Free chapter 路 Read without an account

PAGE 3/4

by Aisha Sani Abdullahi 路 SAI NA AURI MARUBUCI (Nafseen)

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM

*馃グ馃グ WANNAN FEJIN SADAUKARWANE GAREKA YAYANA,ABUN ALFAHARINA,YAYA MUSADDAM馃槝YAYANAH YA FI NA KOWA馃拑ANGON MAI AWARA SON SO FISABILILLAH*

MY GROUP XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH FANS GROUP INA KAUNARKU HAR CIKIN RAINA MASOYAN ASALI馃槝馃槝

Sabeer bai San lokacin da kurma uban ihu ba, "Mammah kizo Anti Nafeesa ta mutu,Mammah."

A rikice Mammah ta fito tana, "Sabeer wai meyafaru ne ba yanzu ta fito karatu kalau ba?"

Sabeer na kuka ya ce, "Ban San tayi zane bane na goge mata tana kallo shine ta fadi."

Dafa kai Mammah tai tare da fadin, "Yah Allah!

Kokarin daga Nafeesa daga wajen tai domin maidata cikin gida, da yake Mammah malamar asibitice kokari tai domin dawo 'Yartata cikin haiyacinta a Dan kankanin lokaci.

Bude Idon da Nafeesa za tayi ta fara, " Mammah Nafseen dina Sabeer ya gogemin, sai ta kara fashewa da kuka."

Mammah bata da zabin da ya wuce ta rarrashi 'Yartata awannan lokacin hakan ya sa ta Jan Nafeesa jiki tana shafa mata baya, "Ki yi hakuri kinji Nafeesa bai sani bane, kuma ai zanene na San zaki Iya zana Wanda ya fi wannan kyau ko?"

Wani Dadi Nafeesa taji aranta nan take ta mik'e "Sabeer Bani Littafina zan tafi madarasa."

Mammah ta ce, "Madarasa da littafin Hausa? Haba Maman Abhi kibari in kika dawo kyayi karatun."

Nafeesa ta fara buga kafa, "Ni dai da abuna zan tafi wallahi."

Tashi Mammah tai kawai tana fadin, "Allah ya kyauta."

Nafeesa kuwa Hijabinta ta Sa har kasa tare da nikabinta ta yafa jakar makarantarta agefenta na hagu sannan littafin hausanta na marubucinta NAFSEEN a hannun dama wato Yar Auta.

Ko da ta isa makaranta anfara karatu Neman waje kawai tai ta zauna tare da bude littafinta domin cigaba da karatu.

Karatu ake yi masu Amman gabadaya hankalinta na kan littafin da take karanta, murmushi ne kawai ke bayyana afuskarta, kara gyara zama tai tare da Jan dogon numfashi ta cigaba da karatun, Malamin ne ya lura da yanayinta ganin cewa hankalinta baya tattare da shi duk da kasancewar bai hango me take kallo ba.

"Ke Nafeesa, ta shi ki karantomin hadisin farkon nan da na kawo."

Cikin Sauri ta ta shi arikice take maganar, "Mallam, ai Nafseen bai fadamin ba aciki."

Sake baki ya yi yana kallonta kawai cen ya daka mata tsawa, "Waye Nafseen? Karatu muke ko maganar wani anan, Iye ba tambayarki na ke ba?"

Sunkuyar da kai Nafeesa tai batare da ta kara kallon malamin ba.

Cikin tsawa ya kara fadin, "Nace waye Nafseen?"

Karaf wata yarinya ta ce, "Malam wani marubucin littafan hausane."

Kara fusata malamin ya yi, "Ah ya yi kyau aiko yau zakiga Nafseen a makarantar nan ganin idonki bani littafin."

Jiki asanyaye Nafeesa ta mik'a masa littafin .

Yana karba ya karema littafin kallo kamar yadda aka Fada sunan marubucin Nafseen,tsaki ya yi Sannan ya fara fata-fata da littafin yana yankawa.

Kuka Nafeesa ta fara yi bilhakki da gaskiya,tun tanayi ahankali har ta fara shidewa daga karshe ma ta k'ame awajen nan take.

Ganin yadda tai, abun ya matukar ba malam mamaki daga yaga littafi, tsaki ya yi yana fadin, "kar in ga kowa ya fita kuzo mu cigaba da karatun mu in iskancine nawa yafi nata.

Kwance take awajen cen kuma ta mik'e tare da wani irin gawartaccen kara,Malam ta nufa kawai tare da damkosa tana wani irin numfashi.

Ihu ya fara yana, " Dan Allah Ku kwaceni Nafeesa za ta kasheni,wayyo Allah na."

Dalibai kuwa sai dariya.

Nafeesa kuwa bata fasa jibgar malam ba.

Dalibanne suka kira sauran malaman dakyar aka karba Malam a hannun Nafeesa sai numfarfashi take tana kara kokarin cacumosa.

Malam na samun hanya ya fice adari yana, "Wallahi Yarinyarnan ba mutum bace Ku bincika." maganar yake cikin Sauri da hakki domin ji yake tamkar zata kara damkar shi.

Suko dalibai ba abin da suke ban da dariya yau Mallam yaji a jikinsa Dama ba baya ba wajen jibgar dalibai.

Ita ko Nafeesa ban da kuka ba abin da take Dan arayuwanta bata taba shiga tashin hankali irin wannan ba Wai Lttafin Nafseen din ta aka yaga a gabanta sai ma take ga kamar har shi din aka taba ba Iya Littafin ba D ji take Zata Iya fada da kowa a yau dai kam.

Wani Malamine yazo kusa da ita ya ce, "Nafeesa me ke damunki ne ?" aiko sai ta Kara sanya wani irin kuka cike da sauti ta ce, " Malam Nafseen dina ya yaga min ya taba min rayuwa ta yamin kacakaca da Nafseen dina Wallahi bazan bar shi ba dole sai ya ji abin da na ke ji ," kowa sai ya tsaya tsaro tsaro yana kallon Nafeesa yayin da wasu ke ganin ta haukace kuma ta hadu da bakak'e aljanu.

Da kyar akasamu Nafeesa tabar wajen,biyu daga cikin Malamamsu mata aka nada domin yi mata rakiya gida ganin cewa lamarin yafi karfinsu har suka bar makarantar bata dai na maganganu ba kaman wata sabuwar kamu ,"wallahi daka rabani da Nafseen gara ka yanki naman jikina wayyo Nafseen Dina sai hakuri ake bata amma bata San ma anayi ba sai kara bankarewa da take.

Da Haka har suka kai gida Mamma na daki taji sumbatu Irin na Nafeesa sai ko ta daura hannu aka tare da fadin, " innalillahi Wa'inna ilaihir rajiun me kuma yake faruwa da Nafeesa lafiya Fa muka rabu ."nan da nan hankalin Mamma ya ta shi abinka da uwa a gigice ta kara so garesu.

馃憤Gajeran labarine Dan haka gajerun fejis za Ku na samu,Amman yawan sharhi kan Sa in kara馃グ

Urs Xayyeesherth _*SAI NA AURI MARUBUCI馃摑馃摑馃摑*_ _(Nafseen)_

13/1/2021

_GAJERAN LABARI馃摑_

NAH

AISHA MOHAMMAD SANI (Xayyeesherthul-humaerath)

_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.