Free chapter · Read without an account

PAGE 16

by Aisha Sani Abdullahi · SAI NA AURI MARUBUCI (Nafseen)

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHIM

*SADAUKARWA GAREKI SISTER ZEEY YAR MUTAN ZAZZAU,ALLAH KARA BASIRA DA HAZAKA INA YINKI WALLE HAR CIKIN RAINA🥰*

*TUKWICI GAREKI MY MAREEYA😍CAN'T LOVE YOU LESS ADDU'AHTA A KULLUM BAI WUCE ALLAH YA BAKI LAFIYA MAI INGANCI BA*

🤔🤔 *SHIN NI KADAI NA FAHIMCE CEWA A LAMARIN NAFEESA SURUKANNA NA DA YAWA,NA DAYA BA SUMA TAKE BA,KUMA BA BARCI TAKE BA🤔SHIN ME TAKE??*

Zata fadi Maryam ne ta riketa Abhi ko yana amsan wayan tafiyarsa yayi bai ma tsaya ba, Maryam ne ta daga ta suka shiga daki sai kuka Maryam dinma take ta kan yi, aiko abin data sani shi ne ya faru Nafeesa faduwa tayi tamkar wata matacciya gefen Idonta sai hawaye ke fita ga shi bata numfashi,Maryam ko tasa niyyan bazata fada ma su Mammah ba sabida Ita a ganin ta yaushe suka Fita a damuwa kan Nafeesa kuma su kuma komawa gaskiya gara suyi farin ciki suma, ta dauka alkawarin bazata fada ma kowa ba in sha Allah har sai Allah yayi farkawan Nafeesa.

Maryam Wayan ta,ta dauka ta kira Umminta ta mata bayani sosai kuma ta fahimta itama anan ta ce mata zata kwana da Nafeesa Ummi ta amince Mata ta ce, " Zan fada ma Abban ki kinji." Maryam ta ce, "thank you Ummi na shiyasa nake kara sonki."

Ummmi dariya tayi ta ce, " yadda Kike a Zuciyata haka Nafeesa take kinga ko ba banbanci ko?" Maryam ta ce, " hakane kan Ummi ", Ummi ta ce to sai anjima ki kula da ita sosae kinji Maryam tace in sha Allah ummi." sallama sukayi ummi tadan wayan aranta ta ce, " bansan mesa Allah ya daura min son Nafeesa da tausayin ta ba ya Allah ka yaye ma wannan yarinyan ka cika mata burinta in dai shine mafi alkairi."

Tana cikin wannan tunanin Abba yadawo ya tadda ta ya ce, "Lafiya kuwa Ina ta magana shiru?" Ta ce , "hmm Wlh ban san ka dawo ba."

" haba uwar gida tunanin me Kike hakane Ina Maryam naji gidan shiru anan Ummi ke ba shi labarin abin da ke faruwa shima shiru ya yi ya ce, " wlh kin ga duk abin da zanwa Maryam Zanyi ma Nafisa,Allah zai cika mata burinta kuma zai yaye Mata." da Ameen ummi ta amsa suka wuce ciki .

Abangaren Maryam kuwa bayan ta ajiye wayan fitowa tayi falo Mammah ke tambayarta ina Nafeesa Maryam me hanaki tafiya har yanzu? yanzuma fitowa nayi nace Maki yakamata ki koma Gida dare ya yi." Maryam ta ce, "Mammah Zan kwana a tare da Nafeesa harna Kira Ummi na fada mata kinga bata da lafiya kuma Abhi yadawo yakamata a samu Mai zama kusa da ita shine na ce zan kwana a tare da Ita." Mamma bata San Erin dadin da taji ba koba komai Nafeesa tayi dace da kawa ta gari bata San da bakin da zata godema Maryam ba.

"Ngode sosai da Erin abin da Kike ma Nafeesa a lokacin da mutane da yawa suke kallon matsalanta kaman ba gaske ba amma ke kin tsaya akan Al,amarinta Maryam nagode sosai, Allah saka miki da alkairi ."tana yi tana zubda kwalla Maryam itama kukan ta Fara "Mammah Dan Allah ki daina Fadin haka ki daina kuka." hannu ta sa tana goge hawayen dake zuba a Idon Mammah,

"Mammah plzz you have to and rest, stop crying kinga Abhi yadawo zan kula da Nafeesa kar ya ga kina cikin damuwa."

