta taka wa Jidda kafa, Jidda ko na tashi ta wasketa da Mariya nan ta ke yarinyar ta fadi aka sa.

Jidda ta ce, "Laaa Amira yasin Aljanune da wannan yarinyar fa kin ga ta fadi."

Amira ta ce, "To kin ga mu tashi ba ruwanmu."

Jidda ta ce, "Tab Wallahi ni sai na mata magani Hajiya Iya ta koyamin yadda ake rukiya."

Amira ta ce, "To nidai ba ruwana Wallahi."

Jidda ta kama kunnen yarinyar ta na gwaranci, ba abin da bata, har A,b,c,d da 1,2,3 ma sai da suka sami damar shiga.

Chan dai jikin Jidda ya fara Duran ruwa taga yarinya ba ta da niyar farkawa, chakulkulu ta fara ma ta ta na, "Wallahi Ku saketa na Fada ma Ku Ku saketa in ba haka ba kakata za ta tsine ma Ku."

Ashe daman yarinya iskancine tana jin an fara chakulkulu ta fara motsawa.

Da guji Jidda ta bar wajen sai da zanin ta ya fadi akasa tsabar gudu wai ajanune Ke bin ta abaya.

Ita ko Amira ban da dariya ba abin da ta ke...

Haka Jidda ta koma gida, ba zani, Iya na ga ni ta fara salati da sallallami, "Ni kuluwa na shiga hamsin ya na ganki tsirara?"

Jidda ta gwalalo ido, "Aljanu na gudunwa shine su ka zaremin zanin ni ban ma San ya fadi ba sai da muka koma aji."

Iya ta kyalkyale da dariya, "Ke ki ka San shakiyancin da ki ka yi dai, Babanki ma ya dawo tashi muje."

________Bayan kwana biyu.

Tun ranar da KHALEEL ya rankwashi Jidda bai kara zuwa gidan ba ko ince ba su kara haduwa ba sai yau da yake weekend ne kuma bai da aiki a office, Hajara ya dauko daga wajen salon kasancewar motar ta ta sa mi matsala, hakan ya sa shi cewa ta rakashi ya gaida Mama kan su wuce gida da kamar ba za ta yarda ba, da kyar dai ta yarda su ka shiga.

Ya na shiga ya Tarar Mama na fama da Jidda ta tsefe kan ta ta ki yarda fir, wai ai satin kitson biyu kuma sai ya yi wata kan ta tsefe.

Da shigarsu Tsawa KHALEEL ya ma ta, nan take Jidda ta fara fitsari awajen tana kuka, Iya na ganin Jidda na kuka itama ta fara, da sauri ta tashi ta shige daki ta kwaso kayansu ahargitse ma ta kulle azaninta, kuka ta ke bilhakki da gaskiya,ga kaya aka da ta daura ta fito ta na, "ke kina mata shima ya zo ya na mata ni na gama lura da Ku in ba kashemin ita kukayi ba bazaku taba jin dadi ba, yau zan bar ma Ku gidannan daga ni har ita sai Ku ta yi," in ta yi magana daya biyo sai goge majina da saman zani, ana kara kakkalo wani hawayen.

Janyo Jidda ta yi tana , "Muje."

Daga Mama har KHALEEL summan tsaye su kaj awajen har ma sun ka sa motsi bare magana.

Hajara kuwa Jan gefe ta yi tana danna wayarta hankali kwance.

Suna fita sai ga Baba ya shigo Mama ta kirashi awaya, da ya ke bai yi ni sa ba.

Ko kallonsa Iya ba tai ba ita dai yau sai sun koma kauye.

Jidda kuwa ta ji dadin zaman birni har ga Allah bata son komawa.

*SHIN YA KUKE GANI? YA DACE ACE JIDDA DA IYA SU KOMA KAUYE, KO KUWA ZAMAN BIRNIN DAI ZAI FI??? MAJORITY CARRY D BOTH*

Urs Xayyeesherth [11/26, 10:03 AM] Xayyeesherthul-humaerath🥰: °°°°°° _*MATAR POLICE*_ °°°°°°

26November2020

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*🤝

__________________________________________________________ _We Are Here To Educate,Motivate, And Entertain Our Readers._ __________________________________________________________

_*Matar Police kirkirarren labarine mai cike da barkwanci, fadakarwa,nishadantarwa tare da sabon salo na mussaman domin farantawa masoya littafaina*_

_*LABARI DA RUBUTAWA*_

_*AISHA MOHAMMED SANI (Xayyeesherthul-humaerath)*_

_LITTAFAN MARUBUCIYAR_ 1- _BABU RUWAN SO_ 2- _KUCHAKAR KISHIYA_ 3- _WASA DA SO_ 4- _AZZAWAJUL-MUKADDAR_ 5- _JAMEEL (Nafseen)_ 6- _KWADAYI 2020_

AND NOW *MATAR POLICE*

_LITTAFINA NA KUDINE INDAI KI NA SON CIGABAN ZA KI TURO KATIN 200 KACAL TA WANNAN NUMBER *** SANNAN KI YI SCREENSHOT DOMIN TUROMIN DA SHEDAR BIYA_

_*BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM*_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.