Free chapter · Read without an account
PAGE 10
BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM
*WANNAN FEJIN NA KUNE KUJI DADINKU MASOYAN ASALI Deeymusah,Mr Mubarak,Momim shuraim,Fatima zahra,son so fisabillah😘Allah bar min Ku*
Dubawan da zai yi kuwa ya tarar group din cike yake ba damar Kara wani in ba wai wani ko wata sun fita ba.
Komawa Private ya yi tare da fadin, "Ba waje fa, group din acike yake sai dai ki bata hakuri ta jira ko wasu zasu fita."
Har cikin ran Farida bataji ba dadi ba Sam kawai sai ta ce, "To ni dai in an samu hali asata Dan tana da bukatar kasancewa agidan matukar gaske."
Wa she gari
Shiru shiru Nafeesa ta ga ba asata A group ba hakan ya sata Kiran Nusaiba,Nusaiba na ganin kiran Nafeesa ta kau da kai tare da yin tsaki, aranta take mita, "Kai wallahi Aunty bata kyautamin ba zata ja min raini." Ficewa tai fuu sai bangaren Anty Farida, tana shiga ta fara, "Haba Aunty Dan Allah, kina so yarinya ta rainani ne wai? Tun jiya kisa asata a group kin ki."
Farida ta ce, "Oh ni kam dai, na bada number ta daman na Fada miki group din acike yake,dole sai wani ko wata ya fita kan asata Amman har na bada numberta."
Nusaiba ta ce, "Ok shi ke nan Amman wallahi ko ta kira ma ba zan kara daukaba sai dai kawai ta gannta a group ta Kara ganin girmana ma,ba na son raini."
Dariya Farida ta yi, "Allah dai ya shirya mana kai."
Da Ameen Nafeesa ta amsa kan ta fice fuu kamar yadda ta shigo.
********Kwanaki nata tafiya har sati Amman ba asa Nafeesa a group ba, hakan ya Sa ta tsintar kan ta da fara rubuta wani littafi Wanda ta mai lakabi da SHI NAKE SO, kamar wasa ta Sa A group din su nan take taga an fara rububi tare da fadin cewa tayi ma su cigaba Dan Allah, har da ma su binta private suna hadata da Allah kan cewa labarin ya yi dadi ta cigaba.
Mamaki Nafeesa take har cikin ranta shin itace take rubutu kamar yadda Nafseen ke yi? Shin itace ake ta rububi kan karanta labarinta,ji take tamkar amafarki domin salo da tsarin rubutun sak irin ba shi ta bi,tamkar shi ke tsara mata labarin, ba mai tunanin cewa sabuwar marubuciyace.
Misalin karfe biyar na Ranar ba yan ta gama tura littafin rububin sharhi ya ragu tana kokarin kashe data da mamakinta kawai sai ganinta tayi tsimdin acikin wani group mai taken MARUBUTA.
Nafeesa ba ta San lokacin da ta tashi tana murna da ihu ba tare da washe baki,kara kallon wayar tai tare da rungumarta, "Alhamdulillah, Allah na gode maka."
Gyara zama tayi tare da wata nutsuwa ta mussaman ta shiga cikin group din, hira ake ba ji ba gani raha da wasa, wannan ya tsokani wannan wancen ya tsokani wancen abun gwanin sha'awa bin hirar ta fara yi ba tare da tace uffan agidan ba, sai dai ga Mamaki har yanzu bata ga alamar gilmawar Nafseen ba,Wanda ko wani suna ta gani sai ta kura ido Amman har yanzu bataci karo da shi ba.
Ganin cewa da alamar duk yan gidan na da saukin kai ya bata damar yin sallama.
Nafeesa "Assalam alaikum"
Wani ba da ba a tantance mace ne ko na miji ba kasancewar ba suna ya ko ta ne amsa da "Wa'alaiki sallam Yan mata."
Nafeesa ta yo reply da , "Ina Hini Yaya zan ce ko Aunty."
Da alamar murmushi aka maido mata da amsa, "duk Wanda kika zaba kina ganin ya yi miki to ba tantama."
Tsintar kan ta murmushin da ya bayyana har a zahiri tayi tare da fadin, "To ina ganin dai Yayane."
"To, aiko kin canka na Yarda ke din fasihiyar marubuciyace." Ya maido mata da reply.
Kan Nafeesa tai Reply Karaf......
Urs Xayyeesherth _*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_ _(Nafseen)_
NA XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH
✨6STARS INDEED
_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_