Mammah ta ce, "to Maryam thanks so much god bless you let me letf but before I have to see Her." Maryam ta ce, "Ok Mamma amma bacci take a Haka suka shi ga dakin tare Mamma taje ta zauna a gefen Nfeesa addu'ah sosai ta Mata kan ta fita a dakin .

Maryam ta kara gyara. Mata kwanciya tana, " Nafeesa Allah baki lafiya in sha Allah burinki zai cika,kuma komai ma zai wuce."

. Abangaren napseen kuwa, replied yayi da look at that baby girl nifa bana tsoro sai dai aji tsorona Dan kiji ." ya tura tare da emoji na gwalo amma shiru bega reply nata ba kuma ga hiran nasu yana sashi nishadi shirun daya ji ne yasa ya Kara tura "yeeee itane Ashe taji tsoron ma.. still shiru yace "aa lafiya kuwa ina ga she have a lot to do Bari nima na sauka ."nan ya sauka.

Abhi ko yana amsan wayan ya kashe shi baki daya yaje ya ajiye sai da dare yayi yadawo daga mosque shida sabeer yake cewa , "Ammyna lafiya kuwa bata fito ba ga lokacin dinner ma yayi." anan mamma ke gada masa ai bacci take ta yi ma Maryam ma zata kwana da ita nan da nan hankalin Abhi ya tashi meya faru da ita mamma ta ce. "aa ba komai kasan dai yau bata jin dadi ana bukatan ta huta ai karka damu ba komai."

amma Abhi dai hankalinsa bai kwanta ba ya ce , "to bari na dubo ta amma nan suka wuce dakin Nsfeesa suka ganta tamkar ba rai a jikinta amma tana numfashi Abhi ya ce, " Maryam Allah miki albarka ." da "Ameen" ta amsa Abhi ya ce, "to kin ga tana bukatan Hutu amma ta biye ma waya kinga ma gara Dana amsa ."Maryam kirjintane ya buga taji wani hawaye na bin face nata aranta tace "Allah sarki Ahi besan rashin wayan shine ya jepata a wannan yanayin ba amma in sha Allah zanyi kokarin ganin abhi yadawo Mata da wayan amma dole saita hakura da kanta dole zan bata hakuri ta danne duk abin da zataji tayi ma Abhi biyayya ."

Fita su kayi Mamma ta ce, "Maryam ta fito suyi dinner haks nan ta fito amma duk hnklnta bayi jikin ta .

Nafseen kuwa ta bude data tare da zumudin ganin Erin amsan da samu wajen Nafeesa amma me sai yaji shiru Kawai ji yayi ransa ya baci ma ko group din be shiga ba ya rupe datan sai kuma ya fara tunani shi kadai "to meye ma bashi na damuwa har haka yayi kokarin cire tunanin ta aransa amma hakan be samu ba Sabida Nfeesa Yarinya ce shagwababbiya Edan yana tuna Erin yadda take masa shagwaba sai yayi murmushi kuma sai yakara cewa meke damu na ne Haka to mema zaisa na damu haka, Abu daya yake tunawa salon yarinya yana matukar birgesa gata yarinya Amman in tai wani abun babbama ba zai ba, duk abunnan bai taba ganin hotonta ba kuma bai taba tambaya ba Amman yana sawa aransa cewa kyakkyawace ajin farko kamar yadda halinta da kalamanta suke.

Maryam bayan tadawo addu,a ta karama ma Nafeesa ta kwanta aiko can cikin dare wajen 2:00 taji nafeesa na "Abhhi Dan Allah kayi hakuri kabani wayana na san Nafseeen ya min reply." Nan take ta fashe da kuka , Maryam ta riketa.

"Abhi ka taimaka min kaji Dan Allah Wallahi rabani da wayannan kaman Ana min baraxana da rayuwats ne Abhi plxxx ."

