Free chapter · Read without an account

PAGE 11

by Aisha Sani Abdullahi · SAI NA AURI MARUBUCI (Nafseen)

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM

🤣🤣DAN ALLAH KAR KUYI KORAFIN GAJERANCIN FEJIN NAN

Ce ta amsa tare da fadin, "Wa'alaika salam."

Batare da ta lura da sunan ba.

Jameel (Nafseen) ya yo reply da , "Ah ya naga kamar bakuwa muka yi agidanne."

Nafeesa ta tura da alamar dariya, "Tab ai ko ni ba bakuwa bace nafi wata agidannan fa, ko kai na rigaka."

Kamar yadda tai dariya Shima hakan ya yi, "Kin San Bamai? To indai kin San Bamai shi kan shi na rigasa zuwa gidannan."

Xayyeesherth ce ta katse masu magana da, "Ah Ah Yaya Jamilu adai rage mana."

Maganar Xayyeesherth ne ya baiwa Nafeesa damar kallon sunan da kyau kamar yadda take tsammani Jameel Nafseen ta ga an rubuta,batare da ta Ankara ba wani irin farincikine ya mamaye zuciyarta, ihu ta fara tana tsalle da rawa ta ma rasa me za ta yi illa rungumar wayar da tai tana rawa da tsallenta.

Xayyeesher ya maidawo da Reply, "Ke Xayyishatu ina wasa da ke ne? Dare ya yi maza jekiyi barci manya na magana kina sako baki."

Dariya Xayyeesher ta yi, "Aradu ban kwanciya yau kam sai naga ka sauka tukunna nima."

"Iyee,ina fadi kina fadi to kinyi abakin chocolate din ki." Cewar Nafseen.

Alamar kuka ta tura, "Haba Yaya Jamilun ba ma haka,gudnyt walle na tahi sai da sahe."

Ya ce, "Yawwa Yar Albarka,Allah tashemu Lafiya."

"Byebye adai kula ban da...... Bata karasa ba ta Sa emojin gudu.

Dariya ya yi, " Allah ya shirya mana kai in ki ka Shiga hanuna zan baki mamaki."

Nan take Xayyeesher ta sauka tana Dariya, Nafeesa kuwa tunda taga sunansa ta ma kasa maido masa da reply kallon sunan take karayi da Mamaki shin daman da gaske zata yi Magana da Nafseen aduniyarnan har suyi wasa da dariya? Ga yadda tai tunani Sam ba haka yake ba, tunaninta zai kasance mai girmankai da jijji da kai amman ko Kadan hakan bai samu ba.

Mentioning Sunanta Yayi ganin cewa ta bace cikin gidan, "@Nafeesa ko dai kin bi sahun Yarinyarcen ne kinyi barcin?"

Wani irin bugu taji zuciyarta na yi ganin yadda ya ambaceta cikin bazata,tana kokarin yi masa reply kenan...

A yi hakuri👏bana da chajine Amman in sha Allah gobe zan yi typing awadace,Ku taba wannan Ku lashe😘😘Ina yinku masoyana son so fisabillillah🥰

Urs Xayyeesherth ***

_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_ _(Nafseen)_

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° NA XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH

✨6STARS INDEED

_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.