Free chapter · Read without an account
PAGE 13
BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM
🤦♀️🤦♀️ALLAH SARKI MASOYAN ASALI ATA HAKURI DANI RASHIN TYPING KAN LOKACI KUN SAN DALILI KE JAWO HAKAN😁NASAN ZAKU MIN UZURI KUMA HAKAN BA ZAI HANA NI GANIN RUWAN COMMENTS BA🥰
GAREKU MASOYAN NAFEESA FATAN BURINKI YA CIKA😁
A dai,dai lokacin da yake shirin yi mata mai gabadaya Nafeesa tai wata irin kara mai kama da na damusa,damkosa tai kawai ta fara jibga ba ji ba gani,jin ihunsa ya Sa sauran mazan da ke waje shigowa ko ajikinta kamar batai komai ba, dukansu ta farayi bilhakki da gaskiya,gabadaya sunyi Jina,jina ba kwari bare karfi,kan kace me har sun fara Jan jiki suna tserewa ahankali,gabadaya sun tsorata "anya kuwa Nafeesa ba namiji ba ce,in ko macece to ba tantama aljanace."abun da wani cikinsu ke ta fada kenan shi ko Mutansir da yafi kowa jibguwa nan take ya sume awajen.
Sai da ta gama jibgarsu kowa ya tsere illa Mutansir da ke kwance ta dawo hayyacinta kallon jikinta ta farayi awani irin yanayi daga ita sai kananun kayan ciki, ta bi dakin ko ina da kallo sai shegen duhu da kyar ta kura ido sannan ta fara hango kayanta gefe guda,cikin sauri ta karasa wajen tare da dauka tana sawa,har yanzu bata fahimci meya faru ba bare abun da ya kawota dakin hakan ya Sa taketa kara hanzari wajen ganin ta bar dakin, kicib da mutum akasanta kallon da zatayi ta ga Mutansir,nan take hawaye ya fara zubo mata, jakarta ta kara hangowa gefe guda ta dauka ficewa daga dakin tayi cikin kuka, abun mamaki duk abun nan da ya faru glass dinta bai bar idonta ba koda na second daya.
*****Tana fita ba inda ta nufa sai bakin titi, tsare mai Nafe tayi kawai ba inda ta nufa sai gida, Mommah bata nan Sabeer ma na Skul duk ba su dawo ba, dakinta ta huce ban da kuka ba abun da takeyi azuciyarta tana fadin, "Kaddarar rayuwata ke nan Wanda ke so na baya sona Dan Allah gangar jikina yake so,ni kuma Wanda na ke so bai San inayi ba,ban San ma ko zai soni ba, da yanzu Mutansir ya Lalata min rayuwata shi ke nan." Fashewa ta karayi da kuka can kuma ta tuna da yanayin da ta tsinci kan ta, atsorace ta tashi ta zauna tana mamakin shin to ma wai "meyasami Mutansir ne? Kar dai mutuwa ya yi? Waya hanasa ketamun haddi ina sauran Abokan nasa
Shin wai me ke faruwa dani ne? Kokarin fara tuna abun da ya faru a islamiya tayi nan take kanta yafara juyawa duhu ta fara gani bata gane komai nan take wani irin gawartaccen barci ya yi awon gaba da ita.
Sai karfe biyu Mammah da Sabeer suka dawo tare ba karamin Mamaki Mammah taji ba ganin Gidan abude suna Shiga kuwa ta nufi dakin Nafeesa kamar ta sani gata nan kwance "ga duk kan alamu tana wannan barcin ne data saba aduk lokacin da aka bata mata rai." Abun da Mammah ta Fada aranta ke nan tana kallon diyartata cike da tausayi.
Kamar wasa har dare Nafeesa ba alamar motsi atattare da ita, Mammah ta zo har ta gaji da dubata lamarin ya sha bambam da Wanda tasaba yi.
Addu'ah kawai Mammah ta shafa mata tare da janyo kofar ta fita.
*****Wa she Gari da Asuba Mammah na tashi ta nufi dakin Nafeesa,tana nan dai yadda aka barta, ba Dan tana numfashi ba kai kace mutuwa tayi,Abun har ya fara damun Mammah gashi Abhi yau zai dawo hakan ne ma ya Dan sanyaya mata zuciya tafi minti biyar tana kallon diyartata kan daga karshe ta fita.
Karfe uku na yamma dai,dai Abhi ya isa.
Da Murmushinsa Ya shigo gidan,da gudu Sabeer ya rungumesa, Mammah na fadin, "Barka da dawowa Oga." Maganar take cike da fara'ah.
Abhi ya dubi ko ina ba alamar gilmawa Nafeesa.
"Niko wai Ina Ammynane?naga kowa Amman ba ita." Cewar Abhi ya na kara waige-waige.
Mammah tai murmushi, "Ammynka ba Lafiya barci take,."
Abhi ya ce, "Ayyah shiyasa gidan ba dadi Sam gaskiya sai na tada gimbiyata muje."
Mammah batace komai ba kawai suka bi bayan Abhi ita da Sabeer, suna shiga Mammah ta fara kwalla.
"Tun Jiya take barcinnan bata farka ba." Cewar Mammah cikin yanayin damuwa.
Abhi ya ce, "Subhannallah, Shine baki fadamin ba? Kuma baki kai ta asibiti ba?"
Mammah ta ce, "Na dubata Amman ba abun da asibiti za su Iya mata addu'a dai itace asibitin da maganin, tanayin hakan mun sani Amman wannan yanayinsa dabanne sai dai muta addu'an kawai."
Sam Abhi bai ji dadin lamarin ya ma kasa magana kawai ficewa ya yi, azuciyarsa yana matukar tausayin diyarnan tasa domin tunda tazo duniya take fuskantar kalubali kala daban daban iri iri.
Addu'o'i da saukan Al'qur'ani kawai suka Sa agaba.
Kwannan Nafeesa shida kwance ba motsi.
****wani bangaren kuwa na Mediya cikin Group din Marubuta anata hira da ban dariya,Mussaman Nafseen da ya Sa yan Matannan d ya Sa su agaba da tsokana, kamar wasa yana kokarin tagging din gaurayen yan matan gidan, sunantane NAFEESA ya fara fitowa awayarsa batare da Sa komai aransa ba kuwa ya danna kan sunan.
A dai dai lokacin Nafeesa..........
Urs Xayyeesherth ***
_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_ _(Nafseen)_
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° NA XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH
✨6STARS INDEED
_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_