Maryam ta ce, "haba Nafeesa ki dawo hankalinki mana Wai yau ke ce Kika tashi ba addu',ah a bakinki keda Kike yima wasu fada akan addu'ah amma ace yau kene kika tashi ba ita?"

nan Nafeesa ta Fara share hawaye ta ce, " Astagfiirullah addu'a ta fara jerowa tana hawaye tana tuna abin da ya Faru Wai da gaske Abhi ya amshi wayana gaskiya bazan iya jure hakan ba.

tana wannan tunanin Maryam tace , "Mata babe oya a tashi a yi sallah ko nan ta Mike tayi alwala ta rama dukkan sallanta ta dear tana edarwa tasa kuka tace, " Maryam meya hanani tafiya kuma Wai da gaske ne Abhi ya kwace min wayana Maryam Idan ya baki ki bani ne Dan Allah kar kimin wasa kinsan yadda nakejikuwa?" Maryam da hawaye suka cika mata Edo ta ce, ' nafeesa ki kwanta ki huta zamuyi maganagobe kinji."

kuka Nafeesa takara sautinsa "plss Maryam kibani amsa Dan Allah." Maryam ta ce ,"promise zan fada Miki gobe amma yanzu ki samu ki huta da kyar Maryam ta lallaba nafeesa ta hakura akan sae gobe.

Wa she gari

Ana kiran asuba Nafesa ta Fara tashin Maryam Sabida ita bacci ko na second daya be dauke ta ba hasalima hangowa take Erin amsan da Nafseen ya tura Mata gobe Maryam na bata wayan shi zata fara dubawa nan suka yi alwala sukayi sallah Nafeesa ta ce , "to ban wayan Habibbty."

Maryam ta ce, "baby girl ki saurari abin da zan fada Miki ."

Nafeesa ta ce , ,"to ban wayan sai muyi maganar."

Nafeesa Maryam ta fada cikin raunanniyar murya Mai dauke da damuwa nan da nan Nafeesa ta ba da attention dinta wa Maryam Sabida tasan abind a zata pada Mata yanada mahimmanci.

"inajinki baby girl da farin cikin ki Dana su Abhi wanne kika fi so ?"

Cewar Maryam.

Nafeesa ta ce, " Na su Sabida suma koda yaushe suna hana Kansu farin ciki domin suga nasamu."

Maryam ta ce to, " yanzu suma suna bukatan taemakonki da kuma kulawanki ."

Nafeesa ta ce , "akan me kenan ?"

Maryam ta matso kusa da Nafeesa tana , "Babe dole zaki yi hakuri da amsan wayan ki wajen Abhi Sabida farin cikin sa domin yana kallon kaman wayan na hanaki samun Hutu dole ki yadda da abin da yayi kiyi hakura ki danne damuwanki a gabansu dukda nas an da ciwo kan amma kiyi hakan Saboda su nasan edan kinyi haka Abhi zaiji dadi kin bi magna din sa yadda Kike nuna so a wayan ki nuna hakan tamkar be dameki ba Edan har Anga hakurinki wayan zai dawo wajenki soon."

Tunda Maryam ke mgnan nafesa kafeta tayi da ido ko kiftasu batayi ga farin cikin ta gaban iyayenta wanne zata bi?

Nafeesa ta...

😍😍MASOYA ASANI CIKIN ADDU'AH IN ANYI SALLAH PLEASE❤️TANAN NABI BUKATAR SOYAYYARKU GARENI,ALLAH BIYA MANA BUKATUNMU NA ALKAIRI👏

Urs Xayyeesherth❤***

_*SAI NA AURI MARUBUCI📝📝📝*_ _(Nafseen)_

*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° _Gidan karamci, rubutu don ci gaban al'umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu._ °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°° NA XAYYEESHERTHUL-HUMAERATH

✨6STARS INDEED

_*SAI NA AURI MARUBUCI...Kirkiraren labarine, mai dauke da nishadi na mussaman, al'ajabi tare da ban tausayi,tsantsar soyayya da kauna mai ban mamaki*_

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.